Advertisements
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 14
Advertisements
Wani irin kallo tai masa yayin daya daga Mata girarsa guda daya fuskanshi cike da Murmushi”
Kabashi fah kace????
Eh na bashi, kuma daga yau zuwa duk ranar da yaga yamai za’a iya daura auren ni ashirye nake”
Advertisements
Karka min Haka Usman, akan me zakace kabada kaitsaye”
Kafarsa ya sauke ya mike sosai, Khadija nabashi Ummee kiyi abun da zakiyi”
Lumshe ido tayi cikin balakin Jin haushin Usman, ta dade Bata budeba yana tsaye yana kallon ta, zuwa can ya bude idon ta jawur tace”
Meyasa baka da adalci?, Damuwar ka kawai ke damun ka baruwan ka da damuwar wani……
Dama ai hakane, Fatima dai ‘yatace, nike da ikon bada auren ta ga wadda naso baki da wannan damar dan haka nina gama mgn nabashi kawai”
Mikewa Khadija tayi afusace goran ruwan dake gabanta ta dauka ta jefeshi dashi bata tsaya hakaba tacigaba da daukan duk wani abu da hannunta zai iya dauka tana jifansa dashi”
Tunda ta fara be motsaba kuma bebar murmushi ba duk da cewa ruwan data fara jeho masa yajika masa jiki, hannunsa yasa cikin aljihun sa yana kallonta kasa kasa harta rasa abun da zata dauka gaba daya falon ta hargitsashi, ita kanta gyalenta ya zame kasa dan kwalin kanta ya kwance”
Rasa abun dauka yasa ta nufi kofa, cikin sauri ya rigata yai saurin juya key sannan ya cire yasa cikin alhajihun sa yana me binta da kallo”
Kabude min kofa na fita”
Kawar dakai yayi fuskan sa dauke da murmushi sannan yace”
Koma ki zauna”
Tafiya zanyi😭
Ahaka Zaki fida kamar mahaukaciya?
Niba mahaukaciya bace saidai in nidakai ne mahaukatan”
Murmushin sa ya fadada sannan yace”
Naji, na yadda, dawo ki zauna mu gama haukan tare”
Jimmm tayi idonta akasa yayin da yasake cewa”
Nace ki zauna ko?
Juyawa tayi ta zauna sannan ya dauko mayafinta akasa ya mika mata ta amsa, cikin kawar da ido ta gyara daurin dankwalin ta sannan ta yafa gyalenta ta mike”
Kusan atare suka isa kofar ya bude Mata ta fice yayin da yadawo yana lekenta ta window”
Ita da Fatima ya hango suna tafiya yayin da Khadija ke share hawaye, har bakin gate sukaje sannan Samha ta juyo jikinta asanyaye”
**********
Aunty Saude bakisan wani abu ba, kirabu da Khadija kar halinta ya dameki, Ina tunanin nafi kowa sanin halinta, dan haka kima daina sauraronta”
Nifa Gaskiya Ahmad zagin da take maka yanai min zafi, muna tare da Khadija tun batasan kantaba kun shaku da juna sosai amman sai nuna maka kiyayya take, Ahmad duniya da fadi kuma akace gari da yawa maye becin kansa, ‘yartata ai ba fin sauran Mata tayi ba, dan Allah kabar Mata ‘yarta ka nemi wata, wlh Ahmad kafi karfin yariyar nan dan dai kaima ka likene guri daya”
Aunty karki damu, idona ya bude naga guri Aunty, ni Khadija bata daga min hankali
Tunda Fatima ta karbeni hannun biyu”
Shiru Aunty Saude tayi tsawo wani lokaci, sannan tace”
Shikenan, amman gaskiya inda za’a bi ta shawarata daka hakura, kajima bakayi aure ba Ahmad, kamata yayi ka nemo Babba yariya wadda zata kwantar maka da hankali, wannan ko kila ace saika jirata, Kai ko daura auren akayi yanzun bazaka sake sosai ba, idan kuma hakane ka auri wata inyaso daga baya saika Kara da Fatiman”
Hmmm Aunty kin kasa ganewa, nifa bantaba ganin wata ‘ya naji inason na aureta ba sai akan Fatima”
Khadija fah?
Kawar dakai yayi sannan yace”
Aunty kibar wannan mgnr Dan Allah, nidai yanzun inson ki daina kallon duk wani abu da Khadija zatayi akan wannan mgnr, Mahaifin Fatima yafi daga min hankali ni, lbrn yadda sukayi ya Gaya mata sannan ya Kara da cewa kuma kinsan wani abu aunty???, Tunda nafurta inason Fatima hankalina gaba daya ya koma gareta, kiyayar da Khadija ke nunawa wlh Kara zugani take aunty, haka kuma yau da muka hadu da Mahaifinta jinayi kamar an bude zuciya an gina min ita aciki, duk da cewa nasan karamar yariya ce, wlh aunty sonta ya shigeni batare danasan lokacin ba”
Cikin ido take kallon kanin nata, tabas bata taba jinsa yayi irin wannan kalamin ba, amman Ahmad kana ganin ita yariyar nason ka?
Guri daya ya tsorawa ido sannan yace”
Mutuwar Sona take aunty”
Dari Aunty tayi tare da shafa kansa tace”
Su Ahmad anga guri, yanzun haka kila yarinta ne nan gama tace bata son ka”
Toh Aunty akace miki tsayawa zanyi ta girman?, dani zata girma aunty, hakane zata gula dani yadda ya kamata”
Hmmm toh Allah yasa rabon kace, yanxun tunda ka dage wacce hanya za’a billowa Uban yariyar”
Shine zanje na gayawa Daddy yadda mukayi”
Daga gidan Aunty Saude gida Ahmad ya nufa, sai lokacin yaji damuwa ya sakko masa yaki nuna damuwarsa ne dan kada Aunty Saude ta Kara kin auren”
Afalon Daddy ya samu Hajjah suna zaune da Alama cikin farin ciki suke, shikuma ya shiga a yamutse”
Ahmad yaya dai, muna farin ciki Kai kuma kana shigo mana ayamutse, yanzun muka gama waya da Alhaji Usman yace yabaka Fatima, dazaran mun shirya yana sauraron mu”
Jimmm yayi cikin lumshe ido sannan yace da Gaske Daddy??
A’a zanma karya ne Ahmad lfyr ka kuwa?
A’a Daddy abun ne ya bani Mamaki”
Murmushi Daddy yayi sannan yace kabar Mamaki da ikon Allah, ni nafison inzanyi abu inyishi da gaske dan haka gobe idan an daura auren Khadija zamuje atsaida mgn”
Ajiyan zuciya yayi sannan yace”
Toh nagode Daddy”
Addu’a sukaita masa sannan ya koma dakin Mamaki abun yaita bashi saidai kuma fah Fatima nasona, ya fada da wannan tunanin ya samu nutsuwa sosai”
***********
Inna Ina Jin zuciyata kamar zata fashe😭
Toh idan kika kashe kanki ai shikenan, bansan wacce irin zuciya gareki ba kinsa ma kanki damuwa, ni Banga abun tada hankali ba, yanzun meye ke damun ki?
Ni komai bemin Dadi Inna danasani ban dakko zancen Auren ba, yanzun gashi nabata goma daya bata gyaruba”
Hmmm Khadija kenan nasan bakomai ke damun kiba sai zancen Ahmad da Fatima, kuma haukanki kike dazon nan ubanta ya Kira Mahaifinsa ya sanar masa yabashi ita, ni Banga aibun Ahmad ba, idan Ahmad nada aibu kema kina da Ita”
Usman ya Kira Daddy yabawa Ahmad Samha Inna???😭😭
Kwarai kuwa, har sun yanke gobe daga gurin daurin aure ki zasu su ayanke mgn”
Shiru tayi nawasu dakiko, sannan ta tashi zaune tace”
Shikenan, daga Usman din har Ahmad din kowanne ya gama iskancin shi, gaba dayan su sunyi ne dan su kuntata min, kuma indai Ahmad ne nabar Usman dashi, insha Allah bazasu kare kalauba albarkacin wulakantani da sukayi”
Khadija?, Wai kwaya kikasha ne??
Mikewa tayi bansha komaiba Inna ku bazaku gane ba”
Ficewa tayi adakin kodata koma dakinta tsuru tayi, bakomai take tunawa ba sai kalaman Ahmad, sabbi suke dawa Mata daya bayan daya yayin da hawaye yaki yanke Mata, har amon sautin sa takeji da kalamar datafi koma Mata rai Ubana yafi karfin ki Khadija saidai ni, idan zaki cini mu hadu agodo, innalillahi wa Inna ilaihir raju’un ta furta tare da share hawaye tana kallon Alhaji Kabiru na kiranta Amman ta kasa dauka gaba daya duniyar tai Mata zafi”
************
Ummee? Albishirin ki?
Goro Abbana”
Kinsan wani abu?
Kaita girgiza tare da kallon sa cikin ido??
Nabawa Ahmad izini yacigaba da neman auren ki”
Sakewa fuskanta tayi kada sannan tace”
Abba bacewa kayi shiya rabaka da Mamana ba??
Jimmm Usman yayi sannan yace”
Yanzun dai nace miki namar izini, idan yazo ki saurare shi, koba kince kina son shi ba??
Eh Abba Amman dakace min haka naji yabani haushi”
Murmushi yayi sannan yace karki Kara tunawa zai cigaba da zuwa indai kina son sa ashirye nake na bashi ke”
Kallonta yayi yaga babu dauki afuskanta dan haka yace”
Yanaga baki sake ranki ba??
Abba nifa inason Mamana kuma yanzun bata tare damu”
Dauke kansa yayi tare da daya sanin furta Mata wancen kalmar zuwa can yace”
Kinaji Ummee nasan abun da nakeyi kinji ko, kibi abun da nace kawai”
Amawa tayi bayan fitan Abba ta ta shiga tunanin, duk da tanason Abba taji wani iri dataji yana da hannu afitan Mamanta shiyasa tun tuni Abba beson Ahmad, wata zuciyar keson taki Ahmad yayin da dayan ke rinjayar dayar ta hanyar kawata masa shi”
********
Khadija zaune gaban Alhaji gafenta Baba ne cikin baccin rai yace
Kin Kira Alhaji Kabiru kince masa wani abu ne??
A’a
Me kike nufi Khadija, Mahaifin ki yace shima ya rasa gane kanki?, Kefa kika kawo yaron nan kuma angama komai give daurin aure yace yarasa gane kanki shi ya hakura, atunanin sa gidan tsohon mijin ki Zaki koma”
Fashewa tayi da kuka sosai hanin haka Alhaji ya dakata da fadan da take yi”
Babane ya amsa yayin da Alhajin ya dakatar dashi saidatayi me isan ta sannan Alhaji ya sake cewa meke damun ki Khadija??
Kasa tayi da kanta tace”
Alhaji Ahmad yagama min rashin kunya kuma Wai Samha zai aura??
Baki Alhaji ya rike au bazancen auren naki bane ma agaban ki zancen Ahmad kikeyi?, Toh inbanda rashin kunya na ‘ya’yan zamani ke har kin isa kice wani abu Kan zancen ‘yarki, kina cewa wani Ahmad yamiki rashin kunya ke meye wannan kike yi?, Wato zancen fasa auren Alhaji Kabiru be dameki ba Zancen Ahmad da ‘yarki kike yi, sabo dake fitsarariya ce, ki godewa Allah ‘yarki ta samu miji kamar sa Ahmad yaron kirkine, ki daina tuna shirmen ku na sako da sako, ni tashi kinani waje tunda ke ba auren bane agaban ki, Amman ki sani baxa mu zuba miki ido kin abun da kikaga damaba, idan nasakejin kin sake daga zancen Ahmad da Fatima ranki zai baci tsawa ya sake daka Mata tashi kibani guri…….
Dakinta ta koma wannan lokacin idonta ya bushe babu hawaye saidai tayi alkawarin daga Alhaji Usman har Ahmad sai kuntata masu kamar yadda suka kuntata Mata, gaba daya ji tayi hawaye ya kafe a idonta aure kuwa da Alhaji Kabiru ya fasa Dadi hakan ya Mata sosai, dan ita yanzun tunaninta guri daya ya taru, insha Allahu saita Yi maganin su daya vayan daya”
Tun adaren Ahmad ya samu labarin fasa Auren Khadija, dariya yaitayi yau fess yake jinsa”
Hakama Alhaji Usman ya samu labarin akan lokaci dan haka ya kasa bacci haukan da Khadija taita masa ya tuna fuskansa dauke da murmushi”
Itako Samha batasan bikin da Ake ba, adaren ta Kira Khadija bayan ta dauka tace”
Umma Abbana ya amince da Uncle Ahmad kuma shikadai ba matsa masa nayi ba”
Toh naji, yanzun auren za’ayi kenan tunda ai kina son shi kikace ko?
Shiru tayi yayin da Khadija ta sake cewa Ahmad din yana Kiran kine?
Tumdai jiya da yazo be kiraba”
Shiru Khadija tayi tana son ta Mata mgn tarasa ta yadda zatai Mata cikin sanyaya harcen ta tace”
Kedai karki kirasa inbashine ya kirakiba sannan da kinga yafara miki zancen iskanci ki kashe wayar ki”
Zancen iskanci?, Tafada azuciyarta tamkawai tace”
************
Ahmad da Galadima akan hanyarsu ta zuwa gidan su Samha”
Galadima ne yayi dariya yace yau zanga yadda ake tadi tsakanin Baba da ‘yarsa”
Kabari kawai Galadima, har Ina rasa ta yadda zanyi inyi Hira da ita da wannan fuska, kasan Bakin nan nawa koni tsoronsa nake, gashi har Khadija nace min Fitsarare”
Hmmm ai batamaga fitsara ba saika auri budurwa
Dariya Ahmad yayi sannan yace atoh me danyen kaya ba”
Galadima ne yayi dariya yace, raini naso kawai agoge amman ai hakan shine daidai Wai🤔 wayaga Budurwa ahannun Ahmad”
Fushewa sukayi da dariya yayin da Ahmad yace”
Kaca kace zan Mata”
Cikin dariya Galadima yaci Subuhallahi ‘yar taka?, Da munga uban banza”
Murmushi Ahmad din yayi sannan yace”
Hakane da wannan, Amman ai inaga aje Uncle dinan zanyi gaba daya”
Gaskiya baka da girma Ahmad, yanzun saikasa Fatima agadoka ka kwana da ita?
Meye aciki, Kai barin kaji wlh Allah ya taimakeku dabe yini adan iska ba, da tuni anyi abun kunya
Hmmm Inama Khadija zataji wadannan kalaman naka data Kara tsanarka”
Kafada Ahmad ya daga, tare da fadin tunda ba ita nake fadawa ai da sauki
Da haka suka isa gidan su Fatima awaya ya kirata, yau bata wani bata lokaci ba ta fito saidai babu gyale ko hijjabi ajikinta, tun daga nesa take murmushi yayin da Ahmad ya gyara Fuskansa kamar bashine yagama shakiyanci yanzon ba”
Tana isowa Yace”
Meye bakisa Gyale ba?
Gaidasu takeyi yayin da Galadima ya amsa sannan tamaida hankalinta Kan Ahmad Uncle Ina wuni”
Meyesa bakisa Gyale ba?
Toni ai Uncle haka nake, ko amakaranta kazo ba haka kake samuna ba?
Makaranta daban nan daban Samha koma kisa Gyale”
Uncle Allah zafi nakeji, ni agida haka nake zama”
Amman jiya aida hijjabi kika fito”
Toh jiya ai bakai bane Moh’d ne?
Kawar dakai yayi yayi murmushi sannan yashafa kansa yace hakane fah, Uncle yace ga Moh’d ya iso koma kisa mayafi”
Toh sakko ka rakani”
Insakko cikin gidan naku zan raka ki??
Hanya dai”
Kokarin sauka ya fara yayin da Galadima ya saki baki yana kallon yadda Samha kayi tanawa Ahmad mgn”
Bayan sun fara tafiya bayansu yabi da kallo”
Samha kuwa Hannunta tasa cikin na Uncle dinta suna tafiya ta matsa yatsunsa yayin da ya shiga basarwa ta hanyar fadin kiyi sauri kidawo”
Tsayawa tayi cak Hannunta nakan nashi tace toh waikai Uncle baza kalli kwalliyata ba saice naje na rufeta kuma?
Tsam yayi sannan yace”
Aina gani kinyi kyau, shiyasama nace kije kirufeta”
Amman Uncle bafa wani kallona kayi ba”
Kallonta yayi sosai sannan yace kina son na kalleki ne??
Kaita daga yayin da ya kawar da kansa can gefe yace”
Ai Ina kallon ki Fatima, ko Aya nake ke nake kallo, irin kallon da kike nufi bazai yiyu bame yanzun sabo da wasu dalilai, yanzun dai kije kisa mayafi idan kika dawo sai muyi hira”
Nidai gaskiya Uncle kabarni ahakana😩
Hade fuska yayi sosai kije kisa Gyale nace ko”
Juyawa tayi tare da fadin”
Kuma bazan dawo ba”
Zonan ya fada tare da kama hannunta, kidawo kinji, ainaga kwalliyar kuma nayaba, kinga yanzun bani daya bane idan nanzo ni daya kimin wadda tafi wannan”
Cikin kawar dakai tace karka Kara zuwa tashi toh”
Dariya yayi sannan yace toh naji, jeki dawo”
Toh kasakar min hannuna man, sai alokacin ya kula hannunta da yake cikin nasa, kasa sakin hannun yayi yayin daya tsura Mata ido, wani yanayi ya shiga me wuyan fasarrawa daker ya iya sakin hannun ta yayin datasa tafin hannunta ta rufe fuskanta sannan tace
Uncle soyayyar kamar baka iyaba”
Jeki dawo saiki koya min”
Shiga ciki tayi sannan ya koma bayan motar ya zauna, yana maida ajiyan zuciya”
Waigowa galadima yayi ya kallesa sannan yayi dariya yace”
Kasamu daidai da kai wato yariyar nan idonta abude yake, toh yanzun daka koma bayan mota ka zauna me za’ayi nan gurin”
Meko za’a??
A’a mutumina ka daina wani basarwa tsume kake narantse da Allah……
Karan wayar Ahmad ne ta katse masu zance yayin da Ahmad yai saurin kallon wayar yace”
Abban Fatima ne….
3 comments