Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 15

Posted by

WATA FITSARA PAGE 15

 

Advertisements

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamido

                          Page 15

Advertisements

Hanyar Galadima ya kallah ganin  babu tahowan Samha dan haka ya juya ya kali Ahamad yace”

      Lafiya kuwa….
Daukan wayar da Ahmad yayi, Galadima na sauraron sa yana cewa toh Abba”

     Bayan ya sauke wayar ya kalli Galadima yace, Abban Samha ne yace na shigo ciki”

Advertisements

     Kai kawai Sani ya gyada masa dan haka Ahmad din ya nufi cikin gidan yana mejin wani iri aransa”

        Samha ce ta tareshi saidai wannan karon ta shiga nutsuwarta babu fara’a afuskanta, har falon Abbanta ta kaishi sannan ta fice tai waje”

      Cikin sunkuyar dakai ya gaida Abba yayin da Alhaji Usman ya kafesa da ido, zuwa can yace”

     Ahmad Ina fatan duk wasu abubuwa da suka faru abaya baka manta dasuba kamar yadda Nima ban manta dasu ba, sanin kowa ne cewa lokaci nacanzawa komai, kamar yadda yake Shirin canzawa yanzun, nasan Kai kanka bakayi tunanin wata rana zaka zauna agabana kamar haka ba,  na wasu abubuwa da yawa basu faru ba, haka nikaina da Ina da masaniyar irin wannan ranar wasu abubuwan bazan aikata ba, badan komai na amsan zan baka auren Fatima ba saidai wani alheri Dana hango hakan zai haifar, inason Fatima fiye da tunanin ka, kuma Ina tunanin kaima bazaka cutar da itaba, nahana kaina tuna komai dan ne dan Ina ganin hakan mafitane sosai, nasan kaiba karamin yaro bane duk da haka kuma niba sa’anka bane, abun da nake so dakai nan shine, bana son hira tsakanin ka da Fatima, ta waya ma ya isa, basai kazo ba ashirye nake nabaka ita duk lokacin daka shirya amman banason zuwan”

     Sanyi jikin Ahmad yayi sosai muryansa kasa kasa yace shikenan zan kiyaye”

      Sallama yaiwa Abba sannan ya fito, ko haduwa beyi da Fatima ba harya isa motar sa ya zauna yana maida Ajiyan zuciya”

    Kallon sa Galadima yayi yace”

     Yaya dai”

    Cikin takaici ya kwashe komai ya gayawa Galadima”

     Jikin Galadima asanyaye yace”

     Toh wannan wani irin abune haka Anya kuwa ba wani abu yake shiryawa ba?

      Tabe baki Ahmad yayi cikin damuwa tare da sake kallon hamya, ganin babu Fatima hankalin sa ya Kara tashi”

         Barin gidan sukayi cikin rashin kwarin jiki yayin da Ahmad ya shiga damuwa sosai”

         *********

Abba bakunce yau zakuje gidan su Fatima ba?

   Eh haka mukaso, alhinin fasa auren Khadija ya dakatar damu, ko baka da lbrn”

   Naji, Allah ya kyauta Daddy, Amman yanzun yaushe zakuje”

     Shiru Daddy yayi tsayon wani lokaci sannan yace”

       Zanyi mgn da Alhajin tukuna”

    Tam Abba Daddy yakamata kuje da wuri fah’

    Karka damu Ahmad”

    Dakinsa ya nufa yayin da Hajjah tabishi da kallo tare da fadin”

   Ikon Allah, Allah ya karkato da hankalin Ahmad Kan aure harya fara rawar kafa”

    Murmushi Alhaji yayi sannan yace ai hakan yafi yanzun ya kunsan zama cikakken mutum”

     Koda Ahmad ya koma dakinsa ya kasa sukuni, ayanzun burinsa be wuce yaga an tsaida magana ba”

   Misalin 10:30pm Samha ta Kira Ahmad da saurinsa ya dauka, muryanta kasa kasa ta gaidasa ya amsa sannan tace”

    ‘Dazon me Abba yace maka??

    Jimmm yayi sannan yace wani abu ya farune?

   Eh man yamin fada kamar ma zai dakeni, har yanzun baya mgn dani”

    Me kikayi masa?

   Bansani ba amman fa Dana shiko akofa na sameshi”

   Jimmm yayi sanan yace to ko ya ganni rike da Hannun ki?

    Bansani ba Uncle, toh meye arike hannun?

    Jimmm yayi sannan yace laifeni Fatima tunda niba muharramin ki bane, nikaina bansan yadda akayi haka ya faruba Amman koma menene ke kika jawo shi”

    Nibani bace Uncle, yanzun dai me yace maka??

   Kawai yace inbar zuwa ne mudinga waya kawai”

    Kai🙄🙄🙄, haka yace?, Me kace masa toh?

    Murmushi yayi kadan sannan yace”

   Toni me zance Fatima, dole inbi umarnin sa indai Ina son auren ki”

    Yanxun bazaka karasa zuwa ba??

   Eh gaskkya”

    Jimmm tayi sannan tace Amman zakazo makaranta ko??

   Shima shiru yayi nadan wani lokaci zuwa can yace”

   Kisa azuciyarki bantaba zuwa makarantar ku ba domin idan har Abban ki yaji Ina zuwa shima laifine Babba Dan haka dole zanbar zuwa, Fatima auren ki nake son yi dan haka dole zan kikaye har ranar dazai bani daman inzo in ganki koma in daukeki agidan Gaba daya, ashirye nake da in aureki, zan iya komai akan inga na mallake ki”

   Hawaye Samha ta share har ga Allah tana son taga yana zuwa sosai takeson ganin sa koda can balle yanzun da abun ya canza salo, fushi taitayi wannan ranar gaba daya taki fita kwanciya kawai tayi adakin ta”

    Khadija kwance adakin ta tun bayan Jin lbrn fasa auren gaba daya gidan wani irin kallo suke mata abinci kawai ake aje Mata kotaci ko kartaci babu abun da ya dame su, kowa fushe yake da ita dan haka jikinta yai sanyi gaba daya hawaye ma ya daina zubowa sai ‘yar rama data yi, hakan ya tuna Mata da kawarta lokacin tana gidan Alhaji Usman Safeena haka kawai taji tanason taje tayi Hira kozata rage damuwa”

    Mikewa tayi ta shirya tasaka banban hijjabi sannan ta nufi dakin Inna tai Mata Sallama”

      Adawo lfy Inna tace batare data tambayi inda zataba”

       Misalin 12:45 Khadija ta isa gidan Safeena, murna sosai Safeena ta nuna ganin Khadija agidan ta, bayan sun natsu tace yana ganki kamar kina da damuwa🤔

    Hijjabi Khadija ta cire sannan tace”

    Sosai kuwa Safeena, acikin tahin hankali nake, narasa inda zan saka kaina kekadai kika fadomin, agidan kowa ya kasa fahimta daga mecewa banyi halacci ba saime ganin laifina, ai kinsan Ahmad ko??

    Nasan dai lbrn sa agurin ki Amman bantaba ganin shi ba wani abu ne??

     Yawo Khadija ta hadiye cikin tara ruwan ido tace”

     Shine yace yana sona, shekarun mu daya dashi wata uku kawai yabani”

  Jimmm Safeena tayi sannan tace”

   Ton ai wannan ba wani abun bane Khadija, meye na tashin hankali”

  Hmmmm, ki tsaya in kaiki Safeena, ni bantaba mishi kallon mutumin dazan aura ba, komai yake daukansa nake ashirme Dan tun yana karami yake nuna kishin sa akaina, dayaga inayin kamar bangane ba saiya fara min maganganun Banza, naki sauraron sa, daga abun nason yin nesa nayanke shawan aure, Safeena kinsan Abun da Ahmad yamin dayaji Ina da niyar aure?, Wai yabani Sati daya injanye ko ko inga abun dazai yi, nacigaba da harka da ranar tacika yaga ban dakatar da zancen ba kawai sai yace waishi Samha yake so”

    Jimmm Safeena tayi cikin nazari yayin da Khadija tacigaba da cewa”

    Ayanzun haka mgnr da nake miki kowa ya sani cikin dangin mu sai murna suke, nikuma sun kasa fahimta”

    Dagowa Safeena tayi tace”

    Abun kam ba Dadi, amman kinsan namiji ba kunya yake dashi ba, kece zakiji abun yamiki banbarakwai shi Ina ruwansa, kisan shawaran da zan baki, kiyi hakuri karki nuna masa baki so, ki nuna ko ajikin ki saiyafi jin haushi, yayi ne daman dan yaga tashin hankalin ki”

   Nariga nanu tashin hankalina Safeena kowa yasan bana so”

  Kash😬 kinyi kuskure, ai beci ki nuna damuwarki ba, ‘yarkima kawai kika zuge ya shikeki batare da anji bakin kiba”

   Hmmm Safeena, Samha bata da hankali, tariga ta saba dashi yana Gaya Mata ta amsa, kuma Abbanta ya sangarta ta tuntuni take cewa Amata aure, ya bata dama tana rashin kunya”

    Iyeee🤔 ita Samhar shekarrata nawa ne yanzun?

   Bata wuce 16 ba Safeena wai harta San wani aure”

    Allah ya kyauta Amman ni Ina ganin ki kwatar da hakali ki, ki nutsu kidawo da hankalin ki jikin ki, abun ba tsari kam Amman anayi, kuma tunda kince tana sonshi mgn kam takare shawaran dazan baki kiyi hakuri kiyi addu’a Allah ya tabbatar da abun dayafi Alheri”

   Kai Ina bazan iya ba Safeena”

   Addu’ar??

   A’a ba nufina kenan ba, Wai meyasa bakwa ganewa ne, Ahmad fah bashi da kunya fitsararrene abu daya nake nunawa naji da Ahmad ya Aure Samha gara abinneni daraina, har yanzun kalmarsa na min amo acikin kunnena, Safeena Ahmad yataba kureni nazagi uban shi, agaban Babanmu ne, inda zakisan dan iska ne bece komaiba lokacin, Amman bayan nakoma daki saiya biyoni, Wai ubanshi yafi karfina saidai shi inzanci mu hadu agodon sa avanbance”

    Subuhallahi😳, lallai fitsarsa tayi yawa, amman beda mutuncin kuma konine bazan so wannan auren ba, Ina wani sauran Daraja kuma”

   Hawaye Khadija ta share sannan tace, kinga irin wannan kalamin yayi su babu  adadi, wato Dan inace mishi fitsarre shine zaice zanga fitsara, ayanzun haka Usman yabashi ita dan shima son ganin bayana yake”

    Shiru sukayi na tsayon lokaci, yayin da Safeena tace”

    Lokaci ya kusan kure miki Khadija, kinbata lokacin wajen shirme, yanzun dama daya nake ganin ta rage miki shine wajen Samha, ita zaki zaunar ki hure Mata kunne shikuma karki nuna masa komai”

  Wannan ma ba dama ce Dafeena, Sahma ba fahimta take ba”

     A’a dama ce Babba ma kuwa, wayaun da bata dashi ke zaki kowa Mata, intakama ki gaya mata yataba cewa yana son ki, Ina da tabbacin duk son da take mishi dazaran taji haka zai fita kanta dole yabata haushi duk rashin yawonta, domin kuwa uwa uwa ce, shikuma Babanta ai bazai bata wadda bataso ba, nidai anawa Ina ganin wannan kadai shine mafita, kinga kin Ahmad yayi bawan bakanin”

        Agidan Safeeena ta wuni har yamman yayin daga bisani ta wuce gida”

    Bayan kwana biyu Daddy da Alhaji sukaje gurin Alhaji Usman inda ya sauke su Agidan Mahaifin sa, inda anan aka yanke mgn har sadaki Daddy ya bayar nan take’

   Bayan Tafiyan su, kakan Fatima Alhaji Musa yashiga cikin gida,  inda yasamu ran Momy bace sai fada take”

    Meya faru Alhaji ya tambaya?

   Usman yafara bata min rai Alhaji, dabi’un sa sun canza, ko mu da muke tsofaffe ma aurar da yariya karama kamar Fatima?, Ace kawai saidai muga masu neman aure daga sama saikace diyar na nutsungulin sa, me yake damun Usman ne?

   Murmushi Alhaji yayi sannan yace”

   Ki kwantar da hankali ki Dan Allah, ni ya gayamin dalilin sa nayin hakan kuma yana da hujja me karfi addu’a kawai muke mukata”

    Shikenan Alhaji, amman gaskiya bansoba, banji Dadi ba Fatima ko tukunya ta taba daurawa awuta?, bare aje ga mgnr shara, dauke kafarta agidan nan nabar yi mata wanka, ko nono arziki  bata dashi”

    Dariya Alhaji yayi sannan yace,  Usman dai yafiki hujjja sai kiyi hakuri”

      Hajjah ko Shirye shirye tafara na tabarban sirikarta Fatima wadda daman burenta da fatanta duk akanta yake, yayin da Ahmad ma burinsa be wuce atsaida ranar bikin ba, kullum suke waya da Fatima kuma yana sammun ta fiye da tunanin sa, sosai take hira dashi komai bata boye masa, tun bayan fasa auren Khadija betaba zuwa gidan ba gaba daya ya dauke kafarsa da gidan”

   Itama Khadija ayanzun ta samu nutsuwa duk da cewa akwai damuwa aranta Amman tana daurewa matuka”

   Tsayon Sati biyu ya kwashe beje gidan su, ayanzu yagama bawa ransa yasamu Fatima”

        *********
Kamar kullum  yauma Khadija tana zaune tsakar gida yara da manya suna sasan inna Yalwa suna hira ana shewa yayin da Khadija ke gefe intaji ana dariya itama yi take koda batasan me sukemawa ba”

     Guje guje taji yaran gidan sun fara, nan ta tabbatarwa Kanta Ahmad ne, rabon dayazo gidan ta manta gaba daya ba’a ganin sa, daure fuska yaran sukayi tana kallon yadda kowa yake neman mabuya”

     Daga ita sai Inna Yalwa suka rage agurin, shigowa yayi bakin sa dauke da Sallama amsawa Inna tayi tana dariya take fadin”

      Wai yaran gidan nan nasa abun da ke hadaka dasu dasunjika sun fara guje guje kenan”

     Basu da gaskiya ne Inna, meya dameni dasu ni rawar Kai ce banaso”

   Tsugunawa yayi ya gaida Inna yayin da Khadija ta dauke kanta, su Hajja Inna ta tambaya yace Duk lfy sannan ya mike yana fadin”

    Ina wuni”

   Banza tayi kamar batajishi ba dan tsayawa yayi tare da sake fadin”

     Nace Ina wuni”

    Mikewa tayi da sauri tabar wajen yayin dayabi bayanta da kallo”

     Juyawa yayi ya nufi dakin sa cikin yanayi irin na tunani, son kawar da damuwar data fara shigarsa yasashi Kiran Fatima”

    Kina Ina??

   Ina gida Uncle”

      Agidan aina kike?

   Cikin dakina”

     Kina waya da Mamanki??

    Eh munayi Amman ba sosai ba”

       Ok toh ya karatu ?

   Lfy Lau Uncle yaushe zakazo makarantar mu”

     Banace miki na daina zuwa ba”

     Dan Allah Uncle kazo Kai yanzun ko ganina bakason kayi”

    Sosai nake son naganki Amman banason Babanki ya kamani da wani laifi ko yaya yake”

    Dan Allah Uncle kadanzo bakomai ai bazai sani ba”

    A’a Fatima nidai kiyi hakuri ba muna waya ba?

   Kukan shagwaba ta fara nidai Uncle kazo dan Allah 😩

   Toh shikenan ya isa ya isa, tsaya kiji”

     Cikin kunkunan kukan take cewa zakazo”?

     Umm zanzo Amman bazan jima ba”

   Mezan taho miki dashi”

      Bakomai nikai kawai nason gani”

   Fadada murmushinsa yayi tare da fadin”

    Ke yanzun bakijin kunyata ko?

     Uncle kabar cemin haka lokacin nema nake Jin kunyar ai”

   Nabari, baki da dama Fatima, toni me zaki bani innazo??

      Jimmm tayi sannan tace idan kazo zaka gani ai”

        Toh shikenan sainazo ko?

Tunda suka gama waya da Ahmad ta shiga tunanin Mamananta har dare sai fado Mata take dan haka ta kirata cikin waya”

       Umma Inna wuni”

    Lfy Lau Samha ya karatu”

    Lfy Lau, mun dade bamuyi waya ba, inata tunanin ki”

    Karya kike ni bakya wani tunanina Samha, tunda bakya Nima na ai, nasan kuma kina waya da Ahmad ko?, Kinfi son shi akaina”

   Allah Umma ba haka bane,   shi fah yake kirana bani ke kiranshi ba”

         Duk da haka dai kinfi sonsa akaina, Fatima shiyasa nabarki Nima bana neman ki”

    Sosai ran Fatima yai Mata wani iri hawaye ne yacika idonta fal cikin son fara kuka tace”

     Nifa wlh wlh ba haka bane Umma aike daban”

    Hmmm, nidaban shi daban ko?, Ai shikenan kije kirike Ahmad shine uwarki shine Ubanki ni babu ruwana”

     Kuka Samha ta farayi yayin da Khadija tai saurin kashe wayarta”

     Kira Samha ta sake Mata akaro na biyu, ajiyan zuciya Khadija tayi sannan ta dauka

    Yaya Akayi ??

     Umma kiyi hakuri kinji”

       Ni bakimin komai ba Samha, amman banason ganin ki da Ahmad”

     Cikin muryan kuka tace Umma fah Ina son shi, meyesa bakya son shi toh😩

     Zafi zuciyar Khadija tayi sosai, saidai dole ta kwantar dakai indai tanason samun yadda takeson gurin Samha cikin sauki”

         Dalili kikeson Sani Samha?, Zan gaya miki dalilin Amman nafison inga gani gaki, yaya za’ayi mu hadu?

      Shiru Samha tayi zuwa can tace Abbana bazai yadda inzo ba, Umma ko zakizo?

     A’a nayi alkarin vazan sake zuwa gidan kuba, ba kina zuwa Islamiyya ba?

    Eh

Karfe nawa?

       Da Yamma karfe 4 Amman kaini ake yi”

     Kiyi kokari ki shirya da wuri zan fito Kamar uku da rabi zan tsaya bakin makarantar idan kikayi ma driver mgn ai zai dan tsaya ko?

      Eh Fatima tace, daha suka rabu, yayin da Samha ta shiga tunanin, damuwa ta shiga irin wacce bata taba shiga ba”

          **********

Washegari, misalin 3:28 Khadija ce zaune da Samha abayan mota yayin da driver yabasu waje”

      Samha nasan kinsan matsayena abareki na uwa, Amman bazan San kisan ciwona ba sainan gaba kadan, kafin nace miki komai inason kisan babu wadda zai nuna min sonki aduniyar nan ciki har da Abban ki”

     Ina son ki fiye da tunanin ki, kuma nafi kowa son naga kina farin ciki, ciki har da Abban ki, nasan koda yaushe yana nuna miki so, nikuma bana tare dake, kar hakan yasa ki dinga ganin kamar ni ba Abakin komai nake ba”

  Nutsuwa sosai Fatima tayi kanta akasa da alama jikinta yayi sanyi”

Khadija ce tacigaba da cewa, jiya kintambaye meye sa bana son ki da Ahmad, kallonta tayi sannan ta dafa kanta tace”

    Kince kin son sa, Amman ni Ina baki shawara matsayina na uwa agurin ki, ki canza tunani, domin kuwa Samha idan kika aure Ahmad bazan daina bakin ciki ba, kuma koshi kikace yazo ya gaidani bazaizoba saboda be beganin darajata, dan haka daga ranar da kika auri Ahmad bani bake Samha, zanji kamar da ana canza ‘Da dana canza ki, harji nake danaga ranar Auren ki da Ahmad gara a binni da raina”

   Cikin sauri Samha ta kalli Khadija tare da zubuwar hawaye layi biyu, cikin rawar murya tace meyasa Umma???😭😭😭

       Zan Gaya miki, Amman Ina son kisan cewa idan kika dage sai Ahmad wlh zanji da ana canzo Yaro Dana canzaki, tunda uwata ta haifini babu wadda yaimin irin cin fuskan da Ahmad yayi min, Samha tsayon lokaci Ahmad ya dauka yana nuna min so naki kulasa hardai ya bude bakinsa ya gaya min da kansa ban amince ba, shine dan ya guma min ya kuntata min yadawo daga baya yace ke yake so”

    Runtse ido Samha tayi sosai ta dade bata bude ba, har Khadija tafara tsorata daga yanayin ta tafara cewa Samha bude idon ki”

     Bata budeba, wani irin jawo kuka takeyi idon ta kulle gam, yayin da take ganin jijiyoyon wuyanta nakara radowa”

    Jiggata tafara tana kiran sunanta daga can ta dawo tare da fashewa da kuka”

   Jawota tayi ta kwantar da itan  Kan kirjinta tana fadin”

   Samha kinaji ki nutsu kinji, banso na gaya miki ba, Dan dai naga kinki ganewa ne, nikaina cikin wani hali nake abun namun ciwo Samha, dama ace iya yana Sona kawai ya tsaya zan hakura kodan irin son daga kina mishi, Amman Kash 😬 yamin fitsara Samha yamin rashin kunya, kalaman da yake Gaya min kare ma bazaiciba idan kika aure shi bazaiga darajata ba”

     Tana goge hawayenta akan kirjin Khadija take fadin”

    Bazan aure Shiba Umma ki kwantar da hankalin ki, shima Abbana na yamin irin wannan mgn Amman ranar da kika masa mgn sai ya amince”

     Ba mgn nai masa akan yabashiba ai, shima Babanki ce masa nayi kar ya yadda Amman dayake shima yanason yaga tashin hankalina saiyace wai yabashi kawai, Ahmad shu’umim mutum ne ya dade yana shirya yadda zai billo min Dan soda yawa idan nace bazan aureshiba yana cemin dana gane bani da wayau, sai yanzun nake gani inda ya dosa, fitsara kawai yasa agaba”

   Umma ki gaya min me Uncle din yake gaya miki???

     A’a bazan Gaya miki ba Samha, ba inason intura miki tsanarsa bane, a’a aure ne tsakanin ki dashi bana so Ina son in nuna masa niba tsararsa bace har yanzun’

    Hawaye Fatima tacigaba da sharewa, basu fargaba sai 5 lokacin Samha taci kuka har idonta sun kunbura, sosai Khadija taji dadin Yadda Fatima ta fahimceta lallashinta taitayi bayan tadan nutsu taima ta sallama”

     Samha kuwa mahaifiyarta tabi da kallo sosai taji tausayinta ya shigeta, batason ta rasata, yayin da ta shiga jin haushin Ahmad me tsananin gaske bana wasa ba, lokaci daya takejin yana fita cikin ranta”

    Gida suka juya kawai Dan babu karatun da zata iya, da isarsu gida dakinta tashiga ta zauna sannan tashiga tunani, yau daya wani irin yanayi yasa tunaninta fara canzawa mezaisa Uncle yaiwa Ummata haka”

   Kuka taci sosai, har dare tanata sake sake, inda ta yanke shawaran gayawa Abban ta ta fasa kawai”

      Falon sa ta samesa yana zaune laptop agaban sa, cikin tafiya ahankali ta zauna gefen sa yayin da Hannun sa yake Kan laptop, dagowa yayi ya kalleta yayi murmushi sannan ya maida kansa tare da fadin”

    Mamana meke damun ki”

      Kawar dakanta tayi can gefe sannan tace

Abba nazo in Gaya maka ne”

   Batare daya kalletaba yace”

   Ina jinki”

   Abba nafasa auren da Uncle Ahmad 😭

    Dagowa yayi cikin sauri yayin da ya rufe laptop din ya mike ya dawo kusa da ita yace meya faru??

      Ni ban son shi ne Abba😭😭

    Shiru yayi yana kallonta da Mamaki Kan fuskansa sannan yace”

    Kunyi fada ne??

     Girgiza kai tayi alamar a’a

    Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yace”

    Shikenan naji kije zan nemeshi inji meye matsalar”

     Abba karka kiraahi dan Allah, ni banson shi ne kawai”

      Kallonta ya sakeyi sosai sannan yace”

        Ina kekikace amiki aure?

    Wlh Nafasa Abba”

Hade ransa yayi sosai sanan yace Khadija tazo gurin ki ko???

   Cikin sauri ta girgiza Kai”

     Jimmm yayi sannan yace meyesa kika canza ra’ayin ki yau??

       Nidai Abba dan Allah abar mgnr bana so ne kawai
Abba”

     Wani irin tsayawa ya daka Mata wadda ya haddasa Mata faduwan gaba sannan yace”

    Baki isa ba Ummee, nariga nafurta nabashi Khadija bata isa ta juya min gidaba, idan kikai wasa zan numa miki koni wanene, idan ke baki san halina ba ita tasan waye ni idan raina yabaci”

    Kara karfin kukanta tayi tare da fadin”

     Abba dan Allah kayi hakuri, wlh auren ma bana sonsa yanzu, dan Allah kace mashi kawai nafasa”

    Mamaki sosai ya kama Usman cikin mazurai sosai tare  kada hannun sa yace”

      Maza maza kije ki tattaro kayanki bazaki maidani Dan iska ba…….

73 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *