Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 16

Posted by

WATA FITSARA PAGE 16

 

Advertisements

WATA FITSARA🤔

     By
Fadeela Lamido

   Page 16

Advertisements

Cikin kuka tace”

    Abba kayi hakuri dan Allah”

   Ki hada kayanki nace karki.bari raina yabaci”

Advertisements

    Juyawa tayi ta fita cikin Kuka

       Meya faru Ummee kike kuka haka”

       Jikin Aunty tafada tana matsanan cikin kuka tace”

      Abba ne yace na hada kayana”

      Ki hada kayanki?, Kin batamasa raine?

         Wai akan nace banason Uncle Ahmad din?😭😭

     Bude baki aunty Samha tayi sannan tace”

     Kema kin cika rigima Ummee Abba ki yana bakin kokarinsa wajen kula dake tare dabin abinda kike so, da yaddarki akai komai, tun ba’aje ko Ina ba kuma kice baki yi”

     Aunty nina fasa ne kawai wlh banaso”

     Fitowa Abbanta yasata zabura au kin zauna ne anan kin kawo karata kome??

   Aguje tanufi dakin ta yayin da Aunty tace”

    Kamata ahankali, lallashinta zakayi, amman yanzun cikin fushi kace ta hada kayanta…

   Hannun ya daga Mata kibarni, zugata akayi nasani amman tana sonshi iskanci ne”

      Shiru Aunty tayi tana nazarin kowa kuma yake zargi?🤔

     Zama yayi sai faman hauci yake yi, yayin da aunty ta mike tabi bayan Samha, samunta tayi tana kuka tana hada kayanta amsa tayi tafara hadama adankaramin akwatinta tana fadin”

      Ke Ummee waye ne yake zugaki?, Kinsan fushin Babanki karki kureshi yana biye abun da kike so meyasa Saida mgn tai karfe zaki billo da wata mgn?

      Kuka kawai Samha keyi takasa cewa kala, har aunty tagama hada Mata kayanta bata iya cewa komai ba”

    Ita da Abbanta acikin mota babu me cewa komai Saida sukayi nisa tagane Gidan Momy zai kaita dan haka taji hankalinta ya kwanta sosai”

    Tunani take cikin ranta, kome Uncle yake gayawa Mamanta har takejin zafin?, Lallai tanason ta sani”😔

      A’a maraba maraba wata sabon gani”

   Jikin Momy tafada tare da fashewa da Kuka”

    A’a yada kuka kuma?

   Hawaye tacigaba da sharewa hakan yai daidai da Shigowan Alhaji Usman, Momy ce tace meyasamu Fatima ne?

     Cikin fushi yace, gatanan Momy Wai kinga Saida mgn yaj karfi tace kuma Wai bataso”

   Toh ai sai Abarta tunda auren ba dole bane, dukka ma har wani isa aure tayi?

     Mommy bazai yiyuba, ban fara komaiba Saida yaddanta kuma Ina da tabbacin zugata akayi, amnan bakomai kallon Fatima yayi yace”

      Zan nuna miki koni wanene, duk irin kula dake din danake bakya ganin ko?

    Kanaji Usman, ya isa haka, yariya dai bawani isa aure tayi ba, sabo da haka abar shi tunda tace bata so”

   Momy ita yariyar nan ita ta nunamin tana da ra’ayin yin aure kuma nabi ra’ayin nata dan gudun samun matsala, wlh Momy ko bata so sai anyi auren”

   Baki Mommy takama, au ko bataso?🤔, Kai auren dole aka maka?

     Hmmmm, gatana ta zauna anan, daga gidan nan sai gidan mijin ki, nasani kwarai Khadija ce tazo min har gida ta hure miko kunne, dan haka bazan lamunta ba, dole zakiyi aure”

   Ganin inda yake huci Mommy tace shikenan jeka zan lallashe ta

        Karki barta taje ko Ina Momy ta zauna agida kawai”

    Tam kawai Momy tace masa sannan yasa kaj ya fice yayin da Momy taciga da Lallashin Samha tana fadin”

    Shiru Abunki, ransa ne yabaci bame miki auren dole kinji ko, Lallashin ta taitayi harsai da tai shiru sannan tace Wai da gaske kince kina son aure?

    Ciki. Turo baki tace nidai yanzun da Amin aure da Uncle gara inyi zamana hakanan?

    Baki Momy taka sannan tace”

    Waye yake zuka ki?

    Ni babu kowa”

   Toh Allah ya kyauta Momy ta fada tana me kallon Fatima”

     **********

   Dadaddare Ahmad ne zaune cikin dakinsa agidan su Khadija waya ya shirye yi da Fatima domin tabashi nishadi a inda ta saba yayin da ya Kira sau 6 bata dauki waya ba abun dabe taba faruwa ba, daga karshema saita kashe wayar”

      Mamaki yaji sosai yayin da ya barma ransa fushi tayi halan beje makarantar su ba, daker vacci ya daukesa aranar yayin da washe gari da sassafe ya nufi makarantar”

     Fitowa driver yayi kamar yadda ya saba saidai wannan karon babu Fatima abayan shi”

    Ina take ? ya tambaya

       Ance yau batazo ba makaran taba”

    Batazo ba ?

    Kwarai kuwa”

   Jimmm yayi yana tunani tunda yake betaba zuwa makarantar ance batazo ba waya ya dauka ya sake kiranta yanaji tana ringing Amman ba a daga ba”

       Sosai hankalin sa ya Kara tashi, rasa abun yi yayi daka karshe ya wuce gidan Hajjah”

        Babu kowa falon sai wayar Hajjah dake kujera da alama kitchen ta shiga”

     Wayar ya dauka yasa number Fatima sannan ya kira”

      Abun Mamaki muryanta yaji cikin kunnen sa tana sallama saidai da alamar bata da walwala”

     Ahankali yace Fatima??🤔

    Jimm tayi zuwa can ta kashe wayar, sauke wayar yayi ya kalla sannan yace”

     Menene haka?, Sanyi jikinsa yayi sosai dan haka ya tsurawa waje daya ido”

      Muryan Hajjah yaji tace lafiya??

     Ba lafiya Hajjah, tunjiya nake Kiran Fatima taki daukan wayata kuma naje makarantar su ance batazo ba sannan nasake kiranta bata dauka ba Amman yanzun dana kira da wayar ki ta dauka”

     A’a🙄 ton me yafaru yaro?

    Shine Nima nake tunani Hajjah”

   Toko gidan nasu zaka ka duba”

     Hajja kinsan Abbanta ya dakatar dani daga zuwa gidan su”

    Haka ne toko shi zaka Kira kaji?🤔

     Shiru Ahmad yayi zuwa can ya shiga Kiran number Alhaji Usman”

    Gaidasa yayi sannan ya danyi shiru yayin da Alhaji Usman yace”

       Lafiya ko?

    Eh lafiya daman nakira Fatima ne tun jiya bata dauki wayaba”

    Kawar dakai Alhaji Usman yayi cikin lalubo abun da zaice sannnan yace kana ji Ahmad?

      Inaji

    Ko kunyi fadane kaida Fatima?

       A’a Abba kullum muna waya kuma Ina da tabbacin lafiya muka rabu”

    Hakane, abun dayasa kaji namaka wannan mgnr dazon tazo min da wani rigima ne irin nata cewa tayi wai tafasa auren, amman nagayata bazai yiyuba dan haka kabarni da ita”

    Jimmm Ahmad yayi cikin tashin hankali sannan yace toh nagode”

   Jigum Ahmad yayi tare da tambayan kansa tafasa auren??

      ***********

   Kwanan Samha uku agidan Hajja kullum sai Ahmad ya kirata Amman bata daukan wayasa”

    Abangaren Ahmad kuwa ya shiga damuwa, Galadima yakira ya Gaya masa yayin da Galadima yace”

   Yanzun Kai wa kake zargi”

    Aini kaina ya kulle Sani, nakamu sosai akanta sai yanzun nake gane ada bansan soyayya ba, domin kwana ukun nan bana bacci”

    Kasan Allah?, Khadija ce zata hure Mata kunne”

    Shiru Ahmad yayi sannan yace kuma fah hakane😬”

     Galadima ne yace aini ko tantaba banayi itace samun ta zakayi Kaja mata kunne”

    Jimmm Ahmad yayi sannan yace”

    A’a, bazani ba, idan naje muna iya yin bacacciya, ita Bata iya fushi ba nikuma bakina ya iya maida zance, idan nakasa daurewa fah, baza ta gayamin nai shiru ba, cikin huci ya karasa mgnr sannan ya mike tsaye ya kama kwankwaso indai Hakane Khadija nasom wahalar dani ne kawai, domin ninasan Fatima nasona haka kawai bazatace tafasa aurena ba saidai In zugata aka yi”

          Hmmm aini nagaya maka Abun da zaka yi”

   Ba yadda za’ayi ne ma muhadu Sani, ayanzun dole nake kaucewa haduwa da ita ayanzun burina bewuce inga an aura min fatima ba, banda wannan ni komai baya gabana ita kawai nake son naga na mallaka hankalin zai kwanta daga lokacin”

       ********

    Meyasa da Ahmad ya kiraki baki dauki waya ba??

      Cikin sunkuyar takai tace”

   Bangani bane,

Baki gani ba?

    Kasa amsawa tayi, shiru yayi yana kallon ta sannan yace”

      Kina nufin taurin Kai zakimin?, Zakisha wahala Ummee domin wannan auren tunda na amsa zan bada saina bashi ke ko bakya so”

     Hawaye ta fara shewa tare da fadin”

    Abba alkari kamin bazakamin auren dole bafa😭😭

     Dan namiki alkawari shi zai baki daman dazaki maidani karamin mutun, baki isa ba Ummee, wayar sa ya daga yasa akunnin sa zuwa can taji yana fadin”

      Nina gama shirina idan Kun shirya sati me zuwa ne za’a daura auren”

     Jimmm taji yayi, sannan taga ya kashe wayar ya mike ya fice”

   Yana fita Fatima ta fashe da kuka har ga Allah ayanzun batason auren ko sunan Ahmad din batason taji an Kira”

        Shikuwa Alhaji Usman daga gidan momy Kai tsaye ya wuce gidan su Khadija, sannan ya kirata cikin waya ya sanar Mata yana kofar gida”

      Sosai taji faduwan gaba kamar zatace bazata fitoba Amman saita mike tafito tana son taji dame yazo,?

     Daga irin kallon dayai Mata ta gane rigima ya kawo shi, cikin kawar dakai ta gaidasa be amsa ba, shima kawar dankasa yayi sannan yace”

    Me kika gayawa ‘yata akan Ahmad??

    Meko nagaya Mata??, Tace nace mata wani abu ne?

     Ina tambayan ki kina tambayata??

      A’a, to naji ana neman lakabamin ni aina nake ganin ta?……

    Cikin daga murya yace”

   Karki raina min hankali Khadija nasanki Sarai, kibar aro wasu halaye sabo dan wani dalili nake na daban, idan da alkunya tunda Ahmad ya furta yana son ‘yarki yakamata ki hakura dashi, ke kanki kinsan abu ne wadda bazai yiyu ba ayanzun, Ahmad ya miki nisa”

    Me kake nufi Usman?

   Kingane abun da nake nufi Khadija, nafahimci Ahmad nason Fatima sosai, meyasa kike son ki hanata auren sa, sabo da karya haramta agare ko???

    Cikin zaro ido tace wacce irin mgn ce kakeyi Usman, tunda nake arayuta bantaba tunanin auren Ahmad, daman tunanin ka kenan shiyasa danazo da mgnr karkabashi kace kabashi kai tsaye, saikace bakasan darajarta ba??

      Cikin ido ya kalleta, Ina Sane da abun da nake Khadija, kece baki da wayau amman ni saidai na kalli mutum, zan aura wa Ahmad Samha cikin sati daya ko bata so”

    Karkayi haka Usman, yanzun sabo da ni kake son ka aura wa yariya ko wanni irin miji?, Kawai sabo dakai farin ciki ni kuma kasani amasifa??

    A’a, karkimin mummunar fassara, ni zan aura wa Ahmad Fatima ne sabo da Ahmad yakai abashi aure, naduba irin gidan daya fito duk wani abu da ake so wajen namijin daya dace abawa aure ya cikasa ke kanki kin sani”

      Haka kake gani?, Nikuma nasan Ahmad bashi da kunya fitararre ne wannan shine dalilina ba wani abu ba”

    Ke kikasan rashin kunyansa, ni bansanta ba”

   Kaima ka sani, domin kaidashi kiris ya rage bakuyi dambe ba, ban taba tunanin zaka bashi aure ba”

    Akan me zan hanashi?, wannan rashin kunyan daya min yayi shine alokacin dayake kishin ki na yarinta dake damunsa, yanzun ko hankali yazo masa ‘yata yake so, kinga kenan yagane bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, dan haka na yafe masa kuma nabashi Fatima”

   Amman ni ai baka min adalci ba, tunda ni da girman nan nawa yasha Gaya min maganganun da basu dace ba, kuma dan iskanci yadawo yace wai Samha zai aura”

  Murmushi yayi, sannan yace wannan kuma matsalarki, ke kika nuna bakisan darajar kankiba da kika kaso auren ki ya ganki atiti kuwa tayaya bazai Gaya miki  yana son ki ba, yanzun taku ta haduko yace Fatima yake so duk kinbi kin haukace, garama ki nutsu, nidai bazan fasaba, ita kuma Ummee Bata isa ba kamar yadda kike tunani, dan haka kibar hure bata kunne”

     Cikin dakiyar dabatasan lokacin data kirkiro Shiba tace shikenan Allah yabaka sa’a, karka fada din, Amman Nika daina zargin nazugata babu ruwana kuma gaka ga Ahmad dinan karka fasa”

    Juya yayi yana kokarin shiga mota yace nadai gaya miki kibar hure mata kunne, yadda kike zaune babu aure haka kike son ki ganta, bazai yiyuba”

    Dariya yayi sosai bayan yadau Hanya sannan ya koma gidan sa”

    Ahmad zaune a office dinsa yakasa komai yau duk da tarin aikin dake gaban sa dan haka ya mike kawai ya tafi gidan Hajjah”

    Baki awashe ya sameta, Zama yayi yayin data taso ta fadashi”

    Albishirin ka?

    Goro ya fada cikin rashin walwala”

    Abban  Fatima ya Kira Daddy ku ayanzun haka ranar juma’a za’a daura auren”

    Jimmm, Ahmad yayi, cikin yanayi irin na tunani, sannan yace, Kwana shidda Hajjah?, Wanni irin aure ne za’ayi cikin kwana shidda, bawani biki da za’ayi kenan???

     A’a mu ashirye muke zamuyi bakin mu gava daya”

    Shiru ya sakeyi zuwa can yace”

    Nidai banason ayi biki nan da kwana shidda kawai, sabo da bazaiyi armashi ba, kenan fah za’a samu fuskar Fatima babu walwala, kowa saiya fahimci halin da ake ciki, dandai  Abbanta yaki bani damar zuwa ne da tunani na shawo kanta”

    Toh Banda abun ka ai auren yanzun din shine mafita, tunda kana ganin zaka iya shawo kanta, idan aka daura auren insha Allahu abun zaizo da sauki”

   Wata kila tunda yanzun bansan meye azuciyarta ba”

   Shiru Hajjah tayi zuwa can yace toh me zai hana idan an daura auren ku zauna nan ko sati gudane kafin asan abun yi”

     Kawar dakai yayi fuskansa dauke da damuwa sosai yace”

   Shikenan Hajjah amman fa gabana na yawan faduwa, wani lokacin ma inajin kamar na hakura, naso ace anyi biki sosai kuma Ina son inga dariya afuskan Fatima bana son ganin damuwa”

     A’a karka hakura ka kwatar da hankalin ka”

           ****

Gidan su Khadija gaba daya ya dauka auren Samha da Ahmad saura kwana biyar”

     Nutsuwa sosai Khadija tayi, tana zuba yake, yayin da mutane ke ganin sakkowanta   ganin yadda take yake vaki”

      Daddare Khadija zaune cikin dakinta ta lalubo number Fatima”

    Adashe taji muryanta bayan ta gaidata tace”

      Abban ki yaki barin zancen ko?

     Eh “

     Shima Shirin auren yake ne?

    Ni ban sani ba ina gidan Momy, Amman inajin Momy tacewa wai ranar juma’a😭

     Yi shiru, kibar kuka kinji, amman duk sanda zai tambaye ki kice baki so”

   Toh aini Umma yabar mgn dani, ko yamin mgn fadane kawai Momy ko in Kira uncle in Gaya mishi da kaina?😭

       A’a, karki kirki kirashi, ba nufina kimai rashin kunya ba, har yanzun kicigaba da kallon sa kamar dacan farko, Uncle din kine, wannan kallon zaki dinga mishi har abada”

    Ni bazan iya girmamashi ba Umma 😩, Ina son in kirashi tunda Abbana yaki yadda😭

    Baki da kunya ko Samha?, Nace miki karki kirashi, zai iya gawa Abba ki kin kira kince kaxa, kuma ki Kara fusata shi, kibari imsha Allahu Abban ki zai tausaya miki, insha Allahu zaiso Kara Jin ra’ayin ki kafin adaura auren “

       Umma bazai min mgn ba fah, saidai kawai inji amce an daura, har makaranta ya hanani zuwa yanzun fa 😭

    Ya isah, ya isa, ki kwantar da hankalin ki, kuma kiyi addu’a insha Allahu baza’ayi ba….

    Mmn Yazeed

7 comments

  1. Pingback: fuck
  2. Pingback: BACU2025
  3. Pingback: Dennis
  4. Pingback: mostbet yukle
  5. Pingback: Cbd flowers uk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *