Advertisements
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 19
Advertisements
Ahmad Gidan su ya kwana Khadija, da alama mafarki kika yi mara dadi???🤔
Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta jigina bayan ta da gado, Inna ce ta dauko dankwalinta ta daura Mata akai tare da fadin”
Kinyi sallah kuwa”
Advertisements
Kaita girgiza yayin da Inna tace, tashi maza, kinsan yanzun karfe nawa?🤔
Kaita daga ta kalli agogo karfe 9:15am dan haka ta sauko da sauri yayin da Baba dasu Inna gaba daya suka bita da kallo
Buta ta dauka ta nufi bayi har yanzun jikinta bebar rawa ba, bayan ta fito alwala tayi ta koma daki, guiwanta babu kawari dan haka azaune tai sallan”
Bayan ta idar ajiyan zuciya taita saukewa sannan sannan ta fara tuna zancen su da Ahmad daren jiya wadda take ganin kaman andau tsayon wani lokacin, tambayan sa tayi wai ana auren dole ne, inda ya bude baki yace Mata”
Ba’ayi, ninasan bakya kina, kawai dai akwai wani tunani naki ne nacen daban, inason ki cire komai aranki muyi aure”
Gaban ta taji ya sake faduwa Kara zurfi tayi cikin tuanin kalaman sa”
Shikenan babu wadda zan fadawa, bazan Kai mgnr mu dake gurin kowa ba kamar yadda kike tunani, Amman nabaki sati daya kijanye zancen auren, idan kuma ba hakaba, zan baki Mamaki, sainasaki kin zubar da hawaye da idon ki nan, sannan Zaki fito da bakinki ki kibude abun da bakison na bude shi, alakacin da lokaci ya kure miki”
Wannan ne kalmarta na karshe dashi wadda taita tunanin me Ahmad yake shiryawa ne, tsayon lokaci ta dauka tana tunani ko baccin batasan lokacin daya dauketa ba
Ajiyan zuciya ta sake saukewa, tunu mafarkinta me muni datayi, wani gauron numfashi ta saki sannan tace”
Allah na rokeka kada ka tabbatar da wannan lamarin, lallai Ahmad akwai abun daya shirya, nasan ahalinsa Sarai tunda ya fadi lallai lallai akwai wani abu azuciyar shi, yace min nizan nemeshi, nikuma nayi ikirarin bazan nemeshi ba gashi na nemeshi cikin bacci na😬
Sannan yace ni zan bude baki ince yataba cewa yana Sona, gashi nabude acikin mafarkina kuma ya karyata ni, komai daya fada nagani, nayi kuka nayi bakin ciki kamar zan mutu, Wai Ahmad wanni irin mutum ne?🤔
Agaskiya akwai abun daya shirya mani, wannan mummunan mafarki ne agereni wadda inda haka ya kasance bansan yaya zanyi ba, Usman ne ya fado mata yayin datai saurin mikewa ta koma bakin gado”
Wayarta ta dauko ta zuba Mata ido sannan ta shiga Kiran Ahmad”
Sosai take son ya dauki wayar Dan ma ya ajeye kudurinsa tun wuri”
Har sau uku ta Kira be dauka ba dan haka ta ajiye wayar tare da ajiyan zuciya, tsaki tayi lokacin data tuno Galadima cikin mafarkimta, tsanarsa taji me tsanani, afili tace halinsu daya, shima Ashe tantirin dan iskane natsane shi, bana son abotar su domin shine nan yake zugashi, shi yake ingizashi wajen Samha😬
Shiru tayi tsayon lokaci sannan tace”
Komai danagani cikin baccina tsaf zai iya faruwa kamar gaske, Ahmad zai iya rufe ido tunda yaga ban yadda dashi zanyi ba, kuma ma inba daman can yana shirya wani abu ba buni buni yana hanyar makarantar su Samha😳 dole saina dakatar dashi”
Mikewa tayi ta fara zaware dakin, dole in dakatar da wannan auren domin Alhaji Kabiru daman can bawani son shi nake ba, kawai nayi nufin aure ne domin in gujewa rashin kunyar sa, mikewa tayi daman hijjabinta najikin ta ta nufi dakin Baba”
A’a Khadija?, Kin fito?, Har kinyi sallah?
Eh Baba nayi”
Yayi kyau, ai naso in kara lekoki, katuwar ki dake kina bacci kina ihu babu Addu’a abakin ki wanni irin mafarki kikayi ne?
Jimmm tayi cikin tunanin abun fadin”
Babane ya sake cewa, naji kina Kiran Fatima da Ahmad??
Cikin in ina tace”
Eh Baba, mafarki nayi wata Babba mota ta tunkaro su gaba daya kuma kamar gaske wlh duk ban dauka mafarki bane Baba”
Subuhallahi, ai haka mafarki yake Khadija, Amman ki dinga addu’a, har yanzun naga biki dawo hankalin ki ba, koda yake dole ki rude Fatima ita kadaice ‘yarki Ahmad kuma mutumin ki ne haka kuka taso kamar tagwaye”
Shiru tayi kanta akasa shiru sukayi tsayon wani lokaci zuwa can tace”
Baba??
Dagowa yayi ya kalleta yace”
Na’am Hadiza kina da mgna ne?
Eh Baba,
Ina jinki,tattaro hankalin sa yayi gaba daya ya zuba Mata sannan yace Ina jiki”
Baba, mgnr aure nane da Alhaji Kabiru najanye”
Kawar dakai Baba yayi, bangane kin janye ba???
Juyowa yayi ya kalleta sosai, yayin data sunkuyar dakai ta kasa mgn”
Babane yayi ajiyan zuciya sannan yace”
Meye hujjar ki, Hadiza kina hauka ne? Kefa kika kawoshi kuma kefa ba yariya bace”
Tsintan kanta tayi da zubar da hawaye Baba kuyi hakuri dan Allah😭
Shiru yayi yana kallon inda take zubda hawaye zuwa can yace”
Ko gidan tson mijin ki kike son ki koma????
Shiru tayi zuwa can tace”
A’a
Shima shiru yayi yana nazari zuwa can yace”
Shikenan, kedai ba karamar yariya bace ba kinsan zaman ki haka bazai yiwu ba, dole zakiyi aure”
Nasani Baba, zanyi nan bada jumawa ba insha Allahu”
Shiru yayi tare da jawo wayarsa yana kallo, saidai zuciyarsa babu walwala yace”
Shikenan jeki zanje nagayawa Alhaji, nasan shima bazaice amiki dole ba, Amman Ina umartan ki daki kawo miji nan kusa, kuma ko kinzo da irin wannan mgnr bazan saurara miki ba lokacin”
Kan Khadija akasa tace nagode Baba”
Be amsa ba, ta mike ta fita tana waiwayen sa, taga rashin Jin Dadi afuskansa sosai”
*********
Dakin ta ta koma har yanzun hankalinta be kwanta ba, Ahmad kawai take son gani ko meyasa yaki daukan wayarta?🤔
Ahankali ta shiga tuna Ahmad tun lokacin kuruciya wadda duk ya dawo mata cikin baccinta, nutsuwa tayi zuwa can kuma taja tsaki, waishi Ahmad daman da gaske yake tun wannan lokacin kishina yake??, Banda abinsa yaya za’ayi in aureshi?, Tsaki ta sake jah sannan tace duk yabi ya nace saikace tsohon maye, abun karyawanta ta kallah Bata iya taba komai idan bataga Ahmad ba, dan haka tahau Shirin wanka, wanka tayi bayan ta dawo ta shirya cikin doguwar riga ta atamba da aka kawata ta da dinki irin na zamani, sarka da dan kunnen gwal tasa tare da awarwaraye sosai taikyau daman Khadija badaga bayaba gurin kwalliya sosai tai kyau, mayafin daya dace da kayan ta dauka tasashi akafada sannan ta dauki ‘yar karamar Jakarta ta nufi dakin Innarta”
Bayan sun gaisa tace”
Inna gidan Hajjah zani”
Cikin rashin walwala tace”
Toh adawo lafiya, ki gaidata”
************
Misalin Sha biyu rana ta shiga gidan Hajjah,
Hajjah ta samu akan suna karyawa tare da Yariyar Anty Saude fiddausi”
Gurin ta nufa yayin da Hajja ta fadada murmushinta tana fadin Khadija?
Kujara ta jawo ta zauna kusa da Hajjah tare da amsawa, bayan sun gaisa Hajjah ta tura Mata kufi tana fadin gshinan”
Hannun tasa ta maida kofin sannan tace”
Ni Hajjah gurin Ahmad nazo yana nan kuwa??
Yana nan yanzun ma na lekasa ganin be fitoba ashewai kansa ke ciwo, lfy ko??
Lfy Lau Hajjah mikewa tayi ta nufi dakinsa yayin da Hajja tabita da kallo”
Tana tura gofar ta hangi shi, meke sabal cikin bargo har kansa, harta karasa bakin gadon tana kare masa kallo, saida tagama yafi tsaye idan yana bacci domin har gani tayi ya tokare gadon”
Ta dade tsaye akansa sannan ta zauna bakin gadon cikin juya masa baya sannan tasa hannun ta ja jaye bargon tare da fadin”
Dallah malam tashi”
Motsowa yayi tare da Kara rike bargon, itama Kara jayewa take ta juya masa baya”
Sakar Mata yayi, sannan ya tashi ya zauna ya jinkina bayan sa da gadon yana fadin daga Ina???
Daga gida ta fada kanta tsaye”
Cikin kawar dakai tace lfy Lau”
Bayanta yake kallo hankalinsa kwance yace”
Lfy Lau nasan baxakizo ba, kedai ki fada abun daya kawo ki”
Juyowa tayi tare da fadin”
Kaidai mafarki nayi wata Babban mota ta tunkaro ka…….
Kodai ta tunkaro ki ba? Yin tambayan yayi yana kokarin sauka agadon”
Kai ta tukaro bani ba, tafada lokacin datake kare bashi kallo daga ahi sai gajeren wando, kawar da idonta tayi adaidai locin dayake fadin”
Badai niba malama, an gaya miki zan mutune ban kaiki gado ba”
Nadai gayawa Baba”
Ya Amin ce??
Eh”
Jimmm yayi cikin godewa Allah azuciyarsa sannan ya mike tsaye, kenan yanzun kin amince da aure na???
Kallon sa tayi cikin sauri, a’a nidai inason ka ajiye kudurin ka mu fuskanci juna”
Wani irin kallo ya Mata, Khadija fuskantan junan daya ne shine in mallake ki”
Amman Ahmad batun yauba nake cema bazan aureka ba ko, waikai dan Allah bakajin kunyata, lokacin danai aure inaga ko kaciya ba’ai maka ba”
Wani dan gutun murmushi yayi sannan yace”
Kin rainani da yawa Khadija, Amman ba laifinki bane ba, ni har yanzun ma ba’a min ba, ke nake jira, na tanadi kayan aiki, idan kinzo sai kimin😉
Ai kaji irinta, ni matsalata dakai kenan”
Idan baki son irin wannan mgnr ki kiyaye ni, muddin kikace Zaki Gaya min abin da kikaga dama toh ki shirya sauraron kalamai na”
Shikenan naji, abar mgnr, yanzun na aje batun auren sai me kuma?
Yauwa, haka nake son ki, ki dinga fahimta, ni Ina son ki kuma auren ki zanyi, bana bukatan dogon lokaci domin nasanki kinsan ni kawai as auren za’a daura”
Amman baka da hakali Ahmad, da Ka daina tunanin zan zauna akarkashin ka, wlh bazan iya kallon ka matsayin miji na ba, 👏🏻 ninan zan iya nemo maka Mata Amman Dan Allah ka aje zancena agefe, yanzun ka Dan baka da kunya sai kayi rayuwar aure Dani, ka fara ta yaya?
Hmmm, Ai baki fini ido ba,
Khadija, nafiki sanin abun da yadace wa kaina, kibar ganin Ina lallabaki ni ko ayanzun nasan na sameki nagama, insha Allahu, tunda naga alamar bazaki nuna mun soba sai kinganki akarkashin iko na”
Amman Ahmad wlh kaidai munafiki ne, shikenan kaje kayi duk abun da kaga dama, Amman dan Allah karka Kara zuwa makarantar su Samha”
Wannan ne kuma baki isaba”
Hmmm, wai Ahmad meyasa yanzun dabu’un ka duk suka canza ne, kazama wani iri yanzun”
Ni daman can haka nake Khadija”
Wlh bahaka kake ba, banda fitsara yanzun babu abun daka iya, wannan bokin naka Galadima na tsane shi, shine yake koya maka fitsara”
Dariya Ahmad yayi sosai sannan yace”
Ya rigani shiga makarantar, Amman nafishi kwarewa, Dan yafi zama abakina fiye da nasa, bakin gadon ya koma tare da fadin”
Tunda nake dake baki taba burgeni irin na yau ba Khadija, Kura Mata ido yayi tare da lumshe su sannan yace”
Kuma kinyi kyau sosai, sannan zan iya cewa tun bayan Dana mallaki hankalina baki taba sani farin ciki irin nayau ba, sosai kika burgeni, sai naji na Kara son ki, nifa Khadija tsintan kaina kawai nayi acikin sonki ni bansan ranar Dana fara ba, kuma banta bawa wata ‘ya mace kallon wadda zan iya rayuwar aure da ita ba saike Khadija, tun sanda nayi tunanin aure ke nake hangowa, haka kuma duk ranar da kwadayina ya motsa ke nake hangowa amatsayin wadda zata kawar min dashi, in takaice miki mgn Khadija, har mafarki inayi dake har wanka yahau kaina”
Sosai Kalaman Ahmad suka furgita Khadija ganin inda yake kankance ido ta miki tana fadin”
Gaskiya Ahmad kana da tsaurin ido”
Ke kike ganin haka🤷🏽♂️ Nina San duk ranar kika jini zaki fara ganin girma na, wata mgnr koda kudi akace ki gaya min bazaki gaya ba, kuma lokacin na zuwa nan kusa, yau cikin farin ciki nake, ko kice kina Sona, ko karma kice, ke karma kice din
Dazaran zancen fasa auren ki ya isa kunnen Alhaji angama insha Allahu, nan bada jimawa ba Zaki zama karkashin ikona, lokacin ne Zaki tantance koni waye”
Mikewa Khadija tayi hankalinta be wani tashiba saidai yanzun Babban burinta tabar dakin Ahmad, mikewa tafara yi kusan atare suka mike, yayin daya nufi kofar yasa key”
Tsaye Khadija tayi tana masa wani irin kollo, tare da fadin meye haka kuma”
Nufota yayi yana fadin tukuici zan baki Khadija……….
Mmn Yazeed
6 comments