Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 2

Posted by

 

WATA FITSARA PAGE 2

Advertisements

WATA FITSARA🤔

     By
Fadeela Lamido

           Page 2

Advertisements

…..Tashi Khadija tayi domin taji ajikinta zai iya zuwa, cikin sauri ta zari karamin hijjabinta tasa, ficewa tayi cikin sarsarfa”

     Inna da kanta ke karkashin gado ta dago da tsintsiyarta ahannunta tace”

    Hadiza meke damunki ne wai, kwana biyun nan baki da aiki sai guje guje waishin Ahmadu kike ma wannan gudun kema🤔

Advertisements

    Hawaye ta share sannan tace”

   Inna Dan bakisan halinsa bane, ya isheni Inna, wlh ya isheni😭

    Rike da baki Inna take kallonta zuwa can tace Amman dai kinyi asara Hadiza, Ahmadu dai kikewa kuka🤔

      Hawayen ta share sannan ta zauna bakin gadon tare da zame hijjabinta tace”

    Inna bashi data ido, kalaman shi babu lissafi, wlh Ina daf dakai karansa wajen hajjah tamin iyaka tashi”

   Toh wai me yai zafine haka??

  Inna waidan yacewa Baba zai iya aurena nikuma yaban haushi nazageshi shine wai ya biyoni daki wai ubansa yafi karfina wai Inna cewa yayi wai saidai shi”

    Subuhallahi🤔 kajimin almurin yaro, toh aike saiki kiyaye sa, zagin ke beso shiyasa ya miki haka, Amman ai Ahamad mutumin kirkine kinga wanncen sallayan shi ya sawo min yace indinga sallah ga wani turare can ma nesa dake nasane shine ya kawo min waccen zuwan da yayi kema ai naga ya miki tsaraba ko”

    Hmmm Inna ni tsarabar sa be dameni ba burina kawai arabani da Ahamad”

   Cikin fada Inna tace ke karki kawo min shashancin wanni abin ne kuma?, Keda Dan uwanki daga ya nusar dake kuma saiki bishi da sharri, idan kinason yabar shiga harkarki kibar tonun sa karki kara zaginsa”

    Aini Inna koma ba’aceba bazan karaba, Inna wata kalmar idan Ahmad ya fadeta har zazzabi sai ya nemi kamani”

       Abun da yafi zazzabima saikiyi Hadiza toh yarone da wayaun sa, ga kuma kudi Allah ya bashi, baya wasa da damar da Allah ya bashi”

      Gintse zancen tayi domin tasan duk abun da zata fada Kan Ahmad Inna ba yadda zatai ba gara taje inda za’ayi abun da ya dace”

    Kwanciya tayi nan, jira take taji fitan Ahmad itama ta fice, hankalinta kwance take kwanci domim tasan duk tsiyarsa bazai biyota dakin uwarta ba”

    Misalin karfe 4 tafito cikin shirinta tsaf babban hijjabi tasa har kasa, tare da yiwa Inna sallama akan zataje gidan kawarta”

      Bayan ta fita adaidaita ta tare tahau, gaban wani gaton gida ya sauketa yayin data doshi gidan”

   Gaton gidane na gaske wadda aka kawata shi da kayan alatu, afarfajiyar gidan motocine barjik, haka gidan yake baya rabo da motocin domin yaran gidan maza da mata kowa da motarta”

     Kasancewa ita ba bakuwa bace agidan kanta tsaye take shiga batare da anmata shamaki ba duk da tarin tsoron gidan”

       Tana dosan falon tafarajin hayaniyar yaran gidan tanasa Kai kuwa suka taso aguje cikin hargowa suke fadin oyoyo aunty Hadiza💃🏻💃🏻

        Rungumarsu tayi daya bayan daya sannan takarasa falon inda ta cikkada mahaifiyar su cikin fara’a tace”

      A’a Khadija, batan Kai kikayi halan?

    Cikin murmushi tace”

    A’a Hajjah

    Toh keda *Yaro* ne halan”

    A’a wlh Hajjah ni dayace”

    Cabdi ashe yau ruwa da kankara za’ayi”

     Wata yariya ce can gefen Hajja tace”

   Aunty Hadiza Amman kwana biyu Zaki mana??

      A’a Basma yau zan koma nazo dai gaida kune Amman Ina smun lokaci zan dawo ai……

   Gyaran muryar dataji ya hanata karasa abun datai niyya kofar ta zubawa ido yayin da yaran falon duk suka zame daya bayan daya”

     Tsaye yayi tsakiyar falon yana kallon yadda yaran duk suka fashe, wannan karon fukansa sake take saidai lokaci daya ya sake tamkewa”

    Hajjah ki gayawa yaranki idan suka ganni sukama kudu saikace sunga mahaukaci??

      A’a gara su nemarwa kansu lafiya dirkansu kake alhalin kuma sudin ba jakai bane ba”

    Zama yayi yana fadin”

    Ni bana dukan kowa Saida dalili Hajjah, kallon Khadija yayi, ke!!!, Ke kuma nan kikayo?

       Cikin Mamaki Hajjah tace”

    *Yaro* Khadija kake Kira ke??

   Kawar da kansa yayi sannan yace”

    Toh gudanawa take Hajjah ki kalleni ki kalleta niba tsaranta bane ba”

    Hmmm *Yaro* bafa wani girma bane Kai mata”

    Toh aina rigata Shan iskan duniya Hajjah”

   Wasu hawayene suka zubowa Hadiza, ahankali tace”

     Hajjah nifa daman karansa na kawo maki”

   Ahmad hajjah ta kalla yayin da yai saurin kawar da kansa can gefe yace”

     Ni mena miki ??

   Kallonta ta maida Kan Khadija tace”

    Khadija Ina sauraron ki”

   Hajjah ki gayama Ahmad yabar shiga harkata niya isheni Hajjah”

   Subuhallahi fada kake kuma da Khadija Yaro, lallai kana da tsaurin ido banda abunka ka kalleta ka dubeka”

       Kallon nata yayi Hajjah ni banga komaiba, bata wani bani tsoro, kuma ni ai ba fada nayi da itaba ki rabo da ita dan Allah, ke Khadija tashi ki wu ce gidan ku”

      Saidai kajani ka kaini Ahmad”

   Ni ai nafi karfin najaki saidai nasa ajaki din tunda haka kike so”

   Hajjah tagumi tayi tasa masu ido tana kallon ikon Allah”

    Idan ka fasa ka raina Allah”

    Cikin tsawa Hajjah tace *Yaro* barnan wajen wuce maza ka bamu waje”

    Hajjah idan natashi sharri zata min”

     Kabar gurin nan tace ko?

    Mikewa yayi yana hararan Hadiza yabar wajen yayin da Hajjah ta maida kallonta Kan Hadiza da idonta yai kwalkwal kamar zatai kuka tace”

   Khadija meke faruwa keda Dan uwanki, aida can bakwa fada sai yanzun kuma abun zai zama rigima?

     Hawaye Hadiza ta share sannan tace”

    Hajjah yanzun Ahmad ya canza, tunda ya dawo rashin mutunci kawai yake min, har a hanya yagannni saiyace wai yaban minti kaza nakoma gida, ubana ne shi? dan yana ganin Baba nacewa ya girmeni kawai kuma saiya rainani, niba sa’arsa bace ba”

    Toh ya isa haka Khadija na fahimta, maza ki goge fuskan kafin yaga hawayen ki, tunda bashi data ido, wannan ai ba wani abun data hankali bane”

    Goge fuska Khadija keyi yayin data rasa inda za’ayi ta karasawa Hajjah irin rashin kunyar da yake mata, Kira taji Hajjah na kwala masa *Yaro* take kwakira kamar yadda take gaya masa cikin sanyin murya ya amsa yayin da ya fito murtuk yanaiwa Hadiza kallon kasan ido”

     Gani Hajjah”

   Nace atunanin ka Khadija tsararka cene??

       Cikin yamutsa fuska yace ban ganeba Hajjah”

    Kadubeta da kyau Yaro nace tsarar kace??

    Nafa girmeta hajiya kwanwata ce, tacika son girma ne kawai ita atunaninta ni kanninta ne, kuma girma Allah ya riga yabani ko kinaso ko bakiso dole kice da mijin iya Baba

    Ka saurareni Yaro, ko bazaka girmamata  ba kabar mata rashin kunya, nasan halinka Sarai, Kai bakasan arainaka Kai Dan me zaka raina wani?

        Niba rainata nayiba, nasan kanwatace, kuma kota girmeni ai abokiyar wasata ce ko?

   Toh batayin wasan ko dole ne??

   A’a badole bane Hajjah”

   Toh abarshi tunda ba dole bane bataso”

    Shikenan anbarshi”

    Shiru falon yayi zuwa can yace”

    Na wuce shikenan??

     Eh wuce, mikewa yayi ya wuce batare daya waiyayi baya ba”

    Baki Hajjah taita Kara bawa Hadiza harta saki ranta zuwa yamman tayi mata sallama ta wuce”

        **********

Ummee kwance saman gadonta tunda ta dawo makaranta, hawaye take sharewa sosai takeson mahaifiyarta da uncle dinta wadda tuntana karama yake kula da ita tare da kawo mata ziyara, makaranta, taso nada tsauri sosai Amman abun mamaki duk ranar da uncle dinta yaxo yana zaune cikin motarsa ake barinta ta fito kuma harsai Dan kansa yace ta koma makaranta”

       Duk ranar da suka hadu da uncle dinta ko ada tana shiga damuwa sosai domin yana tuna mata mahaifiyarta”

      Tashi tayi zaune domin yaune suke zuwa gidan Momy ita da Abban ta, shiri tahauyi tanayi tana share hawaye gashi Abbanta yaki bata waya yace Sam be yadda yabata waya ba”

    Misalin 4 na yamman suka isa gidan Momy, cinyarta Ummee ta kwanta yayin da Momy  ta kalli Abbanta tace yariyar nan rama take Yi, meke damun ta”

     Kawar dakai yayi halan karatu ne Momy Amman bata cikin damuwa”

     Kallon sosai Momy ta kare mata sannan tace”

    A’a fah, Kai Usman yaushe rabon yariyar nan da zuwa wajen uwarta??

     Tana zuwa Momy akai akai ai”

    A’a Sam nasan halin bakar zuciyarka wadda bana fatan yayan ka su gado, nabaka umarnin gobenan kakai yariya wajen uwarta kafi kowa sanin irin shakuwar da sukayi da karfi da yaji ka kwace tana zubar da hawaye tahakura tabar maka, idan kana fushi da uwar  ita ai ka zalinci yariyar ba ruwanta batasan tsakanin ku ba”

     Shiru yayi kawai bayan ya gama sauraronta yace”

    Zansa akaita gobe idan Allah ya kaimo”

  Saidare suka suka baro gidan sai dai har sukayi nisa Abba yaki kallon gefen da take, tasan bacin ran umarnin da Momy ta bayar ne sosai taji ranta babu dadi”

    Mamana kinkai karata wajen momy ko?

     ” Kamar daga sama taji zancen nasa Dan haka ta direrice a’a Abba ni baruna bance mata komai ba wlh Abbana, hannun sa tai saurin rukowa shikenan Abbana idan bakaso karka kaini”

    A’a Sam zansa akaiki ki ganta, dadin abin nima Ina da uwata, kina tafiya nima zanje abani nono, bazan dawoba harsai kema kin dawo bare kewanki ya dame ni”

    Dariya ta saki batare data San lokacin ba, toh nima ai ba nono take bani ba Abba”

    Ki fada gaskiya dai, wannan irin son da kike mata kilama har goyaki take, gashi ni bazan goyoba bare nima nasa Momy ta goyani”

    Dariya Ummee ta sake yi, Abba ai koni Momy bazata iya goyawa ba, kafartama fa danahau cewa take zan karya mata kafa, kabini kawai muje wajen Mama tare”

    Hade fuska yayi zuwa can kuma ya sake tare da fadin”

     Kinason a daki Abban ki ne??

    A’a, waye to zai dake ka??

    Wasa nake miki, ni ai me dukana saidai ruwan sama innaso”

    Dariya tayi, cikin sakin layi tace Abba kasan uncle dina??

      Gabansa ne ya fadi cikin sauri ya jiyo ya kalleta, nasanshi yaya akayi ke kika sanshi”

      Cikin sauri tace, nasan shi, aida idan naje wajen Mama muna haduwa”

    Kina mgn dashi????

     Eh”

   Cikin sauri ya koma gefen hanya tare da tsayawa cak yace”

      Daga yau saiyau Ummee karki sake mgn dashi, natsaneshi, ko ganinsa banson yi, idan kina mgn dashi zamu samu matsala dake irin wacce bakya tunani, cikin tsawa da fada yace”

   Shima akan me zai dinga mgn dake!!! ?

    Tsorata Ummee tayi tare da makurewa guri guda takare fuskanta da hannun ta”

   Komawa Abba yayi ya zauna yana fadin bazakiba Mamana ba inda zaki zan mata izzini duk lokacin dataji ganin ki tazo ta ganki”

     Hawaye tashare sannan tace toh Abba nagode”

    Ganin inda jikinta yai sanyi sosai ta bashi tausayi hanyar ya kama zuciyarsa cike da tunani”

  Misalin 10 nadare bacci ya gagare idonsa, tabbas da Ummee ta dinga haduwa da Ahamad gara yawa Khadija izzinin zuwa duk lokacin data ga dama, wayarsa ya dauko ya fara saka number ta wacce ya kasa gogeta cikin ransa tun bayan rabuwar su, tsintan kansa yayi da Kiran numbar cikin kankanin lokaci ta dauka”

     Sallama yayi bayan ta amsa yace”

         Usman ne

       Sarai tagane muryarsa Amman sai tace”

      Waye haka?

   Hmmm Baban Ummee ne”
Nakirane nace miki duk lokacin da kikaso ganinta Zaki iya zuwa”

     Bata da lfy ne ??

      A’a

   Allah ya kiyaye nicema zanzo gidanka ganin Samha?

   Ok kina nufin kin barmin kenan ko??, Danni bazan bar ‘yata zuwa wannan gidan ba”

   Toh ai wannan bawata matsala bace, kaje ka jikata kasha, katse Kiran tayi tare da jifa da wayar ta fashe da kuka”

      Sosai hankalinta ya tashi, da Ahmad take tattauna irin wannan mgr dan haka ta kirasa batasan lokacin tada fara Kiran layinsa ba, saidai har sau uku be dauka ba sai alokacin ta tuna  ashe fah tasa an mata iyaka dashi🤔

       ‘baccine ya gagari idonta don haka ta sake Kiran sa, wannan karon dauka yayi Amman yaki mgn”

    Ahmad kana jina??

    Imm”

    Bakai Bacci ba??

   Shinfideni kika yi?

    A’a toh daga tambaya?

   Ina jinki, yaya inace kinsa an miki iyaka Dani??

    Eh Amman ba waccen mgnr bace ba?

     Toh Ina jinki”

    Jimmm tayi sannan tace”

   Kadaiga Baban Samha ko?

    Dariya yayi sannan yace”

   Hmm kaji wai kadaiga Baban Samha ko?, Ina ruwana, ni inace cewa kikayi Ina miki rashin kunya, wai har kece zaki kalli tsabar idona kice inai miki rashin kunya, wlh ki raba kanki dani ki bini ahankali na wuce inda kike tunani”

   Toh naji kayi hakuri, Ahmad mubar wancen mgnr yanzun yaya zanyi ne cewa yayi wai duk sanda nake son ganin Samha naje na ganta”

    “Tunda kedin mayyace ai saikije din, ni babu ruwana bacci zanyi”

   “Bacci zakayi?, Samha ce fa mutuniyar ka, nina kasa bacci fah”

     Babu lefi, ke kika kyankwasheta ai, kiyi aure kinkiyi shekara 6 kina zaune sai Kara tsufa kiki yi ahaka, kixo in taimake ki kin tsaya girman Kai”

     ” Katse Kiran tayi domin babu biyan bukata da alama”

  Shima Alhaji Usman kamar yadda Khadija ta kasa baci shima bacci gagaransa yayi dan haka tunda wuri yasa Ummee shiryawa sannan yasa driver sa yakaita”

    “Misalin 8 nasafe suka isa, cike da dauki ta nufi cikin gidan bata mance komai ba dakin kakarta ta nufa tana Kiran Inna!!!

”  Na’am muryan Fatima nake jiyowa🤔

    Jikinta ta fada tana hakki nice Inna kinsan muryana ne?

     Toh bagashiba Fatima kullum kina raina yadda nake tunaki ko uwarki albarka, daga Ina, badai daga makarantar aka sato ki ba?🤔

   ” A’a Abban yasa akawoni??

    “Yakuwa kyauta yaushe Zaki koma”

   Bansani ba andai saukeni”

      Yakyauta, Kira ta shiga kwalawa ke Hadiza ga diyarki”

    Dankwali ahannu Hadiza ta taho ikon Allah tafada afili haka kika girma Samha🤔

      Murmushi tayi sannan ta tashi daga kusa da Inna ta koma kusa da Hadiza tana fadin”

     Ammi Ina kwana?

    Lfy lau ya mutanen gida”

    Lfy lau, Abbana yace in gaidaki”

      Kin iya karya ko?, Jeki gaida mutanen gidan”

    Fita tayi dukda girman gidan tas tagaida kowa sannan ta nufi dakin datasan nanne dakin Ahmad, tura kofar tayi gaba daya tare da gwandara muryarta cikin sigar bada tsoro tare da kaffafe hannunta, tsalle ta daga zuwa Kan gadon da yake kwance tare da fadin”

       Wuuuu👹👹

     Azabure ya tashi domin babu wadda ya taba mishi irin haka, hannun yasa yana mutsuke idonsa sosai tare da zama agadon”

     Kanne idonsa daya yayi bayan ya tabbatar itace sannan yace”

      Sannu da zuwa aljana Fatima, nima  aljanine dan uwanki, nasan da zuwanki tun daren jiya, ninasa Babanki ya sauka daga kudirinsa nacewa mamarki ta dinga zuwa ganin ki…….

   Bakai ka karasawa ba ta saka ihu tare da fadin”

      😳😳 Wayyo Allah na, fita tayi aguje yayin da Ahmad ya fashe da dariya, bayanta yabi ya hangota gudu take ko waiwaye babu, dariya yaci sosai irin wacce ya dade beba sannan ya nufi toilet kusan awa guda yayi ciki sannan ya fito ya fara shiryawa cikin kananan kaya”

     Jikin Inna ta fada wayyo Allah Inna”

   Menene meya faru”

    Tana haki sosai tace aljani nagani”

     Hada baki sukayi wajen cewa a Ina??

    Tana nuna kofa tace adakin uncle”

     Adakin uncle??, Shi uncle din fah”

     Afirgece sosai tace bansani ba nima shinaje nema”

     Inna ce tace waini abun da bangane ba, me kika ganune kika firgice haka”

    Wani nagani kato kan gadon na dauka uncle dinane nahau gadon Ina basa tsoro nace ni Aljana ce shine yace min shima aljanine yasan da zuwana tun daren jiya wai……

    Dariya suka kwashe dashi yayin da Samha ta tsaya kallon su tare da fadin”

     Aljani nagani”

    Eh kuwa kinga babban aljani Ahmadu meyakaiki dakinsa?

     Kawar takai Hadiza tayi tai dariya ganin har yanzun Samha firgice take, janta da hira Inna taitayi harta shiga bata lbrnta da Babanta yayin da Hadiza ke kasawa hirar taso kunne”

       ********

   Cikin siririyar muryansa yai sallama dakin yayin da Samha ta Mike ta koma bayan Khadija”

    A’a Fatima saukar yaushe?, Ya fada yana tsugunawa domin gaidar da Inna”

     Zamowa tayi ta taho gare d’azon nazo nemanka dakin ka naga aljani”

        Dan Allah, gaida Inna yayi yana kokarin gyara zama ta fara kokarin hawa wuyansa, cikin sauri yace”

     Ke meye haka?

    Maka wuya zaka min”

   Hannunsa yasa ya tureta tare da fadin”

     Ai yanzun bada bane malama, Ina zan saki awuyana ki kaini ki baro”

     Komawa tayi bayansa ta rabe, jikin bango tare da turo baki, Satan kallonta Khadija tayi tai murmushi aranta take cewa sabo turkenan Wawa gani take kamar dane”

      Hiransa yacigaba dayi da Inna ko inda Hadiza take be kalla ba zuwa can ya kalli Samha yaga harta fara matso kwallah”

     Idonsa akanta yace”

    Zo nan, wai yayane??

    Kafada ta make, dan haka yayi murmushi yace bazakizo ba?

    Bakaibane kaki yimin”

     Idonsa ya lumshe sannan yace”

    Yanzun saboda Allah Fatima Babanki nasaki awuyansa kamar da?

      Toh aishi Abbana ne Kai kuma uncle”

    Ok uncle wahalallene kenan, shikenan Khadija zoki daura min ita awuyana”

     🙄Aini ba ‘yar isa bace”

    ” Kallonta yayi cikin ido cike da baccin rai yace kina nufin ni dan iskane kenan? Mikewa yayi tare da rike hannun Fatima yana fadin Zaki gane baki da wayau, ficewa yayi dakin”

    Cikin fada Inna tace bakya kautawa kema Hadiza, daga yana wasa saiki kyaba masa mgn ko wasa kike dai toh ya masa zafi, kibishi ki bashi hakuri, me nan nan da naka kuma🤔fada Inna ta fara dan haka ta Mike ta fita, dakin Inna yalwa ta sameshi yana kallon tafin hannun Samha, da alama wanni wasan yake mata dan dai ya kaucewa wanccen zance”

    “Tana saka kafa dakin tace kayi hakuri”

     “Itace sallamar, saboda an matsa miki ko?, zan nuna maki ni cikakken dan iska ne, ai zan kama ki”

    “Ahmad banason irin wannan mgnr, karka manta ‘yatace kusa dakai amman kake gayamin irin wannan maganar”

    “Mikewa yayi da saurinsa yayin da Samha ta mike tabi bayansa, cikin fada Hadiza tace ke zonan”

      “Waigowa yayi ya kalleta, jeki Mamanki na Kira”

     “Ni  binka zanyi ka saya min icecream”

      “Zan taho miki dashi”

    “Nikaje dani😩

     Wai tsaya, guna kikazo ko gun Maman ki?

     Gunka, cikin sigar shagwaba take mgn,  shiru yayi yana kare mata kallo yayin da take Shirin saka kuka har cikin ransa yakejin abun da take, kawar da idonsa yayi daga kanta, daga can ya hangi Hadiza tana hararan sa dan haka ya kalli Samha yace”

     ” Wuce ki bani waje”

    ” Bata tsaya bata lokaci ba ta juya afusace, hambare duk wani abu dake gabanta take cikin fushi sosai ta wuce”

    “Karan dayaji yasashi waigowa ya kalli yadda take hambare butucin Inna dake bakin kofa, bayan yaga shigansu dakin dariya yayi afili yace kagamin yariya, ji yayi bazai iya barinta haka ba, cikin sauri ya koma yana fadin Ina kike?, zomuje”

    ” Tayi bacci Hadiza ta fada yayin daya hangeta kangado sai faman ajiyan Zuciya take, karasawa yayi bakin gadon tashi muje kinji”

     “Kafada ta make”

    Yihakuri kitashi muje

Juyar da kanta tayi can gefe, harara ya zabgawa uwar sannan ya zauna ya kama kafardarta”

     Fatima ni kikewa fushi, dama mutun na fushi da Babanshi ne?, haka kuma zamuyi dake, tonidai ki tashi muje duk abun da kikeso zan saya maki?

     Batare data dagoba tace, zaka sani a wuyanka?

    Wuyan nasa ya shafa tare da fadin mezai hana?, tashi maza ki shiga mota mu tafi”

     Mikewa yayi batare data bari yaga fuskantaba ta wuce yayin da Hadiza ke Satan kallon sa tana murmushi, shikuwa ajiyan Zuciya ya saki bayan yaga fitanta, zuwa can ya maida kallonsa kan Hadiza”

    Ganin tana murmushi yace”

    Kun shafawa yarinya bakar Zuciya uwa Zuciya uba zuciya”

       Eh kaima kuma Zuciya ba”

    Nidin??, Zakiga zuciya acikin jikin ki, ficewa yayi yayin da Hadiza ta dafe Kai tana fadin”

    Kash😬 Nima dai yakamata na daina tankasa”

         ******

  Kusan awa biyu suka kwashe basu dawoba yayin da Hadiza taita zaman jiran su, sosai takeson ta zanta da ‘yarta wadda ta kwashe tsayon lokaci bata sata cikin idonta ba, sosai ta kosa su dawo tana tsaka da wannan tunani taji muyar wani yaro yana fadin”

     Wai yariyar Alhaji Usman ta fito su tafi………

5 comments

  1. Pingback: Discover More Here
  2. Pingback: bdsm
  3. Pingback: pin up app
  4. Pingback: sinhairvietnam.vn
  5. Pingback: jogar FruitCash

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *