Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 20

Posted by

WATA FITSARA PAGE 20

 

Advertisements

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamido

PAGE 20

Advertisements

Ganin inda ya nufota gadan kadan yasa tace”

       Ahmad karka tabani, kokarin ja baya take yayin da yayi kanta gadan kadan”

       Tana isa jikin bango yana isowa, yayin da yayi mata rufa tare da zuba mata idonsa, ya dade ahaka, yayin daya fara shiga wani yanayi, ita kanta Khadija yanayin yadda yai Mata gaba daya jikinta yai sanyi”

Advertisements

      Cikin shakaykiyar muryarsa yace”

       Khadija ina son kidan kalla cikin idona na minti biyu kawai”

     Kawar dakai tayi tare da fadin A’a

     Meye a’a kuma, dago ki gani”

       Cikin nuna jarumta ta dago din kamar yadda yace, saidai suna hada ido tai saurin kawar da nata tana cewa wlh Ahmad Kai dan iska ne”

      Idonsa akanta batare daya cire ba yace yaya akayi na zama dan iska nida ko kaciya ba’aimin ba”

     Saurin runtse idonta tayi domin ita kanta vata gane ta fadi ba daidai ba sai taji irin amsa da yabata”

         Kirjin Khadija yake bi da kallo ganin inda numfashinta ke sauka, lumshe idonsa yayi sannan ya sake budewa yace”

      Yanzun abun da zamuyi Ina son ki kalli cin idona na minti 5 sannan kice bakya Sona nikuma insha Allahu daga yau zan barki”

      Kawar dakai tayi cikin sauri banson ka Ahmad”

     Ba gaskiya bane Khadija, idona nace ki kalla na minti 5 sannan”

    Dagowa tayi ta kalleshi, yayin da tai saurin kawar da kanta”

   Murmushi yayi kina Sona Khadija girman Kai kawai ke damun ki, zan tabbatar miki da haka nan gaba kadan”

        Allah ya tsareni Ahmad, wlh kabar tunanin Ina son ka, Dan kankanin ka dakai?

    Hmmm, baki da kunya Khadija, nafa girmeki amman kin raina min wayau dakyau, sannan nafi wanan wawan girma”

      Karka Kara ce masa wawa koda muka rabu har haryanzun muna tare tunda munada Samha”

    Cikin sauri ya dane mata baki da hannun sa, yayin datai saurin riki gurin tana fadin”

    Kai!!! Ahmad abun har yakai haka?, Ni kake bigewa baki?

    Wacece kedin, zakice wani kuna tare, kinsan me Kalmar ke nufi kuwa??

     Jimmm tayi tana kallon sa sannan tace”

       Ban sani ba, Kaine ka iya karkata zance dan Allah matsan na wuce”

    Tukuicin fah? Ko baki so?

     Meye tukuici kuma?

    Yanxun zaki gani……

   Nika bani hanya na wuce dall……

    Bakinsa dataji cikin nata ya hanata karasawa yayin da hankalinta ya tashi sosai duka tafara kai masa akirji iya karfinta’ tare da gurnani sonyin mgn, dakyau ya riketa yayin data kasa kwatar Khanta”

     ***********

  Hajjah take kokarin shiga dakin baccinta, wani irin nishi takeji kamar irin an danne mutun yana numfashi daker, tsayawa tayi ta kara saurarawa kadan tabbatarwa Kanta tayi dan haka ta saki kofarta ta nufi dakin Ahmad hankalinta amatukar tashi”

     Tura kofar tayi tajita gam, cikin mummunan tashin hankali ta shiga buga kofar tare da Kiran sunan sa”

     Saidata Kira kusan sau biyar ya iya amsawa yayin data shiga jin kukan Khadija”

     Tahowa yayi ya bude kofar, yana maida Ajiyan zuciya tare da shafa kansa tun daga farko zuwa keya”

    Shashshekar kuka Khadija takeyi sosai, saidai Hajjah Bata iya hangota, Ahmad ta tsare da ido yayin da idonsa yai jawur ga wani ruwa kwance acikinsa”

    Cikin ido Hajjah ke kallon sa har yanzun bebar shafa kansa ba”

     Zuwa can taja tsaki tare da fadin matsa ka bani guri……

     Matsawa yayi batare dayace komai ba,

    Hango Khadija tayi tsaye jikin bango kuka kawai take hawaye na zobo mata, jan bakin data shigo dashi ayanzun babu shi, tunawa tayi tagan shi a fuskan Ahmad, cikin sauri ta kawar dakai sannan ta kama hannun Khadija ta nufi kofar da har yanzun Ahmad na tsaye agurin”

     Cikin tsayawa tace bani guri”

    Matsawa yayi, yayin da Hajjah ta wuce rike da Hannun Khadija”

    Dakinta ta shiga da ita har yanzun hawaye take”

     Ficewa Hajja tayi fuskanta Babu walwala, kusan minti talatin sannan ta dawo, kallon Khadija tayi tace”

     Wai har yanzun baki bar kukan ba?, Kitashi kiyo alwala kibar kukan nan haka”

    Mikewa tayi ta nufi toilet din Hajjah tayo alwala ta fito, sallah tayi bayan ta kidar ta mike ta gara gyalen ta sannan tace”

     Hajjah zan tafi”

    Kallon Khadija Hajja tayi sosai sannan ta saki murmushi tace”

      Amman ai kya bari kici abinci ko, koma ki zauna, barinsa akawo miki abinci”

     Zama din tayi duk zuciyarta babu Dadi, haka kuka gaba daya lebenta radadi yake mata, dan haka duk take jinta adarare, musamman idan hajjah na kusa da ita”

        Abinci fiddausi ta kawo Mata, tafara ci kenan Ahmad ya shigo yayi wanka cikin shigar kananan kaya, zaunawa yayi nesa da Khadija yayin da Hajjah kecan  bakin gadonta tana cin abinci”

      Yana zama fiddausi ta kawo masa nasa sannan ta fice”

     Itako Khadija tunda Ahmad ya shigo taji ranta ya bacci dan hakama ta kasa cin abincin”

      Ganin har yayi rabin nasa ita ko tabar ci yasa shi fadin”

      Khadija kici abincin mana….

   Kamar jiransa take tace”

     Bazan ciba Ina ruwanka Dani, wlh Ahmad zan zage ka fah”

     Cikin sauri Hajjah ta dago ta kalle su, adaidai lokacin da yake fadin”

    Tunda dai bazan daku ba aida sauki, ki zakigeni wata rana ko saki akayi bazaki zanga ba”

      Hannun tasa ta ture abincin sannan ta mike afusace tace Hajjah na tafi”

     Koma ki zauna Khadija”

     Hajjah ni tafiya zanyi😭

Ki zauna nace”

    Fashewa tayi da kuka, Hajjah bakya ganin wulakancin da yake min”

    Nagani ki zauna nace”

    Komawa tayi ta zauna yayin da Hajjah ta hade rai tace”

        Yaro dauki abincin ka ka fita”

   Dagowa yayi ya kalli Hajjah sannan ya kalli Khadija yace”

      Ni nafin son naci abinci cikin mutane Hajjah idan nagama zan fita”

     Ahmad?, Hajjah ta kirashi cikin kallon cikin idonsa”

      Amsawa yayi cikin nutsuwa, Dan da wuya kaji takira sunan sa Kai tsaye”

    Ka fita nace ko?

   Mikewa yayi batare daya ce kalaba yabar dakin”

      Kallon Khadija Hajjah tayi sannan tace”

    Ai saikici abincin”

    Nakoshi fah”

    Hajjah bata sake mgn ba dauke kanta tayi harta gama sannan ta mike ta fita”

     Misalin 4 na yamman Khadija taiwa Hajja sallama”

     Bari Ahmad ya fito ya kaiki yamma tayi abun hawa wahala yak……

    Zan samu insha Allah, idan ma ban samu ba zan tafi da kafa”

      Lallai Khadija, wato da Ahmad din ya kaiki gara kije akafa”

    Ahmad dake fitowa yanzun nan ne yace barta Hajjah ai ita zataji ajikinta”

      Kallo Hajjah tabisu dashi tare da fadin, wannan rigimar taku inason naga ranar karewarta, abu tun kuruciya🤔 kowa inda yasa gaban sa daban”

       Kusan atare suka fita da Ahmad da Khadija tana gaba yana bayanta”

      Idonta ne ya sauka akan Galadima dake saman motarsa azaune, wani irin bakin ciki taji, domin ayanzun tunanin ta Galadima ke zuga Ahmad, hararansa tayi sannan ta dauke kanta ta wuce sa”

       Dariyar su taji abayanta yayin, ganin suna neman wuce gona da iri yasa taki waigowa dan batasan kuma wanni kalan iskancin suka shirya ba”

     Ahmad motarsa ya shiga yayin da Galadima ya rufe nasa ya nufi ta Ahmad yana fadin”

      Mutumina wasa wasa Khadija fah tana da kyau”

       Kawar dakai Ahmad yayi, ya a kayi kasan haka??

     Wucewanta yanzun ta wanni kannaro min harara, sainaga dogon hanci tare da dan baki daidai mazubi”

     Hmmm, Kaifa wani lokacin dan iskane, ni ko tana dakyau ko bata da kyau nidai naji nagani, ninasan wacece Khadija, nadade inason zama da ita kuma lokacin ya karato insha Allahu”

     Dahaka suka fita agidan, yayin da suka hangi Khadija tana kokarin isa titi”

      Murmushi Ahmad yayi idonsa akanta yace”

        Barin indan kara tsokanan ta”

     Gafe ya koma yayin da Khadija taji mota abayanta , kallon gurin tayi domin tattabarta ko ahanya take, ganin kwata kwata Bata kan hanya ta gane Ahmad ne dan haka taki waigowa cigaba da tafiyanta tayi cikin nutsuwa”

      Tana isa titi ta kauce can gefe tare da dauke idonta tana jiran taga wucewan su ta gefen idonta”

     Abun Mamaki ko gilmawar wani abun hawa batai ba, cikin tsananin Mamaki tace”

     To waye kebin bayana?, Danasani na waiga, zuwa can kuma tace, ko da yake Ahmad da Galadima ‘yan iska ne, komai ma zasu iya, tunani ta shiga yi, sosai take tunanin hukuncin Da Ahmad ka iya zartarwa idan taki auren sa, tabas Ahmad da gaske yake aurena yake so tunda gashi yau ya gwada min karfi ya riki min baki😭

     Yawu ta tofar tare da share hawaye tace”

       Ahmad bashi da kunya nine yake hadawa da bango sabo da tsaurin ido ya masa yawa”

Koda ta koma gida har yanzun bata samu nutsuwa ba, tajene dan tai masa wayau amman yaki tsayawa hakan ta kasance mgnr ma yaki bari ayita cikin nutsuwa saima dada lalacewa da abun yayi tunda gashi yau Ahmad har bakina ya tsotsa, tsaki taja tare da kawar dakai, afili tace, meye mafitane yanzun?, Ta wacce hanya zan fullo masa, idan yace yanason Samha ayanzun sai hankalina yafi nada tashi🙊

    Toshe bakinta tayi domin gudun kar wani yaji zancen zucinta wadda batasan ya fito fili ba, wata zuciyar ce tace ki aure shi mana, da sauri ta runtse idonta cikin yanayin son kawar da wannan tunanin, afili tace yaya za’ayi na auri Ahmad?

     Wani bari ne nazuciyarta yace Mata baki da wani zabi illah ki aure shi din…..

       Tsintan kanta tayi tana zubar da hawaye in aure shi?, Ahmad ne zai zamo mijina??, Ta yaya zan fara kallon sa amtsayin mijina?, Haba dai abun ko tsari babu, ni inzama mallakin sa karkashin ikon sa, ai sai rainin da yayi min ya Kara gaba, nibazan iya auren Ahmad ba gaskiya bazan iya masa kallon miji ba”😔😔

      ****************

   Ahmad kamar akwai mgn abakin ka”

     Sunkuyar dakai yayi sosai sannan yace”

    Eh Daddy daman Ina son ne muyi wata mgn”

  Murmushi Daddy yayi sannan ya aje wayoyin sa ya zubawa Ahmad ido yace inajin ka?

      Daddy daman inason ingaya maka ne Ina son auren Khadija”

    Jimmm Daddy yayi sannan yace”

      Wacce Khadija??

      Khadija dai Daddy”

Kallon sa Daddy yayi sosai zuwa can ya dauke kansa yayin da Ahmad ya sunkuyar dakai gabansa na faduwa”

      Ajiyan zuciya Daddy yayi sannan ya dago ya kalli Ahmad yace”

     Toh bazance maka a’a ba, Amman ita yariyar dana turaka wajenta fah??

     Daddy ai bamu daidaita ba”

    Hmmm, Ahmad Ina sane sarai bakaje ba”

    Sunkuyar dakai yayi, yayin da Daddy yacigaba da cewa”

     Wato kaidai har yanzun hankalin ka na gurin Khadija ko?, Aida na dauka kuruciya ke damun ka da kake nuna kishin ta Ashe abun da gaskene tunda ai yanzun ka mallaki hankalin kanka”

    Kasa Dagowa Ahmad yayi ya kalli Daddy sannan ya gaza furta komai”

       Shikenan bazan hanakaba tunda haka kake so kuma kaiba yaro bane Amman kayi shawara da Maman ku ko?

         Kai ya girgiza”

    Dan haka Daddy ya dauko wayarsa ya Kira Hajjah nan danan ta bayyana”

      Ahmad ne yazomun da zancen yana son auren Khadija”

     Lumshe ido Hajjah tayi sannan ta budesu akan Ahmad tace”

     Khadija ko Fatima??

      Mmn Yazeed

3 comments

  1. Pingback: th168
  2. Pingback: SEO in Las Vegas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *