Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 22

Posted by

WATA FITSARA PAGE 22

 

Advertisements

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamɗo

Page 22

Advertisements

Mikewa yayi ya fice yana waiwayen Fatima”

      Bayan fitansa ma hawaye taita sharewa cikin sigar rarrashi Hajjah tace”

       Fatima bazakibar kukan haka ba, saikace an kaiki bakon waje? Nine baki sani ba ko Uncle din naki ne baki sani ba?

Advertisements

     Kawar dakai tayi tare da share hawaye, yayin da Hajjah tacigaba da cewa yauwa kibar kukan haka, mikewa tayi ta kama hannunta tare da fadin”

    Muje ki kwanta”

       Kan gadon Hajjah ta kwanta yayin da Hajja ta rufeta da bargo, toh yanzun me zakici???

     Banajin yinwa”

    Ai dole zakici abinci dan allura za’a miki, ficewa Hajjah tayi batare data saurareta ba zuwa can ta dawo ta zaunar da ita sannan ta aje Mata abinci tare da fadin kici koba yawa kema saikiji kwarin jikin ki”

       Ahankali ta fara cin abincin kadan taci ta kwanta yayin da Hajjah ta gyara wajen”

      Ana ida sallar mangariba Ahmad ya shigo ganin shigowan shi gaban Samha ya fadi sosai, cikin sauri ta runtse idonta”

       Tsaye yayi akanta tsayon minti 5 yana kallonta, sannan ya ajiye ledan hannun sa agefen gadon ya shiga shirya allurar”

      Duk abun da yake tana jinsa yayin da faduwan gabanta ke dada karuwa”

      Malama tashi idonki biyu”

     Cikin kausasarsiyar muryan sa yayi mgnr dan haka ta rikice ta rasa abun yi”

     Kinajina ai, ya sake fadi yana zubawa ilahirin jikinta ido”

     Idonta arufe tace ni bacci nake yi”

        Hmmm kin manta kinyi alkawari ko”

      Bude idonta tayi akansa aini naji sauki yanzun ma nagama cin abinci”

    Hannunsa yakai ya taba wuyanta Har yanzun jikin ki da zafi Fatima”

      Bayan hannunta ta nuna masa nan gurin zaka taba”

    Kallon rainin wayau yai Mata sannan ya taba gurin data nuna yace eh lallai kinji sauki toh kwanta abun ki”

     Juyawa tayi tana me sauke ajiyan zuciya”

     Ahmad kuwa zama yayi kujerar dake kallon gadon ya daura kafarsa daya Kan daya sannan ya zubawa duk wani motsinta ido”

      Daga can ya kula da yadda take sauke numfashi ya tabbatar bacci ya dauketa sannan ya mike”

      Ahankali ya yaye bargon kayan nan dai da Abba ya kawota dasu sune dai ajikinta ”
Zagayawa yayi ta bayanta ya zauna ahankali ya bude zip din siket din sannan ya zubawa girin ido ganin yadda ya zauna das a kugunta, sosai yanayin ya burgesa ya dade ahaka zuwa can ya sake saka hannunsa ya  dan zame sannan ya saita allufar sa ajikinta”

      Jin shigan abun jikinta tai saurin kawo hannunta ta rike nasa yayin da yake kokarin zare allurar ta fasa ihu, tare da kiran Abbanta”

      Daya hannunsa yasa yana liliya mata yayinda daya hannunsa ke rike cikin nata har yanzun batabar Kiran Abbanta ba”

    Ya isa haka malama ki rufe min baki”

      Kara kaucewa take cikin kokarin guduwa tunaninta yanzun ne za’ayi allurar”

     Ganin haka Ahmad yace sakeni ai nagama”

      Sakinsa tayi tare da Mamakin akan fuskanta”

   Kallo yabita dashi, ashema ke raguwa ce”

     Niba raguwa bace ba Aidan ban shirya bane”

     Ko?

    Sakowa tayi ta gyara siket dinta sannan ta nufi gadon”

      Magani ya miko Mata tare da ruwa ungu kisha wannan”

       Yamutsa fuska tayi bana sha”

     Aikowa zan miki wata allurar amadadin maganin”

     Uncle gaskiya ka bari nifa ba’a taba min allura ba sai yau”

    Idan bakison allura kitashi kisha magani”

      Karba tayi badan ranta naso ba Tasha tana ya mutsa fuska, kofinta mika masa adaidai lokacin da wayarta ke Kara”

     Hannunsa ya mika ya dau wayar, Sweet mom yagani akan wayar, ahankali ya lumshe ido sannan ya sake budewa”

     Nan danan tanayin fuskan sa ya sauya, batare daya kalletaba ya mika Mata wayar sannan ya zauna agefen gadon”

    Na’am Umma?

     Lumshe ido Ahmad yayi sannan ya Kara baza kunnen sa”

    Ni Ina gidan Hajjah”

    Jimmm yaji tayi sannan yaga ta fara share hawaye tana fadin, shima yana nan”

     Dagowa yayi ya kalleta sannan ya kawar da kansa can gefe”

      Daga nan besakejin tayi magana ba saidai eh ko a’a, zuwa can ta aje wayar”

     Kallonta yayi yaga ta rufe ido, ajiyan zuciya yayi bayan yagama kare Mata kallo”

    Ya dade agurin har 11:00 ta buga cikin dibara ya dauki wayar yasa a aljihunsa, yabar dakin”

      Dakinsa ya koma yayi wanka yayi Shirin kwanciya, ahankali ya nufi gadonsa yana me tuna Fatima cikin ransa, afili yace”

    Ya kamata ace Fatima nakan gadon nan adaidai wannan lokacin😬, nagaji da kwana ni daya, ko bazata min komai ba inji motsinta kusa dani………

    Karan wayar Samha ce ta dakatar dashi, Khadija ce ya fada afili gyara kwanciyarsa yayi ya kwanta sosai sannan ya dauki wayar”

       Samha??

   Abun dayaji Khadija ta fada kenan, lumshe idonsa yayi ya bude sannan yace, Samha tayi bacci”

     Jimmm Khadija tayi sannan ta kashe wayar batare datace komai ba”

    Murmushi Ahmad yayi tare da kashe wayar baki daya”

         ***********

Itako Khadija daren yau bata iya runtsawa ba, gaba daya rasa abun dake Mata Dadi tayi, kawai Dan yanzun tasan makiyanta guda biyu ne Ahmad da Usman”

            **********

  Washegari da safe Samha ta tashi jikinta yayi sauki sosai, kuma hankalinta ya kwanta ganinta gidan Hajjah, sannan taga Uncle Ahmad din ma bewani dau abun da zafi ba, ganin inda Kai tsaye ya kawota gidan Hajjah sannan yace bakomai ya janye zancen auren, shidin Uncle dinta ne, wannan kawai ta tuna saitaji ta kara nutsuwa sosai”

    Sosai take son Uncle Ahmad ko ayanzun komai nasa birgeta yake amman batason alaka irinta aure ya shiga tsakanin su tunda yace yana son Mamanta, wani sabon baccin raine yake samun ta da zaran ta nuna wannan zancen”

      Wanka Samha tayi ta gama shiryawa tsaf sannan ta waiga ta kalli Hajjah tace”

    Hajjah wanni kayan zan saka??”

     Au hakane fah🤔, kamar kuma be dauko miki ba”

     Nufar kodar tayi barin je in tambayo shi”

    Anya kuwa yanzun ya tashi, Amman jeki duba”

     Daga ita sai towel ta nufi kofar”

    Murmushi Hajjah tayi, afili tace”

    Fatima ba wayau kina gudun nasa kuma zakije masa ahaka”

      **********

Dishi dashi yake kallonta, Uncle!! Uncle!!! ka dauko min kayana??

    Ware idonsa yayi akanta daga Sama har kasa yake kallonta, sosai yanayin ya burgesa, kasa cewa komai yayi sai yunkurin tashi yayi ya zauna”

       Cikin yanayi irin na me bacci yace”

     Ahaka kika fito??, Zo, hau ki zauna

     Ba musu ta dare gadon  ta zauna tsakiya tana me gyara daurin towel dinta”

      Murmushi yayi bayan hango duk cikinta lokacin datake gyarawa, yayin da dukiyarta suka bayyana gareshi”

     Zama tayi Uncle nayi wanka fah wani kayan zan saka”

     Mikewa yayi ya bude akwatinsa tare da fadin zoki dauka”

     Sakkowa tayi kamar ba itace jiya take koke koke ba, kodata iso kusa dashi saidata guma gyara daurin towel dinta sanan ta dauki kayan ta juya tana kokarin fita”

       Zo ya fada ahankali, tsayawa tayi tare da juyowa tana kallonsa”

   Kisa kayan anan mana”

        Tabbb, a’a

  Murmushi yayi sannan yace”

   Shikenan jeki”

      Hartakai kofar ya sake cewa,  zo”

       Kafa tafara bugawa cikin kukan shagwaba tana fadin Kai Uncle”

     Kallo yabita dashi sannan yace”

      Karki sake fitowa falo ahaka kinji ko”

     Jikinta ta kalla sannan tace toh, juyawa tayi tabarshi tsaye yana kallonta”

     Ajiyan zuciya yayi bayan fitansa, duk inda yakai da kawar dakai Saida ransa ya biya”

     Bakin gadon ya koma ya zauna yana tunu abun da idonsa yagane masa ayau yayin da hakan ke Kara masa damuwa dan haka ya shiga kokarin share abun acikin zuciyarsa”

        Wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya, yana kokari fita Kiran Khadija ya sake shigowa wayar Samha”

      Dauka yayi yayindata Kira sunanta kamar jiya”

     Gyaran Murya yayi sannan yace tana wanka”

      Sosai ran Khadija ya bacci kashe wayar tayi tana fadin”

       Mezanwa Ahmad ne in huce wannan takaicin dayake kunsa min”

           Tundaga ranar take fargaban Kiran Samha gudun kar Ahmad ya dauki wayar, sannan itama Samha Bata kirata ba har suka kwashe shayon sati biyu ko motsin Ahmad bataji dan ko acikin gidan suna mgnr rabonsa da zuwa tun ranar daurin auren”

        Bangaren Samha da Ahmad kuwa ayanzun ta saki jikinta ganinta zaune gidan hajja kuma baya neman komai wajenta, ko abinci dakin hajjah yake ci, wani zubin dasafe ma basa haduwa dan sanda yake fita office ko tashi ma batayi ba, sai da Yamma shima daya dawo wanka yake su fita tare da Galadima sai bayan isha’i yake zama adanyin hira dashi cikin kowa da kowa har Daddy, so da yawa ma shi yake fara tashi ya musu sallama hakan yasa ta saki jikinta fiye da da, cikin sati biyun nan sun shaku da Hajjah sosai, yadda take bawa Abbanta dariya haka Hajja ke yawan dariya akan wasu lbrn datake bata”

     Kwanciyar hankalin data samu yasa bata damuwa da wayarta da yawancin lukuta take hannun Ahmad daman masu kiranta daga Abbanta sai Mamanta sai kuma Mommy dan haka bata wani damu da wayar ba ayanzun”

        *************

    Yauma kamar kullum Ahmad ne ya dawo da dadde bayan angama hira ya mike ya kalli Hajjah yace”

         Gobe Fatima zata fara zuwa makaranta”

    Masha Allah ka kyauta kuwa”

      Kallonsa Fatima tayi fuskanta dauke da murmushi tace”

      Nagode Uncle”

    Juyawa yayi yana fadin kizo ki amsa kayan makarantar”

    Mikewa tayi atake tabi bayansa, daganin kayan  ta tabbatarwa Kanta canza Mata makaranta yayi, saidai tulin takardun data gani ya tabbatar Mata har yanzun dai ita  din ‘yar gata ce komai nazuwa makaranta ya tanadeshi, kuma me inganci, daga can gefe ta hangi kayan zaki irin nata wadda yasan tafi so kwali kwali, har da wadda ko Abbanta baya saya Mata, farin ciki sosai ya kamata, sunbatan sa tayi batare da ta shirya ba, sosai abun yaiwa Ahmad dadi yayin daya tsareta da ido”

           Ta dade adakin sannan ta fita bayan ta dauki duk abun da zata bukata Dan zuwa makaranta”

     Sakin Baki Hajjah’ tayi bayan ta zazzage mata kayan data dura cikin jakar makarnta ganin kayan zaki birjik”

     Cikin tsananin Mamaki Hajjah tace lallai Ahmad, da hankalin sa ya jido miki kayan zaki tattarawa tayi ta kwashe sannan ta maida takardun”

     Sosai Samha ta kulle, gado kawai ta nufa ta kwanta tana matso kwallah”

         Washegari misalin 7 Samha ta gama shirinta Ahmad kawai take jira

    Sai 7:30am ya shigo cikin shirinsa na zuwa Office, Hajjah ya gaida sannan ya kalli Samha yace”

        Meya faru?

     Tarkacen kayan zakin daka jido Mata na kwashe, tun dare take fushin ai, Kai yanzun sabo da Allah saikace bakasan illar da zai iya Mata ba, sai wata yayi aita kumur su”

    Kansa ya shafa  tundaga farko zuwa keya, sannan yace mancewa nayi kwata kwata”

       Toh kadai dinga kula”

    Insha Allah ya fada sannan ya kalli Khadija dake zunburar baki yace Muje ko”

    Mikewa tayi batare datace kalaba tabi bayansa, tsayawa yayi ta shiga gaba sannan suka fita”

        Bayan sun dau ahanya sosai ya kalleta yace”

     Ya isa haka, zan saya miki wani abun idan munje can”

          Ni kudin zaka bani in saya dakaina”

      Shikenan yafada idonsa akan hanya”

      Bayan yakaita makarantar ya wuce Office cikin gududu Dan kadan ya rage ya makara”

              *********

Karfe 2 bakin gate din makarantar ta masa, daga can ta fito ita da wata tadan darata girma”

      Gaisar dashi yariyar tayi sannan Samha tashiga motar tana daga mata hannu”

     Bayan sun dau Hanya sosai yace har kinyi kawa ne??

        Kai!!😳 Matar aure ce fah”

    Cikin sauri yace au hakane ke kuma budurwa ce ko?

     Wani irin kallo tai masa sannan ta dauke kanta”

        Yaya sunanta taji ya fadi”

   Cikin kawar dakai tace”

    Aisha
Tukinsa yacigaba dayi batare daya sake cewa komai ba”

       Wani Babban Asibiti taga sun shiga tunkafin ya sakko motar ake gaidasa yayinda yake amsawa wasu, wasu kuma ya daga Kai kawai, muje ciki Zaki dan jirani akwai aikin dazan karasa”

       Suna shiga cikin ya nuna Mata gurin zama shikuma ya mike wata hanya tana kallon inda duk yawancin asibitin hankalin su ya dawo kansa, kallon sa taitayi har ya kule yayin data fara jiyo muryan Mata na fadin”

     Doctor Ahmad kenan, shidai kullum baya dariya mgn idan zaiyita kamar yaki ko ya taso da fada kamar uban ka”

        Juyawa tayi ta kallesu  Suma ma’aikatan asibitin ne da kayan aiki ajikin su da alam ‘yan Mata ne”

    Daya daga cikin su ce tace, kuma fah duk girman nan nasa gauro ne beda mata”

       Kai haba, halan sakin ta yayi? ai yana da bakin rai”

       A’a ance saurayi ne betaba aure ba”

     Cikin tsananin Mamaki tace betaba aure ba??

    Tambayan tayi adaidai lokacin da wata maikaciya ‘yar uwarsu ke isowa wajen”

      Waye betaba aure ba??

      Wai Doctor Ahmad Ina ance  betaba aure ba??

      Zauna nan, yayi aure kwanan nan, nima abakin Doctor Sani nake ji, kinsan shi yana sakewa ba irin Doctor Ahmad bane”

   Ciki tsananin Mamaki wadda kebada lbrn tace zanso naga matar sa, gaba daya baya mgn”

    Kice dai baya mgn dake amman yana mgn, kinsan muna haduwa a Office din Doctor Sani, matan ne dai baya mgn dasu, yanzun nan saiya rikita ki da tsawan shi me rugugi, Amman kunsan wani abun mamaki, yanzun kamar soyayya  yake da S Nuhu”

         S Nuhu ? Wacece haka??

     Wannan sabuwar yarinyar da aka kawo baya Kiran sunanta, Sweet heart yake kiranta…..

    Kiran sunanta da Ahamad yayi ya katse mata sauraron su, hannunsa ya mika Mata ta daura nata sannan suka nufi Office dinsa”

      Nan ma gurin zama ya nuna Mata sannan ya zagaya ya zauna atseburinsa wata yariya ce ta shigo tana tattara wasu takardu dake gabansa yayyin dayake rubutu kan wata takarda ya dago yace”

      Sweet heart kije ki amso min sako gurin Galadima kiyi sauri zan tafi ne”

   Cikin girmamawa yariyar ta amsa sannan ta fice”

     Binta da kallo Samha tayi Sweet heart, ta maimaita azuciyar ta sannan ta kalli Ahmad daya maida hankalinsa Kan rubutun da yake ko ajikin sa”

        *********

    Akan hanyarsu ta komawa gida babu abun da Samha take yawan tunawa sai hiran nan dataji anayi akan Ahmad tare da tuna sunan Sweet heart da Ahmad ke Kiran wata dashi, hakanan taji Bata da walwala sosai”

     Tunawa tayi da kalmar Khadija da take ce mata yace ne yana sona kawai dan naki amincewa yake neman tozartani”

   Juyawa tayi ta kallesa sosai ya bata haushi, yanzun hakan ma ba ita kadai bace, ‘yan mata gareshi birjik, har yana kiran su da Sweet heart

     Juyawa tayi ta kalleshi tace Uncle?

    Juyowa yayi kadan na’am yaya akayi”

      Daman ce maka zanyi idan na tashi aure bazan aure Babba ba dan yaro zan aura”

     Tsayawa yayi cak yana kallonta sannan yace”

      Abun da aka koya miki kenan yau amakarantar??

      Tsareshi tayi da ido tare da fadin a’a kawai dai na sani ne”

   Tsaki yaja, sannan yace kinsan me??, Jin tayi shiru yace ki aure yaron goye ma idan kina iyawa”

      Jimmm tayi batare da ta kallesa ba tace”

     Yaron goye kuma me yake dashi?😏

      Cikin sauri ya waigo ya kalleta, bazakace daga bakinta zancen ya fitoba, Fatima baki da kunya ko??

   Juyowa tayi ta kallesa, ton Uncle bakaine kace na auri na goye ba, nikuma nace me yake dashi?

    Ok amsa kike son nabaki kenan??

         Kawar dakai tayi ni banceba kawai dai nafada ne”

          Shiru sukayi yayin da yake tunaninta cikin ransa, tare dajin haushin kalmarta zuwa can yaji tace”

   Uncle?

   Na’am Fatima

Dakace na auri na goye, daman ana auren nagoye ne??

     Jimmm, ya yi karo na biyu sanan yace nasani ko akan ki za’a fara??, Tun da kema ai kadan ne banbancin ki dana goye”

   Tabbb wlh a’a Uncle kaine kake ganin haka”

      Kallo ya bita dashi cikin tunanin kalaminta sannan yace, ya zanyi na tabbatar da haka??

     Kawar dakai tayi kabari nayi aure kaga ikon Allah”

     Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace, nikuma nawa auren Ina kika aje min shi??

     Turo baki tayi aini mungama mgn dakai kuma kace ka yadda Uncle nake dakai”

    Jimmm yayi sannan yace Amman taya zansan ke jaruma ce bayan ba’a gwada ba”

     Toh ai cewa nayi kabari nayi aure kagani”

    Me zangani??, Bayan kina gidan wani lokacin?, Indai kinason na tabbatar da jarumtar ki kisameni agadona anjima”

      Nidai Uncle ka bari, kuma wlh dandai kaine kawai”

    Kallonta yayi sosai sannan yace”

     Ina ganin jarunta acikin idonki amman zuciyata taki yadda da haka saina gani zahiran”

      Hmmm kawai tace yayin da suka isa gida ta fice tabarshi amotar”

      Zama yayi cikin motar yana kallonta harta shiga gida, afili yace nan gaba Fatima fitsara zatayi daganinta, da alama duk sanda nace kule zatace min casss ita sam ba irin Khadija bace inda Fatima ce nake yanko mata zance da alama amsa zata bani ba kunya, dariya yayi sannan ya sake cewa, aini da ajiye kalamaina nayi saita Kara girma Amman na kula dasu ne kadai zan samu na shawo kanta”

      Sakkowa yayi ya nufi gidan bayan yayi wanka ya nufi gidan Su Khadija karon farko tun ranar daurin auren su”

       Da ita ya fara cin karo zata fita dakin Inna Yalwa tana ganinsa ta hade rai yayin dayai saurin kwaucewa ya bata hanya”

    Wuceshi tayi yayin daya bita da kallo, bayan yaga shiganta dakinta ya shiga ciki ya gaida Inna”

      Ya dade suna hira da Inna yayin da yawancin hiran duk akan Samha ne anan yake sanar masu ta fara zuwa makaranta”

     Bayan fitowansa dakin Inna Tsintan kansa yayi dason zuwa gurin Khadija domin yasaba da ita sosai bana wasa ba so da yawa tare suke shawara”

      Sallama gayi bakin kofar har sau uku ba’a amsa ba, tabbatarwan da yayi tanajinsa yashi shiga cikin dakin”

     Kujeran dake kallon gadonta ya zauna, kinaji Ina sallama ki kasa amsa min?

     Lumshe ido Khadija tayi sannan tace”

    Amman Kai cikakken mara kunya ne, ai ban zaci zaka iya takowa kazauna anan gurin ba??

     Sunkuyar dakai yayi me zai hanani zama alhalin kina ‘yar uwata?

       Hmmm dadai banso nayi mgn ko guda dakai ba, Amman kasani dole sainayi, abun da zan gaya maka tunda ka samu abun da kake so kafita daga idona na rufe😎😎 niba tsarar ka bace ba, karka Kara dauko gutun rashin kunyarka kazo min nan alakar da kake fada ta ‘yan uwanta banyinta, sanin kanka ne nafi karfin gutun rashin kunyan ka wlh zanci maka mutunci Ahmad duk ranar daka sake min mgn”

     Jimmm yayi yana sauraronta fuskan sa asake bayan tagama yace”

     Niba wata mgn ya kawo ni ba Allah ya baki hakuri, kawai daman zan gaya mike ne Samha ta fara zuwa makaranta dan ki saki ranki……

     Kaida Samhar duk kunci ubanku, nina Gaya maka raina arike yake yake ne?

    Murmushi yayi sannan ya mike yana fadin, mungode

     Haka ya fito gidan ransa babu Dadi”

       *******

Misalin 9 nadare Ahmad kwance akan gadonsa mgnr su da Samha nai yaita dawo masa wadda sukayi da rana, murmushi yayi sannan dauko wayar sa yana Kiran dayinta”

        Bugu biyu ta dauka cikin siririyar muryansa yace”

     Yariyana yunwa nake ji sosai, ki amsa abinci wajen Hajjah ki kawo min yanzun”

     Jimmm tayi zuwa can tace tam Uncle”

      Sauke wayar yayi tare da tsara kalaman dazai jawo ra’ayin ta dasu…….

    Mmn Yazeed

4 comments

  1. Pingback: Timothy
  2. Pingback: pg168

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *