Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 27

Posted by

WATA FITSARA PAGE 27

 

Advertisements

WATA FITSARA

By
Fadeela Lamido

Page 27

Advertisements

Galadima ne ya kalli Ahmad yace kamar ana ana bugawa ko??

Daya abokin nasu Sa’ed dake zaune kusa da Galadima ne yace eh”

Ahmad dake kishingide asama ne ya daga murya sannan yace Koma waye ya shigo”

Advertisements

Ahankali tasa hannunta ta bude kofar ta shigo tare da rangada sallama cikin ‘yar siriyar muryanta”

Lumshe ido Ahmad yayi dalilin tabbatarwa da yayi Samha ce”

Gaba dayansu baza ido sukayi aka ahanyar yayin da abokansa suke son sanin wacece, yayin Ahmad kesan sanin dadilin fitowanta acikin wannan Daren”

Hada ido sukayi da Galadima daga tsaye tace Ina wuni??

Lafiya lau Samha kece??

Ganin Ahmad din kwance akasa ta zame ta zauna akasa saitin kafarsa sannan tashiga kaida dayan abokin nasu”

Cikin sakin fuska ya amsa tare da kureta da ido yana son sanin wacece ita”

Uncle Ina wuni?

Yana kallon ta ta gefen ido yace”

Lafiya lau, yaya kike, ya kwana rututu???

Lafiya lau, shine ka daina zuwa ko gaida Hajjah baka zuwa??

Eh, ko kinga laifina??, Nayi hakan ne dan hankalin mutum ya kwanta, yanzun daga Ina kike?, wace miki ki fito a wannan daren??

Ni ai Hajjah ce tace, kuma ni daga Gida nake ai”

Amman mena gaya miki akan fitowan ki??

Nifa Uncle Ahmad tun lokacin fah banje ko Ina ba daga makaranta babu inda naje😔

Au kuka Zaki min??

Ganin inda Samha ta fara Shirin matso hawaye Galadima ya fara dariya yayin da Sa’ed yace”

Wacece wannan Wai??

Cikin son bagarar da zancen yace”

‘yata ce”

‘yarka??

Eh, Ina nufin yariyar Kanwata ce”

Dariya Sa’ed da Galadima suka kwashe dashi, Galadima Jin Ahmad yace yariyar kanwar sa ce yasashi dariya shikuwa Sa’ed bayan ya tsaya da dariyar yace??

Gaskiya yakamata kai Aure Ahmad, Anya ma kuwa kana da kanwar data isa ta haifi yariyar nan?

Tashi Ahmad yayi zaune ya kalli Sa’ed yace kana tantama ne??, Amman ai kana da labarin Khadija ko??

Eh nasan Khadija, koba Khadija taka ba??

Ita fah, toh ‘yarta ce wannan”

Iyeeee, Masha Allah, abun ba wuya, Amman Khadija ta iya haihuwa, yariyar nada kyau sosai”

Itako Samha tuni ta turbune fuska hawaye ne yake shirin zobo mata, cikin sauri ta mike ta nufi kofa yayin da Ahmad yabita da kallo”

Idan na fahimceta sunan Khadija dana sakko azancen yabata haushi, murmushi yayi sannan yace”

Ina zaki???

Nina tafi gida??

Zo, ai baki fada min abun daya kawoki ba”

Batare data juyo ba tace”

Aina fasa”

Kizo nace ko, karki fita, ganin bata da niyar tsayawa ya mike yabita harta fice ya fisgi hannunta”

Cikin zaro Mata ido yace”

Ina miki mgn kina tafiya? zakimin rashin mutuncin naki ne gaban mutane???

Hawaye ne suka fara zubo Mata, sosaiya kula ranta yabaci wannan kukan yana da banbanci da nabaya da takeyi domin wannan karon sai ajiyan zuciya take tare da hadiyan yawo”

Meya faru Gaya min kinji”

Bakai bane kakecewa abokanka wani Wai Ummata kanwar ka, kanwar ka, har lbrnta kake basu, kana waini Wai Khadija Khadija😫😫

Shiru yayi yana kallonta zuwa can yace”

Har so nawa zan gaya miki kidaina shiga zancena da Khadija, me kike nufi?, Zaki hanani kiran sunanta ne ne?, Tun Kan kizo duniya muke tare da ita”

Runtse Ido ta tayi, da sauri tare da fadin, kabar Kiran wannan sunan banaso

Jimmm Yayi, tare da shafa kansa tundaga farko har keya sannan yace, shikenan naji nabari”

Jin Bata da niyyar yin mgn kuma taki ta bude idon yace”

Ki bude idon naki nace nabari ai”

Budewa tayi tare da kallon can gefe”

Kallo yake binta dashi, zuwa can yai murmushi yace”

Kenan kin haramta min Kiran sunanta???🤔

Cikin kawar dakai tace toh ai ba sa’ar bace”

Murmushi yayi yana kallon cikin idon Samha yace”

Fatima ninafa girmeta, wata uku cur na bata🤔🤔

Juyawa tayi tana kokarin wucewa, ya sake roko hannunta, shikenan bazan karaba, Allah ya huci zuciyarki, idan na fahimceki kina son mahaifiyarki kuma kina girmamata, saidai abun Dana kasa ganewa har yanzun ni awanni matsayin kika ajeni?,

Banza tayi dashi tare da Kara turo bakinta

Ina jinki Fatima, wanne kikeyi dani?,

Hannunsa ya zuba a aljihun sa, bazakice min komai ba?, Wanne kike yi Dani fatima, indai uba kikeyi dani to ki canza hali dan yanzun bakya girmamani kamar dah, idan kuma miji kike dani to na yaddah”

Kara karfin kukanta tayi, ni Uncle kabarmin irin wannan mgnr, kuma kabar kiran sunan Ummata😭

Ganin inda take kuka yasashi kallonta sosai

Hawaye ya fara share mata, wannan karon sosai yadda ta nuna baccin rai ya shige sa babu zancen wasa ko zolaya yaita Lallashin ta har ransa yakejin kukanta, sannan yace, toh muje ciki ki gaya min”

A’a ni sauri nakeyi driver na jirana”

Sai alocin ya waiga ya hangi driver gidan Hajjah sannan ya juyo yace”

Barin sallameshi zan maidaki dakaina”

A’a tare zamu tafi”

Shikenan naji, muje ciki ai yasan tare zaku tafi, ba inda zaije”

Juyawa sukayi tana gaba yana binta abaya har suka shiga falon”

Shiga gabanta yayi yana fadin taho zo muje, afalo suka wuce su Galadima suka shiga dakin baccin Ahmad”

Wani kwawatattcen daki suka shiga da ita, ko ranar da Abba ya kawota iyakarta falon, dan haka yanzun taga wajen yai Mata masifar kyau”

Bakin gadon dayasha gyara ya zauna yayin da Samha ta tsaya tsaye zoki zauna ki gaya min”

Zama tayi sannan ta shiga wasa da hannunta”

Ina jinki??

Uncle ni kudi zaka bani”

Hade fuska yayi sosai, sannan yace”

Kudi zan baki kamar yaya??

Toh Uncle ko kudin makaranta ta yanzun ai sunyi yawa, kafa jima baka ban ba, Abbana a acct dina yake samin idan yayi tafiya dan haka ko yana gari bana neman kudi”

Cikin dariya yace”

Sosai,🤔 aikin me kike min da zan dinga samiki kudi Fatima??, Bawanki ne ni?, Ko angaya miki haka ake yi?, Kince bakya sona kuma kidinga karbemin ‘yan kudi?, kinki zama tare dani, bare ko adawo lafiya ki dinga min haka kawai ba sidi ba sadada sai naje nayo wahala na tura miki, waima tsaya Hajjah Bata baki kudin makarantar ne har da kika tara min bashi haka?🤔

500 fah take bani”

Toh Ina laifi??, Ko yai miki kadan??

Nidai Uncle yanzu ba wannan ba, kawatace zatai aure, jibi zamu fara biki, kuma bani da kudin anko shine Hajjah tace in Gaya maka”

Shiru yayi na tsayon wani lokaci zuwa can yace”

Harnawa ne kudin??

Kala 5 ne Uncle”

Kudin su na tambaya ai”

Kunnesa ya baza yana jiran yaji ta zabgo masa kudi Amman abun Mamaki sai yaji tace”

Gaba daya 5k ne, amman ko na kala 3 kabani idan kudin sunyi yawa”

Ashe kina da sauran hankali, ya fada yana kare Mata kallo sannan yace”

Zan saya miki, Amman Ina da sharadi, kinga nafarko ni zan sawo dakaina dan bazan baki kudi kitafi kina yawace yawace atiti ba, sannan kince jibi zaku fara biki idan na fahimci ke kwana 5 zakuyi kuna bikin ko?

Kaita daga, cikin sauri ya girgiza kansa, bazan yadda da wannan ba Fatima acikin kwanakin ki dauki biyu ko uku wadda suke da Mahimmanci aciki sannan sharadi na gaba ni zan kaiki awa daya zuwa biyu zan dawo in dauke ki, idan baki yadda da sharedina ba saidai abar zuwa bikin daman ba’a kawo min goron kayyatar ki ba”

Shiru tayi yayin da idonta ya cika da hawaye zuwa can tace”

Goron biki kuma har kaima sai an bawa??

Kawar dakai yayi ina nufin ba’asanar dani bikin da wuri ba, dan haka Ina iya hanawa

Cikin rashin Jin dadi tace” Na yadda”

Toh yanzun ta wacce hanyar za’abi asai ankon??

Kabani kudin saina Kai Mata, ita zata sawo min gobe”

Bata da acct ne?

Bazata rasa ba”

Toh me zai hana tabaki acct dinta saina aika Mata”

Uncle bani dai nakai mata, ai bani da waya”

Jimmm yayi sannan yace haka ne, idan kina da number ga wayarta kiyi amfani da ita”

Amsawa tayi da saurinta cikin nutsuwa ta daura number Zainab bayan ta dauka suka gaisa sannan ta gaya Mata abun da take bukata”

Cikin kankanin lokacin Zainab ta turo da acct number ta, sannan ta mika masa, gashi ta turo, amsa wayar yayi yaita ‘yan danne dane danen sa, sannan ya dago ya kalleta yace natura harda gudummawan ki”

Cikin sauri tadago ta kalleshi sosai ya birgeta har Bata iya kwatanta yadda taji cikin siririyar muryanta tace nagode Uncle…….

Kafin yace komai Kiran Zainab ya shigo cikin wayar sa, yagane number dan haka ya mika mata yana fadin kisanar mata gobe mijin ki zaizo…..

Kara wayar tayi akunnenta daga can cikin wayar Zainab tace”

Fatima 100K nagani fah?

Jimmm, tayi cikin rasa abun cewa gaban Ahmad, daker ta iya cewa eh sauran gudummawa tace”

Iyeee lallai🤔 toh nagode, gobe karfe nawa zakizo amsan kayan??

Ke Zaki fada, kuma Uncle dinane zaizo ya amsa bani ba”

Kash😬😬 dan Allah kizo da kanki mana kawata”

Zainab agida baza a banni ba, jibi zanzoda wuri”

Shikenan Allah ya kaimu, nagode”

Sauke wayar tayi ta mikawa Uncle, hadewa yayi da hannunta ya murza, yayin da Samha ta lumshe idonta ta zame hannunta, kadan ta wun Kura ta sumbaci kumatun sa

Murmushi yayi sosai ta burgeshi, cikin siririyar muryan da besan yana da itaba yace”

Bakijin kewata tsayon lokaci baki ganni ba??

Mikewa tayi Uncle dare fa yayi zan wuce”

Baki bani amsa ba”

Kawar dakai tayi ta kalli gadon duk cikin kaucewa zancen sa sannan tace”

Uncle kanajin dadin ka, ji wannan gadon idan na kwanta akai ai saina makara”

Dariya yayi toh kizo muji dadin tare mana”

🙄 Nagudu ban tsiraba da fada azuciyarta afili kuma tace Uncle Banga wajena ba anan wajen”

Kidai duba dakyau Fatima”

Allah Uncle babu gurina anan”

Toh ai shikenan, har yanzun kina Kan bakar ki kenan, yanzun gaya min, kinyi kewata ko bakiyi ba??

Cikin yanayi irin nashagwaba tace”

Idan kayi kewata Nima nayi naka”

Lumshe ido yayi sannan yace Masha Allah, Allah yasa nan gaba inji kalmomin dasukafi haka sanyi daga bakin ki, mikewa yayi yace Muje”

Sun samu Har yanzun Galadima da Sa’ed suna hira fitowan su yasa su maido da hankalin su garesu”

Samha ce tace Saida safen ku”

Cikin zolaya Galadima yace”

Au Fatima tafiya zakiyi?, nina dauka kwanan gida kikazo….

Meye kwanan gida??

Dariya Ahmad yayi, yana fadin”

Yauwa bata gane ba ka warware Mata

Shima galadima murmushi yayi tare da dafe kansa🤦🏻‍♂️ sannan yace ai nayi shiru”

Kallon Fatima yayi data zubawa Galadima ido tana jiran Jin amsa yace muje rabu dashi”

Bayan kankanin lokaci Ahmad ya dawo yana dariya har yanzun yace, ita fa Fatima ko wacce irin mgn kamata saita baka amsa daidai da zanceka”

Wani irin kallo Sa’ed yaita musu sannan yace nifa bangane ba, Wai soyayya kake da ‘yar taka ne?, Naga abun ne anayin sa kamar soyayya soyayya cikin salon rigima rigima, kai akwai tsantsar soyayyar junan ku acikin idon ku gaba dayan ku

Komawa Ahmad yayi inda ya tashi yana fadin”

Yariya tace”

Eh aini abun da bangane ba yanzun shine da Khadija kakeyi koda wannan yariyar”

Sunanta Fatima, Galadima bashi lbrn Fatima”

Dauke Kai Galadima yayi yana fadin’

Waka abakin me ita tafi dadi”

Murmushi Ahmad yayi sannan yace”

Barin gayama ataikaice, matata ce”

Wannan yariyar?

Eh”

Amman yaya akayi haka ta faru??

Hukuncin ubangiji ne, nabarwa kaina haka Allah ya tsara, kuma ayazon naji dadin rasa Khadija da nayi, tunda gashi ta dalilin rasata Nasamu Fatima, da ace nasamu Khadija daban samu Fatima ba, kuma yanzun ne zuciyata ta nutsu, soyayyar Fatima na ratsani

Wai da gaske kake ko wasa, yanzun yariyar nan matarka ce??

Wlh babu mgnr wasa andaura mana aure nida ita matata ce”

Runtse ido Sa’ed yayi zuwa can ya bude tare da fadin”

Cuttt😬 bani lbr, Ina Khadija? yaya Khadija tayi?

Murmushi Ahmad yayi bayan ya auno fuskan Khadija sannan yace tana nan tana ta fushi dani haushina takeji sosai ko mgn batai dani, nasaba mgn da Khadija sosai hakan yana damuna”

Kusan wata 8 da auren mu Amman abun yaki wucewa agurinta, in takaice maka mgn kaga wannan rigimar da Fatima keyi Ina zargin itace ta daurata ahanya, gaba daya bana Jin dadi wannan yanayin inason ita ta canza min fuska yariyar kuma taki yadda dani”

Jimmm Sa’ed yayi zuwa can yace”

Gaskiya abun da kunya Amman kana iya hada da Khadija kuwa??

Ninama dade banganta ba, Me zai hanani hada ido da ita ? Bani da gaskiya ne?

Galadima ne yayi dariya tare da fadin haba wani kunya kuma, bayan tasan shi yasanta tun tale tale”

Duk da haka dai dole akwai wata kunya atsakani, kawai dai kace min yariya taki yadda dashi, shine mgn, da ace ta yadda dashi da tuni ya russunar dakai”

Dariya Ahmad da Galadima sukayi yayin da Ahmad yace”

Dan nashige Samha kuma sai naji kunyar Khadija?, Niba haka nake ba, tun muna yara muke da Khadija kunyarta name zanji”

Dalla gafara can malam ai aure ya kore komai, Khadija yanzun surukar kace, kuma Ina tabbatar maka dazaran wani abu ya shiga tsakanin ka da yariyar dole zakaji kunyar uwar”

Bazan jiba wlh, niba haka nake ba”

Hmmm Ahmad kenan muna nan dakai nasan ranar nanan zuwa wata rana zaka rakwafar kanka agabanta”

Tsaki Ahmad yaja Sa’ed karfa ka tunzurani, in aikata abun da bashikenan ba, nayi niyar inbar yariyar nan tagama nuku nukunta ta nemeni da kanta tun da nasan ita din ba dutse bace ba”

Galadima ne yace me kake nufi???

Kwafa yayi ya dauke kansa sannan yace”

Inason in nunawa Sa’ed ne, bakaji me yake fada ba wai wata rana zan russunar dakaina agaban Khadija, sabo da kawai ina auren diyarta”

Me zakayi toh Galadima ya fada cikin dariya sannan ya Kara da cewa kadai bi ahakali karka barkowa kanka aiki”

Tsaki Ahmad yaja, sannan yace, Allah ya kaimu jibi, Fatima tana da bikin kawarta zanyi amfani da ranar na nuna muku ainihin kalata…….

 

9 comments

  1. Pingback: dultogel promo
  2. Pingback: jebjeed888
  3. Pingback: go to my blog
  4. Pingback: Manforce
  5. Pingback: click Book of Ra

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *