Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 4

Posted by

WATA FITSARA PAGE 4

 

Advertisements

WATA FITSARA🤔

     By
Fadeela Lamido

                          Page 4

Advertisements

……..Runte ido Khadija tayi dalilin faduwa da gabanta yayi, kallo tabi yaron dashi ta kasa cewa komai, cikin sauri ta nufi dakin inna tana me sauke nurfar fashin tashin hankali”

    Yaya yayadai meya faru kuma Hadiza?

     Inna kinga wai harya Aiko daukanta”

Advertisements

      Yaunaga jaraba, Usman fa baida mutunci,🤔 kinga Hadiza kibashi ‘yarsa, wata rana zata nemeki, kwana nawa ne ma banda rashin hakuri irin naki”

     Inna nime nace? Ai shekaranta nawa be kawota ba bana data hankalina”

     Karya kike rannan Inna kallon ki kin tasa Ahmad gaba kamar kyace wayyo Allah, duk akan Fatima yaron nan yana kokari Hadiza idan baki gode masa ba ai bakya tsine masa ba, dame kike takama idan badashi ba, ya sai miki wancen yasai miki wancen, Amman saboda rashin adalci dakin bude baki kice bashi da kunya, bayan kece Babban marakunya, ki amshe masa ‘yan kudadensa…..

     Muryan yaron sukaji yanacewa”

    Salamu alaikum”

    Innace ta amsa tare da fadin waye nan”

      Wai yariyar Alhaji Usman nanan?

     Mikewa Inna tayi tana fadin, eh

       Wai ta fito driver ta ya dawo”

     Yayi uban me?

    Kash😬 a’a Inna, kallon yaron tayi tace jeka ganinan fitowa”

           Wayarta ta dauka tafara neman layin Ahamad har sau biyar Amman be dauka ba, tsaki taja sannan ta Kira wayar Hajjah bayan ta dauka hankalinta atashe tace”

       Hajjah Ahmad yazo?

    Eh sunzo shida Fatima nan sukaci abinci rana Amman sun fita tuni”

    Kash😬 Hajjah gashi kuma Babanta ya aiko daukan ta”

    Kash subuhallahi, dama bazata kwana bane?

    Eh Nima tunda naga bakazo ba, da kaya ba nasan bebarta kwanan bane Amman nazata sai yamma gashi ko la’asar bataiba ya aiko dan jaraba”

        Wani jarabar yake Nima Khadija, yanzun barin Kira Yaron”

     Hajjah nakira sa har sau 5 be dauka ba”

    Zan sake jarabawa shikuma driver nasa kice masa tatafi gaida kakannin ta tunda dole zasusan bata cikin gidan”

      Fita Khadija tayi bayan ta sauke wayar ido biyu sukayi da driver Alhaji Usman bata iya tuna ranonda ta gansa cikin girmamawa ya gaidata”

   Itama cike da sakin fuska ta amsa sannan tace”

    Ashe Abbanta ba wuni yabarta ba, bansan cewa yanzun aza’azo daukanta ba, saina turata ta gaida kakannin ta”

   Kansa ya dafe, hajiya gashi me gida saimin waya yake Dan daman awa biyu ya bata”

      Toh ai bata fadaba, yanzun yaya za’ayi”

     Shine ai, Amman megida zaiyi fada sosai, kuma dole zai sani”

     Waigen hanya Hadiza ketayi Amman wayam dan haka ta kule sosai da Ahmad”

       Yanzun kawai Amin kwatancen inda take zan daukota ko ki hadani da Yaro”

    Runtse ido tayi sannan tace ai ance antaho kawota Ina Jin sun biya wani gida…,

     Wayarsace tayi Kara cikin sauri ya dauka yana fadin”

     Ranka ya dade, katsesa akayi daga can bangare zuwa can yace”

      Allah ya huci zuciyarka gani tun dazon akofar gidan Amman wai ance tatafi gaida kakannin ta”

      Shiru yayi zuwa can yace”

    Hajiya ce gata ma tsaye, wayar ya ciro daga kunnen sa ya mika mata”

   Kallon wayar tayi sosai sannan tace bazan amsa ba idan ‘yarsace dai ya kwatar da hankalin sa baza’a cinyeta ba, juyawa tayi ta shige gida tare da share guntun hawaye cikin ranta take fadin da wannan zuwa na Samha gara babu, banji duminta ba banyi mgn da ita ba wannan wani irin masifa ce ace kaida danka, zaman kusan awa daya sukayi da Inna sunajira babu alamar Su, daga can taji dirar mota mikewa tayi tayo waje tana Baza ido”

        ************

   Fitowa yayi afusace ya nufota”

    Tsaye tayi gabanta na tsananta faduwa”

    Dafda ita ya tsaya rabon da yasata a ido shekara 6 tun daga ranar daya bata takadda, gani yayi duk ta koma masa yariyar sosai gabanta ya tsaya idonsa jawur yace”

      Ina ‘yata?, bana wasa dake Khadija, bana hada Ummee da kowa, idan ke bakisan ciwontaba nina sani, Ina kika tura min ita??

       Kawar dakai tayi can gefe sannan tace”

    Kakannin ta ta tafi gaidarwa?

     Amman kinsan bana barin ‘yata fita ita daya??

     Yanzun ma ba ita kadai baceba😏

    Kallo yabita dashi tsayon wani lokaci sannan yace”

      Me kike nufi?, Akwai abun da kika shirya Khadija karki raina min hankali, kifitomin da ‘yata idan ba hakaba zan miki wulakanci anan gurin”

    Nanawa kuma ai daman Kai wulakantaccene mara adalci wadda be damu da damuwar wani ba”

     Ai bayau kika saba min rashin kunyaba bazai zama bako awajena ba ‘yadai tawa ce kuma wlh dole ki bani”

     Tsaki tajah sannan ta juya ta shiga gida”

     Afusace yakoma motarsa ya zauna Ina me zubawa hanya ido tare da zuba huci”

    Misalin 5:30pm motar Ahmad ta faka akofar gidan  Khadija, ganin motoci kofar gidan har biyu yasashi dakatawa tare da zuba masu ido”

    Shima Alhaji Usman da saurinsa ya sauka yana kokarin tunkaro motar”

      😳😳😳 Wayyo uncle ga Abbana”

     Abban ki??

    Hangosa yayi yana tahowa Dan haka ya fara kokarin bude motar yayin da Samha tai saurin rike hannun sa”

     Uncle karka fita dan Allah , Babana yace ko mgn karnayi dakai”

     Jimmm yayi tare da gyara zamansa itakuma ta fara kokarin fita, dakatar da ita yayi ta wego”

     Kina nunfi duk abun da kika sani nasai miki nan Zaki barmin???

    Ganin Abban ta yana daf da karasowa idonta cike da kwallah tace”

    Ka boyemin wata rana zan dawo, fita tayi da saurinta ciken dakiya takewa Abbanta fara’a

    Ko kallonta beyi ba kokarin sa ya isa motar”

   Gaban motar ya tsaya saidai babu halin yaga wadda ke ciki kwankwasawa yayi yayin da Ahmad ya tsaya kyam kamar gunki zuciyarsa cike da baccin rai”

     Ganin bazai daina kwankwasa motar ba yaja motarsa yabar layin”

     Kwafa Alhaji Usman yayi sannan ya nufa Samha afusace”

     Wanne Dan iskan ne ya sauke ki ??, Ummee tukuicin da Zaki bani kenan??

    Idonta cike da hawaye tace, Abba driver ne akace ya kawoni gida”

    Mari ya kwasa mata ta dafe gurin, duk abun da ake Khajida tana labe daga zaure tana gani tare da share hawaye, janta yayi ya saka a mota”

     Saida Khadija taga wucewarsu sannan ta koma gida tana share hawaye, Inna ta sanarwa wa sun wuce sannan ta koma dakinta taci kukanta ta koshi”

       ***********
Zaune yake akasan dakin sa na gidan Hajjah, sayayyar daiyaiwa Samha ne zube agaban sa, kallon kayan kawai yake yana share hawayen dake zubo masa na gefen ido tare da hadiye wasu yawu masu zafi, cikin idonsa,  babu abun da yake gani sai yariyar, yadda taita nishadi tana dauka duk abun da ranta keso, gashi mahaukacin ubanta ya dauketa komai batasa abakin ta ba, duk da cewa yasan ko gidan Ubanta duk abun da take so shi take ci Amman yaso tasa wannan kayan abakin ta, sosai yakejin haushin daukanta da Usman yayi, kamar daga sama yaji mgnr Hajjah”

      Yaro, Nina rasa me kakeyi haka?, Ace tun yamman kazauna ka tasa kayan zaki ba, kaje sallah ma kuwa?

     Naje mana, yanzun na dawo”

    Idonsa ta kalla jawur da yadda yake mgn cike da haushi tace”

       Ahuce haka Yaro, ka daga hankalin ka, kaga yadda idon ka yayi jah ma kuwa”

     Haushina daya Hajjah banci ubanshi ba”

     A’a kadaibi ahankali Yaro, kasani ko wata rana yabaka Samha ka aura?

         Habadai Hajjah kintaba ganin mutum ya auri ‘yarsa?

     Sosaima kuwa Yaro, na nawa aka yi, ai irin wannan soyayyar tamafi dadi, yanzun bagashi duk hankalin ka ya tashiba har kuka fah kayi yau”

   Cikin sauri ya kalli Hajjah  haba Hajjah nidin inrasa akan wadda zanyi kuka sai Fatima??

    Baka cikin Hayyacinka, ka dawo Yaro, wannan ba wani abun bane Kai ranar ma ai kasa Khadija kuka”

      Ita taga daman yi Hajjah”

     Murmushi Hajjah tayi sannan tace toh ai shikenan tunda ka musamin amman nidai nahango wani abu”

    Fita tayi ta rufemasa kofar bayanta yabi da kallo sannan yace”

     Lallai Hajjah dama uwar kikace dayafi”

      Gado yahau ya kwanta sanyi yakeji sosai, lokaci daya zazzabi ya rufesa”

     Kwanasa 4 kwance baida lafiya ko abinci baya iya ci ranar da ya cika kwana 5 kwance ‘yan gidasu Khadija sukazo gaidasa, yara da manya mota biyu suka yi”

     Sossai yaji dadin hakan ranar yadan farajin sauki, Hajjah ko Babu wadda yakaita farin ciki, gannin yayyenta tare da iyalinsu sunzo duba jikin Ahmad, ciki harda Khadija”

       ********

    Ina Ahmad fah ko yana gidan nasu??

    A’a Alhaji yana dakinsa be Gaya maka beda lafiya ba?

     Bangane beda lafiya ba Aisha, beda lafiya shine ba’a buga waya agayamin ba?

    ‘yar dariya tayi toh aini gani nayi ba karamin Yaro baneba shiyasa, sannan ciwon nasama neman rigima ne yake yi, so yake yai rigima da tsohon mijin Khadija”

      Wacce Khadija?,  taki?

   Eh kasan sun rabo da mijin tuni, yakawo yariyar wajen uwarta shine wai donme zai dauketa aranar, wai kajifah inji Yaro,🤔  tunda aka tafi da yariyar inbaka lbr har hawaye yayi”

    Allah sarki tausayi ne dashi”

   Bawani tausayi Alhaji ninafara tunanin son yariyar yake yi kawai”

    Kikace ‘yar wajen Hadiza ce??

   Eh aita girmafa ‘yar, inaga zatai 16, ranar nan suka kusan wuni da ita, ainaga abu ranar, zanso kaga yadda yake mata kamar ba yaro ba, cikin rarrashi yake mgn da ita, itama da alama ta shaku dashi sosai”

      Murmushi Alhaji yayi, ai ta masa kankanta, lallai girma ba wuya, ai kinsan shida Khadija suna shiri sosai, inagadai ‘ya ya dauketa, shida zaiyi aure kwanan nan”

    Haka kake gani, ninafi ganin yanason ‘yarnan ta Khadija, Dan baka yadda yake mata bane, dawa Ahmad yake wasa agidan nan, dama can gidan yayan, Amman wannan yariyar  tace wancen tace wance abun mamaki Ahmad ba kyara bare hantara saidai kika ya kwashe da dari ya mata”

Bana tunanin wani abu, ‘yar Hadiza ai aisa ce”

      Haka kake gani, nikuwa inai masa sha’awarta”

       Hmmm Ahmad yana da mata ai ki aje ra’ayin ki gefe?

          **********

    Lale  lale Ahmad, sauki ya samu rabon da in ganka gidan nan tun ranar da Fatima tazo, akace zazzabi ya kama ka ko?

       Murace Inna Amman ai nasamu sauki ya gidan komai lafiya ko?

   Lafiya lau Ahmad ya Hajiyart taka”

    Lafiya lau nasan yanzun Baba bayanan ko?

    A’a Ina zaka sameshi da uwar ranar nan yana kasuwa”

     Hakane, Khadija fa?

   Tana nan, ranar sai kaga rashin mutuncin Usman”

      Bakomai Inna ‘yarsace ai wata rana sai lbr”

    Kwarai kuwa me lbrn ma basai an ganshi ba”

    Mikewa yayi daga tsugunun da yake yace barin shiga ciki”

       *********

Kamar daga sama raga ya fado mata batare dayayi sallama ba”

     Cikin sauri tajawo hijjabi tasa kasancewar babu kayan kirki jikinta”

     Ahmad waikai meyasa baka Sallama”

     Wanni irin kallo yai mata sannan yace”

   Kicedai meyasa banai miki sallama, Ina da dalili Amman amsan sai ranar da muka kasance mu biyu”

     Wayo ta hadiye sannan tace”

      Ku biyu kaida wa???🤔

        Karki sake min rainin wayau kinsan abin da neke nufi, inadan ma baki gane ba ki tsaya kiyi nazari duk abun da zuciyarki ta fassara miki toh wlh karkkyi tantama hakan nake nufi”

        Wayo ta sake hadewa akaro na biyu sannan tace”

    Shikenan naji jeka

    Ni danki ne?, Koke kika kawoni, dakaina na shigo kuma sai sanda nai niyyar fita”

     Cikin ido ta kalleshi shikenan ai saikaita tsayuwa daganan har mahadi ya bayyana, fitsarre kawai”

     Karki saki kirana da wannan sunan

Niba sa’anki bane”

     Ganin inda yake zare mata ido tai saurin cewa, nabari

     Kwafa yayi sannan ya ciro wayarsa ya mika mata”

    Amsa tayi ta rike ahannunta tana kallonsa mezanyi da wayar ka kuma?

     Baban Fatima Zaki Kira ki gaya masa ai ‘yar bashi kadai ya samar da itaba dan haka ya cire kason shi ya bamu namu….

73 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *