Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 6

Posted by

WATA FITSARA PAGE 6

 

Advertisements

WATA FITSARA*🤔

     By
Fadeela Lamido

Page 6

Advertisements

Cikin zullumi ta zauna tare da tunani, idan har Ahmad zaice ta kwana gidan nan toh lallai akwai abun da ya shirya, balakin tsoronsa ne ya sake shiganta tare da tarin tausayin sa, meye dalilin komawar sa haka?🤔, Wata zuciyar ce tace Mata ki kiyaye kanki kibar gidan nan kafin ya aikata abun da ya shirya, mikewa tayi duk da wata zuciyar nace Mata Ahmad din bazai aikata Mata haka ba”

    Ficewa tayi cikin gidan batare da kowa ya sani ba domin tuni Hajjah ta nufi dakin ta”

       Misalin 10 nadare ta isa gida dakin Inna ta nufa yayin da Inna ta dubeta cikin Mamaki tace”

Advertisements

      A’a🤔 keba Ahmad yace kince kwana zakiyi ba??

     Karya yake min Inna”

    Amman kinsan Zaki dawo har kika bari kikayo dare haka??

   Ahmad natsaya jira shine yaki kawo ni”

    Tabe baki Inna tayi toh Allah ya kyauta”

   Daki Khadija ta wuce ta kwanta ba komai take tunawa ba sai inda gaba daya Ahmad ya canza dabi’a rayuwar da ya dauko ta fara bata tausayi, dadin dadawa kuma ayau tanajin tayi Babban rashi domin rashin wadda zata tattauna damuwarta dashi, daman Ahmad din ne kadai take shawara Dashi kwanciya tayi lamo bisa gado cikin rasa inda zata saka ranta”

        **********

*Yaro* Ina Khadija ne naduba ko Ina ban gantaba🙄 banan tayo ba??

      Cak ya tsayar da kada kafar da yake yi, tare da ware ido, baki gantaba Hajjah??

     Eh nashiga daki kafin na fito bata🤔

     Jimmm yayi sannan ya koma ya jingina da bayan kujerar tare da fadin”

         Shikenan😎

    Bangane shikenan ba Yaro, ka Kira wayarta mana🤔

     Kamar bazai mgn ba zuwa can yace”

     Nidai Hajjah gaskiya bazan Kira ba, ai ba karamar yariya bace gida kawai ta wuce”

   Duk da haka dai ka kirata”

    Hajjah kiyi hakuri dan Allah”

   Kallon sa tayi sosai sannan tace”

    Hakan na nufin kunyi rigima kaida Khadija ko??, Wai meye ne yake damun ku saikace wasu kananan yara?🤔

       Hajjah niki daina min zancenta, kirjina zafi yake”

     Zafi Yaro?, toh sannu, amman dai Ina dada baka shawara ko sako da sako idan suka girma barin rigima suke amman naku dada gaba yake, ai yanzun tsakanin ka da Khadija inace sai mutunta juna, banason ganin haka daga gare ku, ni danake ma fatan nan gaba ka auri Fatima🤔

      Karake mgnr tayi tana me daura hannunta kan kafadar sa yayin da Ahmad yai saurin rike hannun Hajjah yana fadin”

    Nidai Hajjah banson wannan mgnr inada wacce nake so….

    Wacece??🤔

    Idan lakaci yayi zaku sani”

   Shikenan Amman katashi kaci abinci ita kuma Khadija ni bara naje na nemi layin ta”

   Tabe baki yayi cikin nuna halin ko in kula”

    Hajjah na wucewa ya mike, matashin ya dauka yayi jefa dashi, cikin zafin rai ya rarumo dayan ya sake yin jifa dashi, be tsaya nan ba harsaida ya har gitsa dakin kaba daya ya haukata komai sannan ya kama kugu yana maida ajiyan zuciya”

        ********

Washegari wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya sannan ya fito, duk da ransa babu dadi ya kirkiran wa kansa fara’a domin kada Hajjjah ta gane halin da yake ciki”

        Ganin babu kowa afalon ya nufi dakin hajjah, zaune ya sameta ta zuba tagumi cikin yanayin damuwa”

     Hajjah?

  Na’am Yaro ka fito??

  Nafito Hajjah, zan fita, Ina kwana?

    Amsawa tayi cike da sakin fuska”

Ga key na agyara min daki”

   Amsa tayi harya juya baya yaji tace”

       Raina bace an hargitsa kayan kenan ko?

     Jimmm yayi sannan ya waigo yace, Hajjah😬…

      Shikenan jeka ai baka son in sani ko?

     Dawowa yayi ya zauna dafda mahaifiyar tasa ahankali ya kamo hannunta ya rike”

   Hajjah bawani abu bane fah, kawai Khadija ce ta bani haushi, wai karana takaiwa Alhaji, shikuma Alhaji yawani goyi bayanta”

   Cikin ido ta kalle sa, dan wannan kayi fushi har haka alhalin kafi kowa sanin irin matsalar ka?, Meye ya hadaka da Khadija?

     Irin dai wancen Karan ne data kawo miki kwanaki”

    Shiru Hajjah tayi tsayon wani lakaci sannan tace”

     Wata kila Khadija tana hango irin abun da nake hangowa shiyasa take ganin kama Mata rashin kunya, dan Allah Yaro kabar Mata abin da bataso, komai kake yi nasan kana sane kake yi, kuna da fahimta mekyau ada banson zumuncin ya lalace”

     Cikin sanyin jiki yace zan kiyaye Hajjah, amman ki saki ranki, naga kin shiga damuwa”

    Toh ba dole ba Yaro, wadda nake kallo naji dadi yana cikin damuwa kuma yana boye min”

   Kansa ya kwatar kan kafardarta sannan yace”

   Hajjah?, Ki kiyi hakuri sannan ki dauki hannun ki me albarka kishafamin kaina, sannan kimin addu’a Allah ya cika mun burina”

    Hannunta tasa taja hancin sa harya zabura tare da fadin, naki, saidai nace Allah ya tabbatar maka da abun da yafi Alheri agare ka, ba burin ka ba, domin wani lokacin abun da muke so wata kila ba Alheri bane, wannan kuma kullum ita nake maka ko kana nan ko bakanan”

    Rungumeta yayi sosai Hajjah nidai Buren nawa nake so?

     Kasan ta shafa, tonaji yanzun zan maka addu’a duk abun da nace kace Ameen”

Tam”

     Allah yai maka Albarka *Ahmad*

      Saida ya Kara rungumarta sannan yace”

    Ameen”

   Allah ya baka mata tagari tare da zuri’a masu albarka”

    Ameen Hajjah

    Allah ya tsareka, gabanka da bayan ka, mugun gani da mugun ji Allah ya nisantaka dasu”

     Ameen Mamana”

    Allah ya cika maka burika na alheri, wadda ba alheriba ya canza maka da mafi Alheri”

    Jimmm, yayi kamar baza amsa ba, zuwa can ya share kwallah ahankali yace”

      Ameen”

   Shafa kansa tayi akarshe tare da sake fadin”

   Allah ma Albarka, ya nuna min auren ka Ina raye”

      Mikewa yayi tare da gyara rigarsa insha Allahu Hajjah har ‘ya’yana sai kin zauna dasu kamar haka”

        *******

   Ahmad zaune cikin motarsa  Galadima zaune agefen sa, huci kawai Ahmad ke saukewa bayan yagama bawa Galadima lbr”

    Shiko Galadima murmushi kawai yake yi zuwa can yace”

     Amman mutumina kabani mamaki dakai saurin karaya, kwata kwata banzaci haka ba daga gare ka, duk da cewa bawani son abun nake ba amman ita harta isa tace bata son ka?, Mezata nuna maka? Banda ma zuciyar taka ta makale a ita din me zakaci da ita, meye take takama dashi!! ????

    Gefe  Ahmad ya maida kansa tare da fadin”

    Girma”

   Girma?, Galadima ya tambaya, sannan ya cigaba da cewa, ai saikace ta nuna maka a daidai inda girma yake, tana nufin kasa sarrafata zakayi ne??

    Wata kila haka take gani, ai naso in nuna mata niba sa’anta bane ba, batakai cikin cukali ba awajena, na tabbatar babu wani halitta tata tadafi tawa girma, toh a Ina girmen yake *Sani*??

    Galadima dariya yayi tare da fadin”

    Aishi nagani Nima, ai kawai ka turketa ta nuna maka inda girman yake🤷🏽‍♂️

    Hmmm matsalata daya bata iya shiru da bakinta, hadini da tsofai take, badan Allah yasa da bakina ba da tuni ta kaini kasa, ita ai tagane son ta nake, kasan me Sani?

     A’a

   Saina auri Khadija ko bata so”

    Ina goyon bayan ka abokina”

       Dakatawa sukayi da hiran sakamakon makarantar su Samha da suka iso, driver ne ya sauka bayan Ahmad ya mika masa kudi kamar yadda suka saba ko wanni lokaci, bejima ba ya dawo Samha nabin bayan sa fuskanta cike da fara’a
Daka nesa ta tsaya tana kallon motar tana fara’a

    Daga cikin motar yake kare Mata kallo wasai yaji ransa fari karrr hango Samha cikin fara’a”

    Karkacewa yayi ya gyara zaman sa sosai yana kare Mata kallo fuskanshi dauke da murmushi”

    Kallo Sani Galadima yabi Ahmad dashi ahankali ya zunguri Ahmad yana fadin”

    Rabon da nagan ka cikin farin ciki haka harna manta”

    Batare daya kalli Galadima ba yace”

      Malam bakaga Samha bane??

    Juyawa yayi ya kalli Samha sannan ya kalli Ahmad da har yanzun idon sa na kanta yace”

     Naganta da Alama so take ka taryeta da kanka”

     Idon Ahmad akanta yace”

    Kwarai kuwa, bakaga ta cuge awaje daya ba, ai tafi uwar fitina, gilashin motar ya bude yaimata alamar ta karaso da hannunsa”

    Bubbuga kafa tafara ganin haka yai saurin bude motar yayi ya nufeta”

     Hannunta ya rike yayin data kwanta agefen jikin shi, garasawa motar sukayi yana me Kara mannata da jikinsa tare da tambayanta karatu tana bashi amsa”

     Ganin Galadima yasa tadan shiga nutsuwa tare da gaidasa sannan ta shiga neman bakin aljihun Ahmad”

     Sanin abun da take nema yasa shi gyara mata gaba daya aljihun dake jikinsa saidata duba sannan ta zunbura baki”

     Cikin murmushi yace”

     Ga kayanki can na ranan nataho miki dashi kici naci in maida sauran, wata rana nasake kawo miki da haka har ki cinye, ninabar shan sweet yanzun”

     Kayan ta jawo tafara ci duk kayan zakine yayin da Ahmad da Galadima suka zuba Mata ido kowa da irin tunanin sa”

     Kaca kace taima kayan sannan ta tattara ta aje ledar ajikinta, uncle din ta kalla wadda tunda tafara be iya cire idonsa akanta ba, Uncle Ina Maman…..

  Ganin inda yake kallonta ta kasa karasawa”

     Uncle daman kallona kake yi?🤔, to me kake kallo??

      Kawar da kansa yayi tare da murmushi, sannan ya juyo yace”

   Ina kallonki ne inajin farin ciki gani ga ‘yata kusa dani, kinsan idan Ina kallonki akoda yaushe kina tunamin da wani lokaci abaya….

    Ainafi Mamana kyau, haka Abbana yake cewa”

     Kallo yabita dashi sosai haka kawai yaji ransa ya baci,  kinsan abin da zan fada ne da zakice min kinfi mamarki kyau”

      Ai idan Abbana yace min Ina tuna mishi da wani lokaci abaya daga karshe cewa yake naso na dauko Mamana Amman nafita kyau”

    Ta gefen ido ya kalketa toh ke kuma sai kiji dadi an kushe uwarki ko?

    Itama hade fuska tayi inason kyau uncle kuma inason duk wani abu mekyau, ni ban ki ace nafi kowa ma kyau ba, kaima da kake kallo na ai ganin kyauna kake”

     Ok shiyasa yake zagin uwarki ke kuma kinajin jin dadi ko, ki daina bari yana yaudaran ki, baki da wani kyau, Khadija tafiki kyau bazana ahada ba, har wani kyau ne dake?

    Sosai Samha ta bata rai wasa tafara da hannunta kwalla cike da idonta daker ta iya bude baki tace”

    Kaima kafini kyau kenan??

     Au🤔 dakin fini kike gani?, Ko ce miki yayi kin fini nima?

       Hawayene suka fara sakko Mata Sani dake gefe dariya yake boyewa ganin inda Ahmad ke huci yayin da Samha ke hawaye, sakkowa suke wani na koran wani

    Ahmad kuwa kallon Samha yake yana huci bakaramin haushi Abban Samha ke bashi ba, Kara kallon Samha yayi sannan yace”

       Shikenan kije saina Kara dawowa”

   Karon farko dayaga tana kuka be lallasheta ba dan haka taki fita cikin motar”

     Kije nace saina sake dawowa”

       Hawaye ta share tare da noke kafada”

    Inafa zata tafi, kuka fa take, baka lallasheta ba kamar yadda ka saba, cewar Galadima daya tsare su da ido”

    Bazan lallashe taba yau, Dan Banga dalilin kukan ba”

    Dagowa tayi ta kalleshi leden dake kan cinyarta tai jifa dashi komai dake ciki ya watse acikin motar har jikin Uncle din sannan ta fice afusace”

      Galadima ya rike baki🤔
Sannan ya shiga kiranta ganin taki waiwayowa yace”

     Wai, 🤔  barkono”

    Ahmad ne ya kalli jikinsa sannan ya kalli Samha data riga ta naisa, kallon sa ya maida Kan Galadima yace”

    Kagani ko ?

   Cikin dariya Sanin yace”

     Yau anyi fada da Uncle, toh Kai akan me zakace bata dakyau?

     Bata da wani kyau Sani, akan me zai dinga sama yariyar girman Kai, umarni yabawa driver subar wajen”

           ********

Samha amota bayan driver ta ya dauketa akan hanyarsu ta zuwa gida babu abun da take sai kuka, duk iya sonta data tsaida kukan ta gagara bari, badan tasan Abban ta beson tana mgn da Uncle Ahmad ba data gaya masa yau sunyi fada da Uncle Ahmad, Amman haushin da Uncle yabata yau batajin zata iya boyewa Abban ta har suka isa gida tana kuka, sosai idon ta suka kunbura tunda take babu wadda ya taba mata irin abun da Uncle Ahmad yai Mata yau, tana kuka ta isa gidan tare da jiran dawowan Abban ta”

         ********

    Ahmad kuwa bayan sun sauke Sani Galadima gidan su Khadija ya nufa, sasan Inna yalwa ya fara shiga cikin son ya rutsa Khadija adakinta, saidai Kash adakin innar ya sameta ta tasa abinci agaba tana ci”

    Dajin Sallamar sa gabanta ya fadi, kallo sukabi juna dashi cikin dakiya yace Ina Inna?

    Kai tsaye tace sunje barka”

       Jimmm yayi sannan ya shigo sosai, hannun rigarsa ya nannade bayan ya isa gaban Khadija”

    Zama yayi ya tankwashe kafa yasa hannu ya dauki culalin daga gabanta tare da deban abincin yakai bakin sa sannan yace”

      Meyasa bazaki aureni ba??

     Kash😬 wai ba anbar mgnr ba??

    Inafa za’a barta, bakinje kincewa Alhaji kina Sona ba??

    Nidin?

   Eh mana, kince masa wai ninace inason ki, iya sanina bantaba bude baki nace Ina son ki ba, sanan kika dawo kikace bazaki aureni ba, ni abun da nake son na sani anan shine meyasa bazaki aureni ba?, Idan har kina da gamsheshiyar amsa nabar Kara miki abun da baki so”

       Jimmm tayi zuwa can tace”

     Ahmad inason kasan cewa babu aure atsakanin mu”

     Injiwa ya gaya miki?, Ke kika haramta?

     Ahmad nifa ba sa’arka bace”

   Kin girme ni ne?

   Koban girme ka kaba shekarun mu daya kaga nafika girma”

    Idonsa ya kankance sannan yace”

    Nunamin adaidai ina girman yake??, Su shekarun mu da kike mgn akai, a daidai ina suke,  indebi naki in karawa nawa?,  Akwai wata hallita datafi tawa girma ajikin ki?, Ki kalleni dakyau……

   Mmn Yazeed

6 comments

  1. Pingback: poker online
  2. Pingback: pgslot
  3. Pingback: situs toto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *