Advertisements

IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 7

Posted by

WATA FITSARA PAGE 7

 

Advertisements

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamido

 Page 7

Advertisements

Kallon nasa tayi kamar yadda yace, dariya ce ta kamata batare data tsan maci zuwanta ba”

     Kulewa sosai Ahmad yayi, nikikewa dariya kuma??

    Eh mana wannan ai abun dariya ne, Allah ya shiryeka ka gane gaskiya amman kabar zancen aure dan Allah”

Advertisements

    Har yanzun baki bani amsan tanbayoyin dana miki ba”

    Kallonsa tayi sannan tace”

   Hmmm Ahmad Ina ka taba ganin andebe shekaru? Girma kuma nasan ka fini Ahmad shiyasa ma kake raina min hankali saboda kana ganin tsakiyar kaina ko??

     Kedai kike raina min hankali, akwai wani abu dazai gagare ni kike tunani??

      A’a Sam, niba haka nake nufi ba, nataba aure Ahmad kaiko ko auren fari bakai ba”

   Ina ruwanki?, nafiki sanin wannan ai”

   Hmmm Ahmad kenan wlh na girme maka Ina da Samha”

    Daman nasan abun da kike takama dashi kenan, nima Fatima ‘yatace, domin da mace ne ni dana haifi kamarta”

     Murmushi tayi sannan tace sai kuma Allah yayoka a namiji”

    Kibar wannan zancen Khadija, ni dai yanzun inason naji Zaki aure ni???

    Wlh babu zancen aure tsakanina dakai Ahmad, ni kabar min zancen rashin kunya akan nace bazan aureka ba, ba Ina tunanin wai akwai abun da zai gagareka bane ba, ni yanzun ai Ahmad kafi karfina ka wuce da sanin tunani na, har tsoro kake bani wlh, toh ni idan na aureka aina shiga uku, dagani jaraba zakayi, auren ne kawai bashi yiyuwa Ahmad”

     Kallo yabita dashi sosai ya tsareta da ido mikewa tayi nidai na shiga uku dakai Ahmad dan Allah kabar lunshe min ido”

     Kice dai inbar kallon ki, haka ne ake lumshe ido, gyara dakyau in lumshe miki ki gani”

    Nikam bazan gani ba Ahmad, kadan ya rage maka ka zama kwarto na rantse da Allah”

     Murmushi yayi har hakoransa suka bayyana, can kasa yayi da murya yace” Zaki aureni?

     A’a Ahmad, dan Allah kabari, bakin gadon Inna Takoma ta zauna sannan tace”

    Daman akwai mgnr da nakeson muyi, wai dan Allah Ahmad haka zan zubawa Baban Samha ido ko mgn baya bari inyi da ‘yata bare inji damuwarta?

    Hm Khadija kenan, aina Gaya miki abun da yadace kiyi kika kiya, nace miki kitambayeshi hakkin ki, da ace kin mai haka daga lokacin zai gane kurensa, shikadai ya samar da ita??, Inace hada karfi da karfe aka yi?, Ai abun hadin guiwa ne, kenan shikadai zai shanye roman?, Idan Zaki bude baki gara ki bude, ni har gidan sai in kaiki idan Zaki mai haka, idan kuma bazaki iya ba karki sake min zancen Samha”

    Dagowa tayi da sauri ta kallesa tace”

   Meyasa yanzun ka rage damuwa da Samha, alhalin da kafini damuwa da barin ta acan din, baka sati saikaje makaranta ka dubata yanzun duk ka bari, danayi mgn saika dauko wani shirmen ka can daban”

    Tafiya ya fara tare da fadin eh narage damuwa da ita din, ni bawan ku ne da zan dinga binta makaranta koda yaushe??

    Hararansa tayi, sannan tazo ta wuce sa afusa ce shima ajiyan Zuciya yayi sannan yabi bayanta ya fice yabar gidan”

Kwana biyu Khadija kwance tayishi gata da lfyrta lau Amman yanayin ta kamar mara lafiya,  damuwa ne cikin ranta, tarasa yadda zatai dashi mgn kawai take son tayi da ‘yarta Amman ya gagara, acikin ranta tafara tunanin kodai shawaran Ahamad din zatabi, tabas akwai cutarwa da rashin adalci, tsintan kanta tayi da Kiran wayar sa, yana dauka tace”

       Ahmad kana Ina?

   Inda kika aike ni😎

    Allah ya baka hakuri, idan kana da kalloci kazo ka kaini gidan Usman din”

    Hmmm, shine nan, idan natashi office zanzo, ki shirya”

       ********

Ummee wai me yake faruwa ne??

   Aunty Abbana ya dawo??

     Be shigoba tukuna, wani abun ne ya faru amakarantar?

    Hawaye tashare sannan tace bakomai, nakosa Abba na ya dawo kawai😭

      Jinan Ummee, kinsan idan Yadawo yasame ki ahaka’ nizaiwa fada?, ni baki daukeni uwa ba kenan, ban da amfani acikin gidan?, Kindawo kusan awa kina kuka ki kasa cemin komai, Ina Jin ki meye ya faru??

    Hawayen ta share sannan tace”

      Aunty waini mummuna ce??

    Jimmm, tayi zuwa can tace, mummuna kuma?

     Eh Aunty wai bani dakyau??

     A’a wannan karyane Ummee waye ya fadin hakan”

       Wani ne Aunty, yace wai bani da kyau, kuma har yana cemin mummuna😭😭

      Wani??, Ummee ?, Kina mgn da samari ko?, Duk wadda yace baki dakyau karya yake Ummee, da alama son ki yake, kinsan wasu mazan da haka suke fara bayyana son su”

      😳😳 So?, Uncle dinane fah”

    Uncle dinki?

  Eh Dan uwan Mamana ne”

    Ina kika hadu dashi Ummee?

       Kallon kofa tayi sannan tace”

     Makarantar mu yazo”

   Shine dan baki da hankali kike jiran Abban ki Yadawo ki gaya masa?, Karki fara maza ki goge idon ki, ki kuma saki ranki, dan uwan mamakine tsokanan ki kawai yake yi ba wani abun ba”

     Aunty yana kallona fah inna kuka be lallasheni ba saima yace wai in fitar masa amotar sa”

     🤔 Bekyauta ba ko Amman na tabbatar wasa yai miki”

    Bazan zake mgn dashiba aunty har duniya ta nade”

    Dariya aunty tayi, ban da abun ki Ummee wayake fada da Uncle dinsa, Babanki ne fah”

    Nidai baruwana dashi Aunty”

Inda Abba na ne baxaice bani da kyau ba”

    Toh kiyi hakuri karki bari Abban ki yaji kinjinko?

    Ahankali ta gyada kai”

    **********

Idan Ahmad ya dawo kice masa yaje inda na turasa kuwa??

     A’a fah, ai tun aranar fah yasame ni adakina “

   Toh🤔 meyace?

   Cewa yayi wai shi akwai wacce yake so”

     Toh akwai wacce yake so?’🤔 Inason nasan me wannan kalmar tasa take nufi?, Ki tambayan min shi”

     Aida kaika tambaye sa Alhaji zaifi Gaya maka cikin sauki”

   Kawar dakai Alhaji yayi zuwa can yace”

   Nalura ke kike daure masa gindi yake abun da yaga dama, ni Umarni nabashi ba shawara ba yaje can din”

     Jimmmm tayi zuwa can tace”

    Alhaji ka fahimceni, Yaro yana da matsala, gara mubisa ahankali har ya kawo mana yariya da kansa”

    Haka zumu yita zuba ido muna kallon shi yana neman shekara 40 babu aure? Baki gudun ya jawo mana mgn??

    Subuhallahi, Alhaji Yaro ai da nutsuwar sa”

    Nutsuwar banza, waliyyi ne shi??, Nagaji da zuba masa ido ki gaya masa yaje inda natura sa”

    Shikenan zan yi yadda kace din Alhaji”

        *******

Cike da farin ciki yau Ahmad ya dawo gida wadda hakan yasa taji kamar karta Gaya masa sakon Mahaifin nasa gudun baccin ransa Amman dole zata fada”

    Yaro?

   Na’am Hajjah”

    Daddyn ka yace wai kaje wajen da ya turaka kuwa??

     Murmushi yayi har hakoransa suka bayyana sannan yace”

     Hajjah kice masa naje har sau biyu batanan inji Ummanta, Amman zan sake komawa”

    Murmushi Hajjah tayi au kaje din shine baka bani lbr ba??

    Naje hajjjah saidai batanan”

    Har Ina cewa Alhaji kace kana da wadda kake so?

    Sosai kuwa Hajjah, inada wacce nakeso, kuma nasan duk ranar da Daddy yaji zaifi kowa farin ciki da hankan”

    Kenan Mata biyu zaka yi??

    Hajjah ai zabin Daddy bazan taba haduwa da itaba bare ma ta ganni tasa rai”

    Jimmm tayi, cikin Mamaki kenan Ahmad akwai abun da kake shiryawa?

     Nibakomai Hajjah Ina zuwa barana watsa ruwa”

     **********

  Lalala gaskiya ganina kana da kyau sosai wannan irin cire wanka haka”

      Murmushi Ahmad yayi Amman gaskiya Khadija tunda nake baki taba burgeni irin nayau ba, duk da kin kirani kanin ki Amman cewan da kikayi nayi kyau yasa na yafe miki”

      Gyara zaman sa yayi lokacin data zauna sosai cikin motar yace”

      Amman ba haka zakiba ko??

    Ahaka zani mana”

     Toh barin tambaye ki wannan uwar kwalliyar wa kikawa??😌

    Ni? Kwaliya kawai nayi dan inyi kyan gani”

      Karya ne, kije kisa Hijjabi ko Babban mayafi”

     Haba Ahmad yanzun Kai wa kawo kwalliya”

    Ni Fatima namawa😎

    Hmmm wai Fatima🤔 toh Nima ita naiwa”

    Kice dai kinma Baban Fatima kwalliya, tunda har yanzun yana makale azuciyarki shiyasa kika gagara aura

    Ahmad ka fara ko?

      Eh nafara Khadija kina nufin nine zan daukeki in kaiki wani katon  ya kelle min ke abanza”

    Yamutsa fuska tayi Allah San bata son kalaman Ahmad amman tunda tanason yakaita dole tayi hakuri dashi”

     Ciki ta koma ta sako katon hijjabi ta fito, hanya suka dauka suna tafe suna hira, jefi jefi yakan sako irin zancen sa daya saba yayin da Hadiza ke sharewa”

    Suna daf da isa unguwar su Samha Ahmad faka kefe tare da fadin ki goge jenbakin ko ki matso na goge miki”

Kin juyowa tayi tana kallon hanya tare da fadin”

      Ahmad muje dan Allah karkasa raina ya fara baci……..

  Ganin dirowan sa tayi tare da zagowa barayin da take, cikin azama yake tahowa harya bude gefen da take”

       😳😳 Hannun sa taga ya fara kokarin kawowa fuskanta yana kokarin kama kanta, firgicewa tayi hannunta take dagawa tare da fadin”

     Zan goge, kanta ya rike da duk hannunsa biyu yana kokarin kawo fuskan shi gareta tai saurin dukar dakan jikin hijjabinta tana gogewa tare da fadin dan girman Allah ka bari gashinan nagoge ai”

   Arikece take duk jikinta rawa yake cikuikuyeta yayi acikin hijjabin cikin shakaykiyar murya yake cewa”

     ‘Dago kanki kafin nadago miki da kaina”

   Kanta akasa tace wlh na share”

     Yana sauke nurfaffashin da Khadija ta rasa na meye shi yace”

     Shine ai zan gani, idan be ida sharuwa ba na tsotse miki”

    Yasharu nace maka ko🙄

    Narantse da Allah idan baki dago nagani dakaina ba kika barin da dagoki saina tsotsi bakin ki”

      Amutukar firgice take jikin ta bebar rawa ba tace toh ka sake min hijjabin mana, yanzun ji mutane suna wucewa suna kallon mu da wanni suna zasu kiramu”

     Duk yadda yama mutun dadi, Ina ruwana, tunda basu isa suzo gabana su fada ba”

      Dagowa tayi sukai ido 4 sosai idon sa yai jawur babu abun da yake sai sauke numfashi tare da ajiyan zuciya”

      Daker ya iya cewa be goguba Khadija, ki tsaya na goge miki”

        Yadda yai mgn yasata kare masa kallo, cire idonta tayi da sauri ta kawar gefe”

      Kallon inda ta kalla yayi tare da ajiyan zuciya sannan ya koma mazaunin sa ya zauna, kwanciya yayi jikin kujerar tare da rufe idon sa yai shiru na tsayon wani lakaci”

    Khadija ko bata sake marmarin kallon sa ba, saidai tana jin numfarfashin da yake saukewa”

    Yakamata Ahmad yai aure ya dade haka, Khadija ke wannan tunanin cikin ranta, wai shi in banda rigima taya za’ayi yace ni yake so, ji irin halin da yashiga lokaci daya lallai ya kamata nai aure, lokacin ne zai cire ran zan aure shi, aure zanyi nan kusa bazan aure Ahmad ba gaskiya, tausayi yabata sosai domin Ahmad mutumin ta ne, Jin numfashin nasa yayi sauki ta kalle shi adaidai lokacin da yake kallonta cikin lumshe ido”

       Ahankali ya bude baki yace Mata Sannu😉

      Nikai zanma sannu muje dan Allah yamma na dadayi”

    Har suka isa gidan bashi da wani kuzari, gida yasha gyara ba yadda suka sanshi ba, komai yanasha gyara,  motocine birjik cikin gidan, sosai Ahmad ya hade rai dan ya tabbatar Alhaji Usman nanan, Khadija ce ta sauko ta nufi gidan yayin da yake cewa saura ki tsaya wawanci ya danne miki hakkin ki😎 dakin shiga ki turo min Fatima……..

6 comments

  1. Pingback: special offers
  2. Pingback: mostbet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *