Advertisements
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 8
Advertisements
Fitowa yayi ya zauna saman motar yana karewa gidan kallo”
Tabas Usman nada kudi sosai Amman wannan bashi ne zaisa ya dinga takama da fadi ba, tare da daukan kowa ba Abakin komai ba ya dade zaune agurin Babu Khadija babu Fatima dan haka ya fara waigen Hanya sosai ya kosa ya ganta”
********
Advertisements
Bayan Khadija sun gaisa da Auntyn Samha guri ta basu ta shige dakin ta”
Samha ya naganki wani iri wanni abu ke damun ki??
A’a
Ranar sai Babanki ya aiko daukanki ko hira bamuyi ba, naso na zauna dake mun dade bamu haduba baki da matsala ko??
Babu Momy kawaidai inasom Abba na ya dinga bari Ina zuwa gurin ki ne😌
Kirage saka irin wannan damur azuciyarki, nikaina inason hakan amman babu yadda zanyi da Babanki, tsananin sa yayi yawa akanki”
Mommy toh ki dawo nan gidan mana”
😳😳 Samha baki da hakali ko? Ko kin manta abun da Abban ki yaimin??
Hawaye ta share toh yanzun Mommy haka zandiga zama ni daya?😭
Baki Khadija ta rike idan kina min haka bazan dinga zuwa wajenki ba, bagashi ya kawo miki Aunty ba ko bakijin dadin zama da ita ne?, Tana takura miki??
A’a nidai nafi son ki dawo wajen Abbana”
Kicire ranki Samha ni aure ma zanyi bazan dawo ba, idan ma rashin zuwanki wajena ke damun ki Khadija kwana nawa ya rage kema ai gidan wani Zaki lokacin kina da damar zuwa wajena iya son ranki”
Ni Ai ba yanzun zanyi aure ba saina girma sosai sabo da nima banson na auri dan Yaro”
Dan Allah, kice babba kike so🤔
Daga kanta tayi tare da fadawa jikin Khadija”
Lallai baki da kunya Samha wato har kin fara aje ra’ayi kuma kike iya fada baki ko jin kunya ta, shekaran ki nawa?
16 ne momy ai anawa kamata aure a class din mu anyiwa mutun biyu aure”
Cabdijam Samha banson karya fah?
Allah da gaske Momy dayar ma har ciki gareta”
🙄 Nabane su,🤔 toh yanzun kodai kema amiki auren ne?
Ainacewa Abbana Amin ranar nan yace wai saina girma”
Amiki?, auren?, Yanzun Samha banda shirmen ki yaya zakiyi ki zauna agidan miji yar cukur dake”
Aidai kawai nabari in girman ne kawai Amman zan iya”
Baki Khadija ta rike tana Mamakin Samha sosai saidai wata zuciyar nace mata shirmenta kawai take yi”
Da Abban ki zai yadda aida an miki kawai an wuce wajen”
In tsofa da wuri?
Toh ba cewa kikayi kina son aure ba?
Ai toh Abba na yabani shawara yace inbari in kara girma, kuma mijina bezoba”
Kwarai kuwa bezoba Samha amman banda wasa da maza kinji ko?
Toh aini bana ganin maza makaranta kawai nake zuwa bana ganin namiji sai uncle, Yamutsa fuska tayi kuma Mommy muyi fada da Uncle ranar na😩
Wanni Uncle din??
Uncle Ahmad mana ranar yazo makarantar mu daga muna mgn yace wai banda kyau”
Bayan kinje gidan namune kuma yazo makarantar??
Eh man”
Daman yana zuwa ne begaya min ba Samha”
Yanazuwa Mommy shine wai yace ni mummuna ce”
Wasa yake miki tashi muje wajensa ku gaisa yana mota”
Ni bazani ba ai ba ruwana dashi Allah kuwa bayace banni da kyau ba har yana korata daga motar sa yaki rarrashina”
Jimmm, Khadija tayi Samha da mutum nafada da Uncle dinsa, ba babaki bane??
Ni Abbana ai baya cewa banni dakyau shi tunda yace haka ni baruwana dashi har duniya ta nade”
Amman baki da hankali Samha tashi muje ki gaidasa”
Ni Allah Mommy ba ruwana dashi😩😩
Shikenan bazan sake zuwa wajen ki ba, Dan ma kin samu yai miki wasa, wucewa Khadija tayi zuwa waje yayin data biyo bayanta tana bata hakuri”
Saida na bushe zaku fito?, Hannun ya mikawa Khadija dake tsaye bayan Khadija da dogowar rigarta dabata karasa Kai Mata kasa ba”
Nokewa tayi tare da make kafada”
Au nidin?? Ahmad ya fada cikin tarin mamaki yana me binta da ido alokacin da take komawa bayan uwarta”
Murmushi Khadija tayi kadan sannan tace”
Ai cewa tayi wai kunyi fada”
Dani din? Ya tambaya yana me Kara binta da kallo”
Can kasa ta gaida sa, be amsa ba tambayanta yake Dani kikayi fada ?
Bakaine kace bani da kyau ba😔”
Kansa ya shafa sannan yai danyi murmushi yace”
Au ashe zancen be wuce ba, nina manta ma, yanzun shikenan munyi fada?🤔
Kanta ta daga”
A’a nikam banason fadan nan Fatima, hannun sa ya mika mata ki matso mushirya ni Ina nasan kin dauki abun da zafi har haka”
Noke kafada tayi yayin da Khadija tai dariya tana kallon su tace”
Ina fah zatazo bayan kace bata dakyau…….
Ke!!! Baruwan ki kinji ko?
Au toh ai shikenan, bude motar tayi ta zauna tabar Ahmad yana kokarin karasawa gun Samha”
Karaf ya riketa ke dan nace baki da kyau kike wannan fushin ‘yar cukur dake kin iya fushi”
Toh Uncle bakaine kace waini mummuna bace”
Toh sai ahanani in fadi ra’ayi na??, ni banga wani kyau da kike dashiba Babanki kawai yana fadane dan kije dadi Amman azahirin gaskiya bakida kyau”
Kuka ta fara yayin da Hadiza ta fito ganin Samha tana kuka tace”
Haba Ahmad yazakana sakata kuka, ke da kyanki tsokarnar ki kawai yake yi”
Ni ba tsokarnar ta take ba, wai Babanta ke ce mata tafiki kyau, gara a gaya Mata gaskiya, ta daina jin kanta, yariya tun tana karama akoya Mata fadin rai”
Ahmad ba girmanka bane wannan, kallon Samha tayi tace”
Samha zonan kinji kinfini kyau rabu dashi kishi yake an kushe ‘yar uwarsa akan ki”
Bakin motar Samha ta tsaya yayin da Khadija ta kamo kanta zuwa madubin motar ta hade kansu waje daya tana fadin”
Kigani fah Samha, aiko makaho ya shafa yasani”
Murmushi Samha ta saki ganin kamarta sosai da mahaifiyarta harma ta zarta Khadija farin fata tare da dogon hancin, bata San lokacin data saki ihu ba harma Ahmad ya Harare su Khadija ce tace”
Ahmad kaima zo akara da naka domin a banbance”
Tabe baki yayi Allah ya kyauta kudai kuyi, yana kallon su har sukayi kare Karen su suka gama sannan ahankali yace”
Kin isar da sakon kuwa?
A’a ai bayanan akace, wani lokacin zan isar idan Allah ya kaimu”
Kina nufin nayi zuwan banza?, Aini ba haka nake ba muna nan harsai ya dawo”
Yamma zatayi Ahmad, muje saimu sake dawowa”
Bata ida rufe bakiba motar Alhaji Usman ta shigo cikin gidan, Ahmad saman motar ya koma ya zauna yana me Satan kallon Samha dataki kulasa Sam yau”
Itako Khadija sosai gabanta ya fadi”
Samha ko fitowa tayi ta nufi Abban ta aguje yana fitowa ta dare jikinsa, rungumeta yayi tare da sunbatanta yace”
Wadan can fa?
Mamana ne tazo Abba”
Lallai ta kyauta Ummee, wancen Ahmad ne ko??
Eh shine”
Cikin son boye bacin ransa ya wuce ciki yayin da Samha ta koma gun Mamanta”
Ahmad kuwa ko kallon Alhaji Usman beyi ba, sannan be kalli inda Khadija take ba”
Sanin Halinsa da tayi yasa ta sakko kawai ta rike hannun Samha suka shiga”
Yana zaune Abban falon sa ya daura kafa daya Kan daya yana kadawa Khadija ta shigo tare da Samha”
Zama tare suna kallo juna da Usman sannan tace”
Ina wuni?
Lafiya lau ya kike?
Lafiya”
Shiru sukayi zuwa can yace wa Ummee Mamana jeki ciki ko”
Mikewa tayi ta fita da sauri tana cike da farin ciki domin bata taba ganin haka atsakanin su ba”
Khadija, naga kamar kina da mgn?
ido biyu ta kalle shi sannan tace”
Akan mgnr Samha ne”
Ina jinki?
Am dama cewa nayi Nima inada hakki akanta??
Kawar da kansa yayi can gefe tare da mike hannun sa asaman kujerar yanawa Hadiza kallon kasan ido tsayon lokaci kamar bazaiyi mgn ba sannan yace”
Ai ‘yarki ce, ke kika haifeta, kinga ko zancen hakki ya kare ko😉
Kasa tayi da murya sannan ta sake cewa amman baka bani hakkina na uwa, shekara 3 bansata a idona ba, kuma daka turota batafi awa biyu ba ka turo a dauketa haka ake yi???
Hmmm Khadija kenan yanzun me kike son ayi?
Sosai taji ranta nakara bacci yadda yake abu gadara gadara tsintan kanta tayi da fadin”
Ka daina danni min hakkina ka kuma dinga turo min ‘yata Ina ganin ta”
Kanshi tsaye yace baki isaba”
Ban isa ba?, amman kasan ba kaikadai kasamar da ita ba ko😭
Daman abun da nake jira ki fada kenan, wannan ba kalamin ki bane, wannan irin kalamin Ahmad ne, shiya turo ki ko???
Hawaye ta share sannan tace bawani turoni da yayi tsakani da Allah kana cutar Dani”
Mikewa Alhaji Usman yayi ya Karasa gaban Khadija, kafarsa ya daura daya kusa da ita tare da dukowa fuskanta”
Kice dai muna cutar da juna Khadija, kullum da bakin ciki nake kwana nake tashi kuma kinsani Sarai kikayi biris dani, amman wannan nasan laifin zuciyata ne, saidai ko kadan baki raga Mata ba har yau, akan me zan ragawa taki zuciyar?, Kina son ingaya miki wani abu Khadija?, Badanke nake turo Ummee ba, Ina turotane saboda farincin ta bawai Dan kiji dadi ba, sannan ki gayawa Wanda ya turoki, shi hakkin naki, karfi yaci daru ya danne, idan yanajin shi rikekken dan iskane mu hadu a kotu”
Mikewa Alhaji Usman yayi ya koma bazaunin sa yayin da Khadija ta mike tana share hawaye tace”
Shikenan ka cinyeta inkaso”
Murmushi yayi tare da fadin”
Yauwa wannan halinki ne tsiwa ki gaida gida ko?
Tafiya tayi tana hawaye yayin da Samha ta nufota”
Kan Samha kawai ta shafa sannan tai gaba yayin da Samha ta rufa Mata baya”
Afusace ta shiga motar tare da fadin muje Ahmad!! ganin tahowan Samha yasa ta sake fadin”
Muje Ahmad mu tafi mana!!!
Baki ganin Fatima na tahowa”
Muje kawai nace maka”
A’a idan ke baki so yin mgn da ita ni Ina so, sakkowa yayi adaidai lokacin da ta iso gefen da uwarta take Ahmad yai ram da ita”
Bude motar tayi ta rike hannun Khadija itama sannan tace Momy menene??
Hawaye Khadija ta share sannan tace”
Bakomai Samha koma gida mu zamu wuce, kiyi sallama da uncle ki koma gida kinji ko”
Jim tayi tana rike ahannun Ahmad, hawayene suka zubomata cikin Sauri Ahmad yakai hannunsa da nufin share Mata tai saurin kaucewa”
Cikin lumsasun idonsa yake kallon ta tare da fadin”
Kibari in share miki?
Kabarni😔”
A’a har yanzun kina fushi Dani??
Kai ta girgiza alamar a’a
Kinayi mana aida ba haka kike min ba, nabaki haushi ko?
A’a
Kicemin eh Fatima banason miskilanci, kicemin wani abu mana kafin mu wuce ko kinason in koma Ina tunani ki ne?
Shiru tayi yayin da ya zuba Mata ido, zuwa can yace”
Fatima toh ke waya ce miki anayin fushi ne da Uncle?
Wannan karon ma shiro tayi tsayon lokaci Khadija na ganin su saidai batajin me suke cewa”
Ahankali Ahmad yace shikenan tunda bazaki min mgn ba, sai mun hadu amakanta kenan??
Wannan karon ma shiru tayi idonta akasa”
Idonshi sosai akanta yace ko kar inzo???
Cikin sauri ta daga kanta”
Kar inzofa kikace??
Kaita sake dagawa”
Shikenan ya fada tare da tsayawa yana kallonta”
Ganin taki wucewa tana tsaye kawai yasashi fadin shikenan jeki”
Juyawa tayi ta nufi gida ko waiwaye babu yayin da Ahmad ya nannade hannunsa agirji bayan ta shiga gida ya koma motar yana me sauke ajiyan zuciya”
Duk Abun da suke Alhaji Usman na kallon su ta window har yaga fitan su gidan sannan ya dawo ya zauna jikin sa asanyaye”
Cikin motar su Ahmad kuwa kowa da abun da yake sakawa”
Bakomai ke damun zuciyoyin guda biyu ba sai haushi, gudu kawai yake zubawa yayin da Khadija keta sauke ajiyan zuciya”
Akofar gida ya sauketa sannan ya wuce gidan Hajjah, kallo kawai Khadija tabishi dashi domin tasan halinsa Sarai hardai yanajin haushi bazai kwana agidan nan ba”
Koda be fadaba tasan haushinta yake ji, haka ta wuni babu sukuni zuciyarta bata Jin Dadi kalaman Usman kawai take tunawa”
**********
Ahmad zaune agaban Hajjah abincine agabansa Amman ya kasa ci, lokaci bayan lokaci yana tsayawa cak tare da rasa abin yi”
Hajjah na lura dashi ya kasa ko taba komai illah Dan tabawa da yake yi”
Zabura tayi kadan Jin Muryan Hajja tana fadin”
Tunanin me kake yi Yaro?
A’a Hajjah abincin nake ci ai”
Hmmm Lallai Yaro, bazaka daima min boye boyen ba?
Ajiye cukalin yayi sannan yace”
Bafa wani abu bane fa Hajjah nina rasa meke damuna ne, kawai fah Hajjah dazon ne mukaje gidan su Fatima nida Khadija, wai taki min mgn kwata kwata”🤔
Fara’a Hajjah ta sake cike da murna tace”
Me yayi zafi toh?
Murmushi yayi kadan yace kinsan Babanta nakoya Mata fadin rai wai cewa take tafi Khadija kyau Dan nace ba hakaba kuma tabar mgn Dani”
Dariya Hajjah tayi toh Kai kajawo rigimar ashe, Kai meyasa kace mata ba haka ba?
Ni kawai kalmarce batamin ba Hajjah”
Hmmm toh ai shikenan yanzun meyasa kake damuwa??
Tsaki yaja kadan tare da fadin”
Banason sabon yanayin nafi son yadda muke adah”
Toh ai saika rarrasheta kabata hakuri”
Haba Hajjah ni ko Khadija banawa bawa hakuri dan namata laifi ballantana ‘yar Khadija”
Eyeee🤔 haka kace?
Toh Hajjah kina kallo fah Khajima rasa inda zatai dani take yi, to nikuma saina gurfana agaban ‘yarta, dole zata sakko Hajjah indai nine”
Wata irin dariya Hajjah tayi sannan tace kudai kuka sani”
Kadan yaci abincin ya mike duk wani iri haka ya karasa wuni duk wani dan shiru da zaiyi fuskan Fatima yake hangowa”
*******
Bayan Sati 1, Khadija zaune adakin Innarta, hira suke ita da Inna Ahmad ya shigo”
Manyan kayane ajikinsa yana zuba kamshi ya tsuguna ya gaida Inna sannan ya nemi guri ya zauna”
Kallonsa Khadija tayi ta kauda Kai sannan tacigaba da cewa Inna ai tabani Mamaki sosai”
Dariya Inna tayi yo ai yaran yanzun da wayaun su ga rashin kunya yaran da kuwa Ina, kuma fa anawa kamarta auren zama fah zatayi daram”
Karaf sukaji Ahmad yace wacece??
Mutuniyarka Fatima, wai kaji dan rashin kunya tacewa Uban amata aure”
Hada rai yayi sosai daker ya iya bude baki yace”
Yariya me kwazo”
Kwazo? Kwazon me?
Tsaki yaja tare da fadin ke kika sani”
Tsaki taja itama tana fadin”
Oho inma dai dani kake nakusa aure kuma nina tabayi Kaine baka tabayi ba”
Murmushi yayi nima bazakiyi kibarni ba, ina me shaida miki rana daya zamuyi aure, kamar yadda nasha gaya miki”
Hmmm Yaro yarone Khadija tafada tare da ficewa adakin”
Inda sabo Inna ta saba da wannan halin nasu tun suna kanana dan haka murmushi kawai take, ganin Ahmad ma ya mike zai fita tace”
Ahmad halan bata gaya maka ta tura me nemanta gurin Alhaji ba ko?🤔
Cikin mummunan faduwan gaba yace”
Wadin Inna??
Hadizatu aita tura wannan yaron dake zuwa”
Cikin hade girar sama data kasa yace, Wai Inna kina nufin Khadija ce ta tura wani gurin Alhaji??
7 comments