Advertisements

Screenshot 20220209 135909 2

YADDA AKE LEMON KWAKWA DA MASARA

Posted by

YADDA AKE LEMON KWAKWA DA MASARA

 

Advertisements

YADDA AKE LEMON KWAKWA DA MASARA

Uwargida na kawo muku yadda ake sarafa Lemon Masara

 

Advertisements

KAYAN HADI

Masara
Kwakwa
Sukari
Madara
Filebo
YADDA AKE HADAWA

Da farko uwargida za ki samu masara danya sai ki cire ta daga jikinta, sai ki dafa ta.

Advertisements

Ko kuma ki siya a wajen masu saida dafaffiyar masara amma su baki mai laushi. Idan kika dafa ruwan ya huce sai ki tsame masarar ki markada ta sannan ki tace.

Sai ki sami kwakwarki ki cire bayanta sannan sai ki goga ta sannan ki markada ta ki kuma tace.

Idan kika kammala tacewa, sai ki sami mazubi ki juye dukkanin ruwan kwakwar da na masarar a ciki sannan sai ki sami madarar ruwa ki zuba.

(amma ana iya sa madarar gari ) sai ki dauko sukari ki zuba a ciki.

Sannan ki sa a cikin na’urar sanyaya abubuwa ta firinji ko ki samu kankara ki hada da ita.

Idan ya yi sanyi sai a dauko a sha.