SAMOSA
Advertisements
KAYAN HADI
filawa kofi 2
kwai 2
butter spoon 1
b.powde spoon1
albasa 2
nama kofi 1
maggi
gishiri
curry
mai
spices
YADDA ZAKI HADA
Advertisements
A soya nikaken nama Sama sama tareda albasa, saiki sa maggi da gishiri da curry da spices.
Ki tankade filawa kisa b.powder butter kwai gishiri saiki kwaba ki muraza tai laushi sai a yanka ta qanana kowane amurzashi har yayi fele fele, sai a zuba sai a zuba spoon 1 na hadin nama ciki alinka gefe biyun yadda ake nadata. Sai a datseta gefe gefen sai a soya.
Kuma ana iya yanka kabeji albasa agurza Kara’s a soya Sama sama a hada da nama. Kuma ana kwaba filawa da ruwa kamar kwabin spring roll idan an gasa a soya a mai.
Advertisements
6 comments