IMG 20211228 WA0002

Tirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka.

Posted by

Tirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka.

 

Tirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka.

A ranar Asabar ‘yan matan TikTok su ka wallafa bidiyo su na dukan abokiyar kwasar rawarsu a TikTok kamar za su kashe Tirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka. gidan iyayenta.

Murnahausanews sun wallafa bidiyon wanda daga bisani mutane su ka fito su na sukar aika-aikar, inda su ka ce lamarin yana kara kazanta don kullum sababbin salo ne ke kara bayyana a kafar.

An samu bayanai akan budurwar wacce aka je har gida aka lakada mata duka, Mai suna Suddenly, cewa wani rikici ne ya hada su da ita, hakan yasa su ka yanke shawarar binta har gida su yi mata dukan tsiya.

Tuni bidiyon ya karade shafukan sada zumuntar zamani inda kowa ya ke ta tofa albarkacin bakinsa.

Kamar yadda kowa ya sani, Kafar TikTok ya tashi daga wurin sada zumunta, inda ya koma wurin barar da mutunci.

Zaka ga babbar mace babu hijabi a jikinta tana kwasar rawa na rashin daraja. ‘Yan daudu ma ba a barsu a baya ba, zaka ga su na musayar bidiyo na zage-zagen juna tsakaninsu.

Tuni dama mutane su ka fara bukatar a rufe kafar TikTok saboda tabarar da ake gwabzawa kuma yana lalata tarbiyyar yaran jama’a.

Akwai wadanda su ka dinga kira ga ministan sadarwa, Ali Isa Pantami akan ya taimaka ya rufe kafar don bata da wani amfani.

8 comments

  1. Pingback: free cams
  2. Pingback: Aviator Game
  3. Pingback: Cbd oil uk
  4. Pingback: checkslip

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *