
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 15
Eh, ta fad’a tare kara matsawa can gefe.
Jimmm yayi zuwa can yace shikenan matsawa yayi can gefe tare da daukan gilashin sa yasa a Ido, tun daga kalokacin be sake mgn ba tsayon lokaci saidai ya Dan juyo ya dubeta ya sake dauke kan sa.
Da yamma lis suka iso tanajin yabawa driver Umarnin ya kaishi gidan Yaddiko, kara kulewa tayi dan ta kosa ta rabo dashi, saidai abun da ya bata mamaki suna isa ya bude motar ya fice tare da fadin, ni anan zan tsaya ka karasa da ita gida.
Rufe motar yayi ya juya abun shi, bayan sa tabi da kallo tare da saurin kawar da abun da zuciyar ta ke kawo mata.
Koda suka isa gida sosai Su Ammi sukayi murnan harma suke tambaya Ina Modibo, nan take sanar dasu gidan Yadikko ya sauka.
Batafi Minti goma da shigowa ba Safna ta shigo, bayan ta gaida Ammi tace’ ” Ammi Ina yake naga motar shi alamar ya dawo, nakira wayar shi kuma be daga ba.
Ai ahanyan wai ya sauka ance yana gidan Yadikko.
Jimmm tayi sannan ta juya ta fita.
*****
Yadikko ya jikin?
Alhamdulillah Modibo Ina samun sauki, Suraj yace min kayi tafiya.
Eh nayi, yanzun ma dawowata kenan.
Allah sarki, sannu da hanya, wanni garin kaje?
Naje Yobe ne Yadikko inda na amsa maganin Nan na kafa.
Kafar ce ta tashi?
A’a Rahma nakai gidan su.
Allah sarki, daman ko Ina son mgn akan ta, wai me kake jira da ita ne? Ina ganin zamanta beda wani amfani agidan, idan tana d’akin ta sai yafi musamman yanzun da kake shirin yin aure.
Yadikko ni abin da yasa na barta Ina son tai karatu, lokaci ya riga da ya canza…..
Katse shi tayi da fadin, a’a ba wannan bane da lili, Suraj ya gaya min daman can bason ta kake ba, ka amso aure ne kawai dan ka taimaki yariyar tai karatun
Ki rabu da Suraj yadikko shirmensa kawai yake yi, banda abin shi ai wannar mgnr be taso ba.
Ta taso Mana, tunda karshen ta dai rabuwa zakayi da ita.
Jimmm, yayi zuwa can ya dayo ya kalle ta yace, “ba wannan mgnr Yadikko, sune dai suke ganin kamar zan aikata haka, nifa yanzun ma abun da ya kawoni kenan, kasa yayi da idon shi, Yaddiko nifa narasa meke damuna ne kwana biyu banda wata nutsuwa, kinga ita Safna nariga nasan halin ta, kuma nagama da ita akan mgnr auren, amman ita wannan yariyar sai wani taurin kai take min, kuma Yadikko daga jiya zuwa yau ta tsoro dashi, dan da ko iya daga idonta ta kalle ni Bata yi bare harta gaya min mgn, kuma wani abu da yake daure min kai halin da take nuna min ya dame ni Ammi.
Ka gaya mata zancen auren naka ne?
eh ta sani.
Toh Modibo banda abinka ai mu mata haka muke kishine ke damun ta ba wani abu bane.
Kishi Yadikoo?, wata mgn Bata taba shiga tsakanin da ita ba fah.
Hmmm, Modibo ai matarka ce, dole taji zakayi aure ranta ya sosu, musamman zataga ita ashirme ka dauke ta.
Ban dauketa a shirme ba fa Yadiko, Ina Bata damar gaya min abun da take so kamar yadda nake bawa Safna.
Ai Safna acikin dakin ka take, itako yanzun nan ka gama cewa wata mgnr bata taba hadaka da ita ba, kuma tana matsayin matar ka ta aure, wadda Bata riga ta tare ba agidan ka. Amma ka tafi ka nemo wani aure ita bata Kai ba kenan…..
Ba haka bane Yadikko, ya fada Yana kallon cikin idon Yadikko.
Ai ita abun da zata gani kenan, barin gaya maka ko bata son ka dole abun yai mata ciwo, Bari kaji Modibo yariya ma ka nemeta da aure ita da bakinta tace Bata sonka wlh taji zakayi aure saitaji babu dadi bare ita da ta taho da auren ka akan ta.
Shiru yayi tsayon lokaci, sannan yace, toh amman nifa Yadikko wannan auren kema kinsan kusan dole akasa ni.
Ai Kai matsalar ka komai maimarta yace maka saikace masa toh, amman badan haka ba uzuri zaka bashi, badai burin shi ka kara aure ba saikace mishi ka kara, amman saika Bari abun har ya kara nisa.
Ajiyan zuciya Modibo yayi tare da fadin, ” yanzun Yadikko kina ganin mgnr auren ne yasata haka, gaba daya fa bata saurareni ba, akarshe ma saita ce wai karna kara mata mgn, wlh Yadikko tunda nazo duniya da wayau na dai, bantaba rasa amsan da zanbawa mutun ba sai yau, gaba daya sai naji na rasa yadda zanyi.
Dariya Yaddiko tayi sannan ta tashi ta zauna Fuskanta cike da Murmushi take fadin, “Yau Allah ya kamo mana Modibo, ai inda Safna ce tai mgn taso mata kake yi, sai wannan da ba baki gare ta ba aka rasa yadda za’ayi da ita, a’a lallai abu yayi kyau, to nidai shawaran da zan baka ka maida hankalin ka ga matar ka.
Shiru Yana nazari, idan Rahma kishinnsa ke damun ta toh sonshi take kenan, cikin irin wannan tunanin ya tafi gida Koda yaje dakin Ammi Basu hadu da Rahma ba haka ya wuce baya wani jin dadi.
Ammi nata shirye shiyen biki hakama can Kanon suna ta shiri, ranar da suka cika kwana hudu da dawowa tana shiga daikin Ammi taga akwatuna har sati hudu adakin Ammi, kallo d’aya ta masu
Ta dauke kanta domin ko ba,a gaya mata ba tasan kayan auren Modibo ne
Ammi ta gaida tana kokarin juyawa tace dawo ki zauna.
Kallon Ammi tayi sannan ta dawo ta zauna kamar yadda Ammi tace.
Tana Zama Modibo na turo kofar, daga kanta tayi ta kalleshi sannan ta kauta idonta, muryan mace taji abayan shi Dan haka ta sake daga Ido sukayi Ido biyu da Safna, hannun su cikin najuna ta hanga aranta tace ji wani rashin kunya, juyawa tayi ta kalli Ammi sannan ta juya ta kalli Modibo dake rike da hannun safna, kananan Kaya ne ajikin shi, haka itama ta matse jikinta tam, kai kace intai numfashi zasu barke.
Zama sukayi daf da juna Ammi Safna ta gaidar cikk da fara tare da daura duk hannun ta akan cinyan Modibo, kayan dake gefen akwatin take kallo.
Tagefen Ido Rahma ke kallo su acikin cikin ranta take jinjina Rashin kunyan su, babu wani alamar kunya ga Modibo ko ga Safna, kallon Ammi ta sake yi akaro na biyu gani tayi ita hankalin tama baya gurin so, kokarin ware kayan take tana fadin, ” toh Safna sai ki zaba.
Lekowa tayi tana kallon Sabbin akwatuna hudu dake here adakin kala daban daban juyawa tayi da kallo Modibo cike da Murmushi tace Hamma na wanne zan dauka?
Lumshe Ido yayi Yana fadin, ” ki dauki wanda ya miki”
A’a toh ni ka zabar min.
Ki zaba da kanki zaifi.
Nifa fa zabin ka nake so.
Satan kallon Rahma yayi yaga idonta akasa sai wasa da hannun ta take.
Muryan Ammi taji tana fadin, tunda ta baka dama ka daukar mata mana.
Muryan Mudibo taji Yana fadin to ki dauki wancen.
Angama taji Safna ta fada sannan ta mike tana fadin, ” Muje”
Jiki Ina zuwa ya fada yana Satan kallon Rahma.
Mikewa Rahma tayi ta nufi toilet din Ammi, bayan fitan Safna Ammi tace yaushe za,akai kayan?
Ammi duk lokacin da kuka shirya kawai.
Amman kasan…..
Kakarin Aman da taji cikin bayin yasata dakatawa tare da fadin, ” kamar Rahma amai take.
Da saurin sa ya daga kansa ya kalli kofar bayin, tabbas kakarin amai ne ke tashi, mikewa Ammi tayi ta nufi bayin kusan minti goma sannan suka fito tare tana rike da ita.
Bakin gadon ta zaunar da ita yayin da Rahma ta gyara zaman ta tana kallon kofar bayin yayin da tabawa su Ammi baya.
Sannu yace ahankali, saidai beji ta amsa ba, dan haka ya kara daga murya yace, ” Aunty sannu”
Wannan karon ma beji ta amsa ba dan haka yabita da Ido kawai, Ammice tace idan ya lafa miki kizo ki zabi naki…..
Ammi ni bana so, ta fada ahankali.
Waigowa Ammi tayi ta kalleta tace, ” bangane ke baki so ba, wanni irin shashanci kenan?.
Ai Ammi inada kaya, abarshi aka sun isa nagode.
A’a bazai yiyuba, juyawa tayi ta kalli Modibo yace, “Modibo, ko wani abu ya faru ne?
Unaisa ya kalla tare da fadin, ” saidai a tambaye ta Ammi”
Rahma wani abu ne?
A’a Ammi ba komai.
Toh hakki kine maza ki sakko ki dauki naki.
Ni na yafe.
Cike da Mamaki Ammi take kallon Rahma, muryan Modibon taji Yana fadin, ” barin zabar mata Ammi….
Kafin ya rufe baki ta mike tazo ta gaban shi ta fice adakin.
Baki Ammi ta saki tana bin Unaisa da kallo harta fice sannan ta juya ta kalli Modibo tace, ” yariyar Nan da nace ka sameta kayi mgn da ita na fahimta kayi kuwa?
Ai Ammi ni bata mgn Dani, bansani ba kila dan taga kwana biyu Ina barin ta tana min abin da taga dama ne, yanzun ammi ki sameta kiyi mgn da ita ta gaya miki abin da take so, kuma ki gaya mata tashiga hankalin ta banson rashin kunya, mikewa yayi afusace ya fice adakin.
******
Momy kince min fa baza’ayi auren ba, amman Momy sai shirye shiyen suke yi, Momy hankalina ya tashi, bazan iya bada Fahat da wata ba, kince inta dannewa kar in nuna kishina nayi Momy amman inata zuwa makura.
Safna ki kwantar da hankali, zakisha Mamaki na, Modibo nakine ke daya babu wacce ta isa ta rabe shi, kema kinsan bazan kashe kudina a banza ba, kuma duk tsaya wahalar da akasha abaya baza’a shata agaba ba, Ina da dibara guda biyu, daya sabo daya irin na waccen karon.
Zaro Ido Safna tayi, Momy banson irin na baya Kar azo a samu matsala.
Safna nidai ki kwantar da hankalin ki kibar min komai a hannu na kawai.
Shikena Momy Ina jira, Momy dan Allah kibani Mama ki, sauke wayar tayi tare da sakin murmushi.
******
Mutumin da kike bazatar dani akan sa ya nuna miki iyakar ki, aure shi zaiyi me zai dake?, nasan kinyi tunanin kinyi miji daya tamkar dubu, dariya yayi tare da cigaba da fadin, ” gara ki canza tunani, idan ba haka ba kuka yanzun kika fara.
nasan wannan kukan naki be rasa nasaba dayin auren sa, Ina Kika baro Afnan din da take fadin ki, ya kikazo bayan gida kika labe kina kuka me Modibo?
Kara mannewa tayi jikin bango dalilin Kara shigota da yake, saidai har yanzun ta gaza cewa komai illa kallo kawai data bi Magaji dashi tare da karanto duk wata addu’ar neman tsari datazo bakin ta.
10 comments
Comments are closed.