Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 25

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
by
Fadila Lamido

Page 25

Amsa taji an bawa matar da cewa eh ita ce, tuni jikin Unaisa ya fara canzawa yayin data shiga raba Ido, kaba daya ta rasa nutsuwa tare da rasa abun yi, dan haka ta mike kawai ta fice adakin, zuciyarta cike da tunani barka tai.

   Tun daga lokacin Unaisa Bata Kara komawa dakin ba, duk da tana son ganin Dada, Amma idon mutane ya mata yawa.

    Hakanan kuma taji haushin zuwa da matan malam Ayuba da Dada tayi sosai take jin zafin duk wani wadda ya danganci gidan.

    Sai dai amryan da taji an kikira ta ya danne damuwar komai dake cikin ranta, dan haka ta kwanta bayan su Afnan kawai cikin tunani.

.       Agefe daya na zuciyarta kuwa tunanin zaman Safna take adakin Ammi.

    Misalin karfe 8 na dare Ammi ce ita da Safna suke kokarin shiga falon Abba, bayan sun zauna ne Safna ta gaidashi kanta akasa yayin da Ammi tai masa sannu da hutawa.

Jimmm yayi na tsayon lokaci zuwa can yace, Safna me ya had’aku ne?, tambayar yayi kawai batare da ya dubeta ba.

   Bata iya cewa komai domin ta rasa ma me zatace ne?

     Safna Ina tambayan me ya hadaku ke da Modibo.

   Hawaye ta fara sharewa dan haka falon yayi shiru tsayon lokaci zuwa can Ammi tace, ” Toh Alhaji akira shi bana.

    Da inason inyi mgn da ita kafin inganshi, Safna inajin ki.

     Kanta akasa kawai ta kasa cewa komai, Ammi ce ta sake cewa Alhaji tunda bataza gaya ba, akirashi kawai ya dauki ta suje suyi hakuri gaba dayan su.

   A’a ba’ayin haka inji Abba, sannan ya cigaba da cewa, irin hakan ne kesa wata Babban barna ta auko gara aji matsalar, wayar sa ya d’aga ya Kira Modibo sannan ya sauke wayar.

   Nan danan saiga Modibo ya shigo fuskarshi murtuk.

    Zama yayi batare daya kalli Inda Safna take ba, gaisar da Abba yayi, bayan sun amsa wajen ya danyi shiru.

       Modibo jiya Maman ku tamin waya cewa ga Safna tazo tace wai kace ta fitar maka agida, nakira wayar ka tun da lokacin amman ka rufe ta, me yake faruwa ne?

    Abba akan mgnr tarewan Rahma ne, Ina gaya mata tahau fada min maganganu inda take shiga batanan take fita ba.

   Jinjina Kai Abba yayi cikin gamsuwa sannan Abba yace, daman nasan bazai wuce akan wannan bane, tunda daidai gwargwado kuna zaune lafiya babu mejin Kan ku, d’agowa yayi ya kalli Modibo yace, “Kai kuma ai hakuri zakayi, da duk wani abu da zakaga tayi kasan mata da kishi, saika lallabata ka bita a sannu, zare Ido be dace ba anan gurin.

    Abba kureni tayi, tana min mgn Kamar ita ta haife ni, duk inda nake son ta saurareni taki, Wai ita saidai dai na zabi daya.

   Murmushi Abba yayi Yana kallon su yayin da Modibon ya cigaba da cewa, duk labarin auren da nake zuwar mata dashi zanyi Bata taba min haka ba sai wanna.

    Toh ayi hakuri, ke Safna kiyi hakuri, ki kwantar da hankalin ki, aini na dauka ma wannan auren kinsan dashi dan kinji tarewa bazaki daga hankali ba tunda an daura auren ai dole ta tare.
Dan Allah kuyi hakuri ku zauna lafiya, Kai kuma Modibo banson duka.

    Nasiha sosai yai ma Safna sannan yace mata ta shi ta koma dakin ta, bayan fita Safna ne Abba yaiwa Modibo fada akan koran Safna da yake yi.

  Harma ya kara da cewa ko baka auren Safna nan gidan su ne, dani da mahaifiyar ta kakarmu daya dan haka Kona aure tana da ikon zama cikin gidan nan.

                           *****
Safna na komawa dakin ta ta zauna afalon ta, ajiyan zuciya taita saukewa, zuwa can ta kira Momyn ta Kamar jira take ta dauka.

     Safna Yaya kin koma?

   Eh.

  Alhamdulillahi, kin bani haushi Safna, ke wacce irin wawiyar yariya ce?, idan kikai wasa saita kwace miki miji kinaji kina gani, haba ki kwanatar da hankalin ki mana.

   Toh Ammi me yasa be gaya min da wuri ba?

     ki rabu da wannan mgnr, kota shigo zata fita, jiya nace Kurfi, yace lokaci ya kore amman mu Bari kota shiga zata fita, toh kiyi hakuri Safna laifina ne nice nayi sake tun farko.

   Hawaye Safna ta share sannan tace Toh Momy yayi Mana wani abu mana wadda Hamma Modibo bazai kusanceta ba.

   Safna duk abun da za’a iyayi komenene zansa ayi ki kwanatar da hankalin.

    Ammi kina gani har marina yayi.

Dole ya mareki Safna, kinyi tashin hankali, kishi ya rufe miki ido, kuma kinsan halin mijin ki a tsaye yake kamar nonon maza, kinfi kowa sanin halin shi baya daukan wargi, kinsan da wannan halin nashi Kika makale sai Modibo, tunda Kika fara son Modibo Safna nake kashe kudi, yanxun gaki adakin shi, kiyi hakuri Mana, wlh Safna idan har Kika Bari Modibo ya sake ki bazan sake kashe sisina ba, ki zauna cikin gidan ki kuma bazan Bari ki wulakanta ba, yadda Kika saba kwanatar dakai hakan zakiyi sai muci Nasara batare da zargin kowa ba akan mu.

    Cike da gamsuwa tace toh Momy.
yaushe zaki zo toh.

   Gobe da Sassafe zamu taso, ki saki jikin ki ayi komai dake karnaxo na sabo kina cikin damuwa, akwai abubun da yabani zan taho miki dashi, idan ba kin kwantar dakai ba zaki lalata Mana Shirin mu, ki saki jikin ki kija kirman ki na uwar gida ta hakane kowa sai saki jiki dake,

   Toh Momy, sai kunzo.

  Da haka suka rabo.

                  *****

Dada wai bikin Afnan din kukazo shi ne Kika kaso su ‘yan wannan gidan?

    Eh, Daman nasan bazaki so zuwan su ba, Modibo yaje har gida ya gaya masu sannan yace idan akwai masu zuwa zai turo mota.

    Yaushe yaje Dada?

   Sati guda kenan da zuwan sa.

  Amma shine beje Dani ba?, yamutsa fuska Unaisa tayi.

  Yaje dake kiyi me acan din?, nice dai kuma gani nazo kin ganni.

   Toh Amma Dada ki mishi mgn duk sanda zashi ya dinga zuwa dani dan Allah.

    Kema ai kina da baki Unaisa, ki gaya mishi Mana.

   Nifa Dada ban iya doguwar mgn dashi ba, muna dad’ewa ma bamuyi mgn ba.

   Lallai Unaisa, baki da hankali har yanzun, kuna gida daya ko daidashi bakiyi kenan?

   Dada idan Mun had’o muna gaisawa.

   Toh Allah ya shirye ki, yanzun gashi zaki tare ai a gidan shi saiki maida hankali dakyau tun da bake daya bace gurin shi.

    Dada ai anfasa tarewar yanzun.

   Haba dan Allah? sai yaushe kuma?

    Yace in shirya a hankali.

   Ki shirya a hankali, uban me zaki shirya?

    Haka yace Dada, yace idan na gama shiryawa saina mai mgn.

     Eh, tunda kece mijin ba?, aina dauka kinyi ahankali Unaisa, yanzun kenan ke cikin duhun kai aka barki, daman yace daga ranki ya baci saiki kama amai, ke ba karamar yariya bace ki maida hankali ki, mgnr tarewa tana nan, kawai ya gaya miki hakan ne, wlh Unaisa ba karamin dad’i naji ba da yazo min da mgnr tarewar ki, Modibo mutum ne baki da abun da zaki saka mishi dashi, ko ayanzun ya daga darajar ki, ana fad’an mgnr tarewar nan kowa cikin Unguwar nan cewa yake zaizo, abun Mamaki harda maza, lokaci daya da Allah yaso ya daga darajar ki saiya jeho miki shi, yanzun ke wannan ba abun farin ciki bane awajen ki?

     Hawayen daya taru a idon ta ta matso ya fito sannan tace, ” dama tarewar tana nan ne?, shifa yace idan na shirya in mai mgn.

    Gatse ya miki, mgnr na nan har an kaimu munga guri, mutanenan sun da Mutunci komai sun zuba miki agurin ko ‘yar da suka haifa sai haka, banason aji kanki ki nutsu ki maida hankalin ki waje daya, yadda ya nuna miki halin daddako kema ki nuna masa, dan Allah dan annabi, ayanzun Modibo Yana da ikon zaba miki miji kibi Umarnin sa ko kinaso ko baki so bare kuma shi kanshi.

  Yadda take shashakar kuka yasa Dada kallon ta tare da fadin, ” kin fara koke koken naki ko?, nasan be wuce kice baku saba ba, a hankali ake sabawa kuma shida yake sama dake beyi wannan tunanin ba saike? ki kwantar da hankalin ki kindai ji abin da na gaya miki.

    Kanta ta d’aga ahankali alamar eh tare da hada kanta da guiwa.

   Mikewa Dada tayi ta fita adakin yayin da Unaisa ta koma bakin gadon ta kwanta rufda ciki tana share hawaye.

    Xuwa can ta mike da shiga bayi adadai wanan lokaci su Afnan suka dawo jin kakarin amai Afnan ta fara dariya tare da bin bayan Unaisa.

        Fitowa tayi tana rike da ita yayin da take danne dariyar ta, kawa yen nasu ma dariya sukayi tare da fadin, lallai Unaisa kedai matsoraciya ce.

    Afnan ce tace ai tunda naga ta saki jikin ta nasan Hamma na ya kifeta.

    Dariya suka sakeyi yayin da Unaisa ta zauna kawai bakin gadon tana kallon su.

    Afnan ce ta sake cewa gara da yai mata haka, da yanxun ta rame, ai banso ki sani yau ba ma, naso ne sai Daren da za’a Kai masa ke.

     Dariya aka sake yi, kallo kawai Unaisa take binsu dashi batace masu komai ba.

                       *******

Ana gobe daura auren Afnan da daddare, Modibo ne ne shida Suraj zaune Saman motar Suraj din suna hira,  Suraj ne ya kalli Modibo yace, yanzun kenan gobe kaima ango ne?

    Lumshe Ido Modibo yayi sannan ya kalli Suraj ya lashe baki tare da fadin, hmm kasan wani abu ne?

     A’a saika fada.

  Banson in fada amman zuciyata ta kasa hakuri tana son lallai saita fitar.

  Dariya Suraj din yayi sannan yace to fadi Mana karta kashe ka.

  Kai kadai nake dashi wandan zan iya gaya maka wannan sirri da zuciyata kadai ta sani, ansha samun ranar aure har azo daf da bikin bantabajin daukin abun ba Kamar yadda nakeji wannan ba, bana so in sako Safna aciki, aje batun da agefe, wannan kadai naji ranar da aka saka yamin tsayo, sannan wuni ya kara tsayo, da daddare har tashi nake Ina dauka gari ya waye, wani lokacin saina duba agogo sai naga a she daren ma alokacin ya fara sabo da yadda nai balakin kowasa inganta a kusa dani.

   Cikin matsanan cin dariya Suraj yace, kanbura uba, wai Modibo dama can son yariyar keke ne?

    Hmmm bansan be zamce maka bs, ni dai kawai ranar da naga anzo neman auren ta wajen Abba kawai naji wani irin kishi ya mamayeni  ni kaina ban San Ina da kishin dayakai har haka ba.

  Lallai dacan baya munso muyi azarbabi, ni, Magaji da Muftahu, Ashe Wala Habaru matar Modibo ce.

   Banson wannan sunan banzan Suraj.

  Dariya Suraj yayi sannan yace, ” nabari, itama yariyar yanzun ta canza sosai kamar ba ita ba dafa ko mgn Bata son yi, yanzun ko saina ganta gurin Mama suna hira harda dariya.

      Eh,ai gwanace gurin dariya na lura, amman laifin Afnan ne ita ta koya mata.

     Hmmm Muma yakamata muyi ma kan mu fad’a muyi auren Nan dai, gashi mun tsaya kallon ruwa, dana sani ma ni nayi ciki da Afnan din.

    Murmushi kawai Modibo yayi yayin da Suraj yaja tsaki yace ni barin je gida Saida safe kuma.

                             *****

Safna zaune abakin gadon Modibo, hannun ta yasa lalle, kallon hannun yayi Yana fadin kinga yadda kikai kyau kuwa.

     Murmushi tayi tana me mishi kallon kasan Ido tare da fadin, ” Nagode”

       Allah kinyi kyau sosai to baki tuna min kanki ba ko sai anjima?

       Cikin Yar dariya tare da sa tafin hannun ta ta rufe idon ta tana fadin, ” wanni anjima kuma ni da nafara yiwa kanwata danadin karfin ka.

     Murmushi yayi har ya bada sauti idon shi akanta yace, Ok shiyasa jiya bakizo ba kenan?

          En mana, anjima ma akwai wani had’i dazan kawo maka irin na angaye.

      Murmushin ya kuma yi har yabada sauti har cikin ransa yaji farin ciki Yana kashe idon sa yace, ” dan Allah ba?”

       Da gaske Hamma.

    Toh saina ganki.

   Mikewa tayi tana Shirin fita yace, idan akwai wani abun da kike bukata kimin mgn ?

    Amsawa tayi sannan ta juya ta fita.

                              ******

Tun ranar dasu Dada sukazo Unaisa ta Zama wani iri, kullum arana batai amai da yawa ba tayi Uku, Modibo be nemita da har wannan ranar ta kasance ta daurin auren Afnan.

    Hidiman biki ake tayi, acikin hidamar bikin ne Unaisa ta gane cewa su Modibo jikokin sarki ne, duk wani shagalin bakin da akayi irin na gidan sarauta ne, bushe bushi kawai ake tare da buga ganguna musamman ranar da aka saka Afnan din a lallai, a harabar gidan akayi komai inda manyan mutane suka hallara, saidai duk shagalin da aka yi mata ne kawai sai maza irin na gida, duk irin kwalliyar da akawa Afnan irin ta aka mata, haka duk wani abu na al’ada da akawa Afnan itama ammata Shi, hatta da alkebar da akasa masu iri daya ce. har akayi duk abun da akayi ko gilmawar Modibo bata gani har yau tada kacen ce ranar daurin auren.

Misalin 1 da wasu yan mutuna gidan ya dauki bushi bushi wannan hakan ya tabbatar ma da matan dake cikin gida cewa an daura auren.

   Karan Motocin kake shigowa cikin gidan ya ya kara daga hankalin Unaisa.

    Yayin da Karan busan ke kada hanyar cikin ta, idan ko ta tuna yau a part din Modibo zata kwana sai taji Kamar ana karkatse mata hanjin cikin ta.

     Shiryasu a kayi cikin wasu tsadandun kaya nagani na fada, sosai suka fito ras dasu, tun ana masu kwalliya ake fadin sanar dasu zuwan Kabir da abokan sa, dan haka Afnan Allah Allah take agana mata kwalliya, ana gamawa kuwa ta mike ita da wasu kawayen ta suka fita Koda aka gama na Unaisa sauran kawayen nasu sunyi suyin da ita Amman taki fita, saidai Afnan batafi Minti 15 da fita ba ta dawo, hannun Unaisa ta rike fuskanta dauke da Murmushi tace, ” tason muje Hamma Modibo na kira ki.

 nnalillahi wa innalihir raju’un, me zan mishi ?

Yanatare da abokan shi, nidai yace in fito mishi dake, be wuce hoto zaku yi, Jan hannun Afnan ke yi yayin da Unaisa ke fadin, kice mishi sallah nake yi ni bazan iya ba…..

12 comments

  1. Pingback: useful site
  2. Pingback: fun88
  3. Pingback: pgslot
  4. Pingback: lekded987
  5. Pingback: sa-kat.de
  6. Pingback: 1win
  7. Pingback: SEO Las Vegas
  8. Pingback: Mega Moolah
  9. Pingback: Alexander Debelov
  10. Pingback: Tipico App

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *