Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 Page 26

Posted by

BA LABARI BOOK

BA LABARI BOOK 2

                        Page 26

Dariya sosai Afnan keyi ganin inda Unaisa ke makalewa, sakinta tayi sannan ta d’aga wayar ta ta karata a kunnen ta, zuwa can ta shiga Fadin, ” Hamma taki fitowa fa.

   Kashh Unaisa ta fada acikin zuciyarta take fadin wlh Afnan Bata da kirki.

   Wayar Afnan ta Mika mata ta tana fadin gashi yace in baki, ” karba tayi ta rike babu musu, ahankali tace Ina wuni?

   Batare daya amsa ba yace mata ki fito Ina jiran ki.

   Shiru tayi dan haka ya sake cewa ko in shigo in fito dake?

   A’a ta fada da saurin ta.

  Toh kizo yanzun nan.

  amsawa tayi sannan ta mikawa Afnan wayar, tare da mikewa.

   Afnan ce ta sake yin dariya tare da fadin, “amman wlh kinban dariya wai Kamar bake ba duk kinbi kin firgi ce.

   Nidai muje karkisa yaga mun dade ya shigo duk ga mutane.

   Cike da dariya afuskan Unaisa suka fara tafiya, Hannun su cikin na juna sai dai yanayin Afnan yafi nuna walwala da zallar farin ciki, yayin daka kalli fuskan Unaisa zata gane cikin firgici take.

      Suna fitowa bushe bushen ya kara yawa, cike gidan yake tab da jama,a maza da mata, daker ta iya tsayawa suka gaisa da Kabir din Afnan sannan suka wuce gurin da Modibo yake tsaye shi da abokan shi.

       Gurin su Magaji da Muftaho suka fara isa, kallo suka bisu dashi yayin da Unaisa tai saurin dauke kanta.

      Tunda ta hangi Modibo jikinta ya fara rawa, bama ganin nasa bane yafi daga mata hankali yadda yake tsakiyar maza da yawa, saidai Afnan tane rike da hannun ta harta isa gaban shi tana Mika mishi hannun Unaisa.

    Cikin sauri ya daga hannun shi ya amsa na Unaisa da Afnan ke mika mishi,  ji tayi Busan ya dawu gurin gaba daya, idon ta akasa tanajin yadda Abokan Modibon ke dariya.

       Afnan ce ta juya zata tafi Amman sai taga itama Modibon ya riko hannun ta ita ya fara kaiwa jikin shi sannan taji itama ya jawota jikin shi ya rungume su Yana kiran Magaji zo mana.

    Shima Magaji cike da Murmushi ya karaso tun daga nesa ya fara yi musu hoto, shiko Modibo fadi yakewa abokan sa ga kanwata ga kuma matata, sunbatan Afnan yayi sannan ya sunbaci Unaisa, yana tsaye tsakiyar su.

    Ganin ita da Afnan ne yasa ta danji sanyi cikin ranta harma ta dan saki jikin ta.

      Hotonan akai tayi harda abokan sa, daga can ya dago Afnan daga jikin shi Yana fadin, ” toh jeki kinbar Kabir a tsaye, nagode ko?

      Murshi tayi sannan ta wuce tana waiwayen Unaisa.

      Cikin tsananin jin kunya Unaisa take wadda yasa har yanzun ta kasa dagowa ta kalli  Modibo, saidai kamshin dake tashi ajikin shi yafi na kullum gaba daya ji take kamshin sa ya huda jikin ta.

     Sai dai itama Abun da Bata sani ba, gaba daya kamshin ta ya riketa Modibo gaba daya ya kasa rabata da jikin shi tunda ta tsaya agaban shi ya sumbaceta yafi a kirga.

    Wasu daga cikin abokan shine ke fadin, gaskiya wannan amaryan akwai kunya, gaba daya ta kasa d’agowa ta kalli mijin ta, daga can taji Muryan wani Yana cewa Amarya d’ago ki kalli mijin ki.

   Kunyace ta Kara rufe ta.

  Ji tayi wani daga dayan gefen ya sake cewa, Amarya Yaya sunanta ne?

    Magaji taji ya bashi amsa da cewa sunanta Rahma.

    Yayin dataji Muryan Mutumin yace _Rahma_ dago ki kalli Modibo.

   Dariya taji Modibon nayi tare da fadin bazata iya ba.

     Tahowa mutumin ya fara har gaban su Yana fadin, aiko saita kalle ka, Rahma Amarya kalli angon ki.

    Rasa inda zatasa ranta yasata fadawa akan kirjin shi sosai take boye fuskan ta ajikin shi, rungume ta sosai Modibo yayi Yana fadin, Isma’il ka rabo da ita bazata iya ba.

    Dariya akaita yi agurin tare da shakkiyanci irin na abokai, alama yaji tana kuka, dan haka ya fara buga bayan ta cikin sigar lallashi, d’aga wayar yayi da hannun sa daya daga can ya shiga fadin Afnan zo ki maidata ciki.

     Nan danan saiga Afnan, dago Unaisa yayi yana fadin rakata ciki, har yanzun abokan nasa dariya suke yi.

   Dakin su Afnan ta maida Unaisa kwanciya tayi a Kan gadon tayi rufda ciki tare da cire daurin dan kwallin ta.

  Ahankali zazzabi yazo ya sauka ajikin ta sai yamma Dada ta shigo, tana fadin, Unaisa lafiyan ki kuwa?

     Dada banda lafiya.

  Oh nidai na bani, Unaisa sai yaushe zaki daina wannan shashancin?

     Dada kaina Kamar zai fashe.

  Toh Allah ya sauwake, Ina zuwa, juyawa tayi ta fita Bata dade da fitaba saiga ta sun dawo tare da Ammi, taba jikinta Ammi tayi tace, Aiko jikin da zafi, magani ta ciro ta Mika mata Tasha sannan sannan da kalli Dada tace, ko za’a bari ne ita sai gobe ?

   Cikin sauri Dada tace a’a ai duk gida ne a kaita kawai tunda ba wani waje bane me nisa.

                        *****

Misalin karfe takwas na dare aka kawo motocin tafiya da Afnan, zuwa wannan lokacin zazzabin dake jikin Unaisa ya sauka, dan haka aka shirya ta, Dada taso a fara Kai Afnan har da Unaisa amman Ammi tace abarta kawai tunda ba wani dadi take ji ba, gaba dayan su falon Abba aka kaisu inda yai masu nasiha me ratsa zuciya akan zanan aure, sai alokacin Afnan din ta fara kuka har suka baro falon kuka take, itako Unaisa zuwa wannan lokacin babu ko digon hawaye afuskarta sai jikin ta ta babu kwari tana lullube cikin gyalen ta me Dan Karan kyau.

    Bayan sun fito  falon Abba tanaji aka saka Afnan amota sannan itama aka nufi part dinta da ita, muryan mata takeji da yawa akanta yayin da ake ce mata shiga da kafar dama.

     Idonta arufe yake tasan dai ta shiga cikin part din Modibon yanzun, tafiya suke yi yayin da takejin gud’a a saman kanta, a bakin gadon aka zaunar da ita muryan Yadikko taji tana fadin, ” toh Rahma Allah ya bada hakurin zama, kibi mijin ki ki mishi biyayya, tabbatarwan da tayi Yadikko fita zata yi yasa ta riko hannun ta jikinta na buga uban rawa.

     Komawa Yadikko tayi ta zauna agefenta tare da zuba mata ido, su biyu suka rage adakin dan haka Yadikko ta kalleta tace, Yaya aka yi?

Yadikko kada ki tafi, Unaisa ta fad’a tana zubar da hawaye.

    Yadikko ji tayi gabanta ya fadin, tsayawa tayi tai shiru tana kallon Unaisa cikin Ido, dafe kirjin ta tayi tarasa mene dalilin faduwan gaban ta, Unaisa ta Kara kalla, wani kyau ta mata, azuciyarta take tunin yanayin Unaisa kamar ba ‘yar Nigeria ba, yin wannan tunanin yasa yanayin jikinta ya canza, cikin sauri ta d’aga waya zuwa can tace, ” Suraj zoka kaini gida banjin dadi”

   Amsawa yayi da toh kawai duk da cewa yaso ya raka Modibo d’akin Amarya, zuwa can Sukaji Muryan Suraj din yana fadin Ammi muje.

Mikewa Ammi tayi yayin da Unaisa ta sake rike Yadikko, kallon ta tayi tare da fadin, ” kiyi hakuri zan dawo kinji, idan na zauna anan gurin me zan miki? yau banji dadi gashi dare yayi, zamewa tayi daga rukon ta Unaisa ta mata tafice afalon ta samu Suraj suka fita tare.

     Ganin Yadikko na share hawaye har suka shiga mota yasa Suraj ya tsaya Yana kallon ta zuwa can yace, Mama menene?

    Ajiyan zuciya Yadikko tayi tare da share hawaye sannan tace, “Suraj yariyar nan ta shiga raina, ina masifar son ta.

Cike da mamaki Suraj ya kalli Yaddiko sannan yace, “wacce yariyar mama?”

   Amaryan Modibo.

    Jimmm yayi Yana kallon yadda Yadikko take sauke numshi dan haka yace dan Allah mama ki kwantar da hankalin ki karki data ciwon ki, menene abun kuka.

   Waigawa Yaddiko tayi ta kalli part din Unaisa sannan tace, ” na baro ta tana matsanancin kuka fah Suraj”

Uhum lallai ma Mama wlh kin ban Mamaki, haka kawai akan wannan yariyar zaki dinga zubar da hawaye, Afnan da take jinin mu ai tana kuka aka afitar da ita daga gidan nan, tundaga nesa nakejin muryan ki kina mata fad’a, sai wannan yariyar zaki dinga ma kuka saika ce wannan yaron da kika kwallafa ranki akan shi, nifa mama banason irin wannan, wlh haushi nake ji, wato yanzun abun ma ba a iya wannan yaron kawai ya tsaya ba harda ‘ya’yan wasu.

  Share hawayen Yaddiko tayi tare da fadin, ” tsaya na sauka, ni yarka ce da zaka dinga daga min murya?.

     Ajiyan zuciya yayi tare da fadin toh kiyi hakuri.

   Ka saukeni nace Modibo ya kai ni.

  Nabari fa Mama nace kiyi hakuri, amman nasan ni kad’ai nake son ki, ke baki damu dani ba, hankalin ki Yana can wani guri.

Toh me ya kawo wannan mgnr kuma?, kawai dai kasa hakan a ranka ne, akwai uwar da zata haifi d’anta ne tace Bata damu dashi ba, Kai na fara samu, kamata yayi ace kai ka tsaya mun, anemo min shi, tun da baban ku ya zuba Ido kawai sabo da yaga ba jinin shi bane.

    Kallon Yaddiko yayi sannan yace shikenan yanzun ki fad’a inda kike son ayi  nikuma na miki alkawarin zan yi yadda kike so, Kuma Baba da kike mgn akai ai Yana iyakan kokarin shi kawai dai idon ki ya rufe ne bakya gani.

  Eh bana gani, sauke ni in Kira Modibo ya Kai ne, shika d’ai ne baya korafi duk abun da nace mishi saidai yace min to amman kaida uban ka kun dinga korafi kenan.

   Ajiyan zuciya yayi sannan yace, kiyi hakuri toh nabari.

                         *******

   Misalin karfe goma na dare Modibo ya fito daga wanka, bayan ya gama goge jikin shi ya dauko wasu sabbi kaya ya sanyan, turare ya fesa sannan ya dauki Babban rigar yana kokarin sanyawa Safna ta shigo.

    Ongo kasha kamshi ta fada yayin da take dire tiren dake hannun ta.

    Waigawa yayi ya kalleta yana gyara zaman rigar sa tare da fadin, sai yanzun kike zuwa?

       Ina da baki ne Hamma na, inata Allah Allah in kawo maka wannan hadin.

   Kallon kofin yayi tare da fadin meye shi.

      Wani Hadi ne na musamman dan kada kanwata ta raina ka.

  Dariya yayi har hakoran shi suka bayya na yana karya hularsa yace, ” bakya kishi ne?

   Tambayar tazo mata a bazata dan haka ta dan diririce, bakin gadon ta zauna sannan tace idan ma inayi yaya zan ai dole inso abun da kake so.

       Haka ne, nagode Safna Allah yai miki Albarka.

     Shiru sukayi har ya daura hular a kansa sannan ya kara daukan turare Yana fesawa.

        In miko maka ne?

   Mugani ya fada batare daya dubeta ba.

   Daukowa tayi ta Mika masa, idon ya zubawa kofin sannan ya kaishi hancin shi Yana sunsunawa zuwa can ya dago yace dame aka hada shi?

    Kai!! Hamma ni ban sani ba.

Baki sani ba?, toh Ina Kika samo shi?

Wata matace dake kawo min tazo dashi.

Ok kin saba saya kenan kina sha ko yanzun haka irin tarkacen nan ne.

   Hamma Yana fa da kyau ana Shan shi ba wani abu bane.

    Murmushi yayi sanan yace na gane, nawa Kika saya?

     Cikin wanni irin yanayi tace 10k

  Hannu yasa a aljihu ya ciro kudi be kirga ba ya mika mata tare da fadin, ” na biya kudin, bayan ta amsa ya dire kofin akan madubin yana cewa, ” amman fa bazan sha ba.

    Wai Hamma sabo da me?

    Saboda Lafiyata lau Safna, ko kintaba ganin alamar ragunta a tattare dani?

   A’a basai da ragunta ake sha ba, Nima abun da yasa na karba naji tace na angwaye ne.

     Nagane ai, shane kawai bazan yi ba, kema idan kinasha ki bari…..

Batare daya rufe baki ba tace an gama.

   Ko kefa, ya fad’a Yana Murmushi tare da fadin nagama zaki min rakiya ne?

Eh to amman kaje kawai su Momy sunan nan suna jira na.

    Ok toh Saida safe yafada Yana mata murmushi itama murmushi tayi yayin da yai tsaye afalon harta fita,

  Cikin matsanancin kuka ta fada jikin Momy, yayin da Momy ta rungumeta tana rarrashin ta, ko Bata fada ba tasan Modibo yayi mata Sallama ne ya tafi dakin Amarya ko ita tanajin ciwon abun bare Safna da take tsananin son mijin ta

Shikuwa Modibo bayan ya tabbatar da fitan Safna ya  bude kofar da zata sada shi da falon Rahma ya shiga, iya tsaruwa gurin ya tsaro, dakin da aka ware domin bacci ta ya nufa, yayin da yaji wani kamshin ya daki hancin shi.

8 comments

  1. Pingback: winomania casino
  2. Pingback: เกมไพ่
  3. Pingback: hit this link
  4. Pingback: miesyrup
  5. Pingback: cosmetic treatment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *