Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 33

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 33
Murmushi yayi har zuciyar sa, sannan ya mike ya fito yayin da ya samu Mama da Suraj zaune afalon sa.

Cikin girmamawa ya gaida Mama sannan suka mikawa juna hannu shi da Suraj.

Mamace tace Ina sarauniyar zazzabin jikin da dama dai ko?

Alhamdulillah Yadikko, ta samu sauki, tana cikin, ki shiga mana.

A’a bazan shiga ba, tunda ta samu sauki ai Alhamdulillah.

Naci Modibo ya sawa Yadikko akan ta shiga amman tace a’a, dan haka ya daga waya ya kira ta tare da fadin, ” kizo ga Yadikko tazo duba jikin ki.

Sauke wayar yayi, babu jimawa saiga Unaisa ta fito cikin hijjabin datai sallah, babu laifi yanzun kam jikin ta yayi kwari.

Kasa karasawa tayi gurin Yadikkon, Sabo da saita wuce ta gaban Modibo dan haka ta zauna tare da gaida Yadiko batare da ta kalla inda Suraj yake ba.

Jikin Yadikko ta tambaye ta, yayin da tace, “Alhamdulillah”

Muryan Suraj taji yace, ” toh ai saiki tashi muje ko?

Cikin fada Yadikko tace bazan tashi ba.

Dan murmushi Modibo yayi tare da fadin, “yauwa Yadikko, kinji yadda Suraj ya kirani dazun kuwa?, har wani tada min jinjiyar waya yake yi wai in gargadi Rahma karta kara Kiran ki…

Rabu dashi Modibo, bashi da hankali, wannan yaron besan me duniya take ciki ba, ni yama maidani karamar yariya, ji yake kamar shine ya haife ni, kome a kayi gani yake ba daidai bane.

Dariya Suraj din yayi, tare da fadin, wane ni, Mama ni dai Kawai Ina fad’a ne da duk wani abun da zai dame ki, itama Matar taka inbanta shagwaba ya mata yawa Bata da lafiya ai saita Kira ka, Wai dan kinibibi sai Mama zata kira.

Eh ta kira ni, me ya dame ka? Ammi ta fad’a tana kallon Suraj din dake murmushi tare da fadin, toh ita amaryan taka bazata gaishe ni bane?

Cikin sauri Modibo ya kalli Rahma dataki yadda su hada Ido da Suraj din, juyawa yayi ya kalli Suraj sannan yace, me zaisa ta gaishe ka?

Au hakama zakace, tarbiyan da kake mata kenan?, ke gaishe ni, na wuce inda kike tunanin a gidan nan, ni gaba nake da Modibo, sannan kuma amini na ne, gaba dayan shi a tafin hannun na yake, sirrin shi kaf babu wadda ban sani ba.

Banda murmushi babu abun da Modibo ke yi, tare da Satan kallon Rahma ta gefen idon shi, Yana me addu’a Allah yasa kada Rahma tace komai aciki ransa.

Yi tayi kuwa kamar ma bada Ita yake ba, dan haka Suraj din ya daure fuska tare da fadin, Ashe har yanzun halin na nan, Mama tashi muje, wannan yariyar halin ta sai Modibo.

Mikewa Modibo yayi, ya iso gaban Suraj tare da jawo hannun sa suka fita waje.

Unaisa naganin sun juya baya ta mike ta fada jikin Yadikko, yayin da yadikkon ta rungume ta, tana fadin baya ga rashin lafiyar Rahma kamar akwai damuwa, meke damun ki?

Tana kwance ajikin ta take fadin, Yadikko gidan ne bayya min dadi…

Rashin sabone Wannan Rahma, ahankali zaki saba, kuma ma in banda abin ki gaki da abokiyar Zama idan kinji zaman nan ya ishe ki sai kiji gurin ta ki rage wuni.

Wacece Yadikko?, kin manta Afnan ai Bata nan?

Ba Afnan nake nufi ba, Ina nufin Safna, abokiyar zaman ki.

Wani irin daci taji, wadda yasata Dagowa daga jikin Yadikko tare da juya mata baya, idon ta cike da kwalla.

Kallo Yadikko ta bi Unaisa dashi, sannan tace, “Rahma?, wani Abu ya faru ne tsakanin ki da Safna?

Batare data juyo ba ta girgiza Kai da sauri, jimmm Yaddiko tayi tsayon lokaci tace, toh me zaisa daga na ambaci Safna duk yanayin ki ya canza haka?

Hannu ta fara sawa tana share hawaye dan haka Yaddiko tace, ” toh da nasan haka ne abin naki da vanzo ba, ai na dauka kina kallo nane tamkar mahaifiyar ki, dan haka nima na dauke ki ‘yata har cikin zuciyata, sabo da d’a na kowa ne, bawa sai me shi, ban dauka kina da damuwar da zaki iya boye min ba.

Juyowa tayi da saurin ta, tare dasa hannun ta tana share hawayen take fadin, ” Yadikko shine fa jiya da safe ya Kira waya Yana cewa wai yayi kwanan wahala, Wai gefen gado aka tura sh,i wai wani har Yana cewa yanzun ma jikin shi ciwo yake yi.

Cikin wanni irin yanayi Yaddiko tace wa ya gaya mawa?

Ban sani ba, waya dai yake yi, da ya gama kuma sai yace wai bari yaje gurinta ta danna mishi wuya

Murmushi ne ya subucewa Yaddiko tana me karewa Unaisa kallo. sannan tace, “ke kuma sai kika kule ko?, toh Ina me tabbatar miki yayi miki hakan ne dan hankaltar dake, nasan bazai aikata haka ba, da gangan yayi, Kwarai Modibo yasan abun da yake yi, tun yana karamin sa ya taso da basira, sannan duk gidan nan shikadai ne yayi karatun addini Mai zurfi, bana mancewa, tun yana d’an shikara hud’u aduniya idan an tambaye shi me yake so yazama idan ya girma sai yace malam, dan haka tun waccen lokacin Mahaifin Ubanshi Mai martaba yake kiran sa Modibo, sai gashi kuma Allah ya amsa fatan shi.

Jimmm Unaisa tayi jin Yadikko tace Allah ya amsa fatan shi, sai ayanzun ta tuna batasan menene sana’ar Modibo ba, haka ma ta Magaji da duk sauran gidan, kanta ne ya fara daurewa domin ita a tunanin ta Ammi da Yaddiko sune yaran Maimarta, saidai kuma tuna kasaita irin ta Abban su Modibo ya fara daburta mata tunani.

Muryan Yadikko ne ta katseta da fadin, ki cire wannan abun aranki nasan bazai yi hakan ba.

Yaddiko da gaske ne fa, a gabana ma yace mata, Wai ita ta samu ma na gaishe ta, wai shi ban gaishe shi….

Batakai ga rufe baki ba Yaddiko tace,” toh ke me ya hana ki gaidashi d’in?

Mancewa na yi.

Toh yayi miki kyau, gobema ki mance, sai ya Kara gaya mata da safen, sannan wannan mgnr karki sake kice Zaki gaya mishi, laifiki ne, idan yai miki zafi saiki gyara, Zama da me mata ai sai kin yi da gaske, dake kad’ai ce, sai ki ta shirmen ki, idan kikai wasa sai kin Zama yar kallo.

Mikewa Yadiko tayi tana fadin, ni zan wuce, dare na yi, kisa hankali dakyau kuma Kikara hakuri.

Bayan Yaddiko ta fiyo har suka fito waje, inda ta hangi Suraj da Modibo zaune cikin mota, hira suke suna dariya.

Ki koma Mana Ina zaki kuma?, Yadikko ta fada tana kallon Unaisa.

Wasa da hannun Unaisa ta shiga yi sannan tace, “toh Yadikko kice mishi ya koma gurin ta yau.

Wanni irin kallo Yaddiko ta bita dashi tare da fadin, ” karki kara sakani cikin irin wannan mgnr, tafi karfina, kije kiyi tayi kece zaki wahala, ai ya riga ya ga gadon baccin ki, shiyasa ya samu abun zolaya.

Afuce Yadikko ta shiga matar Bata sake kallon inda Rahma take tsaye ba idon ta cike da kwalla.

****

Wlh Modibo maye ne, duk yadda yariyar nan take da taurin kai sai da yayi abun da ransa keso da ita. gidan yayi tsit ihun ta kawai ke tashi, duk yadda na toshe kunne na ban dainaji ba, bazan boye maka ba hankali na ya tashi sosai.

Ai Modibo Boss ne Magaji, kuma fa yariyar na son shi sosai wlh, kuma zakace na gaya maka, badai ya kusance ta ba?, kwanan nan zaka ta Zama ‘yar gari, duk wannan ihun da kaji tana yi wata rana da kanta zata nema, shidai Modibo kam yayi Sa’a ga Safna ga Rahma.

Ai tafi Safna kyau.

Bazama a had’a ba Magaji, kuma shima wlh masifar sonta yake yi, kai zan iya ce maka yanzun ne yakejin yayi aure, ka tuna inda yaita rungumar ta shekaran jiya cikin bainar jama’a da tarin a bokan sa, kuma cikin tsananin farin ciki yake da ganin sa, abun yaban mamaki, bantaba ganin Modibo ya rungumi mace ba Kamar yadda naga yayi ranar, nasan ida idan Safna na kokarin shige masa fada yake mata yai ta wani basarwa.

Hmmmm, Allah ya kyauta Muftahu, dole in fita cikin gari in nemi kyakyawar mace me kyaun sura da aji, in huta da ita Kona huce takaici, kuma saina nemi wacce bata taba sanin namiji ba, domin nima inji anai min irin kuka da ihun da naji anayi daren jiya.

Kai dai Mugun dan sa Ido ne, kukan da ihun sune abun sha’awa?

Hmmm, wlh Dan bakaji abun da naji bane, Tabass daka kwatanta yadda Modibo ya tsinci kansa aciki daren jiya, kuka ne na shagwaba me dauke da sinadaran kara kwazo take raira masa, tunda nake kallo fina finai da duk wani kissar ‘ya mace banta bajin irin abun da yayiyar taita masa ba daren jiya.

Toh in baka shawara Mana”

Inajin ka.

Kayi aure, domin duk macen da zaka samu a bariki saura ce.

Mezai kaini yin aure tun yanzun?, wlh idan kaga nayi aure yanzun toh bakaramar kyakyawan mace na samu ba.

Kafada Muftahu ya daga tare da fadin kaika sani, nikam aure zanyi Ina son in maida hankalina guri guda, dan haka zanjewa Abba da zancen.

Wani irin kallo Magaji ya masa tare da fadin, Allah ya taimaka modai namu Ido.

*****

Yauma dakin Unaisa ya kwana saidai babu wani Abu daya Shiga tsakanin su, barinta yayi tai bacci sosai, washegari da safe ya kula ta tashi da kuzari, Bayan sunyi wanka sun shirya ne yace tashi muje Safna na jiran mu.

Nan danan taji zuciyarta ta jagule dan haka ta sata kallon shi tace, ” Nagoshi”

Me kikaci?

Kasa kasa ta karayi da murya sannan tace nidai akoshe nake.

Shine ai nace me kikaci?

Dauke idonta tayi daga kallon shi dan haka ya bita da Ido tsayon lokaci sannan yace, ” ko kin fison na Ammi ne da aka kawo miki jiya?

Kanta ta d’aga a hankali.

Kallo ya fita dashi tsayon lokaci zuwa can yace, ” shi abincin nan din me yasa baki son shi?

Dana Ammi na saba.

Okay dana Ammi kika ba ashe?, nan din gidan Ammi kike?

Kin tankasa tayi dan haka ya sake cewa mgn nake fa?

A’a.

Gidan waye?

Naka”

Toh dole zakici abincin da Safna ta girka, kuma kema zaki girka taci, yanzun ke kinga ya dace ga Safna acikin gidan aje kuma ana karbo abinci gurin Ammi?, tashi muje.

Mikewa tayi cikin dogowar rigar data amshi jikkin ta sosai ta kuma bayyanar sa Surar ta, babu dan kwali akanta sai karamin mayafi data daura akanta zuwa wuyanta kawai, dan haka a ke iya hangen gashin kanta baki sidik yana zuba sheki.

Yana gagaba tana binsa abaya, saidai duk da haka hannun su sarke Dana juna, karo na farko kenan dataga Modibo cikin kananan kaya, sosai suka karbi jikin shi, saidai haushin shi yafi komai ayanzun.

Juyowa yayi ya kalleta da Murmushi a fuskan shi, ganin hawayen da take boyewa sun fara zubowa yai saurin jawota jikin shi yana fadin, ” Kuka?, hawayen ya shiga share mata tare da fadi, toh shikenan na fahimce ki, tunda abun haka ne bari mu nemo mafita, hawayen ya cigaba da tare mata tsayon lokaci sannan yace, ” abun da zamu yi yanzun shine, kiyi hakuri ki cike kwana bakwai sai kifara yin abin cinki da kan ki, Safna ma tayi nata, amman banason a dauko abincin daga gurin Ammi.

Ganin tayi shiru yace hakan yayi miki?

Eh, tace dan haka yace, “yauwa Unaiss ko kefa?,, anjima zaki goya ni?

Kara tura kanta tayi jikin shi, dan haka yayi murmushi tare da sumbatan ta sannan yace muje, wannan karon gaba ya sata yayin da yabi bayan yana me binta da kallo.

******

Safna ce ta gaida Modibo sannan itama Unaisa ta gaida Safna, amsawa tayi da yau cikin fara’a sosai dan Bata dauka zata gaidata ba, kuma tayi zaton Modibo ma da fushi zaizo.

Abincin suka shiga ci, yau Unaisa nacin abincin bakamar kullum ba, waya aka Kira Modibo ya amsa, yanayin mgnr da yake ta gane su Dada ne zasu koma ayau domin Umarni taji Yana fadawa akawo kayan da wuri yau zasu wuce, dan haka ta shiga juya cukala tare da Addu’a Allah yasa su hado kafin Dada ta wuce.

Bayan ya sauke wayar ne yakai abincin bakin shi tare da lumshe idon shi yace, ” Safna abincin yayi dadi sosai, sannu da kokari, idan Unaisss ta cika kwana bakwai itama zata fara girki, Ina ganin haka zaifi ko?

Cikin sauri Safna tace eh yayi kowa zaiyi nashi kenan?

Eh Ya Bata amsa bayan ya cika bakin shi da abinci.

Bekai ga hadiyewa ba ya tsinkayi Muryan Unaisa tana fadin hakali, afara daga yau, ka koma gurinta yau.

Cikin sauri ya dago ya kalleta batare da ya iya hadiye abincin ba, Safna takalli Unaisa tare da tattaro murmushi tace, ai kina da sauran kwana hudu”

Idon ta akan abincin tace, “na yafe”

Modibo kunshe da abincin da ya kasa hadiyewa ya shiga shafa gemon shi tare da kasa cire idon shi akan Unaisa..

8 comments

  1. Pingback: free videos
  2. Pingback: gubet
  3. Pingback: situs toto
  4. Pingback: 7slots indir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *