IMG 20211226 WA0054

BAYA BA ZANI BOOK 2 PAGE 4 to 5

Posted by

 

BAYA BA ZANI BOOK 2 PAGE 4 to 5

BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥

By
Fadeela Lamido

Wattpad fadeelalamido

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*® _PEN: WRITER’S ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

BOOK 2
4-5

 

_____________________________________

…….Kokarin zamewa hannun nata take, Dan bawani rikewa yayi ba, nan Baba ya sake cewa”

Umar baka jina? Idosa akasa”

Cikin sauri ya runtse hannun nata acikin nasa, yayin da Baba ya rike hannunsu gava daya ya Kara hadesu waje guda, Umar kaga haka?, Haka nake son ka rike Asma’u, kanwar ka dan Allah kaji tausayinta ka tausaya mata ka fitar mata da wannan tsoro naka da take ji, bani son ganinta ciki damuwa”

Dakai Dattijo ya amsa sannan Baba ya dube Asma’u da har yanzun take zubar da hawaye, jikinta na rawa yace”

Asma’u Umar mijinki ne, dan uwanki ne Kuma yayan ki, dan Allah kisaki jikin ki kibar rudewa irin haka, ada matsayen Yaya yake gareki yanzun kuwa miji ne kijin ko?, Banda abinki ma Asma’u ni banga abun tada hankali ba, ya isa haka bar kukan, ki share hawayen ki kinji ko?, Zame hannun sa Baba yayi Dan haka Dattijo ma yai saurin zame nasa”

Kuka Asma’u keyi kasa kasa, ganin haka Baba ya sake cewa, Asma’u ke bakijin lallashi ko, wannan kukan bashi da amfanin komai garama ki bari, ayanzun duk abin da kike so ki tambayi Umar Kai Kuma kaji tsoron Allah ka sauke nauyin da take kanka, Dan Allah Umar na rokeka karka bani kunya”

Dakai ya amsa kamar dazon, yayin da yake cigaba da jin kukan yariyar cikin kunnuwan sa, sai dai yaki kallon gefenta”

Baba ne ya sake cewa yaushe zaka koma?

Saida Dattijo yai gyaran murya sannan yace gobe”

Toh yayi kyau, naso ka wuce da matarka toh saidai satin gaba zata fara jarabawa karshe, toh idan tagama saika tafi da ita”

Toh Baba”

Yauwa Dattijo yanzun anan zata zauna ko kana ganin ta koma gidan su?

Ni duk yadda akayi baba”

Toh bakomai, Amman ka saya mata waya kan katafi domin ka dingajin lafiyarta?
sanan kabar mata kudi koda zata bukaci wani abun”

Amsawa yayi sannan ya mike ya fice”

Asma’u naganin fitansa ta kara sakin kuka, Baba zan mutu idan har aka barni daga ni saishi, wlh duk rana da naganni gidansa mutuwa ma zanyi”

Hmmmn kidai kwantar da hankali ki nace ko, kidaina kuka karya jawo miki matsala”

Wlh Baba ban son shi”

Mamace tace, shima ai ba son ki yake ba futsararriya dole aka masa dan wlh yafi karfin ki”

Umma ta kalli Mama ta yamutsa baki sannan ta mike ta rike Asma’u sukabar dakin”

Dakinta ta maidata yayin da Asma’u ke fadin ita gidan su zata wuce, ganin inda Asma’u ta hanata sukuni tacewa Maryam takira Dattijo yaita gida”

Sallama tayi aka bata izinin shiga sannan ta shiga”

Shida Mansir di ne zaune, gaidasu tayi sannan ta kalli Dattijo tace Wai kazo ka Kai Asma’u gida”

Lumshe ido yayi sannan ya budesu akan Maryam tare da aje kofen dake hannunsa”

Ke! Ina wasa dake ne?, Dan ubaki ni abokin wasan ki ne?

Umma ce ta aiko ni fah”

Kibari harna tashi saina karya ki da ubanki”

Juyawa tayi da saurinta, Mansir kuwa fadi yake meye haka Umar, yariya da aurenta yake cewa zaka karyata🤔

Idan tana da aure bazan daketa ba?, takara dawowa nan tagani”

Tabe baki Mansir yayi adaidai lokacin Umma ta shigo”

Dattijo nace kazo kakai Asma’u gida ta matsa zata gida”

Kauda kansa yayi, Umma toh taje mana ni bana jin dadi, ko Abdullahi ya kaita”

Abdullahi ma inaga be kwana gidan ba kaidin dai ne zaka kaita”

Saidai in bata kudi taje ta nemi mota”

A’a Sam bazai yiyuwa Dattijo kodai katashi ka kaita ko ka bada motar ka akaita”

Da sauri ya kalli Mama ganin da gaske take ya maida kansa kasa”

Mansir ne ya tashi ya dauki key din Dattijo yace tafito nakaita”

Daker Asma’u ta shiga motar Saida ta tabbatar ba Dattijo bane zai jata”

Baya ta zauna ta rasa me zatayi ne taji dadi, wato dai ya tabbata dai ita matar Dattijo ce gashi nan harda wani kulwa na musamman ake bata”

Gaba daya komai haushi yake bata daga motar har matukinta duk yadda zatayi Alhaji Babba ya warware auren tayi amman bashi da alamar warwarewa Dattijo kuwa bazata iya dashi ba fada da Dattijo saidai bayan idon sa, badan haba walahi saiya sakeni, zancen hakurin zama dashi ma Babu dan idan ya ganu abun daya faru tsanina da Abdullahi nashiga uku takaici ne yasata dukan kujerar motar, waigowa Mansir yayi, Yaya dai? Ita Kuma motar me tayi ne?

Harara Asma’u ta zafgara masa duk fuskanta akunbure”

Cikin murmushi Mansir din yace”

Haba mana ahuce haka, wata rana sai lbr kibama zuciyarki hakari hakanan

Muryan Mansir din ma haushi take bata ji take kamar ta zageshi harara take ta zaga mishi, duk abun da take yana kallonta dariya ma abun ya koma bashi”

Ganin bata da niyar nuna masa hanya ya fara tambayanta bakinta zubure take nuna masa suna isa ta bude batare data rufe ba ta wuce abunta”

Sakkowa Masir yayi ya rufe motar sannan ya tabe baki afali yace yariyar nan daganin ta akwai tsiwa, bayanta yabi da kallo harta shige gida”

***************

Alamun mutane tagani cikin gidan, da alama suma nan wani bikin sukayi ganin manyan tukwane agefe”

Dakin Inna ta nufa batare da sallama ba ta fada dakin”

Inna da Baba suna zaune adakin ganinta duk suka dago suna kallonta”

Babane yace a’a Asma’u daga Ina haka?

Fadawa tayi gefe jagwaf kan tabarma tare da fashewa da kuka, Baba Wai anmin aure ya Dattijo😭

Bawai bane Asma’u, Dattijo mijin ki ne, yanxun Yaya akayi suka bari kika fito?

Baba kamin alkawari fah kace zanyi karatu har sai nace ya isa haka😭

Dattijo ma nasan zai barki karatu, domin yasan mahimmanci sa Nima ba haka naso ba, Dattijo danane kamar ki, haka Kuma Alhaji mebada auren ki ne ga duk wadda yaso bazan iya cemasa a’a ba bare Kuma ga dansa na cikin sa, dan haka kiyi hakuri bana son wannan kokekoken kamar anyi mutuwa, Dattijo yafiki zafin Kai Amman ance bece komai ba, meyasa bece komai ba?, Saboda yana daraja mahaifin sa amman nasan kasan ransa baya so, to kema inason ki mutuntani ki darajani karki Kara cewa komai”

Wani irin marayan kuka take tare da fadin bana son shi Baba”

Bazakiji abun da nafada Miki ba kenan ko”

Dafe bakinta tayi tare da kallon Inna da alama itama Inna taci kuka ta koshi”

Hawaye taita sharewa yayin da Baba ya fice adakin, Inna ko kallon Asma’u take tana share hawaye”

Itama Asma’u hawaye take sharewa ta gefen idonta cikin kokarin bin umarnin Babanta, tashiga wani mummunan yanayi da bata iya kwantatawa, yayin da takejin zafi idan ta tuna shikenan an yake alakar dake tsaninta da Abdullahi, idan kuwa ta tuna abun da ya shiga tsaninta da Abdullahi jitake rabata da Abdullahi bakomai bane akan bakincin da zata shiga ranar da asirinta zai tonu, meyasa ba’a bani Abdullahi ba?, Meyasa ba’ahadani da Abdullahi ba😭 azuciya take wannan mgnr amman saitaji Inna na fadin”

Kar insakejin kin fadi irin wannan mgnr, Allah yariga yace Umar shine mijin, Ina baki shawara kisawa zuciyar ki hakuri, duk da cewa nayi takaicin wannan aure na wulakanci da aka miki shi Babu zato Babu tsammani amman babu yadda zanyi tunda nasan cewa wani baya auren matar wani, sabo da haka idan ma akwai wata alaka ta soyayya tsakanin ki da Abdullahi wadda bamu Sani ba, ki cireshi tun wuri karki shiga fushin Allah da aure akanki yanzun”

Kuka takeci sosai yayin da tashiga tunanin Abdullahi, acikin ranta take fadin Yaya zanyi ne yanzun?, kamar nikadai ce ma acikin matsalar Abu uku ne keci min rai yanzun”

Anrabani da wadda na shaku dashi, sannan bani da abu mafi daraja da kowacce mace ka takama dashi, kuma anhadani da mutumin da ya tsaneni Nima natsane shi😭 me zance ranar da asirina ya tunu😭 wlh duk nice aciki”

Hawaye ta share sannan tacigaba da tunaninta, ko Inna Abdullahi yake yanzun?,ko yana cikin damuwa bekaini ba, tunda bashi aka hada da azzalumi yana can da matarsa kwana kadan ma kila ya mance Dani”

Irin wannan tunanin taitayi tana share hawaye harna tsayon wani lokaci”

Haka rayuwa tamata zafi lokaci guda komai ya kwabe mata kamar ba ita bace ada take cikin Annashuwa da nishadi”

Haka yauma takwana batasa komai acikinta ba bacci kuwa saidai barawo”

*************

Adaren ranar mansir abokin Dattijo ya wuce shikuwa Dattijo yau da safe ne ya tashi da Shirin tafiya saidai rashin ganin Abdullahi ya daga masa hankali”

Tsakar gidan ya fito ya samu Mama, Mama niba rabona da Abdullahi tun shekaran jiya Kuma Ina Kiran wayarsa baya dagawa”

Eh baya nan ne jiya da daddare tafiya ta kamashe gurin aiki ko dakinsa bashiga ba ga matar tasa ma agidan nan”

Amman shine bazai gaya min ba, Kuma Ina kiranshi bazai dauka ba”

Kila baya kusa da wayar”

Sanyi yaji cikin ransa sannan ya wuce dakin Umma domin yi mata sallama”

Bayan sun gaisa yace Umma ni zan wuce”

Toh kaje gurin Baban ku ne?
a’a yanzun dai zanje”

Toh akwai mgnr da nake son namaka ko saika sake dawowa?

A’a, Umma kiyi kawai”

Wai me Asma’u ta maka ka tsaneta har kake firgitata?

Jimmm, yayi zuwa can yace”

Bata min komaiba”

A’a gaskiya zaka gaya min Dattijo kiyayyar tayi yawa gashi Kuma Allah ya hadaku zama tare, yadda take jin tsoronka abun na damuna tun da aka daura auren tausayi take bani kankanuwar yariya ce bata gama hada 17 ba, bata bacci batacin abinci tunda taji zancen auren nan dan Allah kabar zare mata ido kaji tausayinta”

Jimmm, yayi cikin yanayin dake nuna zancen ya shigesa, kauda idonsa yayi sannan yace”

Ban tsanetaba Umma, ni ban ma wani santaba, sai ranar da ta zageni, ni bani da matsala Umma, rawar kaine kawai banaso, ita Kuma nakula tana da rawar Kai da kiriniya, tare da rashin kunya”

Bata da rashin kunya kuruciya ce Umma tai saurin katse shi”

Toh nidai indai zata tsare wadannan abubuwan babu abun da ya dameni da ita”

Dagowa Umma tayi ta kalleshi duk da cewa bata fahimci zancensa na karshe ba saita bar zancen ahaka”

Koda yaje yiwa Alhaji Babba sallama nisiha sosai ya masa tare da Kara nuna masa girman nauyin da yahau kanshi, sosai nasihar ta shiga jikin sa, wannan yana daya daga cikin abun dayasa yaki yin aure domin wani nauyine ake daurawa mutum Babba, shiko bashi da lokaci”

Shi kanshi Baba yagene nasihar ta shiga jikinsa sosai”

Gidan su Asma’u ya nufa Saida ya biya ya saya waya tare da layin sannan ya nufi gidan”

Yana zaune cikin motarsa akofar gidan su Asma’u, bejin zai iya shiga gidan dan haka yaita zaman jiran ko zai sami yaro”

Tsayuwar kusan minti 30 harya gaji da jira ya fito cikin motar sannan ya hango wani yaro”

Kiransa yayi sannan yace Dan Allah kashiga nan gidan kace Asma’u tazo inji Umar”

***********

Sosai gabanta ya fadi, lokacin da Inna ke fadin”

Umar?, Shine bazai shigo ba🤔, Asmau taso maza maza”

Mikewa tayi cikin tsanin faduwan gaba ta saka hijjabinta ta fita cikin tsananin fargaba”

Ajikin motar ta hangesa cikin Uniform dinsa dan haka tana fitowa daga soron taja ta tsaya”

Kallonta yayi daga sama har kasa, ganin bata da niyar karasowa, ya kyauda idonsa tare da kokarin bude murfin motar, ki karaso mana, ya fada tamkar bada ita yake ba”

Dakowa tayi ahankali duk da haka tsorace take kamar ta zura da gudu ga hawaye afuskanta sosai

Aike ya sameki, har yanxun kinata kuka, ajiyan zuciya yayi sannan ya sake cewa”

Ni ban iya rarrashi ba, Kuma ance inzo in rareasheki, idan kinga zaki bari kibari, idan Kuma kinga bazaki bariba kita yi🤷🏽‍♂️”

Hawayenta ita dai taita sharewa bata ko kallaiba”

Tsareta da ido yayi karon farko daya kare mata kallo, acikin ransa yace Wai yanzun wannan ce matata itace zata iya daukan dawainiyata? Dariya yayi afili tare da dafe kai🤦🏼‍♂️ wlh Alhaji Babba da abun dariya yake, jifah dan Allah Wai aure”

Kallonta ya sakeyi sannan yace, kin sakani agaba kina min kuka, bayan na gaya miki ban iya rareashi ba”

Kuka kawai takeyi hannayenta akan fuskanta”

Ke!! Rufe min baki kafin inci uwarki”

Rike bakinta tayi yayin da hakan yabashi daman kallon fuskanta, kunbure yake suntum yayi jawur idonta kamar garwashin wuta, tausayi yaji tabashi sosai, kawar da idonsa yayi gefe meke sakaki kuka???, Ki gaya min intaimake ki, dan naji kina neman ne taimakon ki jiya”

Dagowa tayi ta kalleshi Babu wannan daure fuskan tasa hakan yabata damar cewa Auren ne ban so😭”

Hmmm aure ne bakiso ko nine bakiso kamar yadda kika fada jiya??

Kaitsaye tace kaine domin gani take zata samu mafita”

Murmushi yayi kadan, sannan yace kici gaba da cewa baki sona dan ubanki
Ke zaki wahala, ni bani da wahala, Abu daya zan iya ce Miki shine kibini sauda kafa ni ba Abdullahi bane da kika raina, ban son rawar kai, da tabara, bana sha’awar zama da ballagazar mace irin ki idan kika kiyaye wannan zakiji dadin zama dani, tunda Baba ya dage, ni baki isa ince maki ban son ki ba, kin yi kadan ni intsaya Ina cewa banson ki aina batawa kaina lokaci ne, kisani duk abun da zan miki umarni baba nake bi karki fassara shi daban”

Hawaye ta share sannan ta sake cewa aini nace ban son ka”

Runtse ido yayi duk da beson yaji haushin kalmartata amman kalmar bata masa dadi, bude ido yayi sannan yace”

Ai daman can nasan baki sona, bazan hanaki kice baki Sona ba, shi wannan kalmar Alhaji Babba ne ya jawota atsanin mu da yace wai ya daura aure, sabo da haka kita fada ba laifin ki bane, amman Ina tabbatar miki daga wannan kalmar ta baki Sona karki Kara furta maka manciyarta idan kuma kina ganin nayi taushi ki cigaba ki gani, uwarki zanci wlh”

Kokari juyawa ta farayi cikin kuka, Dan haka yai saurin cewa zoki dauki wannan ledan”

Juyawa tayi takalla ledan akan kujerar motar yayin da yayiwa hanyar rufa da hannun sa, idosa ta kallah aranta tace duka na zaiyi wlh, ja tafarayi da baya da baya Saida tajita jikin katangarsu sannan ta kwasa aguje tare da fadin banso”

Tabe baki yayi sannan ya dauki ladar ya koma ya zauna tare da fadin lallai yariyar nan wato duk irin kwantar dakan da nayi na rarrasheta bata gani ba”

Itako Asma’u gida ta shiga lokaci daya taji hawaye ya kafe mata, lallai akwai matsala Dattijo zagi kawai yake d’ura min, amman Kuma yace wai lallashi ne yake yi, toh ranar da ba lallashin yake ba fah🤔

Akwai matsala, idota ta matse ganin hawaye be fito ba tace ya kare, hannu ta ciza cikin tabar takaici da danasani, ”

Wani yaro ne yasake shigowa, waigashi inji wani mutumi awaje”

Inna ce ta amsa tare da karasawa gurin Asma’u tace dama awaje kika barshi kika dawo gida, ledan ta daura mata ajiki,

Asma’u na budewa taga wayace tare da kudi wadda basan ko nawa bane Amman dai suna da yawa, ajiyan zuciya tayi tare da shigewa daki cikin sauri ta shiga hada wayar domin Kiran Abdullahi bazata taba yadda akaita gidan Dattijo ba”

***************

Shiko Dattijo har yai nisa yana tuna kalaman Asma’u wani iri yakejin su dan haka yaita shafa kansa tare da ajiyan zuciya kwana biyu kawai da faruwar auren har anfarasani adamuwa ya fada, tuna inda fuskata ya kubura saboda kuka yasashi Jan tsaki, kwata kwata tafiyar batai masa sauri tsaki kawai yake jah”

Kansa ko ya shafa yafi akirga, da kanshi ya tambayi kansa meke damuna ne kalmar bata Sona ne ko ko kukan da takeyi ne?🤔

Saidai kukan da takeyi, gangarawa yayi gefen hanya domin sake gwada kiran Abdullahi cikin ikon Allah ya dauka”

Abdullahi tafiya Babu sallama kuma kana sane Sarai Ina gari”

Yaya naga bakajin dadi ne kawai”

Hmmm, toh ya Amarya?

Aini bangari ma”

Haka Mama tace amman dai an maka tsiya vasusan kayi sabon aure bane?

Ninace zani Yaya saboda tafiyar nada mahimmanci”

Lallai Amman kuwa kaban Mamaki duk wannan zumudin kamar zakaci Babu”

Dan sautin dariya Abdullahi ya fitar sannan yace yaushe zaka koma?

Ina hanya yanzun haka, daga gidan Baba malam nake, naje wajen kawarka Baba ya matsamin inje wai in rarrasheta, amman haka nabarota sai kuka take Wai bata Sona, ba rashin son nawa ya dameni ba kawai inason tabar kukan, toh ka kirata kabata hakurri……

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *