
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
🕊🕊🕊🕊🕊
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
Biamillahir Rahamanir Rahim
1-3
✏Wata kyakyawar bafulatana ce tafe sai faman sauri take, sakamako wani gaggarimin hadari daya hadu yayi bakin kirin lallai idan ruwannan ya sameta ahanyar nan zata yabawa aya zaki ,gashi ba gida gaba ba gida baya waigawa tayi sosai ta kalli bayanta wani laffiyayyan iska ta hango ya nufuta dan haka ta kwasa da gudu ,amman ina tuni kasa ya cika mata ido dole ta tsaya tana share idon tana kuka wani kara ta faraji abayanta wanda bata tabaji ba, dan haka ta fara tunanin ko iska takaita wani duniyar daban ne, kara dunkulewa tayi waje daya tana kuka meban tausayi
muryan wasu maza ta faraji akanta daya daga ciki yana fadi ke baki da hankali kinajin mota bazaki kwauce ba.
” shiru tayi batace komai ba ”
ya cigaba da magana ke bazaki tashi ba saina sa mota na latse ki dayan ko ban da yan wake waken shi babu abin da yake. jitayi ya sake cewa big boy yariyar nan fah inajin kurma ce.
da katawa yayi daga wakar da yake rairawa yace
” Ok yayi kyau d’aga mun ita mugani ko tana da kayan marmari ”
dariya dayan yayi sannan yace
” kai fah matsalar ka kenan ba dama kaga mace sai ranka ya biya”
kama ta yayi ya d’aga ta, tanajin an d’aga ta tafara kokarin guduwa amman rokon da yayi mata bana wasa bane dan haka ta kasa gudu gashi idon ta har yanzon ta kasa budewa bare tasan wacce duniyar iska ta kawo ta, ji tayi yana fadin big boy zo ka duba ta yamma nayi.
wanda aka kira da suna big boy ne ya fara takowa yana zuwa gaban yariyar yayi birki yana kare mata kallo yana wani ya mutsa baki zuwa cen yace
” babu laifi sai dai tayi kankanta da yawa amman babu komai samun ita amota na d’an matsa ta ”
fashewa tayi da kuka tana tunanin wannan wani gari ne iska ta kawota wanda ake matsa mutane
tanaji suka sakata acikin abun da suka kira da suna mota dan haka kukanta ya karu ,
hannun taji yana yawo asaman kirjinta bige hannun ta fara amman ina karfin namiji da mace ba daya bane tuni ya yaga rigar dake jikinta ya rage daga ita sai zani uhu take iya karfinta amman kaman dad’a ziga shi take zuwacen ta farajin abu na yawo atsakanin cin yoyinta tun daganan bata kara sanin inda take ba, zuwacen ta farajin hayaniyar mutane akanta wasu daga ciki suna fadin daniju ce yar gidan malam habu.
itako tana kwance tanajjin su ,wasu suna fadi adauketa akaita gida wasu kuwa cewa sukayi kar ataba ta.
daker aka samu wata tsuhowa da tace ita zata kaita gida domin kuwa dana kowa ne hijjabin ta ta cire tasawa daniju domin kayan dake jikin ta sun yage ahankali ta riketa sukka nufi cikin gari.
abunka da karamin gari tuni lbr ya isa kauya kafin su isa yara da manya suncika kofar gidan malam habu.
hayaniyar mutane ne ya fito da malam habu dan dawowar shi daga kasuwa kenan.
sallaman da tsuhuwar tayi shi ya da katar da malam habu cikin mamaki ya kalli daniju dake rike hannun tsuhowa tana dingishi cikin tashin hankali yace
” ke kuma daga ina Allah yasa ba wani bala,in kika kwaso ba”
daga bayanshi aka bashi amsa ahaiye nanaye yau dai ga abinda muke fada ana karyata mu ai tuni na fada yariyar nan bin maza take amman uwarta ta karyata ni toh yau dai ga zahiri.
cikin fada malam habu ya daka mata tsawa tare da fadin badake nake magana ba.
bayan tsohuwar ta zaunar da daniju sannan ta kalli matar dake kusa da malam tace
ina mahaifiyar yariyar nan take?
malam ne ya fara kiran salamatu.
cikin sauri ta fito idonta cike da hawaye.
tana daga tsaye ta kasa cewa komai .
tsohuwa ta shiga yi musu bayanin ayanayin da ta same ta.
cikin kuka salamatu tayiwa tsohuwar godiya har kofar gida ta rakota .
bayan ta koma cikin gidan ne ta isa gaban daniju ta kama ta tanufi bandaki da ita basukai ga shiga ban dakin ba malam habu yace
” dakata salamatu ”
cikin sauri ta tsaya tajuyo takalleshi.
cikin tashin hakali yace salamatu lokaci yayi da zaki tura yariyar nan wajjen ubanta indai tana dashi, inkuwa ba haka ba zata barmin gida yau dinnan dan bazan yadda ta lalata min tar biyan yara ba.
cikin kuka salamatu ta tsuguna tana ba malam hakuri amman yace ina sam bazai amince ba mikewa yayi ya fara hankad’a daniju kofar gida .
biyosu salamatu tayi tana kuka tana rokan sa yayi hakuri tuni yaran dakke kofar gida suka zagayeta suna mata wakka.
cikin matsanan cin tashin hankali salamatu ta koma cikin gida cikin sauri ta fara hada kayanta dana danijju domin kuwa bazata taba bari daniju ta bar garinnan ita kadaiba gara ta kaita gidan uban ta inyaso saita dawo.
fitowa tayi cikin sauri ta nufi kofar gida malam ya bita da kallo yace
me kk shirin yi ne?
cikin kuka tace zan kaita katsina ne gurin babanta.
atakaice malam yace ban yadda ba babu inda zaki idan ko kika sa kafa kk bar gidannan abakin auren ki.
murmushin takaici tayi sannan tace babu komai malam na amince domin kuwa fatima itace ‘yata kwaya 1 wanda na haifa aduniya dan haka bazan bari ta salwanta ba dan idan na barta batasan inda zata nufaba Allah yasa haka shine mafi alheri.
bece komai ba har tabar gidan ila tashin dariyar baraka da takeji.
9 comments