Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 34

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
Fadila Lamido

EXQUISITE WRITER’S FORUM.

page 34

Kafar sa ya mika ya take ta Unaisa, dagowa tayi ta kalleshi, yayin daya zafga mata harara, cikin sauri ta dauke kanta, gyra fuskan sa yayi jin Safna tana cewa, ” Kanajin Abun da take fad’a.

Nan danan ya saki murmushi tare da cewa, ” Inajin ta Safna, rabu da ita kawai mashirmanciya ce.

Cigaba yayi da cin abincin, yayin da ya dago yaga Unaisa na kokarin sake yin mgn, dan haka ya daure fuska tare da cewa, ” idan Kika sake mgn anan gurin saina bata miki rai”

Fasawa tayi, a hankali take cin abincin yayin da bacin ran Modibo ya kasa boyuwa, daka kalli fuskan shi zaka gane ransa abace yake, bashi da wani walwala.

Itako Safna can kasan zuciyar ta ya soso ganin yadda Modibo yake daure fuska sabo da matar shi ta fadi abun da be mishi ba.

Ya riga kowa tashi agurin, part din Unaisa ya shiga, ganin haka Safna ma ta mike ta nufi part dinta gurin ya rage sai Unaisa kadai, juyawa tayi ta kalli Babban falon na Modibo wadda yake cike da Kaya na alatu tare da mayan hotunan sa wani shi kadai wani shi da Safna, tsaki taja sannan ta mike, hakanan taji ranta duk ya jagule wadda ta rasa dalili, part dinta ta bude babu shi afalon dan haka ta zauna agurin, haka nan kuma sai taji tana fargaban had’uwa dashi.

Zaman kusan awa tayi a gurin, sannan ta mike, fitsari ne ya matse ta, kuma sosai take tajin shakkan haduwa dashi, dan haka ta nufi daya dakin dake gefe, wadda Bata taba Koda leka shi ba sai dai tana tura kofar ta jita rufe, dan haka Bata da Mafita dole ta nufi dakin cikin gudu gudu sauri sauri.

Bata kalli inda yake ba ta nufi toilet din, daga yadda ya ganta ya gane matsuwa tayi, kuma daman yayi tunanin tana falo.

Bata jima ba ta fito, kokarin fita take yace ke zo Nan.

Ja tayi ta tsaya dan haka ya sake cewa cewa nayi kizo fa.

Ahankali ta isa, Yana zaune ya mike kafa tare da nade hannun sa a kirji, Yana kallon cikin idonta yace, ke sabo da kishin har kike bada kautar mijin ki ? baki da hankali Ashe?.

Ni ba kishi bane.

Unaiss, nasan ki ba tun yau ba, sai dai na kalle ki, ko tari kika yi nasan me kike nufi, ai sanin hali yafi sannin kama, dan na yaba girkin Safna ranki ya bacci ko?

Ni ba haka bane.

Haka ne Mana, ai nasan halin ki, tuni kike shareni, tare da nuna halin ko in kula a gareni, amman a karkashin ranki akwai tarin soyayya ta.

Kallo shi tayi kad’an ta maida kanta domin bazata iya gaya mishi kalmar dake bakin ta ba.

Kiyi mgn inajin ki, ni nasan halin ki sarai, ba haka ake nuna kishi ba Unaiss, karki sake min irin wannan abun, kuma shi kishi bugawa ake yi, kowacce kokarin kwace mijin take yi, hannun sa ya mika ya rike nata, kiyi hakuri kinji ki sake jikin ki, wannan kishin naki ki dan rageshi kadan kinji?, yana wahalar dake da yawa na lura shine yake saka ki damuwa.

Kawar dakai tayi tare da fadin bashi bane.

Jikin sa ya jawo ta, ya sumbata, sannan yace, ” shine Unaiss, ina so acikin wannan kwanakin namu na farko mu saba, kiji dadina kema Kamar yadda naji dadin ki, domin dare daya kawai kin bani farincike, wadda ban da abun da zan kwatanta shi, har inajin Kamar aduk duniya kome zan baki bazan biya ki ba, sabo da irin farin cikin da naji, wlh Rahma, da mutum na iya saka mutum cikin zuciyar sa, da nasaka ki domin ki gano halin da take ciki, domin baki na bashi da kalmar dazai kwantan ta yadda kike acikin zuciya ta, nasan ban taba bud’e baki nace miki Ina son ki ba, duk kuwa da tsayon lokacin da muka dauka da aurena a kanki.

Haka kema ban taba bude baki da irin wannan kalmar ba, wasu sun dauka cewa shi so bayyanar sa yana ga baki ne, mutun ya fito yaita ihu yana kiran I love you, da sauran su, Wai shine soyayya, wadda yawance abaki ne kawai, babu shi azahiri, domin da akwai ta zuciya zaka kani ne a aikace kafin kaji a baki, Ina fatan kin fahimce ni?, yanzun kamar ni din nan ban da bukatar wai sai kin bude baki kince kina sona, nariga da nasan wannan, sabo da nagani a hankalce, masu iya mgn nacewa,aiki da hankali yafi aiki da agogo.

Dagowa tayi ta kalle shi, yayin da idon su ya sarke Dana juna.

Eh Mana ko kina son kiji ne daga Baki na kuma.

Kawar da idonta tayi cikin yanayin dake nuna tajin kunya.

A’a kici gaba da kallo na, ai yanzun kuma Ina mgn na ne Kai tsaye da zuciyar ki, naji daga gare ta wai tana son in fada da baki, ko ba haka bane azuciyar ki???

Tashi Unaisa tayi zubar ta juya baya sannan ta koma ta zauna, duk da haka be ishe ta ba, Saida tasa hannun ta biyu ta rufe fuskan ta shi.

Ni ki wani daina jin kunya ta, kalmar Ina son ki tayi kadan, sai dai in ce miki kece zuciya ta.

Murmushi Unaisa ta saki batare data kalle shi ba, duk da baya ta juya masa ya fahimci tayi murmushi, dan haka yace, “juyo inga murmushin Mana”

Cikin sauri ta mike tana kokarin barin gurin, hannu sa yasa ya dawo da ita baya, sannan ya had’a jikin shi da nata yana fadin, ” Ina son naga murmushin fa.

Boye fuskanta take yayin da murmushin da ke kara yawa yadda yake dago mata Kai yasa ta fara dariya tare da kokarin tura kanta cikin kirjin shi, tana dariya har Yana bada sauti.

Gaba daya Modibo ji yayi kamar ya tafi wata duniyar ta taban, ada yadda take mishi fushi fushi be yi niyar sake kusantan ta ba har sai ya koma dakin Safna ya dawo, amman sabo da wannan yana yin da suka shiga tuni yaji ya fara kai hannun sa jikin ta.

Wannan karon babu wanan rawan jikin Dan haka zai iya cewa ta dan saki jikin ta, bata ture shi ba sai dai bata mayar da martani, ji yayi ya tafi wata duniyar, yayin da yake lasan jikin ta, tsayon lokaci ya dauka yana Abu daya sannan yaji ta fara koke koke.

Cikin wata irin Murya yake fadin, ki saki jikin ki babu abun da zan miki, wasa kawai zanyi dake in barki.

Duk da haka Bata daina wannan koke koken ba, ganin yana kokarin Kara gaba tace, ‘ befa warke ba dan Allah ka barni.

Muryan sa a dashe ya ke fadin, “Haba?, be warke ba?, kice Allah?”

Allah kuwa.

Toh Kira sunana sai in barki.

Hamma Modibo.

Cikin sauri ya tura bakin shi ga nata tsayon lokaci sannan ya dago yana fadin, “saura daya sunan?

Kawar da kanta tayi tare da fadin, ni a’a,

Har yanzun yana saman ta, ina son ki fada fa Unaiss, ni ina nan idan har bazaki fadi ba.

Zan fad’a.

Toh inajin ki.

Fahat, tunkan ta rufe baki taji ya shigeta gaba daya hakan yasa ta Kara dumaucewa domin Bata zata ba, hakama waccen ranar mamayan ta yayi, sai yaga yayi abin da mutun ya saki jikin sa sannan yake yin abun da yaga dama, wannan karon ma kuka tai tayi yadda take kuka yau ko ana farko batai ba, sai dai wannan karon babu ihu.

Saida ya samu cikakkiyar nutsuwa sannan ya saurara mata yayin da taci gaba da raira kuka.

Daker ya iya raba jikin shi da nata, Yana maida numfashi, Sai da ya nutsu sosai sannan ya fara rarrashin ta, ganin taki shiru ya mike ya nufi bayi, tsayon lokaci sannan ya fito, bakin gadon ya isa yasa hannun shi Yana kokarin daga ta tai saurin tashi zaune.

Muje in taimaka miki kiyi wanka, kukan ya isa haka.

Kaucewa tayi tare da fadin, da kaina zan yi.

Eh zan rike ne ai.

ni banso.

Toh shikenan sai kin fito, vayan tayi wanka ta fito ta same shi ya gama shiryawa, kallon ta yayi sannan yace zani masallaci.

Amsawa tayi a hankali, sannan sannan tacigaba da shiryawa, muryan Dada da taji yasata farin ciki sosai, batare data daura dan kwali ba ta fito tare da fadawa jikin da.

Shine sai yau zaki shigo?, Unaisa tai mgnr cikin shagwaba.

Cikin tsananin farinci Dada tace, yau ma Sallama mukazo mu miki, tsofai tsofai damu me zamuzo gidan yara muyi, aini tunda kina dakin mijin ki alhamdulillah, wannan yafi min komai farin ciki, Allah ya jikan Innawuro da Baffah, da suna duniya da sunga irin ni’imar da Allah yai miki.

Matan Malam Ayuba dake gefe ne ke fadin, ” haka Allah yake ikon shi.

Ta gefen Ido Unaisa ta zafga masu harara domin balakin haushi suke Bata.

Zaman kusan minti shabiyar sukayi sannan Modibo ya shigo yana fadin, ” Mama an gama sa kayan.

Mikewa suka yi yayin da Unaisa ma ta mike ta biyo bayan su, Modibo be hanta ba in banda binta da kallo ba abun da yake yi.

Koda suka isa gaban Motar su Dada suka shiga shi hankalin shi na gun Unaisa, hawaye ta fara sharewa ganin Dada ta shiga motar sannan tai maza ta isa gurin Ammi, cike da Murmushi Ammi ta rike hannun Unaisa tana fadin, Rahma yi hakuri ai data dinga zuwa kema zaku dinga Kai masu ziyara.

Lallashin harama taitayi har motar su Dada ta tashi yayin da Unaisa taita daga masu hannu tare da kokarin boye hawayen ta.

Bayan motar ta wuce ne Ammi ta kalli Rahma tace ya jikin naki?

Tsintan kanta tayi da kasa amsawa tare da tsananin jin kunyan ammi.

Au Rahma kunya na kuma kike ji? ni babu ruwana ki saki jikin ki, Modibo zoka ka rike ta kuje.

Batare data dago ta kalli Ammi ba ta fara tafiya tare da fadin, ” zan shiga gurin ki ne.

A’a zo kibi mijin ki.

Yadda ta nufi part din Ammi da saurin ta yasa Modibo fadin, Ke! karki shiga, kizo ki wuce.

Ja tayi ta tsaya sannan ta juya ta nufi part dinta batare da waige ba.

Murmushi Ammi tayi tare da fadin, ai yanxun ji zasuyi kamar an daure su, sun saba da Zama su biyu.

Dariya Modibo yayi bayan yaga Unaisa ta bace sannan yace, ai Ammi gara Afnan da wannan yariyar, Afnan ta fita wayau.

Dariya Ammi tayi sannan tace Allah ya kauta itama da wayaun ta.

******

Sakon ya iso?

E Momy ya kawo min dazon, toh kin bashi waren takalmin sa na Kamar daman?

Ni Momy duk kafa biyun na bada ma kila idan had’a dukka biyun aikin yafi sauri, har da Kaya kala biyu.

Kika hado?

Eh.

Dariya Momy tayi harya bada sauti sannan tace, “waye ya aiki ki kwaso mishi kaya.

Toh Momy idan aka bukata fa, gashi muna da nisa.

Lallai Safna ba karamin so kike ma Modibo ba, yanzun su wannan wadda ya kawo min, na Babban ledan shine wadda zakisa a abincin shi, na rubar kuma matsi ne, karkiyi wasa dasu kudi sosai na biya, kuma aikin shi Sha ne yanzun magani yanzun, Amman karki yi amfani dashi saiya gama kwanakin shi ya dawo dakin ki…..

8 comments

  1. Pingback: Gary
  2. Pingback: pump diaphragm
  3. Pingback: VOX Casino app
  4. Pingback: 電子 菸 推荐

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *