Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 35

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadeela Lamido

Page 35

Amsawa tayi zuciyar ta cike da faricin ganin cewa Momy ta fara yun kurowa.

Sosai take son Modibo yanxun haka jinta take duk a takure, kusan kwana nawa batajishi kusa da ita ba, abun da Bata taba gani ba tunda sukayi sure.

*****

A yauma kamar kullum, Modibo tarairayan Unaisa yaita yi har yaga ta dan saki jikin ta, Sarai yasan halin ta abun da take so da wadda Bata so dan haka ya dinga binta da ‘yan dibaru Yana karbe hakkin sa, acikin kwana bakwai da yayi adakin ta yasamu tsuwa mara misaltuwa kuma ya fuskanci akwai Dan sakin jiki daga gare ta ba Kamar dacan ba.

Yau zaibar dakin ta Kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, amman akarkashin ransa sai yanajin yau din babu dadi, gani yake kamar zai tafi wani gari ne yai nisa da gida, sosai hankalin sa yake atashe.

Misalin karfe goma na safe Modibo ne da Unaisa, zaune yake Kan dugowar kujera yayin da ya mike kafa tare da kwantar da Unaisa Kan kafar sa, hannun sa Kan kirjin ta yayin da hankalin shi ke Kan tv tun bayan da ya lura bacci ya dauke ta.

Zuwa can ta motsa tare ta juyawa ta fuskanci tv, karasa hannun sa yayi ya zagaye ta tare da leko da kansa, Yana fadin, Ashe baccin ba me nisa bane?

Dan murmushi tayi, yayin da shima Modibo yai murmushi tare da mayar da kansa ya kwanta da daya hannun sa tagaba ya sako mata key din mota saitin fuskan ta, madubin tabi da kallo tsayon lokaci sannan tasa hannun ta ta karba tare da fadin me zan tashi?

Naki ne, na baki a matsayin tukuici.

Tsintan kanta tayi cikin tsananin farin ciki wadda yasata tashi ta zauna batare data San lokacin ba, kallon sa tayi cikin Ido sannan ta lumshe Ido, fuskanta cike da Murmushi tare da runtse key din a hannun ta take fadin, Nagode sosai Allah ya saka da Alheri.

Lumshe Ido yayi karon farko da yai mata wani Abu ta nuna taji dadi kenan, zuwa can ya bude idon shi akanta tana tsananin murmushi yace, ” babu godiya tsakani na dake, domin kaina naiwa.

Tsintan kanta tayi da sake fadin, ” nagode.

A’a nace miki babu godiya, dama cewa kikayi Allah ya barmu tare ki haifa min kyawawan yara masu kama dake.

Tafin hannun ta tasa ta rufe fuskan ta cikin yanayi najin kunya.

Bude idon ki ni har yanzun baki min godiya ba, idan kina son inji dadi har cikin raina ki taso ki sunbace ni sannan ne zansan eh lallain kinyi farin ciki.

Dauke hannun ta tayi daga fuskan ta takalle shi sannan ta kawar dakai, har yanzun murmushi be barta ba.

Rahma nace gani ki sunbace ni zanyi tsananin farin ciki da hakan.

Tunkafin ya rufe bakin sa tasa sandan hannun ta ta rufe fuskanta tare da fadin, Hamma nifa bazan iya ba.

Sabo dame ?

Kunya nake ji.

Toh barin rufe idona, Amman idan Kika min anan saiki min anan sannan na karshen anan guda uku nake so.

Kumatun sa ya nuna, gefe da gefe na karshen ya nuna goshin shi, sannan ya rife idon shi kam har tana iya hango yadda ya matse idon.

Mikewa tayi tsaye harta tsaya akagaban shi, batabar jin kunya ba duk kuwa da cewa idon ta arufe yake, ahankali takai bakin ta Kamar yadda yace haka tayi tana jin sa kowanne sunba da takai mishi Saida ya saki ajiyan zuciya bayan tayi na karshen ne ya nuna bakin sa idon sa arufe yana fadin, ” saura gyara, kimin gyara anan”

Batare dawani Bata lokaci ba takai bakin nata cikin kosawa ta koma ta zauna, sai dai tana daura bakin ta anashi yai caraf dashi tare da rike kanta.

tsayon lokaci ya dauka yana Abu daya daker ta samu ya saketa yayin da Yana sakin ta ta nufi daki cikin gudun

Cikin wani irin yanayi yayi murmushi, Zama yayi ya saita kanshi sannan ya mike ya gyara wuyan rigar sa sannan ya nufi dakin.

Daga bakin kofar yace barin danje na dawo yanzun..

Amsawa tayi da toh, bayan fitan sa ne ta Kira Dada batare data bari sun gaisa ba tace Dada albushirin ki?

Goro Unaisa na.

Fari ko ja?

Fari Dada ta fada tana dariya.

Hamma Modibo ya bani mota.

Tsananin murna Dada ta nuna tare da yi musu addu’ar Zama lafiya.

Bayan ta sauke wayar Ammi ta Kira bayan sun gaisa sai kuma ta rasa me zatace mata, tsintan kanta tayi dajin kunya.

Rahma da mgn abakin ki, Yaya aka yi?

Rasa inda zatayi tayi daker ta iya hada kalmar Ammi ya saya min mota.

Jimmm Ammi tayi sannan tace, ” Modibo?”

Eh

Kai Masha Allah, alhamdulillahi Modibo ya kyauta, Allah ya kara hada kanku shima Allah ya saka mishi da alheri, Allah kuma ya zaunar daku lafiya,

Shiru tama ami Bata iya amsawa ba duk da Daman Ammin batai tsammanin zata amsa din ba.

Bayan ta sauke wayar Afnan ta kira bayan sun gaisa ta fada mata kautar da Hamma yai mata.

Eyeee Lallai su Hamma Modibo an iya wayau, wato har ya miki wayau kin saki jikin ki ya more abinshi.

Ba wani morewa kefa daman ‘yar iskace.

Bazancen iskanci, duk ranar da Kabir ya barni nazo gida Zaki ban labarin daren farkon ki.

Menene daren farko?, sunan wani littafi ne ko?

Dariya Afnan tayi tare da fadin, wato Raina min hankali zaki yi.

Zakiyi bayani ne, Dan nasan inda Baki bashi komai ba bazai Baki ba.

Ba abun da akayi Afnan dacan da yake min hidima wani Abu na bashi?

Oho muku kudai kuka sani, ranar Nan da ya kirani nasan halin miskilancin ki ne yasa ban gaya miki ba, Kamar dai Yana cikin fushi ranar yace wai na dinga baki shawara wai baki da wayau saina Bari sai mun hadu.

Me yace na yi?

A”a ni haka kawai yace min, bece min ga abun da ya faru ba.

Wacce rana ce to?

Yau kwana 4 kamar.

‘Yar dariya Unaisa tayi sannan tace, Ina sane, shine yake santin abincin ta nikuma nace ya koma gurin ta na yafe sauran kwana 4.

Agaban ta?

Eh Mana.

A lallai dole yace Baki da wayau, dama dai ke dashi ne, mgn fa kika gaya mishi hakan da kika yi, kuma a gaban kishiya.

Toh ai shima yasan akwai ni agurin ya fada a gabana.

Gaskya Auty Rahma kina da zafin kishi, gashi ahaka dai lafiya amman akan Hamma Modibo bakya d’aga kafa

Ke kike ganin haka, hira suka cigaba dayi ita da Afnan irin ta wadda sukai tsananin shakuwa.

Misalin karfi 2 Modibo ya dawo, sannu tamai sannan yazo ya zauna agefen ta Yana dauki da Murmushi, hakika ya shaida tana cikin farinciki tunda har ta gayawa Ammi kyautar da ya mata, damuwa daya ne a kasan ransa ta yadda zai yi mata sallama ya koma dakin Safna, dan haka yai nufin mata dibara, kallon ta yayi kasa kasa yace, ” Yau kwana bakwai rabon ki da Afnan ko?

Kanta ta d’aga Masa.

Murmushi yayi tare da fadin, ” kinga da batai aure ba yau saita taya ki kwana ko?

Jimmm tayi cikin nazarin kalamin sa sannan tace, ” Bakomai ai ko Bata nan”

A’a Nasan fa kin saba da hira da ita sosai dole zakiji wani iri.

Babu komai.

Lumshe Ido yayi sannan ya duba agogo tare da fadin, ” toh barin je anjima da dare zanzo na rufe miki kofa.

Zan iya basai kazo ba.

Zanzo nace ba sharan ki nake nema ba ai.

Kawar dakai kawai tayi batare dayace komai ba.

Mikewa yayi batare da yace komai ba, sunbatanta yayi sannan ya fice.

Kofar ta kalla sannan ta had’eye yawun bakin ta, wata zuciyar ce ta fara raya mata gashi can yana tattaba Safna Kamar yadda yake mata, tsaki taja tare da kawar dakai.

Yadda zuciyarta ke ta mata zafi yasa ta ta mike ta fara aiki, dakin ta fara gyarawa sannan ta koma falo, sannun a hankali ta gyara ko Ina duk cikin kokarin kawar da tunanin dake zuwar mata cikin zuciyar, wata zuciyar ce ke ce mata matar sa ce fa tare kika gansu Dan me zai dame ki, duk abun da kikaga ya miki ya mata kabin ma ya sanki.

Wannan tunanin da tayi ya kara daga hankalin ta, afili tace toh indai haka ne me zai Kai mutum auren me mata, tsaki taja sannan ta nufi kitchen karo na farko kenan da ta shiga da sunan girka wani abu, komai akwai na bukata babu abun da babu, duk inda taso ta daura abincin daidai cikin ta kasa, yadda abincin ke buga kamshi taji ranta ya fara baci, bata tunanin Modibo ya tabacin girkin ta, Ina amfanin auren mijin wata?, gashi ranar da zatayi kirkin farko babu mjin ta, tsaki ta kuma ja.

Abincin na daf da dahuwa taje tai wanka ta sauya kaya, kwalliya tayi sosai tare da fesa turare kala daban daban.

Kai tsaye kitchen din ta nufa ta bude abincin, haka nan tayi tunanin ta zuba ta kaiwa Abba, wata zuciyar ce tace mata Ai Ammi nawa Abba kirki kullum me rai da motsi bazai kalli wannan ba, sai dai duk da haka bata daijin son kaiwan ba, dan haka ta sakko da Sabbin kuloli ta hada abincin a ciki, kadan ta zuba ta fita ta zauna afalon taci kadan, sannan ta dauki waya tayi rubutu ta tura mishi.

Zani in gaida Abba, shine abun da ta rubuta.

Wayar ta zura ma Ido tana jiran ne kawai ya kirata yace karkije ko Ina, harta tanaji amsa bashi, toh Ina da sakon da za’a mikawa Ammi, saidai harta gama tattara kalmomin ta be Kira ba har kusan karfe tara sannan taji Karan shigowan Sako.

Adawao lafiya.

Lumshe Ido tayi domin batai tsammanin ba, mikewa tayi cikin dauki da zumudi ta dauki karamin gyale ta yane kanta dashi sannan ta dauki abincin data hada ta fice.

Ma aikatane ke ta shawagi a haraban gidan, yayin da hasken fitulo ya haske ko Ina, Kaitsaye Falon Abba ta nufa domin tasan daidai wannan lokacin Ammi ke Kai masa abinci.

Da Sallama ta shiga yayin da gaba dayan su suka dago suna amsawa.

Fuskar Ammi ce ta cika da Murmushi tare da Fadin, Rahma ke kadai?

Eh Ammi Zama tayi akasa yayin da Abba da Ammi suka had’a bakin wajen ce mata tahau sama mana.

Zama tayi, kawai akasan yayin da Ammi ta dage saita hau sama.

Dole tasa tahau badan ranta yaso ba, idon ta akasa ta gaida Abba sannan ta gaida Ammi.

Juyawa tayi ta kalli Magaji dake zaune kusa da Abba Yana cin abinci, kasa kin gaidashi tayi sabo da idon su Abba batare data kalleshi ba tace Ina wuni?

Lfiya, ya fada batare daya kalle ta ba.

Ammi Unaisa ta mikawa Abincin Sarai ta gane Abba ta kawowa dan haka tun acikin zuciyarta ta fara yaba d’abi’ar Unaisa.

Wannan fa?, Ammi ta tambaya.

Na kawo ma Abba ne, ta fada kanta akasa.

A, Masha Allahu, yau zanci abincin gidan Modibo.

Toh Alhaji aina riga na zuba maka gashi nan.

A’a Banci kawo nan ki zuba min.

Cike da dariya Ammi takai gaban shi tana zubawa tana fadin, Masha Allah diyata ta iya girki.

Jan abincin yayi ya fara ci, yanaci yana sa mata albarka, Ammi ma zubawa tayi tana kokarin kawai bakinta tacewa Magaji ko azabu maka?

Kamar jira yake ya miko na hannun sa dan haka Ammi ta amsa ta zuba masa.

Sosai Unaisa tayi mamakin ganin yadda Magaji kecin abincin, tass ya cinye.

Abba ma cinyewa yayi Yana ta Kara sa mata albarka.

Tuni take son tashi Ammi na cewa ta zauna mana ta rage dare, dan haka ta zauna kawai ta zurawa Tv Ido yayin da takejin Ammi da Magaji da Abba sunata hira suna dariya.

Satan kallon Agogo Unaisa keyi karfe goma gashi har yanzun Modibo be kirata ba Kamar yadda yace zai dawo anjima, ranta ne taji ya soma baccin domin tasan tunda goma tayi bazai zo bane, mikewa tayi idon ta akasa tace Ammi Saida Safe.

Toh Rahma Allah ya tashemu lafiya, Abba ma godiya ya mata sannan ta nufi kofar, Haushin karnukan da takeji yasa ta ja da baya, da alama me gadin ya saki karnukan domin daman dare nayi ake sake su, Abba ne ya kalleta ganin ta tsaya, juyawa yayi ya kalli Magaji yace, Magaji zoka rakata, ga kayanta ka dauka….

10 comments

  1. Pingback: mostbet apk
  2. Pingback: PinUp APK
  3. Pingback: 7slots apk indir
  4. Pingback: av
  5. Pingback: switching

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *