
BA LABARI BOOK 2
By
Fadeela Lamido
Page 36
Mikewa yayi batare da yace komai ba, ya dauki kayan yayi waje, abaya Unaisa ta bishi, yayin da taga sai zafga sauri yake yi, dan haka ta dinga binshi da sauri.
Yana Isa matakalar Dake bakin Part dinta ya aje kwadon, tare da juyawa, gani tayi harya gota ta dan haka ta karasa da sauri tana kokarin bude kofar, ganin ta murda kofar taki ta bude yasa ta juya ta kalli Magaji dake tafiya babu waiyaye, duk iya yadda ta ke juya key din yaki ya bude, dan haka ta sake kallon Magaji da yakai tsakiyar gidan.
Acikin ranta take fadin, yanzun Yaya zanyi, ko inkira magajine kafin ya wuce, wata zuciyar ce tace me zaisa ki kira shi alhalin kinsan halin shi, ai Modibo ya kamata ki Kira, dan haka ta shiga danna mishi Kira, saidai harta katse ba’a dauka ba, Kira ta sake yi shima ba’a daga ba cikin sanyin jikin ta sauke wayar tare da juyawa ta kwalawa Magaji Kira.
Juwo wa yayi ya tsaya, d’aga murya tayi tace, ‘ nakasa bude kofar dan Allah ka duba min.
Batare da yace komai ba ya fara takowa har ya iso gabanta Yana fadin, ke nifa tsoron ki nake ji, yanzun nan saiki kulla ma mutum sharri.
Batace komai ba, har ya amsa key din, zurawa daya ya bude, sannan ya Bata key d’in, kwadon ta dauka tana kokarin shiga ciki take fadin, akwai abun da mutum beyi bane akace yayi dahar zakace kar a maka sharri?
Kallon yabita dashi lokacin data shige cikin dakin taja kofar da karfi, Magaji kuwa da Mamaki yabi kofar da kallo, betaba tsammanin zata iya fada Masa haka ba yadda yaga nutsuwar ta agurin su Abba, tabe baki yayi sannan ya juya ya fara tafiya.
Saidai Yana fara takawa yaji ta sake kwala mishi Kira, batare da ya juyoba ya daga murya yace, “menene?”
Nakasa rufewa ne.
Dariya ce taso kwace mishi cikin dakewa yace, kada Allah yasa ki iya rufewa Mana, ki kira mijin ki Mana, Zaki wani damu mutane da Kira, Magaji! Magaji! saikace ke Kika rada min, ba yanzun nan kika gama min rashin kunya ba?
Wucewa yaso yi amman sai ya tsinci kansa da kasa yin hakan, dan haka ya fara Kiran Modibo, sai dai be dauka ba dan haka ya barshi kawai, komawa baya yayi sannan yace, juya key din kike yi, ki sake juyawa sannan in kinsa sau daya zaki juya.
Muryan Ammi yaji tana fadin, Magaji Yaya Aka yi?
Ammi Bata iya bude kofar ba.
Karasowa Ammi tayi tana fadin, akira Modibo.
Nakira shi be dauka ba, juyawa yayi ya kalli Kofar yace ta rufu ?
Eh, ta fada daga ciki, Ammi ce tace Magaji gwada budewa.
jawo kofar yayi sannan ya sake ya juya yacewa Ammi ta rufo.
Ammi ce tace toh Rahma mu kwana lafiya.
Daker ta iya amsawa, sannan ta wuce cikin daki tana sauke ajiyan zuciya, ta dade zaune sannan mike taje tai wanka tare da saka kaya ta hau gado, gaba daya ta kasa Bacci juyi kawai take a Kan gadon
Misalin 11 daji wayarta ta Kara tana dubawa taga shine kin dauka tayi harta yanke, zuwa can taji ya sake kira, anan ma din bata dauka ba Saida ya Kira har sau hudu tana gani taki ta d’aga sannan ya bari, saidai Kiran shi din yasa ta ta danji dadi ba aran ta.
Daker Bacci ya iya daukan ta, washegari da safe ko tana tashi ta fara gyare gyare, ko Ina ta gyara ya dauki Kamshi, wanka tayi bayan ta shirya ne ta nufi Kitchen tunin abun da zata dafa ta daidai cikin ta ta shiga yi batakai ga yanke sharawa ba taji an turo kofar tare da Sallama.
Amsawa tayi batare da ta juyo ba, kinga jin Muryanta a kitchen din yasa ya shigo cikin, tsaye yayi abakin kofar cikin Shirin zuwa aiki, murmushi ya sakar mata dan haka tai saurin kawar da kanta, fuskanta daure tace Ina kwana.
Lafiya lau kin tashi lafiya?
Lafiya lau.
Jiya nata kiranki inji kin dawo baki dauki wayar ba.
Ban gani ba.
Baki gani ba?
Eh.
Kingani mana.
Ni bangani ba har na dawo nayi bacci banga Kiran ka ba.
Okay, toh Ina ganin lokacin da nakira kinyi bacci kenan ko?
Eh.
Amman ai kinga kirana da safe ko?
Har yanzun ban dauki wayar ba.
Baki ma San na Kira ba kenan?
Eh
Toh Yayi, shiru yayi tsayon lokaci sannan yace, ” Allah ya huci zuciyar mu annan gaba sai a kiyaye, ni zan fita yau na koma aiki.
Daker ta iya cewa Allah ya bada sa’a.
Ameen toh ki matso Mana
Ahankali ta fara matsawa agaban shi, shima tahowa yayi ya rungumeta tare da sunbatan kumatun ta Yana fadin, kiyi hakuri, kinji ko, muyi waya da Magaji yace min kin kasa rufe kofa, dariya yayi idon shi akanta sannan ya sake cewa sannan Abba ya kirani yace min Allah ya amfana, kin Kai mishi wani Abu ne?
Eh.
Lumshe idon sa yayi tana kwance ajikin shi idon shi akanta ya sake cewa, Abba yaji dadi sosai, harma yai Mana addu’a kinsan me yace?
A’a ta fada tare da girgiza kanta.
Ki kalleni saina gaya miki toh.
Dagowa tayi ta d’aga kanta ta yadda take iya ganin fuskanshi.
Cewa yayi wai Allah yasa mu haifi ‘ya’ya masu albarka.
Cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa.
Bakice Amin ba?
Cikin jin kinya sosai tace, ” ai kaima nasan bakace mishi Amin ba.
Ni din?, ke! kin sanni kuwa?, banfa Bari ya rufe baki ba nace Amin Abba.
Idonta akasa tayi murmushi harta fitar da sauti.
Shima murmushi yayi sannan ya sake cewa toh bani labari me Kika kai mishi?
Abinci ne fa.
Abinci?
Eh
Shiru yayi tsayon lokaci yana tunani, be taba kawo irin wannan tunanin ba, wato shi kyauta ko kafi karfin abun dadi gareshi domin duk tunanin sa turare Unaisa takaiwa Abba, baya tunanin Ammi ma ta taba cin Abincin Safna bare kuma Abba.
Sunbatan ta yayi sannan yace zanje karna makara saina dawo ko?
Allah ya tsare ta fada a ahankali, ficewa yayi yayin da itama ta fito falo.
Zama tayi cikin sanyin jiki sosai zuwa can taji Muryan sa a waje tsintan kanta tayi da mikewa ta isa bakin window ta yaye labulen ta tsaya tana leken sa, saitin Window ta motar take, saidai da tazara sosai, mgn suke shi da Safna sai dai Bata iyajin me suke cewa, tsayon lokaci ta dauka a haka har Saida taga wucewan shi sannan ta koma ta zauna zuciyarta cike da haushin Safna.
Tunda ga lokacin Bata sakejin duriyar shi ba, har dare, tasan cewa da yamma yake dawowa dan haka zuciyarta tacigaba da raya mata Yana can gurin Safna, haka zuciyarta taita mata zafi tsayon lokaci duk da cewa wani lokacin tana ma kanta fada akan haushin Safna da take yawan ji.
Yauma be shigo ba sai misalin goma na tare, atsaitaye suka gaisa yayin da yabita da Ido yana fadin, ” ke! kina cin abinci kuwa?
Ina ci.
Anya kuwa? naga duk kin fada ne, kinci abinci yau kuwa?
Naci fa. ta fada idonta akasa.
Kallo yaita binta dashi sannan yai mata Sallama ya fice.
Duk abun da ta saba tayi sannan ta kwanta, bacci ne ya dauketa yau me karfi dalilin jiya bata wani samu baccin ba.
Washegari ma kamar jiya ya shigo bayan sun gaisa yace, ” Zanfita, sai yamma zandawo kuma dai kinsan yau Safna bazata bani abincinta ba, kece zaki bani, part dina yau nakine dan haka ki koma can da wuri insamu abinci acan haka kema kanki in same ki a can, key ya Mika mata tasa hannun ta karba tare da sunkuyar dakai.
Naga Kamar kina da Mgn.
Cikin wasa da hannun ta tace, “ni nafi son nan basai naje can ba”
Hannun sa ya zuro acikin aljihu sannan yace, ” ba neman sharawan ki nayi ba kina so ko baki so dole ne kije can.
Bata iya amsawa ba, shima be jira amsan nataba ya juya ya fita.
*****
Misalin karfe hudu ta gama komai dan haka tai wanka ta gyara jikin ta yayin da ta feshe jikinta da ture me dadin kamshi, saidai ta kasa shiga part din nasa kamar yadda ya umarce ta.
Zuwa can taji tsayowar motar sa tsayon lokaci tanata jiran shigowan sa amman shiru babu shi har akayi sallah mangari ba.
Tunani yadda zatayi ta shiga yi wayarta ta katse mata tunani da karan
data dauka.
Ammi ce dan haka tai saurin dauka, sallama tayi tare da gaida Ammi sai dai daga sallamar har gaisuwar Ammi Bata amsa ba, cikin fada ta shiga fadin, ” Rahma ashe baki da wayau?, toh maza maza ki dauki abincin sa ki Kai masa, karki yadda ya fara sauke fushin shi akan ki, bashi da dad’i, tashi maza maza.
Mikewa tayi bayan ta sauke wayar, shirye take tsaf dan haka ta dauki kyan abincin ta bude kofar da sazata sadata da falon shi ta shiga, babu kowa afalon ajiye abincin tayi tare da kallon falon, ganin sa tayi kaca kaca, kallo ta gama kare Masa sannan ta nufi dakin sa.
Tura kofar tayi ta shiga dakin Modibo akaro na biyu arayuwar ta.
Komai Burkice ta Nan ma kugunta ta kama ganin ko Ina kaca kace, afili tace wlh da gangan tayi haka, da gangan ta lalata ko ina….
11 comments