IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 38

Posted by

WATA FITSARA PAGE 38

 

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamido

                      Page 38

Bayan sun dau hanya alhaji Usman be saurara masaba cigaba yayi da mashi nasiha sosai nasihar ke shigarsa saidai har yanzun yana tunanin yadda zai tsaya gaban Khadija da sunan yazo bata hakuri,  sosai abun ya dameshi”

        ***********

  Khadija zaune agaban Babanta kanta kasa take fadin”

    Baba haka to zanta zama yana wulakantani, nidai gaskiya abarni nadauki mataki, dan Allah Baba kucire hannun ku kubarni dashi nikadai nasan me nakeji azuciyata, Baba wannan abun da yaimin yafi komai yimin ciwo Baba😭

     Khadija duk wadda akace masa yayi hakuri tofah an cuceshi, kiyi hakuri ni zanje insamu Babanshi mu zaunar dashi ahankali za’a gaya mai gaskiya basai kinje wani kotu ba, Banda abunki Ahmad ai Hassan dinki ne dan uwanki ne najini”

   Niba dan uwana Bane Baba, ada can ne yake ahaka yanzun ko bashi da burin da ya wuce yaga na wulakanta”

   Bekyauta ba Khadija, adai yi hakuri kawai, anhadu kota Ina, zancen Kotu be tasoba, ai sai asaki ajarida ga wata tana shariya da sirikinta”

    Ni bandamu ba Baba wlh bandamu ba”

     Jinan Khadija, idan ke ba abun kunya bane agareki mu iyayen ku zai zamar mana abun kunya, Ahmad be kyautaba Kuma zamu zaunar dashi banson insakejin ancemin kina Kiran kotun nan karma ki soma ba agidana ba, tashi kije”

     Hawayen daya zubo Mata tashare sannan ta mike batare da tace komai ba, tafe take tana hade hanya ji take kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu saboda takaicin Ahmad yanzun ne takejin haushin sa sosai Ashe da ba haushin sa takeji ba, gado tafada tare da fashewa da kuka sosai abun bakin ciki adakeka ahanaka kuka”

      Wayarta ce tayi Kara cikin wannan halin da take ciki ko waya Bata iya dauka dan haka tai banza da ita tare da cigaba da kukanta”

     Har sau uku yaga Kira bata dauka ba agogon wayar ya duba karfe Tara da rabi nadare, juyawa yayi kadan ya kalli Ahmad dan beson ya fahimci akwai wani abu atsakanin shi da Khadija ganin taki daukan wayarsa”

    Ahankali ya shiga lalubo number Baba bugu biyu ya dauka bayan sun gaisa yace”

    Baba daman nida Ahmad ne munzo gurin Khadija, nakirata awaya bata dagaba”

   Cikin farin ciki Baba yace yanzun nan tabar dakinan idonta biyu ku shigo kawai, halan kaji abun dake faruwa tsakaninta da sirikin nata”

     Murmushi kadan Alhaji Usman yayi sannan yace eh Baba shiyasa ma na daukoshi yabata hakuri”

       Masha Allah ka kyauta sosai ku shigo kawai sirikin naka yai maka jagora”

     Murmushi yayi kadan sannan ya sauke wayar yana fadin”

     Ahmad muje ciki”

     Jikin Ahmad a sanyaye suka nufi cikin gidan, babu kowa atsakar gidan kowa na dakinsa haka suka ratsa har izuwa kofar dakin Khadija”

      Ahmad ne yai sallama yayin da Khadija ta tsaya cak daga kukan da take rairawa”

     Sake sallamar da akayi ya tabbatar Mata da eh lallai muryan Ahmad ne yasata saurin tashi tsaye tare da sanyan dan karamin hijjabin ta take fadin”

      Wanni dan Iskane??

     Jimmm Ahmad yayi tare da runtse Ido”

     Adaidai lokacin da ta isa bakin kofar Alhaji Usman yayi sallama”

   Jimmm tayi sannan ta amsa tana tsaye tsakiyar dakin”

     Mushigo?, Alhaji Usman din ya tambaya??

    Eh tace, domin takagu tagaka Ahmad agabanta kuma lallai taji muryan sa”

    Alhaji Usman agaba Ahmad nabinsa abaya tsayonsu daya idan ka gansu saika dauka wane da kanin sa, dan manyata kawai Usman zai nunawa Ahmad”

      Tsaye tayi tana kallon Ahmad kallo me cike da tuhuma irin kallon da tajima batai masa irinsaba”

     Zama Usman yayi akujerar dake gafe, Ahmad ma kokarin zama yake acan gefe Khadija tace karka zauna mun adaki”

     Zauna Ahmad Alhaji Usman ya fada sannan yabita da kallo tare da fadin”

      Zauna malama dare nayi”

     Gefen da Ahmad yake ta kalla dan haka batace komai ba takoma bakin gado ta zauna ranta abace”

   Kallo Alhaji Usman yabita shi tare da fadin”

    Ahuce haka malama, ga Ahmad ya gane kuskuren sa nakuma rakosa yabaki hakuri”

    Bazan tayi dashi cikin kallon can gefe”

   Cikin kura Mata Ido yace”

   Kinajina ai, Ahmad yazo bada hakuri”

    Bana so, ya cuceni ni, ya wulakantani sannan ya kwaso wasu guntayen kakafuwan shi yace zayazo bani hakuri nabanza Saida ya gama wukantani saa……

   Ya isa Malama, kiyi hakuri, Kuma bazai sakeba, duk abun da ake son yagane yagane, Kuma yabiyoni ya baki hakuri duk wadda akace ma yayi hakuri an cuceshi ne ni……

     Nifa Babu wani dadin bakin da za’a min, agaban idona yafada abun da ranshi keso, nasan halin shi sarai wlh akwai ahakan azuciyarshi shiyasa ya fada Kuma wlh saiya gaya min yadda nayi na zubar masa da ciki”

  Tsaki Alhaji Usman yaja kidaina maimata mgnr ban bana sonta kinji ko”

    Eh mana, dole abun yaimin ciwo Ina ruwana da wani Wai cikin sa, Babu abun da yadame dashima barewani kayan kazantar sa, bana son ganin Ahmad agabana kaika kawoshi ka fitar min dashi zan iyayin komai idan Ina ganin shi nan gurin….

   Toh🤔 bakyason ganin shi Kuma kike tunanin zaku shiga kotu?!, dan Allah ki kwatar da hankalin kibi komai ahankali zai wuce daga yau insha Allahu, wannan damuwar da kike nunawa tayi yawa”

     Sai yanzun Ahmad ya dago ya kalli Khadija sutum yaga fuskanta ta kunbura bakadan ba, wani iri yaji shi domin baya kinta abu daya ke masa nauyi yadda zai bude baki yace Mata yi hakuri, wannan abun shi yakeji banban aiki agareshi ko yayi niyyar ya share daya tuna yadda sukayi wasa da yadda take masa kukan rigimarta lokacin kuruciya saiyaji bashi iyawa”

    Muryan Alhaji Usman yaji yana fadin”

      Ahmad taso ka tsuguna nan kabawa mamanku hakuri”

   Kauda kai Khadija tayi yayin da Ahmad ya meke tare da fesar da isa ya tsaya atsakiyar dakin duk cikin kokarin kokartawa”

    Wadonsa ya dan ja sama kadan, sannan ya tsuguna saitin Kafafun ta yace, kiyi hakuri dan Allah, ki Kuma gafarceni👏🏻

      Runtse idonsa yayi saka makon saukan Marin dayaji akumatunsa, muryan Alhaji Usman yaji yana fadin”

      Yaya haka Kuma Khadija??

   Cikin kuka sosai tace”

    Nikadai nasan bakin cikin da nakeji cikin raina, har yakai ga inajin gara ma in mutu inbar duniyar da wukancin da Ahmad yamin”

     Cikin bacin rai yace, Amman kina da matsala Khadija, bashine yake baki hakuriba, yana tsugune avanki Kuma kina Marin sa, haka akeyi?

    Sonake ya rama, nasan kuma zai iya”

      Abba kabarta indai hakan zaisata tahuci toh taita dukana hartaji zuciyarta tamata sanyi”

    Baza’ayi hakaba Ahmad tashi kawai tashi, na kawoka ne ai sullhu tunda bazaki sauraremu ba juyawa yayi yace, tashi kawai muje Ahmad”

   Kin tashi Ahmad yayi, domin ya hango fushin Khadija makura irin Wanda betaba ganinsa ba, tsitan kansa yayi da dafa kafarta tare da cewa”

      Allah ya hucizuciyari
Ki Maman mu, Kiyi hakur,i Allah Kuma yabaki hakuri, da yardan Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagane kurena”

   Ajiyan zuciya tayi sannan ta zame kafarta da hannunsa ke Kai hannun ya sauka kasa, ahankali yasake daurawa Kan dayan yana sake fadin”

      Kiyafe min Dan Allah👏🏻👏🏻

  Kara zame kafarta tayi tare da sauke ajiyan zuciya akoro na biyu”

   Murmushi Alhaji Usman yayi koda Bata bude baki tayi mgn ba yasan ta huce, hakama Ahmad tunda yaga tayi ajiyan zuciya har biyu yasan lallai ta huce”

      Kauda kanta tayi zuwa can ta rankwafar da Kan nata ajikin gado”

    Hannu Alhaji Usman yasa ya dago Ahmad yana fadin”

     Tashi aita huce Kuma muje na kaika gida, motarka Kuma zansa abiyoka gidan da ita, jikin Ahmad asanyaye yabar dakin shikuwa Alhaji Usman tsaye yayi yana karewa dakin kallo sannan ya maida kallonsa ga Khadija yace”

     Zafin ranki Kara gaba yake, maimakon yaja baya, Ahmad din sirikin ki kika mara??, Wacce irin jarabarbiya ce ke??

   Batace komaiba Kuma Bata dago suka hada idoba, dan Alhaji Usman yace shike nan koma dai menene ya wuce banson ki kasa bacci shiyasa na kawoshi ayau, yanzun dai kin huce saiki kwanta kiyi bacci”

    Batare data dagoba tace nijeka dan Allah ka dame ni”

    Kaina Kuma Zaki dawo??, Jibeki  dan Allah kina nan atakure kinki kidawo dakin ki ki huta, kina nan ke daya Babu abukin rayuwa”

    Tasowa tayi daga kwancen da take tace”

    Kaima dai naka gidan naga kai daya kake zaune, garani a gidan iyayena nake”

    Rufewa mutane baki agurin, Kan nasame ki”

   Bazanyi shiru ba Ina ruwanka da aurena, duk baku kuka batamin shirina ba da tuni Ina gidan miji n……

   Dallah gafara nan kina da wani mijin daya wuce nine??

    Bazan dawo gidan ka ba fah”

     Zaki dawo insha Allahu nan kusa, ke koson arungemeki bakyayi shekara kusa na 10  kina zaune babu aure”

   Aini ba yar iska bace”

   Nasani, Amman ki fara Shirin komawa dakin ki daga yau, dan Allah dubi inda kike rayuwa, atakure

     Adai gidan Ubana nake”

   Aiba wani abu nace ba nima din, Ina miki kwada yin nishadi ne bawani abu ba”

   Kanadai yiwa kanka”

   Eh to haka dinne , inajin kamar in tafi dake daga yau  domin kina bukatar kuwalata Amman bakomai lokaci na nan zuwa insha Allahu, abu nagaba dazan gaya miki karkice na cuceki ki shirya da kyau, kindai San ko wanene nidin to yanzun nafi da, nidake kusan ince miki banbancin kadan ne, dan haka kizo da shirin ki

   Tsaki Khadija taja dan Allah katafi wlh ka isheni ni”

    Zan tafi, Amman dan Allah kifara tunanin dawowa dakin ki ki huta daga wannan matsalolin, ke kanki Khadija zakifi mutunci a idon kowama idan kina gidan mijin ki, rankwafowa yayi saitin kanta Ina matukar nemanki kusa dani, kuma kema haka domin nasan gonata nanan Babu wadda ya shiga, idan na tuna halin ki da nutsuwar ki hankalina na kwanciya, saitin kunneta yakai bakinsa ahankali yace”

   Dan Allah kiyi hakuri  Kidawo dakin ki kada gurin yayi tsatsa”

    Tsintan kanta tayi tasa hannunta duk biyun akirjinsa ta hankada shi baya”

       Fashewa yayi da dariya sannan yasake runkwafawa ya sun baceta adadai lokacin da take komawa karshen gadon, murmushi yayi sannan yace Saida safe dan Allah ki dinga daukan wayata kinji?

     Ficewa yayi, yayin daya nufi dakin Baba Kai tsaye bayan sun gaisa Baba yace”

   Ina mutuniyar taka?, an daidaita dai ko??

   Komai ya wuce Baba”

  Masha Allah, haka ake so, Amman da tace
Saita kaishi kotu, Kai Khadija akwai son girma”

    Allah ne ya Babata Baba “

  Hakane Usman to ya mgnr
ka da ita, batace komai ba kaima bakace komai ba”

        Eh am daman Baba muna shawaran ne akai”

   Jimmm Baba yayi sannan yace”

  Kana nufin Kun daidaita ??

   Eh to kusan haka din ne Baba”

    Alhamdulillah, naji dadi sosai da kuka daidaita kanku, abun da zan gaya maka karka tsaya biyewa shirmen Khadija kayi shawara da zuciyarka ko iyayen ka shine mgn, abun da nalura dashi Khadija har yanxun zaman gida bayya damunta kasan halinta  tasan naka Banga amfanin Jan lokaci ba”

     Hakane Baba insha Allah zakaji ni”

          ***********

Afusace ya shiga gidan yana tafe yana hade hanya, wani irin bakin ciki yakeji cikin zuciyarsa tamkar ya kurma ihu haka yakeji”

   Duk mutanen dake gurin be kalli kowa ba, kansa asama yace su afalon,  Jin in da ya bugo kofar garam yasa Hajjah mikewa cikin gudu gudu ta isa dakin”

     Kodata tura kofar rufe gam tajita yayin data farajin kara da alama watsi yake da kayan dakin nasa, buga kofar tafara da karfi tana Kiran Ahmad!!  Ahmad!! Mayake faruwa?

    Wannan Kiran da Hajjah kewa Ahmad yasa Samha tasowa tana rike da maran ta saka makon matsanancin ciwon da maran keyi tun bayan fitowanta wanka”

    Harta isa inda Hajja ke buga kofar tana rike da maranta Jin Karan cikin dakin  Ahmad hankalinta ya tashi sosai………

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamiɗo

           Page 39

Ganin yaki budewa hankalin Samha ya tashi, Bata taba ganin yayi irin hakaba hawaye ta fara tana fadin Hajja menene😭😭, meya same shi??

     Ina zuwa Fatima barin ganshi tukuna nemi guri ki zauna”

     Cikin kuka ta karaso bakin kofar tare da bugawa tana bugawa tana cewa Uncle dan Allah ka bude kofar Uncle kabari dan Allah”

       Jin muryan Samha jikinshi yayi sanyi sosai, tsayawa yayi cak ahankali ya karasa bakin kofar ya bude”

     Ganin Samha rike da ciki ya riketa yayin da Hajjah ta zuba mishi Ido zuwa can tace”

     Meya sameka haka??

     Bakomai Hajjah”

   Bakomai??

    Eh bakomai, Samha ya kalla yana fadin ciwo yake yi ne??

      Kaita daga cikin kallon Hannun shi, Jan Samha yayi zuwa ciki yayin da yacewa Hajjah ku shigo”

    Batai musuba tashiga dakin yayin ta take kallon inda ya hargitsa dakin, hannun tasa tafara dauke abubuwan daya zubar tana mayarwa majiyarsa wadda ya riga ya fashe kuwa tattarawa tayi ta kwashe tanayi tana kallon sa adaidai lokacin da yake kokarin bawa Samha magani”

    Saida ta gyara ko Ina tsaf wanka ya shiga bayan ta tabbatar da cikin Samha ya lafa harta fara bacci”

      Gurin kofar toilet din Hajjah ta isa, Ahmad na koma daki, karka Kara yin wannan haukan koma meye kayi hakuri tunda bazaka gaya mana ba”

      Sainazo Hajjah dana fito zan sameki adaki”

    Toh Ina jiran ka”

    Toh Hajjah”

    Juyawa tayi ta kalli Samha take kwance Kan gadon shi bacci yayi gaba da ita aranta tace Allah ya baki lafiya”

              **********

Meya Bata maka rai kadawo gida cikin fushi haka Kanata hauka?, Koma meye nasan yana da nasaba da Kiran da Mahaifin Fatima ya maka ko yaji abun da kace ne yace ka sakar masa ‘yarsa???

      A’a Hajjah, daukana yayi yakaini gurin ta wai saina Bata hakuri”

    Masha Allah, ya kauta, daman wannan ne ya baka haushi??

    A’a Hajjah tsugunawa fa nayi agabanta Ina Bata hakuri, amman ko kunya bataji ba kawai ta daukeni da mari”

    Fashewa Hajjah tayi da dariya yayin da Ahmad ya tsaya yana kallon Hajja cikin takaici yace”

     Hajjah dariya kike min??

    Yaya bazanyi dariya ba Ahmad, haushi kabata, naji Dadi data maka haka, ko banza zataji zuciyarta ta Mata sanyi, toh Ina jinka cigaba, ka rama dai ko??🤔

     Himmm,Hajja kema kinsan bazan rama ba, yama za’ayi in rama, kawai lokacin ta ne inda dane ita kanta bazata soma ba, dan kafin ta cire hannunta afuskanta
Na bashi wlh”

     Dariya Hajjah ta Kuma yi, sannan tace yanzun dai zancen ya mutu dai ko???

    Ya mutu, tunda ta kaskantar Dani, dama haka take so, taga ta wulakantani yanzun kam burinta ya cika, ninama kosa tayi aure hankalin ta ya dauke akanmu,  yanzun nagama fahimtar ta son girma gareta na masifa tunda akayi auren na da Fatima hankalinta be kwantaba sai yau, saboda tanaganin bazan girmamata ba amman yau natabbatar hankalinta ya kwanta, Hajjah har wani ajiyan zuciya take soboda ta kaskantar dani kinga dasafe fah ta mareni anan gidan yanzun Kuma takuma marina”

  😂 Toh tunda ta huce abun ai yazo da sauki, ni kaina namatsu tai aure, zaman ya isa haka, Allah ya fito Mata da mijin”

   Himmm ai Abban mu kamar yana son ta koma itace taki, kinsan halin taurin kanta, Kuma dacan din takoma da yafi mata dan shikadai ne zai iya da ita”

   Kadai kama bakin ka maza dai Fatima tajiyoka”

   Cikin sauri ya kalli kofar  sannan yace banson ta sani kuwa taurin kanta yayi yawa itama”

    .Murmushi Hajjah tayi sannan tace ni abun yayi min dadi ahaka ai da inata tunanin yadda za’ayi awarware rigimar kaima dai kamar wani karamin yaro kaban haushi sosai, waiwani anyi ganganci”

    Nifa Hajja kiyayyar da take nuna min yasani fadin hakan, yanzun Kuma na fahimceta son girma ne da ita, dole na Bata tunda Allah ya kaddara min son ‘yarta”

    Ka kauta wa kanka kuwa dahar ka fahimci haka”

      Hmmm barin je in kwanta Hajjah nagaji Kuma kaina ciwo yake min”

     Allah ya tashemu lafiya Ahmad kasha magani kafin ka kwanta”

         **********

Radadi yaji anhakali yana shigan shi ta gefen da Khadija taima maruka har biyu”

   Hannunsa ya nufi daurawa akan kumatun nasa akan hannu yaji ya daura nasa, Dan haka yai saurin bude Ido”

     Samha yagani ta mishi runfa juyawa yayi ya kalli agogo sha biyu saura sannan ya dawo da hankalin sa kansa adaidai lokacin da take fadin meya sameka anan???

   Murmushi yayi sannan yace”

     Mamace ta mare ni”

    Mari? Wacece Mama??

      Umman ki mana”

   Jimmm tayi zuwa can tace”

     Toh ai da be tashiba gurin  yanxun ko ya kunbura”

    Ai wani ta Kara min, Abban kine yakaini inbata hakuri shine tamin duka”

     Dariya Samha tayi sosai sannan tace”

       Agaban Abban??

      Eh mana”

    Yana kallo ta mare ka ?

      Eh menene?

    😂😂😂Bece mata komaiba? Kai Kuma ya kayi”

      Murmushi yayi ganin inda yake dariya sannan yace”

    Yayi mgn, Kiran sunanta yayi yace meye haka wance nakawoshi yabaki hakuri Kuma saiki kama dukansa, nikuma kinsan me na yi??

    A’a😬

   Tsugunawa nayi nadafa kafarta nace Mamanmu kiyi hakuri ki kafarceni baki bahimceni bane”

     Dariya Samha ta sakeyi sannan tace bakaji haushin marin ba??

    Banjiba, Amman naji wani irin, Amman ba yadda zanyi sabo da Ina son ki”

       Dariya tayi, sannan tace nasan Ummata tahuce insha Allah  yanzun tunda tamaka duka🤪 amman dai kabar sonta ko??

    Kwanciyarsa ya gyara sosai akan gadon sannan yai ajiyan zuciya tare da murtuke fuska, banson wannan mgnr kinji ko, ni ban taba sonta ba, daman ina shiri da itane saboda jinina yana dakon zuwan ki, akwai alamar jinina yasan cewa uwar ‘yayana tana gurinta, nikuma rashin hakuri da barin zance yasani yin wannan shirmen”

    Ni ban taba sonta ba dan yanzun ne nake gane meye so bayan kin kasance agidana,

    Murmushi tayi tare da gyara kwanciyarta ajikin sa, Uncle Nima kasan me?, dacan haukana kawai nake ban wani San so ba wlh”

    Ai har yanzun ma haukan naki kikeyi bakisan son ba”

     Cikin sauri ta kalleshi da gaske Uncle”

      Shima tsareta yayi da ido sannan yace ko kin sani ne???

      Uncle kana son kasan me nake ji ne?

     Umm”

    Toh kabari sai mun koma gidanmu”

   Cikin murmushi yace shikenan Kuma bazan mantaba”

       Kokarin mekewa tafara zata sauka agadon ya riko hannunta, Ina zaki??

      Zan koma dakin Hajjah”

  Kiyi me acan din??

   Kwanciya zanyi”

    Nan azaune kike??

   A’a Amman gara nakwana acan din”

   Tashi yayi zaune, bangane me kike nufiba Fatima??

        toh Uncle kana son in kwana anan ne Hajja tace bani da kunya?

     Ita baruwanta da wannan bazan tunanin ba, Babu abun da zatace”

   Toh aini bani da lafiya fah”

   Nasani Babu abun da zan miki Amman inason ki kwana kusa dani kawai”

    Zama tayi cikin kwalkwal da ido yayin da ya koma ya kwanta, jira yaitayi ta kwanta taki kwanciya zuciyace ta fara taso masa dan daman daurewa kawai yake Amman Marin da Khadija tamai yana matukar batamaSa
Rai cikin fushi yace”

  Tunda bazaki kwanta ba tashi ki tafi”

Mikewa tayi cikin sauri ta fice, yayin dayabi bayanta da kallo, bayan fitansa afili yace halin da bata dashi ada take kokarin tsoro dashi goben nam zamu koma gida”

         ********

   Mamaki sosai Hajjah tayi ganin Samha ta dawo kwata kwata batai tsammanin zata dawo ba duk da cewa tafison ta dawo nan din, tana bukatar kulawa sosai, yadda Ahmad ya fada cikin Samha tsayon wata uku ne sannan ya fita”

            *******

   Washegari Khadija ta tashi da farin ciki da annashuwa, ko banza ta tabbatarwa kanta yanzun Ahmad yana son Samha, so ba irin na wasa ba, bakinshi ya mutu, kamar bashi bane bakin shi yasaba da fitsara, yayi sanyi gaba daya, bantaba tunanin zan sa hannun nadake shi batare daya rama ba, saigashi har yana dafa kafafuwana yana bani hakuri, badan nafi karfin sa ba saidan kawai ya yarda ya amince ni mahaifiyar matarsa ce, zuciyata tamin sanyi yanzun, shiru tayi zuwa can tace yanzun inda ace dana mareshi ya rama fah🙄🤦🏼‍♀️ Dana shiga uku🤔 Kuma yaci gama da zama da Samha, wata kila da mituwa zanyi, Wai Allah na🤦🏼‍♀️ to meyasa ma namareshi🤔

     Wannan lokacin wani irin taji cikin ranta, sannan taji tana matukar son yin mgn da Samha wadda taita kiranta jiya taki dauka”

       Ahmad kuwa yaso ya wuce da Samha ayau Amman Hajjah ta hanashi wannnan yasashi tattara kayansa ya koma gidan sa badan yayi fushi ba saidai kiyayewa tunda bazuwa gurin shi zatayi ba”

     ****************

  Alhaji ni karya yake min wlh bamu daidaita ba”

    Kash😬😬 agaskiya Khadija kina da matsala, shekaru ki ya wuce ace kina irin wannan abubuwan”

   Dan Allah kiyi hakuri ku gafarceni, sau daya yazo gurina Kuma nagaya mishi bana ra’ayin komawa”

    A’a kina nufin ya mana karya kenan??, toh yanun gaya mana nufin ki, haka zaki tsofa agida tunda kuruciyar ki har ki tsofe muna kallon ki Kuma??

    Kasa ta karayi da kanta, Alhaji ni indai akan mgnr aure ne na yaddda koma wanene kubani Amman dan Allah kubar mgnr Usman ni banson shi”

    Shiru sukayi zuwa can Baba yace Meye hujjar ki, na baki son Usman din yana da wani aibu ne??

    Ni gidan ne kawai bazan koma ba Baba”

   Kaji wani iskanci Alhaji ya fada, sannan yacigaba da cewa nakula abun da banason muyi dake lallai ke sai anyi dake, wato kin yadda azaba miki koma wanene Amman Banda Usman mukuma Usman din shine wadda mukaga yafi cancanta dake, muna muki sha’awar cigaba da zama dashi domin
Bashi da wani aibu, iya zamanki dashi bamusan rikicin kuba, rabuwan aure kawai kikazo mana da labrin Kuma da muka tuntubeshi hakuri yabamu, dan haka muka daukeshi akan cewa kandsara ce, dan haka indai in dauke mu iyayen ki, Kuma zamu  baki shawara ki dauka tu muna baki sharawa da ki koma gidan tshon mijinki, idan kuma yadda kike so din ne toh nidai nacire hannu na, Allah ya taimakeki akan abun da kike so”

    Jinjina Kai Baba yayi tare da fadin”

  Nima ai hakan take aguna, shawara ce idan Kuma be miki ba shikenan”

     Alhaji ne yace Ina jinki me kika ce???

     Kanta akasa ta hadiye wani abu dayazo Mata wuya tace, shikenan na amince😔

       Yauwa ko kefa, Alhaji ya fada, sannan yace Insha Allahu nan gaba zaki gode mana, koma me yahada ku kiyi hakuri, tunda har shima ya hakura ya dawo gareki, idan ma shine da laifin aiya gane kurensa, tunda gashi yanzun kedin dai yake nema, ke Kuma saiyi hakuri, idan kin kisa wanin da zaki aura kinsan me zaki tarar?, Ko wanne aure yana tare da kalubalai, ledan dake bayansa ya jawo yace rike nan”

   Hannun tasa ta karfa yayin da Alhaji yace Sadakin ki ne dazon Babanshi ya kawo, juma’a me zuwa yake son adaura aure”

    Sakin ledan tayi acikin ranta tace duk wannan uban kudin ne Sadakin nawa?, Afili kuwa cewa tayi kubarshi a hannun ku”

   A’a naki ne ki rike kayan ki”

   Jimmm tayi, zuwa can tace”

     Naji kace Juma’a, Alhaji jibine fa juma’a,🤔 ni gaskiya ban shirya ba”

    A’a yace baya son komai, Dan haka Babu wani shiri da za’ayi ko karamar yariya ce ke da zakiyi bidi’a??

    Kaita girgiza”

   Baba ne yace duk ma wani Shirin da zakiyi kwana biyun ya isheki”

     Nasiha suka Kara Mata sannan ta tashi ta fice”

      Dakin Innarta ta wuce  tana Shirin fadawa gado tace kinga Khadija, wuce dakin ki kiyi kukan, nikam ba anan ba, nagaji da ganin ki agida daganan har jibin karki shigo min daki”

     Juyawa tayi afusace, dakin Inna Yalwa taso zuwa saidai ita madin batasan Shirin data matan ba dan haka kawai ta wuce dakinta waya ta dauka cikin fushi ta shiga Kiran Usman”

         *********

Zaune yake aharabar gidan yana kallon yadda aka kawata gidan da sabbinn furrani nazamani, sosai gidan ya canza ga sabon feti daya Sha, kananan kaya ne ajikin sa yana kallon gidan yana kubar ruwan dake hannun sa, sosai yanayin ke masa dadi kafafuwan Khadija yake hangowa tana kokarin shiga gidan, maabociyar lallece Dan haka yanzun ma lallen yake hangowa Kan kafarta, ga son kwalliya kamar me”

     Wayarsa dake gefe ce ta dauki Kara dubawa yayi ganin sunan Khadija yace Yar halas taki ambato, yanzun nake tunanin ki cikin raina, amnan bazan daukaba yariya, nasanki sarai, sai kin huce tukuna, yana kallo harta katse ta sake Kira har sau uku”

   Murmushi yayi sannan yace lbrn ya sameta kenan”

         Nishadi ya dingayi yau ras yake jinsa”

     Washegari ana gobe daurin aure ta sake kiransa nan ma be daukaba, saidai da Yamma ya Aiko driver sa ya kawo mata kudin lalle da kitso, amsa tayi Dan batason tayi wani abun da za’a ga laifinta”

    Bayan ta shiga gida kiransa ta sakeyi, nan ma be lagaba, haka da daddare taita kiransa be dauka ba”

      Sosai take son yin waya dashi dan haka taita nacin Kira Amma fir yaki dauka”

       Samha ce ta fado Mata cikin sauri ta kirata yayin da suka gaisa Khadija tace ya jikin ki’

   Naji sauki Umma”

   Har yanzun kina gidan Hajja ne??

     Eh”

     Meyasa har yanzun baki koma ba toh??

      Gobe ai yace zan koma Umma”

     Ok yanzun kedawaye wajen??

    Ni daya ce Umma”

    Ok, Kira Babanki kice nace ya kirani”

      Lumshe ido tayi tare da wani irin mugun Dadi sannan tace tam💃🏻💃🏻💃🏻

       Kashewa tayi ta Kira Abbanta kamar jira yake ya dauka yana tambayanta jikinta”

     Batare da ta amsa ba Tace Abba kasan me??

     Saikin fada”

    Mamana ce tace Wai ince ka kirata😅

      Murmushi yayi jij yadda Samha ke murna sannan yace toh zan kirata Mamana ya jikin ki ?

   Naji sauki Abba, am Amman… Abba …..

   Ina jikin ki yi mgn?

   Abba Kun shirya ne??

    Zadai mu shirya Fatima insha Allahu😎

     Cikin Kara ta kashe wayar yayin da Usman yayi murmushi, bayan kusan minti 20 Samha ta sake kiranshi Abba tace baka kirata ba😫😫😫

   Kinaji Mamana, Ina tare da baki be yanzun,  idan na gama abun da nake zan kirata”

      Yadda yace Samha ta gayawa Khadija, amsawa kawai tayi da toh domin tasan ba haka bane koda tasa Samha ta kirashi batar kiransa ba Amman yadau na Samha yaki daukan nawa”

     Kwanciya tayi cike da haushin shi karan sako taji jikin wayarta, tana dubawa ta ganshi Kamar haka”

    _Ki kwanta kiyi bacci dare yayi, idan Kuma bakyajin baccin kibar yariya tayi baccinta, Ina tare da baki gobe da rana zan kiraki_

     Tsaki taja sannan ta aje wayar can gefe”

       ***********
Da misalin Karfe daya aka shaida daurin Auren Khadija da Usman akaro na biyu wadda aka daura amasallacin juma’a bayan dawowa daga daurin auren gidan Baba ya cika da maza wadda yawucensu yan uwa ne, Babu Mata sosai domin bawani shagali akayi ba”

      Ahmad da Galadima zaune akan motar Ahmad bayan dawowan su daga daurin auren akofar gidan su Khadija”

    Galadima ne yace mushiga ciki mana mumusu Allah Sanya alheri?

    Cikin kawar dakai Ahmad yace, iyakata nan, inshiga Mamamu tace nazo Mata rashin kunya,  in zaka saika dawo, nikam Ina nan”

     Dariya Galadima yayi sannan yace”

     Wai Ina ‘yarka?, tazo kuwa??

    Ina tunanin Bata da lbr, kasan tana gidan Hajjah, Nima Alhaji ya gayamin daurin auren, Kuma naje da safe bataimin zancen ba”

    Kai Kuma aidasai ka Gaya Mata”

    Me zance Mata?, Ita ya kamata da Gaya min, sai ince Mata Maman ki zatai aure, itama fah wata irin rikitatta ce, yanzun tace nama mmnta rashin kunya, inason in dauketa yau tana farin ciki dan haka ba abakina ba👌🏻

       Lalllai Ahmad kamar bakai ba??

   Hmnn Galadima Banda abunka Ina ruwana da wannan mgnr haka kawai in ballo wa kaina ruwa, Ina farin ciki sosai kuma nasan fatima zataji Dadi sosai idan taji iyayen ta zasu sake zama tare Amman ba’a bakina ba🙁

         *********

   Mamana albishirin ki?

     Cikin sauri tace”

     Goro Abba”

   Murmushi yayi sannan yace, inason ki cinka ne da kanki, buri kine yau yacika”

      🙄 Abba da gaske?, Kun shirya da Umma ta ne??

    Wucce nan Fatima, yau dinan an maida auren mu anjima zata tare”

      Wani irin uhu tayi, Jin zata fasa Masa kunne yai saurin kashe wayar fuskansa dauke da murmushi”

     Samha kuwa cikin uhu tana daka tsalle take gayawa Hajjah, murmushi tayi tana fadin”

   Ai ninaji tun jiya Yaya ya kirani, Ahmad ma ai yana can yaje gidan”

      Dakin Hajjah ta nufa cikin gudu gudu tare da dan karamin kuka ta dau wayarta”

wayar Uncle takira ya kamar jira ya dauka”

    Yaya akayi ne ??

    Cikin kuka kuka tace”

    Toh ai Kaine kaitafiyan ka ka varni Kuma baka gaya daurin aure ba”

   Ya isa haka, nabiya ne dauki Galadima s……

    Wani nan nasan Dan karkaje Dani ne”

   Kintaba ganin inda akaje da mace daurin aure?

    Kukan ta Kara sawa, toh naji Uncle dan Allah kazo ka daukeni ka kawo nu😫😫

      Diriricewa ya fara tare da sakkowa daga saman motar kukanta ke daukan hankalin sa cikin rarrashi yace”

    Fatima?, Yanzun Inna dauko ki Ina zan kaiki da yamnan nan”

    Uncle ni koma inane ka kaina dan Allah ko gidan Baba ko na Abba”

   Ba inda zan kaiki da yamnan nan ki shirya maza ki hada kayanki yau zamu wuce gida”

     Kukan ta Kara sawa Bata taba masa irin hakaba dan haka duk yabi ya daburce kokarin rarraahinta yake yayin da take kokarin nuna Mata tanason ganin iyayenta ayau”

   Cikin kuka sosai take fadin”

   Uncle wlh bantaba kwana agida ba Dan Allah ko kwana biyu ne”

       Jin kukanta na yawa gashi taki sauraron shi ya kashe wayar yana fadin”

     Baki da hankali yariya”

             ********

    Kiran Alhaji Usman ne ya shigo wayarta lokaci uku saura, ganin sunan sa yasa tai saurin daukan wayar ta dannan tare da karawa akunnenta”

      Amarsu ta ango”

   Karka Kara”

    Murmushi yayi sannan yace”

    Kirarin kune irin naku na amare”

   Hmmm burin ka yacika an matsamin dole in koma gidan ka, kasani tilastamin akayi Kuma bazaka sameni yadda kake soba Dan yanzun bada bane”

    Nima din Khadija ai yanzun badan bane, komai ya canza kamar yadda ya canza miki”

   Karyane wlh ni yanzun ba Khadija da kasani ada ce”

      Haka nima, ba Usman din da bane, Kuma Zaki tabbatar da haka anjima”

     Tsaki taja wlh banson ka na tsane ka”

     Nasan karya kike fada yariya, nasan abun da ke sakaki fadin haka kishine bawani abu ba”

     Tsakin takuma bugawa sannan tace”

    Kudin dakabani na lalle da kitson banyiba kuma bazanyi ba hakanan zaka gannin tsurata Dan haka ka aiko a amsan maka kudin ka”

    Lumshe idonsa yayi sannan ya girgiza Kai ya bude yana fadin”

     Nima mancewa nayi nabada, yanzun natsani lalle, har kitson idan nagansu zuciyata tashi take, nagodewa Allah da bakiyi ba gaskiya ni me sa’a ne, duk abun Dana roki Allah yabani”

    Turiri taji kanta yafara kashe wayar tayi batare daya kashe ba yaran gidan su tafara kwalawa Kira bayan yariyar tazo tace jeki Kira min  Aisha agidan su tamin lalle…….

4 comments

  1. Pingback: discounts
  2. Pingback: pg168
  3. Pingback: Aviator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *