
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
PAGE 36
Karasawa Hajjah tayi ahankali tana kokarin dagota, sai alokacin takula ta jinin dake bin kafarta”
Kasa komai Khadija tayi Banda tsabar firgicin dake damunta, cikin tsananin Tashin hankali Hajjah tace da Khadija ki yiwa driver mgn mutafi Asibiti kawai”
Adirice ta fita yayin da Hajjah tafara kokarin daukan Samha dako motsi batai”
Sosai Khadija tafita cikin hayyacin ta, gaba daya ta kasa sukuni sai kallonta take tare da addu’a cikin ranta”
Hakama Hajjah sai aikin fifita Samha take har suka isa”
Asibitin su Ahmad suka nufa suna isa akai ciki da ita yayin da Khadija da Hajjah suka tsaya curko cirko”
Galadima mane ya gansu cikkin fara’a ya karaso ya mika gaisuwa sannan Hajjah take sanar Masa Fatima ce ta fadi”
Cikin firgici sosai ya jajanta sannan ya nufi Office din Ahmad”
Rubuce rubuce yake yi yayin da gabansa ke faduwa Jin antaba kofar ya dago ya kalli Galadima sannan ya maida kansa ga aikin sa”
Wai kasan su Hajjan suna asibitin nan kuwa???
Wacce Hajjar? Tawa?
Eh ita”
Nan??
Eh, harda Maman Fatima”
Lafiya?, Me sukazo yi?
Kamar sunce Fatima ce ta fad…….
Mikewa yayi batare daya shirya ba yafara kokarin fita, yayin da Galadima ma ya mike ya biyo bayan shi”
Idon sa Akan Hajjah ko kallon gefen da Khadija take beba tukan ya iska Gaban Hajjah yake fadin”
Wai Fatima ta fadi???
Gaba dayan hankalin mutanen gurin ne ya dawo kansu harda ma’aikata adaidai lokacin da Hajjah ke fadin”
Wlh tsautsayi dai baya wuce ranar sa”
Dafe kansa yayi tare da neman wajen zama yana rike da kansa”
Galadima ma ne ya dafashi yana fadin Sorry Ahmad ka shiga ka gani wani hali take ciki”
Rike hannun Galadima yayi kawai ya jima be tashi ba zuwa can ya tashi da taimakon Galadima ya shiga dakin da aka shigar da Samha”
Nan fa ma aikatan suka fara tan bayan Galadima wace tashi babu lafiya yayin da yake bada Amsa matar Dr Ahmad”
Ayau wasu da dama sukasan yana da aure yayin da wasu suke balakin son suga matar tasa”
Khadija kuwa hankalinta yafi na barawo tashi domin kuwa irin jinin dataga Samha nazubarwa gani take kamar bazata tashi ba, haka nan ta tsinci kanta da zubar da hawaye”
Anba awa daya baya babu wadda ya fito daga dakin har yanzun Khadija hawaye kawai take sharewa, tsinta kanta tayi na dannan numan Usman ganin yamma nashirin yi babu wani lbr”
Kamar jira yake ya dauka, saidai jin Khadija na kuka gabashi Mamaki cikin tashin hankali yace”
Meya faru??
Hawayen ta share sannan tace”
Muna Asibiti Samha ce ta fadi”
Runtse idonsa yayi tare da fadin”
Da cikin??, tana Ina wanne halin take ciki yanzun??
Banda masaniya dan tunda suka shiga da ita basu fitoba wajen awa 4 kenan”
Ina Ahmad fah ??
Yana ciki shima”
Sosai hankalin Alhaji Usman ya tashi bayan sun gama waya da Khadija Momy ya Kira ya sanar Mata itama hankalinta tashi yayi yayin da ta nufi asibitin batare data shirya ba”
Misalin 6:00pm Galadima ke sanar masu cikin Fatima ya fita”
Arikece Hajjah tace, damuwata Fatima Sani, tana nan dai lafiya ko??
Alhamdulillah Hajjah abun da ke cikin dai aka rasa”
Bakomai Sani Allah ya basu wani, yanzun Inna Ahmad din daga suna ciki har yanzun”
A’a sun fita ta baya, ku zauna ku huta za’a fito da ita bada jimawa ba”
Kokarin juyawa yake yayin da Hajjah ta sake cewa Sani Ina Ahmad din”
Yana nan zuwa Hajjah bayajin Dadi ne”
Zama sukayi jimmm saidai hankalin su ya kwanta yanzun”
Sai bayan sallar mangariba Aka fito da Samha kwance kawai take tana bacci”
Wani daki na musamman aka basu, har akayi isha’i babu Ahmad, sosai hankalin Hajjah ya koma gurinsa”
Alhaji Usman tare da Momy sukazo yayin da Momy ta jima zaune kusa da Fatima hannunta cikin nata, haka Abbanta ma tsaye yayi kanta tare da Mata addu’a cikin zuciyarsa yana me godiya ga Allah dayabar masa ‘yarsa kwaya daya a duniya”
Ahankali yake Satan kallon Khadija dake zaune can gefe idonta kunbure, tausayi tabashi domin yafo kowa sanin irin yadda Khadija ke son Samha tun tana jaririyarta”
Cika dakin yayi sosai yayin da Daddy da Mahaifin Alhaji Usman suka hallara agurin zuwa wannan lokacin an fara tambayan Ahmad”
Ahankali akaita raguwa lakacin da Usman zai wuce tare da Momy yaso yadanga Khadija saidai babu fuskan yin hakan”
Dakin ya rage Daga aunty Saude sai Khadija da Hajjah, mikewa Khadija tayi Hajjah ni zan wuce”
Ki wuce Inna anan zamu kwana nidake”
Jimmm tayi sannan ta koma ta zauna, yayin da aunty saude ke fadin’
Ni banga kanina ba”
Nima nemamsa nake yi Rabona dashi tun rana”
Mikewa tayi ta fice, itako Khadija cikin ranta ta kule sosai Da Ahmad basai wani ya fada Mata ba tasan fushi yake da fitan cikin tunda yakai har wannan lakacin bezo kan Samha ba kilama ya gwammaci Samhar ta mutu shi yasamu Yaro tunda ya jima be haihu ba sosai taji yana Bata haushi”
Zuwa can Aunty Saude ta dawo jikinta asanyaye tace
Hajjah autan ki fah kuka yake yii, da alama ya kwallafa rai akan cikin nan”
Kukan lafiya? gotai gotai dashi?🤔
Wlh Hajjah kuka yake yi”
Tsaki Hajjah taja sannan tace kiramin shi”
Tabe baki Khadija tayi tare da sama kofar ido aranta take fadin Wai kuka🤔 daman akwai abun da zaisa Ahmad kuka, tunda nake ban taba ganin kukansa ba, baringa ikon Allah”
Sun jima basu shigoba kamar bazasu dawo ba zuwa can saiga Aunty Saude tana rike da Hannun Ahmad yayin da kansa yake asunkuye baka hango komai sai tsinin hancin sa tare da Dan bakin shi”
Suna zuwa saitin gadon Ahmad ya zame hannun sa ya tsaya akan Fatima dake Bacci tare da kura mata ido”
Ya dade ahaka yayin da duk suka bishi da ido, zuwa can saiga hawayen sa na diga agefen Samha”
Tausayi sosai yabawa Hajjah, hannunsa ya ciro cikin aljihun sa ankali yasa afuskan Samha, yana gyara Mata gashinta daya barbaje agoshin ta”
Bayan ya gayama ma sake mayar da hannunsa yayi cikin aljihu Ya sake zuba mata ido”
Hannu Hajjah ta mika ta rike na Ahmad tare da Fadin”
Wai yanzun Yaro abun harda su kuka?, Ka kwatar da hankalin ka Allah zai baku wani, meye amfanin kukan?
Kara gyara wa yayi cikin juya masu baya yana Kan Samha sosai, hare fuskansa dakyau yayi sannan yace”
Ni ba kuka nakeba Hajjah”
Hmmm asai dai Kuma kar a Kuma, Ahmad ai mun auna arziki Allah yakamata mu godemawa”
Alhamdulillah Hajjah, Allah shine abun godiya amman gaskiya nayi bakin ciki kuma wannan abun akwai Sakaci aciki”
Gani irin kallo Hajjah tamai sannan ta koma kallon Khadija da ta mike zata tafi tace”
Khadija Wai saurin me kike ne, kitsaya nan mukwana tare”
Kasa kasa yayi da muryarsa ta yadda Hajjah kadai zataji yace”
Barta ta tafi mana Hajjah, aita gama abun da ya kawota”
Juyawa Khadija tayi ta kalleshi, taji yayi mgn saidai bataji me yace ba, kuma tabbas taga wani irin kallon dayai mata tana juyowa ya dauke kansa adaidai lokacin da Khadija tace me akace???
Hajjah ce tai saurin cewa badake yake ba, koma ki zauna”
Hannun Ahmad yasake sawa ya gyarawa Samha hannunta yana me cewa kuje Hajjah zan kwana tare da ita”
Kallo Hajjah ta bishi dashi sosai hakanan taji ranta ya baci dashi, mikewa tayi ta gyara mayafinta batare da ta kalli gefen da Ahmad din yake ba, tace Allah ya bata lafiya Khadija muje”
Driver ne ya maidasu gida ko ahanya babu me magana sosai ran Hajjah ya baci da Ahmad”
Bashin Salloli suka gabatar ganin Khadija ta zuba tagumi Kan sallaya yasa Hajjah tace kiyi hakuri Khadija ai muma godewa Allah mun auna arziki”
Mikewa tayi kawai tace Hajjah barin je in kwanta nagaji”
Allah ya hutar da gajiya ki duba kitchen ki samu madara kisha”
Toh Hajjah”
*******
Itako Hajjah dakin Daddy ta nufa, cikin murmushi ya kalleta yana fadin kin hakura kin taho kenan”
Zama tayi gefen sa cikin yanayin damuwa tace”
Ahmad ne ya bata min rai Alhaji, ka dinga mashi fada fah bashi da mutunci😔
Meya faru??
Zargin Khadija yake akan fitan cikin nan, wanni irin tunani ne wannan?, Alhaji gaskiya kayi mishi fada sirikarsa ce Khadija ayanzun ‘yarta yake aure dan haka dole ya girmamata, inba hauka irin na Ahmad ba yadda uwa take son danta har yake tunanin Khadija zata iya yin wani abu makamcin wannan kawai dan ta zubar masa da ciki idan ta rasa ‘yarta fah?
Bazai yiyuba kam gaskiya kiyi hakuri shima din kila ba haka yake nufiba kin masa bahagun Fahimta ne”
Fada fah yayi Alhaji agaban ta saidai bataji me yace ba, nidai kawai ka mishi Fada, Khadija ‘yata ce Mahaifinta ya rage min nono bazan yadda ya dinga wulakantata ba, duk son da yake nuna yanawa yariyar nan karyarsa yace yafi uwarta sonta, dan haka yadawo cikin hankalin shi inba hakaba wlh shima ranshi zai baci dan yanaji yana gani Fatima zata gagare shi”
Ajiyan zuciya Daddy yayi sannan yace ahuce haka, dole zan masa fada kiyi hakuri”
Mikewa Hajjah tayi ta fice dakin”
Washegari da Safe Daddy ya dauki Hajjah suka wace asibitin, Khadija kadai agidan zuwa can Hajjah ta dawo sannu Khadija taimata sannan ta Mata yame jiki”
Nan Hajjah ta fadada fuskarta tana fadin”
Me jiki tana zaune abunta ta samu sauki sosai, can muka Iske Babanta tare da yayarsa din nan, tanako ta tambayan ki Wai tajima Bata ganki ba”
Allah sarki Khadija tace kawai”
Mikewa tayi da niyyar barin wajen Hajjah tace duba nan Khadija”
Dawowa tayi ta zauna Saida Hajjah ta kureta da ido sannan tace”
Wani abu nalura dashi nake son tabbatar wa, Mahaifin yariyar nan kamar yana son mayar daki dakin ki🤔
Jimmm, tayi sannan tace ni a’a Hajjah ba haka bane Kuma koma akwai hakan cikin ranshi toh ni gaskiya bazan koma ba”
Sabo dame Khadija?, Inace kaddara ce ta rabaku tunda kikayi aure dashi babu yaji bare saki sai rana daya kwatsam, kula baki taba kawo korafin wani mugun halinsa ba bamu tabajin kanku ba”
Hajjah nidai Allah kibarmin mgnr sa, wlh ko Maza sun kare bazan koma masa ba
Ikon Allah aini inace ko Albarkacin Fatima Zaki koma”
Bazan koma ba Hajjah ni dashi har abada”
Toh ai shikenan Allah ya fito miki da nagari kibar zaman nan haka kin jima agida Kuma Khadija barasa manema kikayi ba🤔
Hajjah zanyi dazaran lokacin yayi…….
Ganin turi kofar Ahmad yana rungume da Samha yasata tai shiru tare da dauke kanta daga gefen su”
Kusa da Hajjah ya direta yayin da ya kalli gefen Khadija ya dauke kansa tare da kara hade fuskan sa”
Hajjah ce ke kallon Samha tana cewa sannu Samha Allah zai baku wani karku damu kinji”
Hawayen da Samha take makalewa ne suka sakko sauyi tayi tasa hannunta ta share tare da Satan kallon Mamanta sannan tace”
Sannu Umma”
Yauwa Sannu ya jiki?
Bata amsa ba jikin Hajjah ta koma ta kwanta tare da cigaba da share hawayenta da kayan jikin Hajjah”
Lura tayi da Yadda Samha ke kuka amman tana boyewa Bata son tagani”
Ahmad kuwa Banda kunbure kunbure babu abun da yake yi, yana zaune kawai, inda Samha kawai yake kallo kafarsa daya Kan daya”
Itako Khadija Mamakin take ganin Ahmad ko inda take bayya kallo barema har ya gaidata kamar yadda ya samo yanzun ko me hakan ke nufi🤔
Wayar Samha dake hannun Ahmad ce ta fara kuka dubawa yayi yaga Abbanta ne dan haka yai saurin mikewa ya bata wayar”
Abba na😭
Na’am Mamana ya jikin naki?
Cikin fashewa da kuka tace da sauki Abba”
Menene Mamana meke saki kuka??
Bakomai Abba😭
Shiru yayi yana nazari zuwa can yace”
Mamana kuyi hakuri mana, kamar yaune Allah zai baku me zama insha Allahu”
Toh Abba ai nasha wahala fah sosai”
Kinaji Mamana nace ki kwatar da hankalin ki, zan tayaki Addu’a Allah ya baki da sauki”
Hawayen ta share tare da fadin”
Ameen Abba”
Sai anjima Allah ya Kara sauki”
Ameen ta sake cewa sannan ta aje wayar agefenta tana me cigaba da goge fuskanta”
Mikewa Ahmad yayi ya karaso wajen yana fadin”
Bari mukoma gida ta huta Hajjah, anjima zan dawo”
Jimmm Hajjah tayi zuwa can tace ai inaga kabarta anan tadanji kwari tukuna”
A’a Hajjah gwara dai muje gida kawai zaifi wani lokacin zan dawo miki da ita”
Sosai ran Hajjah ya bacci, cikin tsananin fushi tace”
Shikenan, Fatima tashi kuje, nikuma karna sake ganin ko kafarka agidan nan tunda nice baka yadda dani ba, nazubar maka da ciki ko?
Cikin Ido ya kalli Hajjah alokacin daya fito da idonsa waje”
Itama Khadija da ido ta bishi aranta take fadin me Ahmad ke nufi ne? Bazai taba cewa uwar shi ba saidai yace ni sabo da ya raina nani, Ido ta zuba masa tana son fahimtan inda ya dosa yayin Hajjah ta mike tace kuje kawai”
Ni Hajja bance keba ai Amma wannan kiyayya ce kawai ba wani abu ba idan……..
Afusace Hajjah tace”
Ahmad idan ka sake cewa wani abu adakin nan Allah ya isa nonona dakasha ban yafe maka ba”
Dole yaja bakinsa tare da runtse idonsa afusace yabar dakin kamar zai tashi Sama”
Khadija kuwa tuni taji kanta namata tiriri, har zuciyarta take jin haushin dakatar dashi da Hajjah tayi domin taso ya fadi abun da yake zuciyarsa”
Kallon Samha tayi tare da Jin wani bacin rai ya bijiro mata kwata kwata Samha bata ta tarbiyya tana mgn Da Abbanta kamar tanayi da kawarta Kuma abun bakin cikin batajin kunyar sirikarta wacce irin Fitsara ce wannan, juyawa tayi ta kalli Hajja dake kokarin shiga toilet tace Hajjah ai da kin sani kibar Ahmad ya fada abun da yake zuciyar shi, wannan mgnr nasan dani yake bada kowa b…….
A’a a’a Khadija kull, ai be isaba Khadija, kinfi karfinsa Sam badake yake ba ai kinsan daman daker ya kawota shi tunanin shi yafini iya kula da ita yaushe zaice ke Khadija, ai saiya kashe auren sa da kansa, kinaji nine kinga kwanan su daya da zuwa nan abun ya faru kuma ai tunda take ciwon yana gida yana kula da ita tunanin sa zaice rana daya dan ya fita anyi sakaci, hauka yake zaice ke, ko shi din zai nuna miki son Fatimar ne??
Duk da cewa tafi gasgata da ita yake taji dadin Mgnr hajjah, jimm tayi zuwa can tace”
Nidai Hajja kiyi mgn dashi, irin wannan rainin naguda tun farko naki auren Samha da Ahmad gashi yanzun ya fara faruwa, tun farko beganina da mutunci ya raina ni”
Nace miki badake yake ba ko🤔
Hajjah nifa banji mamaki ba kawai abun da nakeson yasani bazan dauki wukancin shiba, mikewa tayi tare da jawo gyalenta afusace tace”
Hajjah ki gaya mishi bansan yana zargina basaiya kaini kotu, idan Kuma shi be kaini ba ni zan kaishi”
Subuhallahi🤦🏼♀️ ke!! Khadija!! Ficewa tayi afusace batare data saurari Hajjah ba”
Cikin kuka sosai Samha ta mike tafi bayan Khadija tana fadin Umma dan Allah ki tsaya karki tafi dan Allah”
Aharaban gidan tasha gaban Khadija tana matsanancin kuka, Umma kiyi hakuri wlh bahaka bane kwata kwata beyi irin wannan mgnr da kukeyi ba wlh bece komai ba, kiyi hakuri idan ya dawo zan fada Masa zamewa nayi”
Wani lafiyayyen mari Khadija tabawa Samha, hannuta tasa ta dafe tare da fashewa da kuka Cikin kukan take fadin”
Umma kiyi hakuri, dan Allah badan niba Umma”
Ai bakisan darajata ba Samha koda yake kema baki da mutunci yadda yake kema haka yana fitsara gaban iyayen sa kema kinayi gaban naki iyayen tare da sirikan ki ‘yar karamarki dake bakinsan kunyaba, toh ‘ya mace kunya adoce agunta kwata kwata dabi’un ku basu dakyau babu tsari, natsana dabi’un ki”
Kanta asaka ta share hawayenta sannan tace zan gyara Umma kiyi hakuri kinji”
Ko ki gyara ko kada ki gyara ruwanki, kina zaune da mara mutunci badole nakima yayi gaba ba, ni matsa kibani guri hannun tasa ta hankadeta ta fadi kasa, tana kokarin wucewa taga hannun Ahmad yana kokarin daga Samha yayin da ita Kuma Samha ta rike Khadija”
Korarin janta daga jikin Khadija yakeyi yaji Saukan lafiyayyen mari ahuskansa”
Dafe gurin yayi tare da sakin Samha yana kallon Khadija”
Zoka rama”
Cikin sauri ya kalli Samha tare da sunkuyar da kansa”
Kazo ka rama nace”
Har yanzun be dago kansaba”
Dagowa Samha tayi daga jikinta tana fadin”
Kazo karama shikadai ne ya rage maka amman Fitsarar ka vabu wacce ban gani ba”
Wani abu me daci ya hadiye tare da karayin kasa da kansa”
Itako Khadija ta tsare shi da ido ganin yaki dago kanshi tace dan iska kawai mara mutuci karka Kara matsowa kusa dani ba Khadija dakani dabace wlh sai inci ubanka”
Dagowa yayi ya kalleta tare da saurin maida kanshi kasa”
Kada Kai tayi tare da fadin Ina jiranka bazan San kai tantinri bane saina ganmu akotu ni da kai Ahmad…
Wucewa tayi ta bar gidan yayin da Samha ta nufi gidan tana kuka”
Shiko Ahmad ya dade tsaye aguri zuwa can ya jinjina kansa tare dayin kwafa ya nufi cikin gidan”
Kan gadon Hajjah ya samu Samha ta kifa Kai tana kuka shima kwanciya yayi tare da jawo ta jikin sa”
Fatima meye yake faru wa ne”
Cikin matsancin kuka tace”
Uncle narasa inda zan saka kaina, Wai dan Allah me kake nufi da maganganun daka yi dazon nan, anan gurin, Ummana tace ita kake zargi Hajjah Kuma tace da ita kake😭😭😭
Jimmm yayi zuwa can ya zame Dan kwalin kanta yana shafa kanta yake fadin”
Fatima Ina cikin damuwa sosai, bazan iya tuna abun da nace ba dazon”
Ummana tace kana zarkinta akan barin da nayi”
Ni ban fada ba Fatima, Ina son ki aje wannan aranki, babu wadda nake zargi”
Ajiyan zuciya tayi sannan tace wlh Uncle zamewa nayi Kuma Hajja ma saida tace min in bari tamin nace dakaina zanyi”
Kanta ya sunbata sannan yace shikenan ya wuce In ankwana biyu zamuje mubata hakuri naga tayi fushi sosai”
Kanta ta girgiza alamar gamsuwa sannan yace to share hawayen ki ki saki ran ki”
Yadda yace tayi sannan yayi murmushi tare da fadin Ina zuwa barin inje gurin Hajjah in dawo”
************
Tamin laifin sannan ta zazzagini, ta dakeni sannan Kuma duk ace wai nine Banda mutunci Hajjah?, Harta iya bude baki tace miki wai nakaita Kotu, wato tanaganin akwai zumunci babu abun da zan iyayi ne??, Hajjah kema ki nutsu dakyau ki gani Hajjah Ina tunanin rabon data kwana gidan nan tun tana budurwa, meya kawota aranar da mukazo, Kuma batasan da cewa zata iya kwana gidan nan ba Saida taga zamu kwana anan, nifa Hajjah yanzun ne nattabatar da tsantsan tsanar da Khadija take min”
********
Wacce irin mgn ce Haka kike yi Khadija”
Eh, nasan kajinin Sarai, lokacin da nake gaya maka kar ayi auren nan alokacin ne Kai kuma kayi niyarsa saboda ka kuntata min, kayi abun da ranka yake so baka nemi shawarata ba, toh ga irin abun da nake gudu ya fara faruwa, yanzun Ahmad zargina yake akan fittan cikin Samha”
Runtse Ido Alhaji Usman yayi, take jikinsa yayi sanyi gaba daya”
Cikin tsananin Mamaki yace shi Ahmad dinne yake zargin kina da hannu akan zubewan cikin na Samha?, Ikon Allah, garin yaya irin haka ke faruwa??
Himmm yanzun ne kake da lokacin sauraron Jin ta bakina, ai bazaka gane waye surukin kaba saikajimu akotu, idan ba haka nayiba Ahmad bazai kiyayeni
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 37
Ina zuwa Khadija”
Duk bakai kaja komai ba, Kaine ka nuna bani da daraja dole Ahmad ya wukantani, kuka Khadija tafara dan haka ta kashe wayar tunda tafara tunanin Ahmad zarginta yakeyi tayi kuka ba sai yanzun da take waya da Usman batai niyyar yin kuka ba, dan bataga abun kukan ba Amman yanzun ta tuna irin yadda aka nuna ita bakomai bace lokacin auren Kiran da Usman yayi shiyasata saurin share hawaye sannan ta dauka”
Khadija, kiyi hakuri kinji?, Zanyi wani abu akai, ni bansan cewa irin haka nafaruwa tsakanin ki da Ahmad ba, abun da nasani kawai mutumin ki ne, kuna shiri, kuma bashi da wani aibu yafito gidan mutunci kuntashi tare, abu nagaba Kuma ninasan yadda rashin zuwanshi gidan nan ke damunki sannan nafahimci yana kishi akanki tun farkon zuwana wajen ki wadda Saida nakyauda idona daga wulakancin sa sannan nasamu na aureki, Khadija wannan dalilin ne yasa daya fara zuwa wajenki gidana naji natsaneshi banson shi banson ganin sa sosai nake kishi dashi dan gani nake yana zuwa ne kawai yana kalle min mata, Khadija banbar kishi da Ahmad ba harsai ranar da naji da kunnena yace min wai yana son Samha, tundaga ranar nafara bacci me Dadi wadda rabona dashi tun muna tare, sannan nasawa zuciyata zaki dawo gareni, hankalina bekara tashiba sai ranar da kikacemin karna bawa Ahmad auren Samha, tundaga ranar hankalina be sake kwanciyaba saidana daura auren, dan Ina da tabbacin Ahmad zai riketa dakyau, inason ki gane wani abu guda daya, duk abun da yafaru akan auren Mamana banyi dan na wulakantaki ba kuma bansan akwai wani takun saka tsakanin keda Ahmad”
Yanzun Ina neman wani alfarma agare ki”
Babu wani alfarman dazan maka bana neman sulhu tsakanina dakai, nagaya makane domin kasani, idan daman so kake ya wulakantani to kazuba ruwa akasa kasha, idan Kuma kana tunanin mutumin kirki kabawa Samha to yanzun kasan wanene shi”
Duk na fahimta Khadija, abun da nakeson dake kicire mgnr neman sulhu tsakanina dake anan gurin, yanzun kawai abun da nakeso dake kawai kibani lokacin zanyiwa tumkar hanci”
Me?? Wlh wlh bazan yadda ba, nine zaice nazubar mishi da ciki??
Khadija😬😬 dan Allah ki daina Maimaifa wannan mgnr bata da Dadi Jin, ke uwace, kiyi hakuri, wannan ba girman ki bane”
Au sai in zauna yaitamin iskancin dayaga dama wlh idan bekaini kotu ba nisaina kaishi kwana daya nabashi inajiran Sammaci, katse Kiran tayi yayin da taga Inna agabanta”
Bataso sukaji mgnr ba dan haka ta fara share hawaye”
Cikin sanyin jiki Inna tace Ahmad din ne yace kece kika zubar da cikin”
Hawayene suka zubo Mata eh Inna yana zargina akan haka”
Shiru Inna tayi, yayin da Inna Yalwa tace bemiki adalciba kuwa, ba ance faduwa tayi ba koko nufinsa ke kika hankadeta, wannan aiba abun dazai yiyu bane”
Barshi Inna wlh yana Wasa danine, narantse idan bekaini kotu ba nisa……
Hannu Innarta taga mata tare da fadin”
Kiyi hakuri kibi komai ahankali, wata kila kiyayyar da kike nuna masa yasa yafada haka”
Inna ni wacce kiyayya ce nake nuna masa, kawai dai bana sakar masu fuska dagashi har Samha, Kuma ni rashin kunyace daman banaso…..
Wayarta ce ta sakeyin kara dan haka ta dauka yayin dasu Inna sukayi waje”
Khadija?, Ki kwantar da hankalin ki zanyi wani abu akai”
Naji”
Banason kin ji ai nasan kinji daman, kicemin to, nafi kowa sanin halin ki idan ranki ya baci”
Ni gaskiya kwana daya kwai nabashi”
Shikenan naji anjima zankiraki Kuma nagode da kika Gaya min banjiki kawai a kotun ba”
Kashe wayar yayi tare da mikewa tsaye ya kama kugu tare da fadin”
Rigimammiya kawai”
Yawo yafarayi afalon yakai ya kawo zuwa can ya daga waya yasa akunnen sa”
Ahmad ya Kira ciki. Girmamawa ya gaidasa, saidai yaji Muryan alhji Usman ba yadda yasaba jinta ba”
Ina son ganin ka aina zamu hadu??
Jimm yayi sannan yace toh zanzo gida anjima”
Ina jiran ka saikazo”
Kashe wayar yayi sannan yacigaba da cewa Hajjah”
Nifa ta dade tana nuna min kiyayya kawai dan Ina kyauda kaina ne”
Duba Ahmad, Bata yadda za’ayi ace kana auren Fatima bazaka girmama Khadija ba, bazai yiyu bane”
Ina girmamata Hajjah na dauka ta hakura yanzun sai jiya nagane indata dosa, tunda batason alakarmu da ita “
Shikenan Ahmad naji Khadija batason auren ka da Fatima, ta zubar maka da ciki nikuma a matsayina na uwarka nace kasakar mata ‘yarta dan gudun lalacewan zumunci”
Kawar dakai yayi can gefe, Hajjah ni inason mamata”
Nikuma indai nina haifeka matsawar bazaka girmama Khadija ba nabaka Umarni kasaki Fatima daga lokacin kana iya yin daben da Khadija tunda Kai din dan iskane”
Cikin sauri ya kalli Hajjah, yayin da ta sake cewa eh, aini bansan rashin kunyarka takai hakaba tunda Khadija take fadin Kai fitsararrene banta yadda basai yau wlh Ahmad baka da ta ido, aini ban dauka zaka yi irin wannan mgnr ko gabana ba bare gaban Khadija”
Yawun takaici ya hadiye sannan yace”
Nifa Hajjah ki kwantar da hankalin ki nayin mgnr ne kawai badan ranki yabaci ba Hajjah
Ido Hajjah ta tsura masa zuwa can ta fara hawaye”
Hajjah kukan kuma??
Tashi kaje Ahmad banson kanin ka”
Mikewa yayi jikinsa asanyaye kallon Hajjah ya sakeyi kiyi hakuri Hajjah indai nine bazan sake tayar da mgnr ba”
Banza tayi dashi tana binsa da kallo harya fita”
Koda ya koma dakinsa yadda Hajjah ke kuka ne yaita damun sa, zuwa can ya tuna yadda Khadija ta kwasa masa bari, cikin sauri ya kawar da kansa, zagin data kunduma masa ne ya fado masa, runtse idon sa yayi yana me Jin takaici, Tsaki yaja tare da mikewa tsaye Samha ce ta fado masa arai afili yace”
Bani da yadda zanyi dole Khadija zataci darajar Fatima, Amman Ina bakin cikin zagin data min tunawa yayi da acikin jikin Fatima da ya fita tsintan kansa yayi da fadawa gado ya dafe kansa sosai yake bakin cikin fitan cikin Fatima”
Itako Samha takira Khadija yafi so 10 taki dauka, sosai jikinta yai sanyi sabo da fadan data mata, hakuri take son takara Bata Amman taki dauka”
Misalin 8:00pm Ahmad ya shigo dakin Hajjah
Sallama yayi ya tura kofar babu kowa adakin Daga bayan shi yaji muryan Hajjah tana fadin”
Tashiga wanka”
Ajiyan zuciya yayi sannan yace toh Hajjah ni zani gidan su, Babanta ya kirani dazon Wai yana nema na”
Tunanii Hajjah ta shiga sannan tace”
Lafiya??
Shine zani inji Hajjah”
**********
Wayar hannunsa ya aje agefensa sannan yace nasan zakayi Mamakin Kiran ka danayi, wata mgn ce danaji bataimin Dadi ba nake son najita daga bakin ka”
Kan Ahmad akasa sosai ya kasa Dagowa Ya kalli Alhaji Usman”
Ahmad, nan gurin babu karamin yaro, nasan ciwon kaina Kuma nasan kaima kasan ciwon kanka dan haka Ina rokonka kada mu batawa juna lokaci, amsa kawai nake son kabani”
Batare da ya dagoba yace Insha Allahu”
Yaya Khadija tayi ko ince wacce hanyar Khadija tabi ta zubar maka da ciki?, yamutsa fuska Alhaji Usman yayi sannan yace, tace kana zarginta akan ita tai dalilin fitan cikin, hankalina ya tashi sosai, taya uwa zata yi wannan aikin inason in sani??
Kasa mgn Ahmad yayi harsaida Alhaji Usman yace inajin ka”
Abba ni bance haka Kai tsaye ba, itama kawai ta dauki abun da zafi ne”
Wani irin kallo Alhaji Usman yai masa, sannan yace, inason ka maimaita min abun daka fada harta dauka da zafin??
Kara kasa yayi da kansa sosai ji yake kamar kasa tabude ya shiga, ni nasan tabbas nayi mgn cikin baccin rai yanzun bazan iya maimaitawa Abba”
Ido Alhaji Usma ya kura masa sosai, sannan yace idan na fahimceka kana dai zargin nata kenan??
A’a Amman dai nayi Mamakin zuwanta gidan rabon data da takwana tun kafin tayi aure, sannan aranar mukaje itama aranar tazo shiyasa kawai nazargi wani abu”
Wannan ba hujja bace Ahmad, Fatima dai ‘yar Khadija ce, ita ta haifeta, idan ta samu rabo Bata so, har yakaiga tana son ya zobe bazata cutar da ‘yarta ba, kwai hanyoyi da dama da mata kanbi wajen yin irin haka, batare da an zargesu ba, Kai likitane basai nama bayani ba, ni ance min Fatima tsantsine ya debeta tafadi, yanzun misali wannan cikin da kake ikirarin anzubar maka, be iso duniya ba fah?
Kai Ahmad ya jinjina”
Yayin da Usman yaci gaba da fadin”
Ka kwantata min inda yazo duniya wanni irin so zaka mishi, akwai alamar zaka so shi Kuma zaka tarairaiyeshi kamar Kwai???
Kansa akasa yace hakane Abba”
Toh inason ka kwatanta son da kakeyiwa cikin, Khadija nayiwa Fatima fiye dason da kakeyiwa cikin ka, acikin ta rayi rayuwa tsayon wata tara, tayi nakudar ta bayan ta iso duniyar ta shayar da ita, sannan ta bata duk wata kulawa da uwa take bawa danta, tagoyata abayanta har ta girma, ashe koda ba ita tabaka auren taba ta taka muhimmiyar rawa arayuwar ta wadda ta cancanci ka girmamata matsayinta na mahaifiyar matar da kake fatan tazamo uwar ‘ya’yan ka, kaduba yadda iyaye ke kaffa kaffa da ‘ya’yan su, suna girma ne son yaron na dada shigajikin mutum, bafa baya yakeja ba Ahmad, akullum ta Allah son yaron karuwa yake koda kuwa ace yaron bawani kyautata maka yake ba yana Bata maka rai wani ma yana dauko mgn amman duk da haka ji jake kamar Kara maka sonshi ake, nasan zaka iya ganin Kamar Khadija bason Fatima take ba, saboda yadda takeyi wasu abubuwa nata amman inason kasani Kaza tana taka dantane badan bataso ba….
Ashe kuwa Khadija bazata zubarda wani abu ba dan Fatima ta taka tafadi tana da juna biyu idan ta mutu fa sanadin haka Ahmad??
Ina tabbatar maka idan har zatayi haka toh kenan zata iya kasheta”
Sosai zufa tafara zubuwa Ahmad, ji yake kamar ya tsaga kasa ya shiga”
Ido Alhaji Usman ya tsura mishi sannan yace”
A agaskiya Ahmad bakawa Khadija adallaci ba wajen furta wannan kalmar kaci mata fuska, Kuma kayi rashin kunya, matsayinta na uwa, nasan bata gimeka ba, Amman Kuma ta wani bangaren ta girmeka, tunda tahaifa takuma baka yakamata tazama me mutunci a idonka”
Kwata kwata ban tsammaci irin haka daga gareka ba”
Kasa cewa kumai yayi jikinshi yayi sanyi sosai dago kansa yayi kadan tare da fadin”
Zan gyara Abba nafahimci nayi kuskure Kuma zan kiyaye gaba”
Yauwa yayi kyau hakan, Amman dai Fatima batasan wannan mgnr ba ko??
Eh Bata sani ba”
Toh karka yadda ta sani, kasan dai yadda aka tarota daker, sannan zan daukeka yanzun muje kabawa Khadija hakuri”
Jimmm Ahmad yayi cikin yanayi irin na me tunani, tabas ya fahimci kuskurensa Amman yana tunanin yadda zai tsaya gaban Khadija dasunan Wai yazo bata hakuri😬 tuna yadda take fuffuka jiya yakeyi idan yaje gabanta ayau yasan komai na iya faruwa to mema zaici mata ne?🤦🏻♂️
Ahmad bakace komai ba nace zamuje yanzun mubata hakuri?
Toh shikenan Abba amma a…
Amman me ina jinka”
Dagowa yayi yakalli Abba kadan yace”
Ina nufin gobe zanje dakaina wajenta”
Murmushi Alhaji Usman yayi kadan sannan yace”
A’a yau zamuje basai gobe ba, inason Khadija ta huce dan tayi fushi sosai ba kadan ba”
Shikenan Abba”
Mikewa Alhaji Usman yayi yayin da Ahmad yafara gaba cikin yanayi na girmamawa suke tafiya tare da Alhaji Usman, tsintan kansa yayi da faduwan gaba, yaso ace koda zai bata hakuri yazama shida itane, har suka fita farfajiyar gidan yana cikin tunani tabas yadda yaga Khadija tayi fushi jiya idan yaje gabanta ayau zai fuskanci wulakanci”
Motar Daddy suka shiga yayin da yarasa abun yi, neman mafita kawai yake……..
https://askoff.ru
https://asklong.ru