Advertisements

MAJIN MARAINIYA PAGE 6

MAJIN MARAINIYA PAGE 6

Posted by

MAJIN MARAINIYA PAGE 6

 

Advertisements

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed

16-18

Advertisements

ummi karasowa tayi da gudu ta rike jalal tana fadin jalal baka da han kaline ,me yayi maka, da ker ummi ta janye jalal daga jikin sultan, hancin sa har ya fara fitar da jini.
ummi matsawa tayi kusa da sultan tace sultan jeka gida zan zo na same mamar ka, yace ummi amman dai kin ga abinda yayi min ko?
na gani kuma zanyi maganin sa, ka kwantar da hankalin ka.
sultan girgiza kai kawai yayi, ya shiga motar sa yabar wajen.

Jalal na tsaye sai huce yake yi , safna kuwa dama tun da taga fada ya kaure ta ruga da gudu ta shiga gida

ummi ce ta juyo ta kalli jalal dake tsaye ban da huce babu abin da yake yi, tace muje ciki, gaba ya shi ga ummi nabin sa a baya.

Advertisements

suna shiga ummi tace me kake nufi da kake koran ma safna saurayi.
sai da ya dukar dakai sannan yace ba abin da nake nufi ummi kawai tarbiyan da akama safna ne ban ji dadin ganin ta ahaka ba, kuma ummi be kamata abarta tana kula samari ba, ummi sultan fah ba mutumin kirki bane lalata yaran muta ne kawai yake yi.

sai da ummi ta karewa jalal kallo san nan tace, jalal ni fah na haifeka kar ka manta kamin alkawarin babu aure tsakanin ka da yarinyar nan , to meye naka na tada hankalin ka dan ka ganta da wani, to bari kaji na fada maka daga yau babu ruwan ka da safna sultan auren ta zai yi kar na kara ganin kaje kusa da su , inhar kana son azauna lafiya.

amman dai ummi ai be kamata ace za,a mata aure yanzun ba.
babu ruwanka ba abinda ya shafe ka, suna cikin haka suji sallaman hajiya baturiya mahaifiyar sultan tana rike da hannun sultan, jalal be sauri me zasu ce ba, ya nufi dakin kairat ya samu safna kwance sai kuka take, ya dade tsaye akanta bata ma san ya shigo ba, sai da ya kare mata kallo sannan yace safna, da sauri ta dago ta kalleshi.
Ya sake cewa safna kina kuka na korar miki saurayi.

gargiza kai tayi tace ba haka bane yaya ni fada ne bana son naga anayi.
Jalal murna ta kama shi ashe dai tana da hankali.
yace safna daga yau karki kara zuwa gurin sultan , ba auren ki zaiyi ba kamar yadda ummi take fada, in na kara ganinki da sultan ranki zai baci, ya sake kwantar da murya yace ko kina son sultan din ne?

Shiru tayi, tayi kasa da kai dan jalal ya mata kwar jini da yawa, dan gani tayi ya kara mata kyau duk wanda tayi dace ta samu jalal a matsayin miji ta more.
Jalal sake maimaita tambayan sa yayi safna nace ko kina son sultan din ne.
kanta akasa tace ni dama ummi ce take tura ni.
dadi yaji sosai ban da shi akwai wasu da ke zuwa gurinki ne? eh tace dashi.

to daga yau koma wanene yazo karki Kara fita, kuma safna me yasa kike fita waje a haka, har ki zauna kina hira da wani dubi jikin ki fah duk awaje yake, kanki ko dan kwali babu, haba safna sai kace ba yar musulmai ba, baki da hijjab ne ko gyale.

safna ta kalli jikinta gaskiya jalal ya fada kwata kwata be tace ba, tace ina dashi yaya amman ummi tace na dai na sanya hijjab idan zan fita.

Jalal shiru yayi nadan wani lokaci san nan yace karki kara saka irin wadan nan kayan, mijin kine kawai ya kamata ya ganki da su, kuma inzaki fita ki sanya hijjab ko gyale , kinji ko?

juyawa yayi zai fita safna ta bishi da kallo har ya kule.
lokacin da jalal ya fito ummi kadai ya samu a falon dan haka besan me suka shirya ba, zuwa yayi ya wuce ummi da sauri ya shiga dakin sa,
ummi binshi tayi da kallo ta mike ta shiga dakin safna, wani mugun kallo ta mata sannan tace jalal nan ya shigo?
eh.
me yace miki?
cikin in ina tace ba komi.
saukan mari taji a fuskar ta ke dan ubanki ni zaki ma karya zaki gayamin ko sai na miki illa.
safna tana kuka tace cewa yayi karna kara fita gurin wani.

Lallai kuwa ashe ba zaman lafiya kinzo har gida zaki rabani da dana, to baki isa ba

Bayan kwana uku da yin haka jalal yasa ma safna ido sosai dan yanzun yana zama agida sosai .
yau ko ya kula ummi shirye shiryen fita takeyi, ya name guri ya zauna afalo duk da cewa ummi fushi take dashi, ba kamar da ba.

kalon shi tayi taga bashi da niyar tashi tace yau bazaka fita bane?
zan fita amman sai an jima.
tabe baki tayi ta kira safna tamika mata wata leda tace kaya ne aciki maza ki sa kizo mutafi, ta karba ta juya.
jalal ko jira yake yoga wani irin kaya ne.
ummi ta gaji da jira, ta sake daga murya tace wai me kikeyi har yanzun.
cikin sauri tace ummi ganinan zuwa ta kara kasa da murya ummi yaya jalal fah yace na daina yawo a haka.

ummi tsaki tayi, ki fito kina bata min lokaci, ta mike ta fita, jalal na zaune saiga safna ta fito ta matse riga da wando ne jikin ta sai wani dan kamin gyale, a tsorace ta wuce shi ya bita da kallo, har ta fita yaga bazai iya jurewa ba ya mike yabi bayan su
Lokacin tuni ummi ta shiga cikin mota,itako safna kokarin shiga take, jalal yace safna karki sake ki shiga cikin motar nan.
cikin fada ummi tace wai kai jalal Ina wasa dakai ne ko ni abokiyar wasan ka ce,
ummi wlh safna bazata fita tsirara ba

4 comments

  1. Pingback: 789 club
  2. Pingback: evolution gaming
  3. Pingback: About BAU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *