MIJIN MARAINIYA PAGE 13

MIJIN MARAINIYA PAGE 13

Posted by

MIJIN MARAINIYA PAGE 13

 

💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘

Story
&
written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝

51-53

Alhaji yace shikenan hajiya duk inda kikace haka za,ayi,haka kowa ya koma ya kwanta kowa zuciya babu dadi, jalal kuwa bayan ya koma daki kuka ya saka gidan da aka dade ana ginawa saida aka gama kashe kudi, zargi kala kala ya ziyarci zuciyar shi gaskiya yana zargi sultan da mahaifiyar shi ,kafin safe idon jalal yayi jazur sun dan tasa .

karfe bakwai jalal ya fito sanye da jallabiya fara sol , da bakin glass a idon sa, saboda baya son afahimci halin da yake ciki , saida ya fara gaida su hajiya sannan ya wace dakin alhaji, yana shiga yacire glass din ya rike ahannun shi, alhaji ya kalli jalal yace wai kai ba kasan kaddara bane ji inda fuskar ka ta koma saikace ba musulmi ba.
Jalal yace daddy ba haka bane abin da yake bata min rai nasan gidan nan kona shi akayi kuma wlh nasan bazai wuce sultan bane dan nasan shi kadai ne zai min haka.
dakatar dashi alhaji yayi cikin fada karna kara jin kafadi wannan maganar mubarwa Allah kawai shiyafi, kuma daurin aure nanan insha Allah ajima za,a daura .
dadi sosai jalal yaji yace daddy nagode yana fitowa dakin ummi ya shiga suna saune ita da wata kawar ta data kwana agida.
ummi tace kardai kacemin kuka ka kwana kanayi jalal kana sone kayi kanka illa akan yariyar da badamuwa tayi dakai ba.
dokar dakai yayi yace ummi me yasa kikace haka, ni nasan safna nasona kawai domuwa ne ya mata yawa shiyasa ma nafi son adaura auran ko hakalin ta zai kwanta, nima kaina hakali na ba,a kwance yake ba bare kuma safna.

hajiya adama kawar ummi dake zaune agefe tace rabo da ita jalal kaji , ance maganar bikin nanan ko?
eh yana nan in Allah ya yarda
hajiya adama tasa ke cewa toh yanzun a ina zaka zauna kenan?
yace nima ban sani ba.
jalal ya gaji da tambayoyin su dan haka yace ummi bari naje

bayan ya fito yayi tunani yaje yaga halin da safna take ciki dan haka ya doshi daki, dakin cike yake da mutane, su anty nusaiba ne sauran dai duk besan suba, bayan yagaida su, ya hango safna daga cen bayan anty nusaiba, yace anty dan turomin yariyar cen, yajuya zaita fi anty ta tsaida shi tace zoka zauna kuyi maganar adaki dan abin ya fara bani tsoro, mikewa sukayi suka fita jalal yashigo cikin dakin ya zauna abakin gado yace safna tashi mana, ke wacce irin amarya ce har yanzun kina kwance.

mikewa tayi ta gaida shi, jalal yace safna kinji abinda ya same mu ko, dan Allah karki ce zakisa wannan abun a zuciyar ki ya dame ki,
tace bakomai yaya Allah yasa haka shi yafi alheri
ameen safna .
ta sake cewa yaya me yasame ka a ido naga yayi ja?
jalal yayi mamakin ya akayi ta gani bayan ba kallon shi take ba kanta akasa, dariya yayi yace ta yaya akayi kikaga idona bayan ba kallona kikeba?
juyar da kai tayi tace nifa gani nayi kamar yayi ja
Eh ai naji shine nake tambaya ko kina da ido ne atakiyar kai dan ni kanki kawai nake gani.
safna bata ce komai ba tayi shiro tana wasa da yatsun hannun ta.
daidai lokacin aka kirashi awaya yadauka yana fadin amir kun iso ne, ok to ganinan zuwa.
juyawa yayi yakalli safna yace, yarinya zama ki bari ne, dan yau a gado daya zamu kwana.
dasauri ta kalli jalal ta sake yin kasa dakai.
jalal yace a,a ki kalleni da kyau.

karfe 2:30 Jama,a da dama suka shaida daurin auren abduljalal da safna acikin wa,inda suka shaida daurin auran harda baffa wanda alhaji yaje ya taho dashi yaso yaki zuwa amman alhaji yace yayi danshi, dan haka ana daura auran alhaji yaba da mota aka mai dashi gida, jalal kuwa da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki.
acikin gida kuwa safna ce da wasu kawayen ta su biyu bata san waya gaya musuba sai dai kawai ganin su tayi,tana ganin su kuwa suka shiga fira tuni ta manta da bacin ran dake damunta anty tashigo ta ajewa safna wasu kaya tace maza kisaka kije waje jalal na kiranki zaku gaisa da abokan sa.

tun safe safna bata fitoba sai yanzun tana fito falo su hajiya ne da mutanen ta cike afalo suka saka guda, safna kuka tasaka musu yau gata atsakiyan dagin miji bata da kowa, dagin miji sune gatan ta wannan abu kawai in tatuna yana sata cikin baccin rai sai a yanzun wani kalma na goggo yake fado mata ki zauna anan bari naje na dawo haka banzayen kakan ninki suka ma uwarki har ta mutu bata kara sakasu a ido ba, goggo tana nufen mahaifiyar tama haka abarta, ko shiyasa bata taba gani wani dan uwan mahaifyar taba kara rushiwa tayi da kuka hajiya tace fatima kawo ta nan, hajiya fatima ta kawota har gaban hajiya kwatar da ita tayi ajikinta taita mata nasiha.

bayan ta dan natsu hajiya tace tashi kije ki gaida ummin ko, sai ki wuce gurin su jalal din.

sun shiga ita da kawayenta ta gaida su suka amsa ba yabo ba fallasa.

sun doshi gurin rinsu jalal, jalal ya hango su tun daga nesa da sauri ya daga waya yace anty dan Allah ki leko ki mayar da safna gida tasaka hijjabi.
dariya tayi tace haba jalal kabarta mana yau daya dai

kafin yakara wani magana sun iso wajen dan haka ya daure fuska suka gaida su cikin sakin fuska suka amsa dayan daga cikin abokan ne wadda suke kira amir ya farawa safna tsiya amaryar mu kirike shi da kyau duk abinda yake so abashi dan kinsan shagwabebbe ne ko cokali be iya rikewa ba.
jalal yace toh malam ya isheka haka kuma.
amir yace be isaba safna kinajina nina san halin jalal tare mukayi karatu jalal bashi da matsala amman yanada fushi idan antaba shi, ya kalli jalal yayi murmushi sannan yace safna abu nagaba jalal nada tsananin kishi .
da sauri jalal ya kalli amir yace wai amir lfyr ka kalau kuwa, ke ku wuce gida.
amir yace yazaka koresu ka barsu mana ai ban gama ba, hirace ta barke takanin safyya kawar safna da amir amir , jalal zuwa yayi yakama hannu safna yashiga da ita har cikin gida.

da daddare mutane suka fara watsewa bakin hajiya kowa duk sun wuce gidan ta ,sai hajiya da anty nusaiba kawai suka rage barayin ummi kuwa daga ita sai kawarta madina safna kuwa na dakin su da ita sai kairat, kairat tace anty safna kikace da bikin ki zamuyi shagali amman yanzun sai naga ba,ayi komai ba, natabayi yaya yace wai kece baki so ayi.
Safna tace haka yace miki wayau yayi miki shine baya so,kairat tace ai dama yaya yacika wayau haka ma da yace in kukayi aure zai tafi dani yanzun kuma yace wai wasa yake min, kuma wlh bazan yarda ba saina biku yaya zaku tafi kubar ni ni kadai agida
safna tace ai bama inda zamu bakiga gidan ya kone bane.
suna cikin haka jalal yashigo dakin yace safna kizo hajiya nakiran ki tamike suka fito tare ahanyar su ne jalal ya ce safna koda an tambaye ki Ina kike son zama kafin musami wani gidan kice abarki adakina.
dauri safna ta fara kuka wlh yaya bazan iyaba .
yace daurewa zakiyi safna ,ko kin fi son hajiya ta wuce dake, ni indai hajiya ta wuce dake bazan iya barciba wlh me zanyi agidan nan, to sai dai nima na biko.

gani tayi kamar ba,a cikin hakalin shi yake ba, matsowa yayi yariketa safna ki taimakeni karki bari atafi dake.
safna ko azuciyar ta tafi son tabi hajiya dan gidan nan kwata kwata baya yi mata dadi jita take kamar a kaya take.

Suna shiga falan alhaji ,suka ga kowa kowa ya hallara har ummi da kanin alhaji bayan sun zauna aka fara yi musu nasiha kanin alhaji baba salisu yace to jalal hajiya nason ta tafi da safna gidanta kafin agama gyara ma gidan ka dan haka nace bari muje ta bakinka tukuna dan yanzun kai kake da iko da ita, meye ra,ayin ka?
shiru yayi kansa kasa.

Safna ko tunani take azuciyar ta wato jalal shi yakasa magana ita kuma zai sata tayi rashin kunya.

Jalal beyi magana ba saida baba salisu yakara maimaita tambayan shi.
sai da jalal ya juya gurin hajiya sannan yace toh hajiya harda ni zaki tafi ko?
duk falon dariya suka saka banda safna da ummi dan ummi kara tamke fuska tayi.
baba salisu yace ja,iri ai dani zakayi magana bada hajiya ba.
Jalal bece komai ba sai faman sosa kai yakai yake.
baba salisu yace indai na kula da kyau, jalal be yadda atafi mai da mata ba.
anty nusaiba tace toh hajiya kibar mai matarsa kawai tunda baso yake ba, da sauri ummi tace nima dai abinda nagani kenan.
hajiya tace a,a nima ba matsawa nayiba kusha zaman Ku, in ma dakinka zaka kaita bisimillah.

hajiya ta sosa mai inda yake mai kaikayi dan haka ya farawa anty nusaiba alama da ido , banza tayi dashi kamar bata gani ba.
baba salisu ya kula dan haka yace jalal kamar kwai magana abakin ka, nusauba me jalal yake gaya miki.
dariya tayi tace yaya nima ban fahimce shiba.
yace toh kuje waje kuyi magana duk abinda yake so ya fada kar yaji kunya ai matar sa ce.
anty tace jalal kayi hakuri mana kasan fa mamar ka bazata yarda dahaka ba.
anty nidai kawai ku kaita dakina ina da dalilina inhar kuka tafi baku kaita dakina ba nasan ganin safna ma sai ya gagareni ummi zata iya hanani shiga dakin su safna.

suna komawa anty tace yaya shifa wai so yake ta koma dakinsa.
baba salisu da alhaji suka hada baki to dan wannan shine ka kasa fada kai da matar ka, nusaiba kai mishi matar sa daki kizo mutafi.
ummi mikewa ta tasaka kuka agidan nan, za,yi wannan kwama calar wlh wlh bata isa ta hada gado da jalal ba.

10 comments

  1. Pingback: Saphir Thailand
  2. Pingback: strip tokens
  3. Pingback: Medical1
  4. Pingback: 7slots indir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *