Advertisements
BALABARI BOOK 1
By
Advertisements
Fadila Lamido
Page 1- 2
Bismillahir Rahamanir Rahim.
Advertisements
Manyan motocine guda guma zafafa ke shigowa cikin unguwar, banda kyalli babu abun da motocin keyi yayin da suke tafe cikin nutsuwa.
Sannu ahankali take tafiya cikin babban hijjabinta tare nikaf dinta baki yayin da hijabinta ya kasancen kalar sararin samaniya, karan motocin da takeji ne yai masifar gigitata, yayin da yai sanadin gushewar hankalinta, diriricewa ne da dimuwa ya same ta lokaci guda wadda ya haifar mata da rawan jiki tare da gushewan hankali harya kaita da curewa guri guda.
Hayaniya ne ke tashi bisa kanta, cikin yanayin firgici take jin muryan maza saman kanta suna fadin, ” sannu ba dai kiji ciwoba ko?”
Wata muryan taji cikin fada ana fadin, aigara taji ciwon ko Yayane, tunda musamman ta shigo da tsuguna saboda tanason tajawa mutane bala’i toh Allah ya fiki, idan mutuwa kike nema dan ubanki kije ki tari tanka, dallah tashi ki bamu waje, cikin tsawa yake mgnr, kokarin tashi take ta hangi wasu karafuna wadda ke zama wa mara lafiya kafa suna tahowa gare ta.
Sandunan karfin tabi da kallo batare da tabi tsawon sadar ba, lumshe ido tayi alokacin data hangi wata kyakyawar kafa fara sol cikin cikin wani tsandanden takalmi, kallonta ta maida Kan daya kafar wadda sai wannan lokacin ta kula da ita, daure take tam da dauri irin na wadda ya samu karaya ko wata mummunan matsala, dan an nade kafar tunda Kan tafinsa har ya wuce kaurin sa.
Yajima tsaye agabanta saidai ta kasa dagowa ta dobe shi, yayin da ta kasa cire idon ta akan daya kafar sa me lafiya, kuma ta kasa mikewa gaba daya.
Ahankali taji yayi gyaran murya kadan, wata irin murya taji me cike da kasaita yana fadi ahankali, ” tashi ingani babu wata matsala da ta sameki ko?”
Ko motsi batai ba yayin da idon ta ke iya hangen kafafuwan su, zasu iya kaiwa kimanin mutum ashirin, kuma dukan maza ne cikin kayan alfarma da takalma masu tsada, wani abun Mamaki ada dukkan nin su mgn suke cikin hayaniya, amman wannan me rike da karfin na fitowa gurin yayi tsit.
Kamar daga sama ta sake tsintar irin wannan muryan tana sake fadin, ” Ina magana dake ne fah”
Wannan lokacin ma bata tankashi ba yayin da takeji ajikinta kallonta yake saidai ita bazata iya kallon nasa ba.
Ke bakiji ne ana miki magana dan rainin hankali kinyi banza da mutane, tashi ki bamu waje, nasame ki agurin nan takaki zan yi, wani dake can gefe kifadin haka cikin tsawa da hargagi, tsintan muryan mutumin dake tsaye agaban ta tayi Yana cewa, ” Magaji bita ahankali”
Bata sakejin muryan wani ba duk suna tsaye yayin da kadan daga cikin su suka koma mota suka zauna.
Kyawawan kafar ta ya zubawa ido sannan ya koma kallon idon ta dake cikin ni’kaf, kasa cire idon nasa yayi har aka dauki tsayon lokaci, sosai idon nata ya burgeshi har baya iya misalta wa, tare da kasa cire idonsa akan nata, acikin ransa yake fadin ban taba ganin idon dayai kyau da ni’kabi kamar wannan idon ba.
Tsayon lokaci suka diba babu me cewa komai, zuwa can taji anbude motar sannan taji ance, Modibo kazo mu tafi dan Allah, muna da abunyi fa, sannan akwai tafiya me tsayo agaban mu.
Ta kanta zamubi ne?, baka ganin ta zauna ahanya?
Tahowa yayi Yana fadi cike da fada ke!! Dallah tashi……
Shiii ka koma ka zauna harsai lokacin data tashi.
Afusace ya juya yayin da gurin ya sakeyin shiru tsayon lakaci.
****
Ahankali ta dafa kasa ta mike batare da ta iya daga ido ta kalli kowa agurin ba ta koma gefen hanya tana karkade hijjabin ta, bayan ta gama ta kara komawa can gefe sosai ta fara tafiya.
Gaba dayan su kallo suka bita dashi sannan suka shiga motar suka fara tafiya.
Koda sukazo saitin ta kallo wadda aka Kira da suna Modibo ya bita dashi, har suka wuce ta yana waigen ta.
Magaji kuwa kallo ya bishi dashi, sosai hakan ya zamar masa bakon al’amari ga Modibo, saida sukai nisa sosai ta yadda ko alamar yariyar basa gani sannan Modibo ya dawo da kansa yana kallon hanyar da suka dosa.
Tafiya me nisa sukayi sannan suka iso wani madaidaicin gida, bayan sun faka motocin su ne suka fara fitowa tare da saurin bude motar da Moddibbo yake.
Cike da kasaita ya sauke kafarsa me lafiya, sannan suka tsayar da sandan karfen bayan ya sako daya kafar, sandar ta shiga tsakanin hakarkarin sa, dakin dake kofar gidan suka nufa mutum biyu ne a bayan sa.
Sallama sukayi bakin kofar yayin da daga cikin dakin aka amsa sallamar tare da fadin, ” kun iso kenan, ku shigo sannun ku da zuwa”
Shiga sukayi bayan sun gaisa mutumin dake dakin ya kalli Kafar Modibo yace, ” Yaya kafar taka?”
Alhamdulillah ba Kamar daba.
Yauwa haka ake so.
Matsowa mutumin yayi yana kallon kafar Modibo tsayon lokaci sannan yace, ” insha Allahu ya kusa zama tarihi, mikewa yayi ya fara hado wasu magunguna tsayon lokaci sannan ya dawo gaban Moddibbo ya zauna, ahankali ya shiga warware nad’in da akama kafar, saidai be gama warewa duk ba ya tsaya ya yana tofa addu’oi tsayon lokaci sannan ya bude wata roba Yana shafawa kafar mgani, bayan ya gama sake nade kafar yayi, yayin da Modibo ke runtse ido.
Sannu yamai yayin da samarin dake gefe suma suke masa sannu, dakai ya amsa, yayin dayai shiru kansa akasa kawai sai zufa ne ke karyo masa.
Tsayon lokaci ya dauka sannan ya dago ya kalli Malamin yace, ” Baba maganin Yadikko ya kare, kuma Alhamdulillah tana samun sauki.
Masha Allah, Malamin ya fada sannan ya kara da cewa zan baku wani ku kaimata da yardan Allah zata samu sauki.
Maganin ya hada masu, sannan suka fito cikin girmamawa da mutunta juna.
Yanzun ma d’in rike yake da sandunan karfen dake cikin hakarkarin sa, yayin da mutun biyu ke bayan sa. tun daga ganin fitowan su sauran abokan tafiyar su suka bude motar da Modibo zai shiga, wadda itace ta kasance a tsakiya.
Saidai suna kokarin rabashi da sandunan suka lura hankalinshi baya wajen shiga motar, daya daga ciki ne yabi inda idon Modibo yabi da kallo domin son sanin abun da yaja hankalin sa haka.
Wata yariya yagani tana kokarin bude wani madaidaicin gida da mabudinta a hannun ta, kallon ta yayi sosai, duk da cewa baya ta juya masu, ahankali ya maida idonsa ya kalli Modibo sannan ya sake kallon yariya.
Matukar mamakine ya kamashi, yayin da duk aka gama shiga cikin motar amman Moddibbo tsaye yake.
Modibo muje mana tafiya ce fa me nisa agaban mu.
Lumshe ido yayi sannan ya shigar da kafarsa me lafiya yayin da aka taimaka ya zauna da kyau, adaidai lokacin da yariyar ta gama bude gidan tana kokarin tura kofar Modibo ya kalli wadda ke gefen sa yace, ” Magaji ka Kira min yariyar can”
Lumshe ido yayi sannan ya juya cikin azama, beji mamakin jin Modibo yace ai kiranta ba, saidai yadda yake kallon ta abun ya bashi Mamaki.
Kokarin shiga gidan take wadda aka Kira da suna Magaji yace, ” ke! kizo ana kiran ki.
Ta cikin nikabi ta juyo kadan ta kalle shi, sannan tasa kai ta nufi dogon zauren nasu.
Ke!! nine nake miki mgn keke tafiya, wanni irin rashin tarbiya ne ke damun ki dahar zan miki mgn ki kalleni ki wuce?
Ko kafin ya rufe baki ta idan shigewa gida, dan haka ransa yai mugun baci sosai zuciyarsa ke masa zafi, afusace ya juya yayin da Modibo cike da kasai ta yace, ” metace maka?”
Batace komai ba asali ma kallona tayi ta wuce abun ta.
Juyawa Modibo yayi ya kalli gidan sannan yace, naso inyi mgn da ita kwarai Magaji.
Ba girman ka bane Modibo, bata bata da darajar da zakayi mgn da ita, ni kaina dan dai kawai kai kace inje, har yanzun dai idan taimako zaka bata kabani zan koma nakai mata.
Gidan Modibo ya sake kallo batare da ya cire idon sa agidan ba ya ce muje kawai.
Jin haka Magaji yayiwa driver Umarni batare da wani bata lokaci ba motar ta fara kokarin tashi, hakan ne yabawa Motocin dake gaba damar fara tafiya sannan ta Modibo ta tashi yayin da wasu kebin bayan tasu.
Modibo kuwa babu abun da idonsa da zuciyar sa ke iya hango masa sai idon ta wadda ya hanga cikin ni’kabi tare da farar fatanta dake gefen idon ta sai kuma farar kafar ta me daukan hankali.
******
Zaune take adan madaidaicin tsakar gidan wadda yake share tsaf, kanta ta hada da guiwa tsayon lokaci, akoda yaushe idonta sun kasa daina kallon kafafuwan sa guda biyu daya me lafiya daya mara lafiya, tsayon sati daya kenan ta kasa barin tuno kafar tasa, wannan dalilin ya fara sata hawaye dan takasa fahimtar me hakan ke nufi, daker ta iya yakece tunanin ta mike domin karasa sharar data fara, bayan ta kammala ne tai wanka, shiryawa tayi tsaf kamar kowanne lokaci yadda ta saba fita sannan ta fito ta jawo kofar dakin, gidan ta kallah komai tsaf dan haka taji wani sanyi cikin ranta sannan ta fice tare da sawa gidan kwado.
Tafiya take gefen hanya sannu kan hankali har ta isa wani gida namarasa karfi sosai, sallama tayi cikin siririyar muryar ta tare da saka kanta acikin gidan.
Wata Dattijowa ce ta amsa fuskanta sake.
Jikinta yariyar ta fada, tana fadin, sannu da aiki Dada.
Yauwa sannu dai Unaisa, tun dazon nake ta xoba ido jiran zuwanki harnai tunanin yau bazakizo ba.
Cikin zazzakar muryan ta tace, ” zanzo Dada idan banzo ba ai banajin dadi.
Cikin yanayin tunani tsohowar da takirata da Dada tace, ” hakane, sannan wani al’amari yafara min yawo cikin kaina.
Da sauri yariyar ta kalli Dada tare da cewa, Dada mene shi?
Jimmmm tayi zuwa can tace, ” yanzun matasa duk sun lalace, sa’anan duk unguwar nan kowa yasan da cewa ke daya kike kwana cikin gidan nan, gashi girma nata miki sallama, ‘karashe mgnr tayi tana kallon fuskar yariyar da takira da suna Unaisa.
Nan danan idon yariyar ya cika makil da hawaye, yayin da matar ke cigaba da fadin, ” aduk sanda nasa hakarkarina akan shinfida ta tun bayan tafiyan ki duk fargaba yaki bari na, Unaisa bakijin tsoro?”
Kwallar da take makalewa ce ta zubo zuwa kan kumatun ta, yayin da tai saurin sa hannunta ta share tare da girgiza kai, banaji Dada, Innawuro tace tabarwa Allah amanata, ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu babu abun da zai faru.
Allah yasa Unaisa, tashi maza ki dauki kayan ki wuce, alhamis me zuwa basai kinzo ba zan kawo da kaina, ya makarantar kina zuwa dai ko?
Dakai ta bata amsa sannan ta sauke nikabin ta tare da nufa kayan ta dauka sannan ta mata sallama ta kamo hanya.
Tana saka kafarta akofar gidan wani kyakyawan matashi na sawo kai, ahankali ta kauce ta bashi hanya yayin da ya dan tsaya yana kallon ta, fuskarsa dauke da murmushi yace, “Habaruwala!”
Jimmm yarinyar tayi sannan ta fara takawa ahankali kamar yadda ta saba, shikuwa wannan matashin bebar fada mata wannan kalmar ba har saida tai nisa sosai.
Sosai ta kosa ta isa gida domin tsakanin gidan da gidan Dada akwai tazara, daf take data karasa gida ta hangi wasu jerin gwanon motoci masu kyalli da daukan hankali, motocine manya manya na alfarma jere kofar gidan Malam Baba Kamar yadda ake kiran shi cikin unguwan, shahararrene malamin gyaran karaya da duk wani maganin gargajiya, dan haka duniya tasan dashi kofar gidan sa be rabo da baki akowanni lokaci, saidai tunda take cikin unguwar bata taba ganin zuka zuka motoci har haka akofar gidan ba, sai wancen satin daya wuce, saiyau data take ganin kamar sunfi naranar kyau.
Cire idonta tayi daga kallon kofar gidan Malam Baba sannan ta tsallaka kwatar dake kofar gidan tahau kan dakalin.
Ledan dake hannunta ta sauke tana lalibo mabudin gidan.
****
Magaji jinan, da hannu yai masa nuni da kofar gidan da budurwa ke kokarin bude kofar.
Kallon yariyar yayi sannan ya juya ya kalli Modibo.
Dauke ido Modibo yayi sannan yace, ” kamin mgn da ita, kayi kokari ka kawota nan gabana, Ina son in ganta a nan gurin yanzun nan.
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 5- 6
Gaba daya motocin ne suka tashi lokaci guda, bayan ta suke bi a hankali, ita ko Unaisa ko waige batai, gudun ta kawai take tamkar wadda kura ya biyo ta.
Layin nasu nada tsawo sosai, ga hanyar babu kyau dan haka sannu ahankali motar ke tafiya yayin da suke iya hangen yadda yariyar ke falla gudu a gaban su.
Magaji ko ajiyan zuciya yake saukewa, ko ahaka yasan ya fanshe walar da taita bashi dan haka kallon mugunta ya ke ta binta dashi, shikuwa daya matashin ban da dariya babu abun da yake har yanxun, yayin da Modibo ya hade fuska, idon sa akan ta, baya kawarwa zuwa can yaiwa driver Umarni daya tsaya domin wannan lokacin motar suce agaba.
Dan tsayawa sukayi kadan yariyar ta kara nisa sosai dasu sannan yace muje.
Magaji ne yabi Modibo da kallo, cikin nutsuwar sa yaga Yana bin yariyar da kallo dan haka shima ya juya ya kalli yariyar da tayi nisa dasu sai arta gudu take, Modibo ya sake kallo yayin da yaga sai shafa gemon sa yake tare da shafo kansa, sunkuyar da kansa yayi yai murmushi sannan ya dago ya sake kallon Modibo yace, ” Modibo!”
Lumshe ido yayi sannan ya juyo ya kalle shi.
Nace kodai mahaukaciya ce?
Lumshe ido ya sake yi akaro na biyu tare da fadi ahankali, ” lafiyarta lau”
Ganin tasha kwana suka kara gudun motar, suna saka hancin motar akwanan sukaga ta shige wani gida ta rufo kofar.
****
Matsanancin hakin da take yasa Dada rikecewa, kara shigewa cikin jikinta take tamkar zata shige cikin ta tare da haki babu kaukautawa.
Unaisa menene??, gayamin me yake faruwa?
Shid’ewa tayi gaba daya, yayin da Dada ta kara rudewa, girgizata take tare da Kiran sunanta, ganin babu alamar numfashi yasa ta zame ta, ruwa ta dauko aguje ta dawo ta shafa mata afuska sau uku sannan taji taja dogon numfashi, zama tayi sosai ta kara daurata jikinta tare da rungume ta sosai, tsayon lokaci tana rungume ajikin ta, ajiyan zuciya kawai take saukewa, saida Dada ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan tace, ” menene yake faruwa Unaisa, gayamin mene ya firgita ki har haka?
Hawaye ta share tana manne ajikin Dada, Hankali tace, wannan ba’kin na Malam Baba ne suka tare min kofar shiga gida.
Jimmm Dada tayi sannan tace, ” akan wani dalili?”
Bansani ba Dada, har biyoni suka yi da mota.
Shiru Dada ta sake yi, sannan ta mike ta leka kofar gidan, bata jima ba ta dawo tana fadin, kindai tsorata ne Unaisa, amman babu wani daya biyo ki, mayafinta ta dauka ta sake fita, tsayon lokaci sannan ta dawo tana cewa, naje har layin naku babu kowa inajin sun wuce.
Ajiyan zuciya Unaisa tayi mekyau sannan ta dauki nikaf dinta ta daura, itako Dada gaban murho ta isa tana kokarin daura girkin dare, yayin da hakan yayi daidai da shigowan wanni Dattijo, ganin Unaisa ya sashi yaja ya tsaya tunda nesa yana fadin, ” tunda kin ajeta annan ni bari na koma”
A’a Malam shigo mana, firgita tayi ne yau abun da bantaba ganin tayi ba, shiyasa hankalina ya tashi har ka ganta anan.
Eh shiyasa zan baku waje ai, idan ta firgice dake lokacin zaki gane abun da ake gaya miki, nagaya miki batun yau ba bana son ganin Baharuwala acikin gida na, amman muje zuwa duk wadda ya bari sauran tuwo ya Kona shi shiya so.
Malam hakuri zaka yi, abun duk da kaga ya koro bere ya fada wuta to yafi wutar zafi, ka tausayawa yariyar nan Malam, tana tsananin son kulawa.
Tunda kina tausaya mata kin dauke Mana, banda batan basira ta yaya za’a ce yariyar da kowa yaki ta keke daya ki makale mata, duk dangi kowa yaki ta saboda bakin naci kinna nan da ita.
Amanar Innawuro ce Unaisa agareni Malam, ko duk duniya zasuki Unaisa ni bazan kita ba, Unaisa dolena ce.
Shikenan, Allah ya baki sa’a, amman Baharuwala tabarmin gidana, banson nadawo na same ta agidan nan, komai na iya faruwa idan nazo na same ta, afusace ya fita, Dada kuwa bakin aikin ta ta koma ranta bace.
Mikewa Unaisa tayi ta isa gaban Dada, cikin muryar ta kasa kasa tace, ” Dada zan tafi.
Batare da Dada ta juyo ba tace, ” anan zaki kwana.
Sunkuyar dakai tayi kasa tare da fadin, ” bazan iya kwana ako inaba idan ba’a dakin Innawuro ba Dada.
Da sauri Dada ta kalli Unaisa sannan tace, ba inda zaki, idan suka dawo cikin dare suka miki wani abin fa?
Bazasu dawo ba, na kula duk sati suke xuwa tunda sun tafi nasan bazasu dawo ba sai wani alhamis din.
Jimmm Dada tayi sannan tace, Ina zuwa toh bari naxo na raka ki.
Bayan Dada ta gama daura kirkin har gida ta raka Unaisa, acikin ranta take tsananin tausayawa rayuwar ta, fitowa tayi tana tafiya tana hawaye, bakin cikin yadda mutane suke gudun Unaisa ko shege ba’a masa haka.
Unaisa kuwa yau kuka taci tana nade akan gadon Innawuro.
Tun daga wannan ranar duk alhamis gidan Dada take wuni, Dada ke lekowa har saita taga wucewan motocin sannan ta koma gida.
Islamiya kawai ke fitar da ita bata zuwa ko Ina sai gidan Dada wadda daman duk alhamis tana zuwa, sai dai yanzun zama take har yamma sannan ta koma gida.
Akwana atashi asarar me rai, yau sati hudu kenan batasa motocin a idonta ba, dan haka hankalinta ya kwanta, ayanzun batajin fargaba ko tsoro.
Saidai acan cikin zuviyar ta lokaci bayan lokaci tana tuna maza biyu data hanga zaune bayan motar masu kama daya.
Ranar juma’a kuwa ko kofar gida bata zuwa tana cikin gida arufe.
Yau asabar tun misalin goma tafito cikin Shirin makaranta, fararen kaya ne ajikinta tass har hijjabin, sai bakar safa dake kafarta tare da bakin nikabi, sosai kayan suka karbi jikin ta.
Tafiya tafara sannu ahankali harta fita daga cikin unguwar ta isa titi, adaidaita ta tsare tahau tare da fada masa sunan makarantar tasu, bakin makarantar aka sauke ta yayin da ta ciro kudinsa ta Mika masa ta nufi cikin makaran tar.
Sallama tayi sannan ta isa kujerar ta ta zauna, kasancewar mutum daya daya ake zama, saidai har aka tashi batai mgn da kowa ba baya ga daukan karatu.
Misalin hudu ta iso gida cikin saure ta nufi kofar tare da lalibo mabudin ta cikin jakar makarantar ta, jimmm tayi jin karan karfe bayan ta, tamkar dai takowa ake da karfe, dan haka gaban ta yai wani irin bugawa.
Nan danan jikinta ya fara rawa yayin data kasa dago mabudin, banda rawan jiki ba abun da take.
Hannu tasa ta rike hannun kofar, jinda tayi kafar ta nason kada ta, ahankali takejin Karan na dad’a matsowa gare ta, har tazo ta fara hango kafar karfen dake tahowa tare da wata farar kafa cikin kyakyawan takalmi, daya kafar kuwa daure take, anan take ta tuna ta taba ganin wannan kafar.
Tahowa yayi harya ya isa jikin kofar gidan ya jingina bayan sa yana kare mata kallo.
Bata iya dagowa ta kalli fuskarsa ba Kamar wancen karon, sunkuyar da kanta tayi kasa tare da rawan jiki abaiya ne.
Tsayon lokaci suka dauka haka zuwa can yayi gyaran murya cikin wata irin murya yace, “kowa ya hanaka dakin kwana dasafe saiya ganka, dan murmushi yayi kadan sannan yasake cewa yaya sunan ki?”
Kara sunkuyar dakanta tayi tsayon lokaci suna ahaka.
Kara lumshe idon sa yayi sannan ya bude akan kyawawan gashin idonta yace, ‘inajin ki aunty na kimin mgn mana, sauke mgnr yayi da ajiyan zuciya me karfi, sannan ya sake cewa, “gudu da waiwaye fa shike kawo mugun zato.
Yadda yake mgn yasata kara lumshe idonta, har cikin ranta taji zakin muryan tasa, saidai babu wata kalma da zata iya furtawa.
Muryar tasa ta sakeji cike da kasaita yana fadin, ” meyasa bazaki min mgn ba?, gashi ni ina tsanin son inyi mgn dake.
Lumshe ido ta sake yi yayin da ya zubawa gashin idonta kallo tsayon lokaci sannan yace, “ke kadaice a gidan?”
Wannan karon ma babu amsa, wani irin kallon yake mata wadda kusan shi kadai yasan ma’anar sa sannan yace, ” toh ba komai, kowa yaki tsotse hannun beji dadin miya bane, dagoya yayi daga cikin kofar sannan ya gyra sandar sa ya taka gefe hankali.
Tsaye yayi agefe yana kallonta yayin da Magaji yake bayan su yana jin duk yadda suka yi.
Ganin ya tashi kofar gidan tayi kokarin dawo da nutsuwar ta, sannan ta lalubi mabudi ta bude gidan ta shige.
Bayanta yabi da kallo kafin yaji tasawa gidan sakata, lumshe idonsa yayi sannan ya kara kallon kofar gidan, gidane na marasu karfi amman gyare yake tsaf, yaji siminti tare da lafiyayyen kofa.
Modibo muje yamma nayi, Magaji yayi mgnr Yana kallon fuskar Modibo, cikin sauri ya fara takawa yayin da Magaji yai saurin rikeshi Modibo ka manta kafarka babu lafiya ko?
Tafiya yacigaba dayi yayin da Magaji ke binsa abaya har suka isa inda motarsu take, da taimakon Magaji ya shiga motar sannan shima ya zaga ya shiga
Wadda ke zaune mazaunin driver ne yace, ”
Kun rutsata ko?
Magaji ne ya bashi amsa, Ina fa, gata dai a tsaye amman bazata yi mgn ba saboda rashin d’a’a, bata amsa kowacce irin mgn koda kuwa sallama ce Muftahu, saidai kaga tana karkad’a kwayar idon ta me kama dana mutanen farko…
Batare da Modibo ya kallesu ba yace, ” wacce irin mgn ce kake yi?, ga dukkan alama yariyar kurma ce, tanaji amman bata iya mayarwa.
Kasa Magaji yayi da murya sannan yace, “kada kayi tammanin alheri, a inda bakaga haske ba.
Cikin sauri Moddibbo ya runtse ido tsayon lokacin sannan ya bude ahankali, cikin muryarsa me dadin saurare yace, “Idon da yaga sarki baya tsoron galadima Magaji, lallai Ina son nasan wasu abubuwa game da ita.
Muftahu ne yace, ” tayaya zaka san wani abu game da ita alhalin tana kurma ko bebiya?
Kara lumshe ido Modibon yayi akaro na biyu sannan yace, ” wannan ba matsalar ku bace.
Basu sake mgnr ba saidai dukkan su ukun kowa da abun da yake sakawa cikin ransa
*****
Unaisa kuwa tsaye tayi jikin kofar harta tabbatar da tafiyan su, ajiyan zuciya ta sauke sannan tai saurin shiga cikin gidan, cikin gudu gudu ta canza kaya sannan ta sake fitowa akaro na biyu, wannan karon gidan Dada ta nufa tana ta tafe tana waiwayen bayan ta.
Kamar daga sama Dada ta ganta, iya sanin ta Unaisa bata zuwa wannan ranar dan haka ta tabbatar lallai akwai wani muhimmin abun da ya kawo ta.
Cikin sauri ta taho gareta ganin inda take waiwayen bayanta yasata kallon kofar sannan ta juyo ta kalli Unaisa tace, ” Unaisa meke faruwa?”
Batare data dauke idonta daga kallon kofar ba tace, ” Dada! Sun dawo”
Cikin tsananin faduwan gaba tace, ” suwaye?”
Dada mutanen nanne dake bibiya ta.
Kofar Dada ta nufa da sauri yayin da Unaisa tai saurin fadin, ” sun wuce amma dada nafara tsoron karsu dawo.
Yamutsa fuska sosai Dada tayi, tare da fadin, ” me suke nema ne Unaisa, me suke ce miki?, Firgicin da kike shiga idan kin gansu yana daga min hankali, wai daga Ina suke?
Bansani ba Dada, amman Kamar ba ‘yan kasan nan bane, nataba ganin fuska guda biyu iri daya acikin su akusa da juna, Basu da banbanci Dada, sannan wani jarababbe ke yawan biyo bayana yanai min mgn, sannan akwai mara lafiya akafarsa guda daya tare da tulin motoci da suke zuwa dasu.
Jimmm Dada tayi, zuwa can tace, ” narasa gane me suke nema, Unaisa me suke ce miki.
Dada bana iya tunawa.
Kare mata kallo Dada tayi sannan tace, bazaki koma gidan nan ba Unaisa, maza shiga bandaki ki kama ruwa kiyi alwala kizo ki shige dakina.
Kamar yadda ta fada haka tayi, tanajin dawowan Malam mijin Dada bayan isha’i, misalin goma Dada taiwa Unaisa sallama ta wuce turaka tare da kara jadda mata karta yadda malam yasan tana gidan.
Misalin sha biyu da rabi Dada taji alamar zare sakatar dakin ta, bude Ido tayi da sauri tare da kara baza kunnen ta, tabbas dakinta ne kuma harda alaman tafiya, tashi tayi zaune batare data shirya ba, Malam ta kalla sai bacci yake dan haka tai saurin daukan buta ta zare sakatar dakin, Malam din ne ya motsa cikin fada yake fadin kullum Ina miki gargadi ki dinga shigowa da robar tsuguno.
Cikin sauri ta fice tana fadin, ” mancewa nayi Malam.
Gilmawan mutum tagani zauren gidan nasu yayin da ta kalli kofar dakinta dake bude, cikin sauri ta nufi zauren albarkacin farin watan dake sararin samaniya take ganin hanya, ahankali ta furta waye Nan! ?
Cak ta tsaya saboda tsananin kaduwa da rawa da zuviyar ta tayi…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
PAGE 3- 4
Cikin sauri Magaji ya juya ya nufi kofar gidan adaidai lokacin da ta dauki ledan ta take kokarin shiga gidan, cikin kaukausar muryan sa yace , ” ke!!”
Babu alamar ta jisa yaga ta daga kafarta tashi gidan.
Ina miki mgn kina tafiya?, ko kinason ki nunamin baki da tarbiya ne kamar yadda yake azahiri, Ganin da yayi ta kule cikin gidan dole yasa shi yin shiru yayin da bakin ciki ya cika masa zuciya, kasa komawa yayi jin ana sawa gidan sakata.
Daker ya iya juyawa ya koma motar ya shiga ya zauna tare da kauda idon sa daga gefen da Moddibo ke zaune.
Moddibbo ne ya kalle sa yace, ” ta maka mgn?”
Batare da Magaji ya kalli Modibo ba yace, ” a’a, batace dani kala ba”
Ka mata tsawa ne ko?
Kawar da Ido Magaji ya sakeyin sannan yace a’a
Jimmm Modibo ya sake yi sannan ya sake cewa, ” ka koma ka buga gidan lallai ko wanni hali ake ciki yau Ina son in ganta anan.
Batare da Modibo ya gama mgnr ba Magaji ya fita, babban rigar sa ya gyara tare da daidaita zaman hularsa sannan ya koma kofar gidan.
Tun kafin tafara jin bugun kofar turaren sa ya fara mata sallama, zaune take bakin kitchen tana kokarin daura girki, cikin sauri ta mike, acikin ranta take fadin, mutanenan ne na ranar nan, me suke nema gurina, me yasa suke bibiya ta, gaba daya jikinta rawa ya fara tanajin yadda yake buga gidan, zuwa can taji shiru dan haka ta fara takawa ahankali ta isa zauren sannan tasa hannunta akan kofar tare da zura idonta ta kafar kofar.
Wasu maza matasa ta hanga zaune bayan motar su biyu, fararene sosai wadda sukafi kama da larabawa, sai dai shaddace lafiyayya ajikin su babban riga wadda akayiwa ado da aiki irin na zamani, mutun biyu kawai take hanga wadda suke zaune cikin farar shadda, saidai ganin su take tamkar mutum daya ne saboda tsabar kamar da suka yi, mgn suke wadda batajin me suke fadi, shagala tayi da kallon su bata Ankara ba saigani tayi motar ta wuce.
Cikin gidan ta koma ta zauna, gaba daya ji tayi jikin ta ya mutu babu wani karfi jikinta, fuskar mutane nan guda biyu kawai take iya tunawa, cikin ranta take tunani, sudin suwaye?, daga Ina suke haka, kuma me suke son ce mata?
Iri irin wannan tunanin taita yi har ya dauke ta dogon lokaci dan haka ta kasa girkin, tattara kayan tayi ta ajiye sannan tai alwala ta nufi daki.
Gaba daya yau ta rasa sukunin ta, komai ne baya mata dadi, fuska iri daya guda biyu sun tsaya mata axuciya, rasa abun yi yasata fara zubar da hawaye Koda dare yayi daker bacci ya iya daukan ta, cikin ikon Allah washegari ta tashi da sauki, duk aikace aikacen gidan tayi sannan tayi abun karyawa ta kwanta, kasancewar yau juma’a babu islamiya, baccin da bata samu jiya ba shi tayi wannan lokacin.
Misalin daya ta shi, Nan ma sallah tayi sannan ta zauna tsakar gida, yau daya ta farajin zaman gidan ya dame ta, sosai take sha’awar tayi hira kamar yadda takejin mutane nayi, saidai tana tuna gargadin Innawuro.
Washegari ta kama asabar dan haka ta nufi islamiya domin shikadai ke debe mata kewa tun bayan data kammala secondry school bata dawowa sai yamma liss, wannan ya matar da ita tunanin data fara sawa ranta akan samarin guda biyu.
*****
Yauta kama alhamis dan haka tun safe take dakon zuwan Dada amman ba ita tazo ba sai misalin biyu da rabi taji ana buga gidan tare da fadin, Unaisa taho bude min.
Jin Muryan Dada yasata runtumowa da gudu har jikinta na bari ta bude kofar tare da fadawa jikin ta.
Rungumeta Dada tayi cikin nuna so da kauna tace, ” nasan kinata zuba Ido ko?
Harna fara tunanin zuwa fa Dada, toh ai gani muje ciki, kayan hannunta ta amsa tana kokarin juyawa ne ta hangi motocin yauma a kofar gidan suka aje wasu motocin.
Ganin inda take kallon motar Dada ta kalleta tace, “Daura aure ake ne a unguwar?”
A’a Kamar dai Bakin Malam Baba ne.
Kallon motocin Dada ta sake yi akaro na biyu sannan tace, ” lallai kuwa Malam Baba kullum dada shahara yake, dubi irin wannan zuka zukan motoci haka, nan gaba ai bazai saurara aikin mu na yaku bayi ba tunda irin wanna motoci na masa layi.
Juya sukayi suka nufi gidan yayin da Unaisa ke fadin, ” Dada waddan nan fah tare suke zuwa sukuma tafi tare, Ina tunanin mutum daya ne mara lafiyan.
Lallai Kila wani babban mutum ne daya shara, cikin gidan suka shiga yayin da Dada ta cire gyalen aQqta ta rataye kan igiyan shanya sannan ta nufi ta barman da Unaisa ta shinfida masu, abinci data taho dashi ta zuba sannan suka shiga ci tare cikin kwano daya, hira suke sosai suna daf da karasawa Dada tace, Ina son nai wata mgn dake Unaisa.
Da saurinta ta kalli Dada.
Itama Dada tana kallon cikin idonta tace, ” mgn ce akan aure…
Batakai ga Rufe bakiba Unaisa ta juya baya tare da hada kanta da guiwa.
Dada ce tacigaba da cewa, bansan me kike nufiba, aduk lokacin da nai miki mgnr aure saiki juya min baya ranar bana sake ganin walwalar ki, da ace Innawuro da kawu basa zaman lafiya da nace Kila wani mugun abun kiga yanai mata, nafiki sanin halin su dan nafiki zama dasu, sosai nake son kiyi aure, abun dake daga min hankali mutanen unguwar nan, duk wadda yazo koron sa suke, basa taba bari zancen yai kwari.
Cikin turo baki Unaisan tace, ” ni bakomai Dada taimako na ma suke.
Yadda tayi zancen kasa kasa yasa Dada tace mene kikace?
Nace taimakona suke yi.
Jimmm Dada tayi tsayon lokaci tana nazarin mgnrta sannan tace, ” shikenan naji, suna taimakon ki tunda suna kore miki manema, duk wadda yazo yau gobe baya kara zuwa, hakan baya daga miki hankali, har kike iya cewa taimakon ki akayi, shikenan saiki ta zama babu aure daga nan har a busa kaho, ki kare rayuwar babu miji tunda kina ganin hakan daidai ne.
Hawaye Unaisa ke sharewa, kallon ta Dada tayi tace, ” in dai dan nayi miki wannan zancen ne kibarmin kuka, ni inason naga kiyin aure ne kafin mutuwa ta kuma tana iya zuwa kowanni lokaci tunda bakiso na bari, inna mutu saiki rayu ke kadai tunda hakan kikafi so
Cikin shashshekar kuka tace, bazaki mutuba Dada tare zamu mutu.
Ai bamuzo tare ba bare mu mutu tare, ni daya nazo, ni daya zan mutu, dan haka nake son ki kaunaci aure.
Toni Dada taya zanyi aure alhalin ban iya zama da wani ba, ban iya mgn da wani ba Dada, bana hira da kowa kwata kwata mutanen da suke min mgn basufi a akirga ba, wlh Dada bazan iya mgn da kowa ba,
Lumshe ido Dada tayi sannan tace bazaki iya mgn da kowa ba ko?, nafahim ceki, bazaki iya mgn da kowa ba bare aje ga batun zama irin na auratayya ko?
Batakai ga rufe bakiba Unaisa ta mike ta nufi adaki, cikin rufda ciki ta fada Kan karamin gado.
Bayan ta Dada tabi da kallo, sannan tasa tagumi, idan tana kirgawa daidai shekaran Innawuro hudu kenan da rasuwa lokacin Unaisa nada shekara sha uku aduniya, jimmm ta sake yi, lallai ya kamata ta sauke nauyin dake kanta ta aurar da ita, wanni irin mummunan faduwa ne ya same ta lokacin da ta tuna sukar da mutanen unguwar ke kaiwa akan Unaisa, cikin ranta ta shiga tunanin mayuyacin abu ne Unaisa ta aure acikin garin nan, indai so ake Unaisa tai aure dole ne ayi nisa da ita, tabbatarwan da tayi tunanin beda wani amfani yasa ta mikewa domin tasan Unaisa bazata taba yadda akaita wani gari ba, mayafinta ta cira akan igiya ta yafa, cikin yanayin dake nuna fushi take tace, nina wuce.
Mikewa Unaisa tayi da saurin ta nikabin ta ta daura sannan tai saurin bin bayan Dada.
Itako Dada tana saka kafar ta kofar gidan ta hada Ido da nawasu maza guda biyu zaune saman motar, ganin sum kalleta tai saurin dauke idonta tare da mayar dasu Kan Unaisa tana fadin koma abun ki banso rakiyar taki.
Bude baki tayi da nufin yiwa Dada mgn itama suka hada Ido dasu, daya daga cikin sune ta hangesu a mota shida wani irin sa sak wani harara taga ya zafga mata me cike da zallah tsana dan haka ta maida idonta ga dayan.
Shikam kallonta yake yana murmushi dan haka tai saurin sakawa gidan kwad’o sannan tai sauri ta zura hannunta cikin na Dada.
Dama baki fitoba Unaisa, domin bana son a dinga fahimtar ke daya ce agidan.
Bakomai Dada insha Allahu.
Allah yasa amman duk da haka ki koma gida na gode.
Sallama sukayi, sannan ta juyo daman ba wani nisa tayi ba, matashin Nan ne ta hango fuskarsa dauke da masifa yana sauka daga samar motan.
Yi tayi Kamar bata ganshi ba ta koma gefen gidan su yayin da daga matashin yayi sauri ya rigata isa kofar ya tsaya.
Daga cikin ni’kabin take kallon shi sama da kasa, acikin ran ta take fadin, ” banda abinsa bata jikin sa zaiyi da hau Kan dandamalin gidan mu, kafar sa sheki take hakama takalmin sa tamkar ba kasa ake takawa dashi ba, da dai ace tana da damar yi masa mgn data tambaye shi me yake nima gurinta dahar yake kokarin Bata kata kayan sa.
Daga can nesa taja ta tsaya ta cikin ni’kabi take kallon irin kallon wulakancin da yake mata.
Juyawa tayi ta kalli motocin bata iya hango kowa sai mutun daya da shima ya sauko daga saman motar yanxun.
Cikin wani irin murya taji matashin yace, ” ki karaso kina bata mana lokaci, koda yake bayau kika fara ba.
Ganin bata da niyar matsowa ya sashi ya sake fadin, bakijina ne?
Wannan karon ma babu alamun zata amsa shi dan haka yace, idan kika bari na iso gurin daukan ki zanyi cak in direki agaban shi.
Zoro Ido tayi yayin da taga yana kallon cikin idonta sannan Yana tahowa gareta ahankali
Shikuwa matashin yana tahowa ne yana kallon gefen idon ta da yai tsananin nuna hasken fatar ta, tsintan kansa yayi dason ganin fuskar ta dalilin ganin kwayar idonta beyi kama dana hausawa ba, acikin ransa yake fadin, ” meyasa take boye fuskarta koda yaushe?, daga idon sa yayi ya hange Modibo yana zaune cikin mota idon sa akansu, meye sa Modibo yanace son mgn da yariyar duk da kasaita irin tasa?, ganin babu me amsa masa ya sauke idon sa akan yariyar yana meji acikin ransa shi ba mgn yake sonyi da yariyar ba Fuskanta kawai yake son gani.
Itako babu abun da ke mata yawo aka Sai cewan da taji yayi zai dire ta agaban shi, shin waye shidin?, me zasu min ko me zai min?, yin wannan tunanin yasa ta fara ja da baya, daga can bayanta taji wani irin murya me sanyin sauti tana fadin, ” Magaji rike ta karka barta ta gudu”
Jin haka yasa Unaisa ta kwasa aguje yayin da Magaji ya rufa mata baya, saidai yana tsallaka kwatar ya tsaya yayin da ya hangi yariyar har tayi nisa.
Komawa cikin motar yayi yana ya tsuna fuska, yayin da yasamu wannan matashi da suke zaune tare yanata dariya dariya.
Shikuwa Modibo dake zaune abayan motar tsaki yayi sannan ya duba agogo yana fadin, ” muje, bi bayan ta karta bace mana.
Wani irin kallo Magaji yaiwa Modibo ganin inda yake ciccin magani ahankali ya bama driver umarni dan haka suke tashi jerin motocin su cikin kokarin bin bayan ta…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4ohdpom4UjFUX3yaUb5Hl
BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 7- 8
Dakewa tayi, ta hanyar boye firgicin ta tare dayin kasa da murya tace, ” Unaisa! lafiyar ki?”
Cikin sauri ta dago ta kalli Dada adan firgice dan batai tsanmmanin ganin ta ba, dago hannunta tayi daga Kan sakatar da take kokarin cirewa sannan tace, ” lafiya lau Dada”
Unaisa, me yake damun ki?, kuma Ina zaki da wannan Dattijon daren?
Gida zani Dada, dakin Innawuro, nakasa bacci kuma na tabbatar matsawar ba dakin Innawuro na kwanta haka zan wayi gari ban runtsa ba.
Wani irin kallo Dada taiwa Unaisa sannan tace, ” ko zaki kwana bakiyi bacci ba babu inda zaki da wannan tsohon daren, ki koma ki kwanta kar Malam ya fahimci wani abu, kin sani sarai idan Malam ya ganki anan duk zuviyoyin mu bazasu yi dadi ba, idan safiya ta waye saiki tafi inda kike sakewa, banda abunki Unaisa garadan maza ke kawo miki hari, wadda harke dake ganin su kince baki rike me suke cewa.
Ai Dada dana kasa bacci na tuna kalmomi biyu da mutumin ya fada, natuna mara lafiyan kafar yace, gudu da waiwaye shike kawo mugun zato, sannan ya sake cewa kowa yaki tsotse hannu beji dadin miya bane.
Lumshe ido Dada tayi zuwa can ta bude sannan tace, ” yaje ya tsotsi hannun uwar sa, danni ban gane inda zancen shi ya nufa ba, wlh Unaisa ke macece bana miji ba, kuma kinkai minzilin da maza zasuyi tunanin kasancewa dake musamman idan suka fahimci cewa ke kadaice agidan….
Dada gobe zan dawo, ni yanzun idan ba jina nayi dakin Innawuro ba hankalina bazai kwanta ba.
Wato kina nufin kin kafe kenan sai kinbi hanya awannan lokacin?
Shiru tayi dan haka Dada tace, shikena, Allah ya tsareki aduk inda kike, juyawa tayi ta nufi dakin da ta fito saidai bata iya runtsawa ba tunda taji alamun Unaisa bata dawo ba, idon ta bushewa yayi tunani da zullumi sun hanata bacci.
*****
Unaisa kuwa cikin tsanin firgici tare rawan jiki ta isa gida, bayan ta bude gidan ta shiga bakinta dauke da addu’a, tsitt gidan sannan ta bude kofar dakin ta shiga tare da kunna wutan lantarkin dake dakin, take haske ya gauraye dakin, hannunta tasa ta cire nikaf din dake fuskarta ta ninke ta aje a inda ta saba ajewa, sannan ta cire hijjabin, shima ninkewa tayi ta adana sannan ta dauki rigar da ta saba sawa idan zata kwanta ta cire kayan jikinta ta saka su, wani mayafi ta dauko babba ta yafa tare da daurewa a wuyan ta, dan tunda ta fara nono ko ita kadai adaki bata iya barin kirjinta abude, zaune tayi abakin gadon ta hada kai da guiwa, kanta abude.
Gashin kantane ya baje agadon bayanta yayin da da yakai tsakiyan bayanta baki sidik.
Tsayon lokaci ta dauka ahaka, hawaye na zuba afuskarta yayin da nutsuwa take kara shigarta, sai misalin 3 ta kwanta bajimawa bacci ya dauke ta.
Washegari da sassafe Dada ta iso bugu biyu tayi Unaisa ta gane Dada ce dan haka taje da saurinta ta bude kofar tare da fadawa jikin ta.
Lumshe ido Dada tayi jin Unaisa jikinta, a jiyan zuciya ta sauke me karfe sannan suka nufi gidan Unaisa na kwance ajikinta.
Cikin daki suka nufa, yayin da Dada tabi Unaisa da kallo tsayon lokaci sannan tasa hannunta ta cire nikabin fuskarta zuba mata Ido tsayon lokaci sannan tai maza ta rike kunnen Unaisa.
Cikin sauri Unaisa ta yamutsa fuska tare da kanne idonta daya tare da nuna alamar tanajin zafi tace, Dada kiyi hakuri Allah akwai zafi.
Aina dauka bakisan inda ke miki ciwaba Unaisa, kara matse kunnen Unaisa Dada tayi tana bin kyakyawan fuskarta da kallo.
Dada nasani fah.
Meyesa kika biyo hanya da daddare?
Hannun Dada dake rike da kunnenta ta rike sannan tace bazan kuma ba Dada kiyi hakuri.
Sakin kunnen Dada tayi har yanzun tana binta da Ido take cigaba da fadin, ” Unaisa na yanke wata shawara zan sake zuwa gida da mgnr ki akaro na biyu…..
Girgiza Kan da Unaisa keyi yasa Dada dakatar da zancen ta, meyasa Unaisa?
Dada dan Allah ki barso, yanzun shekara biyar da rasuwar Innawuro tun Ina wuro na raye Basu taba min kallon arziki ba, ranar da Innawuro zatabar duniya ta tara gaba daya dangin ta tayi yinkurin barmasu amana ta basu duba halin da take ciki ba sukace Basu amsa ba, haka dangin Baffah da sukazo gaisuwar Innawuro, hawaye Unaisa ta sharewa sannan ta cigaba da cewa, suma cewa sukayi Baffa tabas nasu ne amman ni kar’a kara dangantasu dani, Dada dan Allah na rokeki karki kara dangantani da kowa, nima bana tunawa da kowa, kawai dai bana mancewa Innawuro tace tabarwa Allah amana ta sannan tabarwa ke, bana son alaka da kowa Dada, nafison na ganni ni kadai Kamar yadda Innawuro tabarni ni daya, ni kaidai ta haifa hakama Baffa na.
Itama Dada hawayen dake makale a idonta ta share sannan tace, ” amman Unaisa yanzun fa kinkai minzilin aure matukar ba aure kikayi ba hankalina bazai taba kwanciya ba, bacci na zai zaba rabi da rabi ne, Koda ace tare dake nake kwana nake tashi zuwa wannan lokacin aure ne ya dace dake, bare kuma ace ke kadai kike rayuwa acikin gidan nan, kuma cikin Unguwar nan babu wadda be sani ba…..
Aguje Unaisa ta fita adakin, binta da kallo Dada tayi sannan ta mike da sauri tabi bayan ta, gefen Famfo ta same ta tana sheka amai, cikin tsananin Mamaki ta shiga taimaka mata, bayan aman ya tsaya ta wanke mata fuska sannan ta rokota suka dawo daki, saman gadon Unaisa ta kwanta tare da jawo katon mayafi ta rufe jikinta, karkarwa jikinta keyi alamar tanajin sanyi, ganin haka Dada ta mike ta tattara ragowan kayan abincin dake dakin ta daura girki.
Misalin 12 ta sake shigowa har yanzun Unaisa karkarwa take dan haka ta janye mayafin ahankali ta sake taba jikinta har yanzun da zafi fau, ajiyan zuciya tayi sannan tace, ” Unaisa, yau kuma dan nayi mgnr aure shine harda zazzabi??
Dada gaba nane yake faduwa.
Take faduwa akan me?
Hawaye ta share da tafin hannun ta naji ne kince wai nakai munzalin aure.
Kallo Dada tabita dashi gefen idonta yayi ja sabo da share hawaye, Koda babu kwalliya afuskarta Unaisa kyakyawa ce sosai, kawar da fuaka Dada tayi daga kallon Unaisa sannan tace, aida nace kinkai minzilin aure Ina nufin munzalin farko kuma mataki tara muke dasu.
Ajiyan zuciya Unaisa ta sauke me karfi sannan tace, Allah yasa kafin nakai na na taran Allah ya yanke numfashina kamar yadda ya yanke na Innawuro.
Kallonta kawai Dada tayi sannan tace to ki saki ranki ki bude jikin ki ko zazzabin ya sauka.
Saida Dada ta tabbatar zazzabin Unaisa ya sauka sanan ta wuce gida.
Tun daga wannan ranar mullum saitaga Motarsu ko inzata makaranta ko idan ta dawo, saidai bata kulasu duk Kiran da zasu nuna suna mata bata kulasu.
*****
Muftahu Moddibbo yana damuwa da lamari yariyar, hakan na bakanta min raina, wata biyu kenan muna zarya hanyar Nan da bata da kyau amman ko kadan betaba nuna yagaji da bibiyar ta ba, saidai ma kaji yana cewa wai kurma ce, tun bana yadda harna fara yadda, saboda duk kiran da zanwa yariyar bata taba Koda dago kaine ta dubeni har bakaken mgn na gaya mata amman bata ko nuna alamar tasan me nake cewa ba, har takai yanzun nikaina inason nasan ta acikin idona Ina son inga fuskarta sosai.
Wani irin kallo Muftahu yaima Magaji, Moddibbo ya gaya maka dalilin son yin mgn da yariyar ne??
Kaima kasan bazai gaya min ba.
Toh karka fara son ganin fuskar ta, bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane, sannan kuma barin kara tunatar dakai dan wata Kila ka manta, In za’ayi tubka ayi mata hanci dan gudun kata da warware.
Bangane ba?, To idan ma wannan mgnr kake Muftahu ai idon da yaga sarki baya tsoron galadima, kuma ninasan halin Modibo ciki dabai, sai dai yace zai mata abun da ya saba ba abun da nasaba ba.
Idan ko har ya mata abun da ya saba hnmmm rayuwarta zata canza.
Ni kuma fa?, Idan namata wadda na saba?
Gyara zama Muftaho yayi acikin kujerar motar sannan yace, ai babu hadi Magaji, Kai kanka kasan cewa zama dame turare yafi zama da ma’keri, domin zama dame turare kobe baka turaren ka fesa ba kaji kamshi ajikin ka, zama da makeri kuwa ko be konaka ba taratsatsin wuta ya ya same ka.
Lumshe ido Magaji yayi tare da fadin, naji, sauka min amota akwai inda zani.
Cikin sauri Muftahu ya fice a motar Yana murmushi yayin da Magaji ya zagaya ya shiga motar tare da figanta aguje.
*******
Ya dade atsaye a kofar gidan ganin babu alamar zata fito kamar kullum jiran fitowarta yake ganin ya jima ya waiga yace, Moddibbo Ina tunanin bata cikin gidan…..
Tana ciki Magaji kacigaba da bugawa,
Wani mutumi ne da yazo wucewa yai karaf yace, ” tana ciki amman ba bazata taba bude kofar ba barema har tayi mgn.
Muftahu dake jingine jikin motar ne yace, ” toh me yasa haka?
Babu wadda zai gaya maka dalilin.
Modibo dake cikin motar ne yai saurin Kiran mutumin da yaga Yana kokarin wucewa, bayan ya karaso gaban motar daker Modibo ya iya bude baki yace, ” abokina bani lbrn abin da ka sani game da ita.
Kallon Modibo yayi acikin ransa yake fadin, ” Allah yayi hallita anan gurin da alama, Ance kyakyawan ce ita, kyaun ta ya shahara, ni makocinta ne amman bantaba ganin fuskanta ba, kafarta kawai zaka gani ya tabbatar maka da cewa fara ce sosai, kuma ita kadai take rayuwa agidan.
Toh Ina iyayenta?
Iyayen ta sun kasance tsofaffi ne tukuf domin ance lokacin da suka haifeta shekarun su arba’in da biyar da aure basu haihu ba…..
Dafa bayan sa yayi tare da fadin, ” Ina zuwa malam ni inason nai mgn ne da ita amman abun ya gagara, nabita nabita amman ko kalma daya bata taba furta min ba, hakan yasa nafara tunanin ko kurma ce?
Ba kurma bace, amman bazata kulaka ba, kayi hakuri kawai abokina duk nacin ka bazata yi maka mgn ba, domin tunda nake bantaba jin muryan ta ba, kullum zatazo ta wuce bata mgn da kowa, an tabayin wani saurayi da yayi nacin sonta, da tazo zata bude gidan yake shigewa
shekaran sa daya da wata biyu yana shiga gidan bata taba tankashi ba, dan haka ya gaji ya daina zuwa.
Lumshe ido yayi sannan ya bude su sukayi ido 4 da mutumin cike da kasaita yace, ” meyasa take rufe fuskar ta?, bama wannan ba, kana da tabbacin ba kurma bace ko?
Ba kurma bace an tabbatar min da hakan
Idonsa ya daga ya kalli Magaji dake kofar gidan yace, ” Magaji ku cire min kofar gidan” bayan bada Umarnin nasa bude murfin motar yayi yayin daya zuro kafarsa me lafiya…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: https://chat.whatsapp.com/BEUl8JVOPSiCNIsfscHdU4
BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 9- 10
Ba Magaji kadai ba duk wadda yaji Umarnin da Modibo ya bada saida ya zare Ido, ciki har makocin Unaisa, gaba daya ji yayi kafarsa takasa daukan sa, Ido ya zuba masa cikin tsananin Mamaki take kare masa kallo tare da son sanin waye wannan.
Magaji kuwa cikin sauri ya koma cikin jerin motocin da suka taho dasu, ba jimawa saiga wasu maza biyu tika tika sun fito cikin motar, gidan suka nufa gadan kadan yayin da Magaji da Muftahu suke jinkina bayan su jikin daya daga cikin motoci 8 da sukazo dasu yau.
Gidan sukabi da kallo, suna kallon yadda majiya karfi suke dukan kofar gidan, idon Magaji akofar gidan yake motsa leben sa tare da fadin, ” Modibo ya nace lallai sai yayi mgn da yariyar nan”
Shima Muftahu be kalli Magaji ba idonsa akan kurar dake tashi dazaran sun daki kauren yace, “ni wannan ba matsalata bace, ni yanzun Babban burina mukoma gida nagaji da garin nan wlh, babu nishadi acikin sa.
Tsaki Magaji yaja, naso in riga Modibo ganin fuskar yariyar nan.
Me yasa?, Muftahu ya tambayi Magaji.
Kafin ya bashi amsa Karan faduwan kofar gidan yasasu mikewa, duk suka nufi kofar, kusan a tare suka isa kofar gidan da Modibo, sandan karfen sa guda biyu yake takowa, manyan kayane ajikinsa farar shadda kal kafarsa daya cikin wani hadadden takalmi yayin da daya kafar aka nannade wandonta ya wuce guiwa kadan, can kasa kuwa nade yake da bandeji tundaga tafi har kusan guiwar sa.
Da taimakon Magaji da Muftaho yahau Kan dakalin kofar gidan sannan sannan ya shiga gaba Magaji da Muftahu suna binsa abaya.
Siririyar hanyace duwa suka bi har suka isa dan tsakar gidan da ba wani girma gareshi ba, Sallama Modibo yayi har sau uku ganin babu amsa yasa kansa cike da kwarin guiwa.
Tsananin rawa da jikinta ke yi yasata makalewa abakin kitchen tai tsaye, idonta akan kofar gidan, dan haka suna shigowa suka hada Ido, duk da cewa jikinta na matsancin rawa be hadata kuresu da Ido ba.
Mutun biyu ne masu tsananin kama da juna, daya lafiyye daya kuma bashi da lafiyar kafa, farare tasss Basu da banbanci da larabawa yayin da na ukun beye kama dasu ba saidai shima akwai kama sosai
Magaji ne yace, ” idan baki cire bushashshun idon ki akan mu ba saina taka cikin yariya, au ke wai da kinajin kikai banza damu, kunga min yar iskar yariya tanaji tai banza damu fa.
Modibo ne yace, ” bana son hayaniya, bashi bane ya kawo mu.
Amman Modibo yariyar iskancinta yayi yawa, ace tana yar musulmai amasa Sallama ya gagare ta?, dan kaniyar ki ki bude fuskarki Kona baki Kashi agurin.
Lumshe ido Modibon yayi sannan ya sake bud’e su akan yariyar da gashin idonta ke sama da kasa, hada Ido sukayi yayin da yaga wani kyalli na tashi kwayar idon ta Kamar an diga zaiba, daker ya iya tattaro kalmar kanwata bude fuskar ki, inason inji matsalar ki wadda ya sa kika zabi zama ke daya.
Ko motse batai ba, hakan ya fusa ta Muftahu da Magaji sosai sai dai Basu da ta cewa tunda Moddibbo na gurin dole sai abun da yace.
Modibo ko kare mata kallo yayi tsayon lokaci sannan yace, Muftaho ku danne min ita ku cire min wannan abun da ta rufe fuskarta dashi.
Nufarta suka yi batare da wani bata lokaci ba, sai dai suna daf da isa gaban ta ta fito da hannunta daya data makale abayan, ta wata wukace ta bayyana yayin da take nunasu da wukar.
Walwalin da Magaji da Muftahu suka hangi wukar nayi yasasu zare Ido cikin tsananin mamaki suka tsaya cak suna kallon juna.
Modibo kuwa Murmushi yayi me kayatarwa domin ya tabbatar da cewa yariyar ba kurma bace, cikin muryansa me dadin saurare yace, ” tunda bata son ku tabata ku barta ku dawo baya zata bude da kanta.
Afusace Magaji yace, Moddibbo ka koma mota yariyar nan bata da tarbiya da alama yar sara suka ce, kaga wai ni take saitawa da wuka, juyawa yayi ya kalli Unaisa yace, ” kinci darajan Modibo dake tsaye anan gurin amman dana nuna miki ke karamar ‘yar ta adda ce, mara d’a’a kawai, kina amafani da suturar musulunci amman bakya daraja sallama bare ki daraja na gaba dak…
Hannu Modibo ya daga masa, dole ya hadiye sauran zancen, cikin tattausan murya Modibo yace, ” idan kaga ruwa ya gurbace Magaji to ka bincika yana zaune guri daya ne, ka kwantar da hankalin ka har mu fahimci menene matsalar ta.
Cike da haushi yace, Modibo nifa balakin tafasa min zuciya take yi, kuzo mu tafi kawai.
Lumshe ido Modibo yayi, sannan yace, “Ina son in zauna kubani gurin zama”
Nan danan suka shiga kallon gidan babu wani abu dayai kama da kujera dan haka Muftahu ya dauki tsintsiya ya nufi dakalin dake kofar dakin ya share, ahankali Modibo ya fara takowa harya iso gurin, kallon Magaji yayi sannan ya maida kallonsa gurin yariyar Yana fadin, Magaji ka shiga cikin dakin ka dauko darduma ka shinfida min anan kafin na zauna.
Dakin Magaji ya nufa kamar yadda Modibo ya bashi Umarni, shigo Modibo idonsa akan Unaisa ganin yadda ta juya kwayar idonta tana kallon Magaji daya nufi dakinta yasa ya mayar da kallon sa gurin Magaji, harya daga labulen yaji Modibo na fadin, ” dawo Magaji, tace bata amince ka shigar mata daki ba” mayar da kallon sa yayi gurin ta yayin da yaga ta sunkuyar dakai akaro na farko.
Cikin dibara ya zauna agurin tare da ajiyan zuciya sannan yace, ” kubani minti 10 ganinan zuwa yanzun”
Fita sukayi cikin sauri yayin da Magaji ke fakar idon Modibo Yana zuba mata harara.
Ficewa sukayi ya rage da Unaisa sai Modibo, tsit gidan yayi tsayon lokaci idon Modibo akan kafarsa me ciwan zuwa can ya maida hankalin sa kanta idon su cikin na juna yace, ” na dade Ina son in samu irin wannan damar, nasan kinaji na amsawa ne bazaki yi ba, kowa da halin sa Kamar yadda ni kuma nafi kama Wahainiya, bance dole sai kin min mgn ba, amman Sallama na daya daga cikin sunayen Allah madaukaki, sai ya sashi a cikin halittunsa domin bayinsa su rika bayyana sunan a cikin ko wane hali, ta hanyar mu’amala yau da kullun da zamantakewa da amana da sauran al’amuran su na rayuwa, ta yanda zai zamo abun Ambato sallama a tsakanin su, Su kuma bayyanar da sunan a cikin maganganun su da kuma aiyukan su, Wato su bayyanar da hakikanin sallama a cikin zuciyar su, da furucin su, da al’adun su, da kuma akidun su, da halayensu domin su tsira daga sharrin shaidan, Hanyar samun wannan tsarin ita ce tsoron Allah (takawa), Dukkan wanda ya siffantu da takawa (tsoron Allah )Allah zai tsarkake mashi addini sa, da hankalinsa, da ruhi da kuma zuciyar sa, kai da dukkanin gabobin sa daga zunubi.
Da sauri Unaisa ta cire idonta ana Modibo ta sunkuyar da kanta kasa, shikuwa kara zuba mata Ido yayi sannan yaci gaba da cewa, “ganin yadda sallama yake da karfi kuma da mahimmanci a tsakanin Musulmai, da Kuma wajabcin amsawa wanda aka yi masa idan yaji kuma yana cikin natsuwa yasa duk wadda a ka yiwa sallama muddin yana da tarbiya na addini zai amsa maka wannan sallamar taka, dan haka zan sake yi miki sallama akaro na hud’u Assalamu alaikum
Batare daya rufe bakin sa ba yaji wata zazzakar murya tana fadin, ” Amin wa’alaikas salam.
Lumshe ido yayi har cikin ransa yakeji zazzakar muryan da baya tunanin ya tabajin me zakin ta.
Kallo ya bita dashi tsayon lokaci Yana kallon yadda take kifkifta idon ta saidai taki yadda ta kalli gefen sa.
Ko ke fa kanwata.
Har cikin ranta taji kalmar kanwata daya furta, domin tunda ta taso babu wani mutun dake danganta kansa da ita bayan Innawuro da Kawu, sai kuma Dada wadda har gobe tana tsaye kanta duk da cewa dangin uwa dana uba sunki ta
Muryar sa ta sake ji Yana cewa, ” Yaya sunan ki?”
Dauke fuskarta gaba daya tayi daga gefen sa.
Ajiyan zuciya yayi, Haba kanwata, ni bandamu da ki bude fuskarki ba, amman Ina matukar son kina amsa min mgnr da nake miki, bansanki ba bansan ko wacece keba, nima kuma nasan baki san waye ni ba, acikin zuciyata naji lallai Ina son in daimake ki, amman hakan bazai yiyu ba har sai kin bude baki kina min mgn, zan iya taimakon ki batare daga fuskarki ba amman bazan iya taimakon ki alhalin banji matsalolin dayasa kika zabi zama guri daya ba, naji cewa bakiyin mu’amala da kowa, kina da makota dama da hago gabas da yamma amma kowa bakiyin mgn dashi menene yai zafi haka kanwata???
Sunkuyar dakai tayi tare da lumshe ido”
Tsayon lokaci Modibo ya dauka Yana kallon ta sannan yace, ” ni bazan bar mgnr ba kanwata, ki rike fuskar ki banson ganin ta, banzo da wata manufa ba baya ga taimakon ki tsakanina da mahallici na, meyasa kina ‘ya mace budurwa kike zama cikin gida ke daya, Ina iyayen ki?, Idan kuma sun rasu Ina dangi uwa dana uba?
Lura yayi hawaye na sakowa daga idonta yana jika gefen ni idon ta.
Tsayon lokaci suka dauka ahaka sannan yace, kibar kukan haka, nabar tambayan, amman bance bazan kara ba, nagani acikin idon ki na takura min yau, Mutun rahama ne kanwa ta, zama guri daya be dace dake ba, rashin mgn da mutane kuma na haifar da tusheshshen tunani mara kan gado, kamar yadda zama aguri uku suke da matukar amfani, zama amakaranta, da zama a mahauta, da zaman fada.
Zama a makaranta ko bakayi karatu ba idan kayi mgnr addini kaji, a mahauta idan ana fid’a ko fince kayi, a fada kuwa zaka karo da mgnr tsofaffi dan nan ne matartarar mgn, mikewa yayi sannan ya dauko sadar sa da suke gefen sa ya sasu a hakarKarin sa sannan yaci gaba da cewa, zan tafi amman zan dawo, karki ‘ki bude kofar dan zansa acire ta, waigawa yayi ya kalli gidan kowanni kusuwa idan zan dawo zan kawo miki abokan zama nau’in tsuntsaye, juyawa yayi har isa tsakiyan zauren yaji Kamar yaji amon muryan ta, dan haka ya dakata sannan ya juya ya koma ciki…..
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
PAGE 11- 12
Tsare ta da Ido yayi sosai sannan yace, “Me kika ce?
Sunkuyar dakai tayi da saurin ta zuwa can ta dago ta kalleshi.
Murmushi yayi tare da lumshe ido, daker ya bude baki yace, ” kofar gidan ki zansa a mayar miki, bin ta yayi da kallo shikenan ko?
Batare da tace kala ba ta juya afusace ta shige d’aki.
Bayan ta yabi da kallo sannan ya juya ya fita.
Modibo da Magaji ne suka taho cikin kokarin taimaka masa, mutumin nan ya gani har yanzun yana tsaye be wuce ba, bayan ya iso gaban motocin su ya tsaya gurin wannan Mutumi ya tsaya Yana fadin Malam ya sunan ka?
Sulaiman nake, ya bashi amsa a takaice.
Shima ataice yace, Sulaiman Ina iyayen yariyar nan??
Ance iyayenta sun rasu, ita kadai take zama agidan tun bayan rasuwan su.
Sunkuyar dakai Modibo yayi zuwa can yace, ” kenan yanzun bata da kowa anan?
Nidai bansan kowa nata ba.
Yaya sunan ta?, Modibo ya sake tambaya.
Eh toh bansan sunanta ba, amman gaba daya Unguwar nan suna kiranta BAHARUWALA.
Cikin rashin fahimta Modibo yace wanni yare ne wannan??
Karaf Magaji yace fulatanci ne.
Sulaiman Modibo ya kallah sannan yace, me kalmar ke nufi?
Idan akace Baharuwala anan nufin BA LABARI.
Zaro ido Magaji da Muftahu suka yi, Modibo kuwa lumshe idonsa yayi, sannan yace da Sulaiman Ina ne gidan ka?
Wani gida ya nuna masu wadda tsakanin sa da gidan Malam Baba gida biyu ne.
Kallon gidan Modibo yayi sannan yaciro kudi mai yawa yabawa Sulaiman Yana fadin, dan Allah kasa agyara akofar nan yanzun nan, sauran canjin ka rike.
Jimmm yayi yana rike da kudin cikin sanyin jiki sosai.
Ahankali Modibo yace, ” Yaya dai ko akwai matsala ne”
A’a dan maida kofa aiki nane, amman gaskiya banzan iyayin wannan aikin ba, ko yanzun ma dan naga bani daya bane na tsaya anan agurin.
Wani irin kallo Magaji yaiwa Sulaiman sannan yai saurin takawa ya isa saman motan ya zauna.
Shikuwa Muftahu Modibo yabi da kallo alokacin da yake fadin, ” ka dauko kayan aikin muna nan har ka gama.
Da sauri Sulaiman ya nufa gida yayin da Modibo ya koma cikin motar ya zauna, Muftahu kuwa kusa da Magaji ya zauna suna mgn kasa-kasa.
Moddibbo kuwa wayarsa yake dubawa, kira ya tarar barkatai duk daga gida, mutun daya ya kira wadda ya tabbatar duk mesun yasan halin da suke ciki zaiji sannan ya kashe wayar.
Sulaiman be wani dauki lokaci ba ya dawo ya shiga aiki nan danan ya maida kofar sannan sukayi sallah tare da musayan number tsakanin Magaji da Sulaiman kamar yadda Modibo yabada Umarni.
******
Tsaye tayi tana kallon kofar gidan da aka maida, bayan ta tabbatar da tafiyan su, cikin gida ta koma ta zauna saidai har yanzun hancinta yaki daina jiwo mata kamshin su, sosai gidan yake zuba kamshi tamkar suna cikin gidan har yanzun.
Gajiya tayi dajin kamshin da yaki wucewa, dan haka ta shige daki ta rofe kofar, ayanzun kam babu kamshin sai kuma tunanin su da yadawo mata, tarin tanbayoyi ne cike da cikin ta game dasu, daga Ina suke?, suwaye su?, ashigowan su nayau duk taji sunayen su, masamman Magaji da wadda suka Kira Modibo yake yawan Kira, cikin ranta takejin ta tsanesu gabadaya musamman Magaji, domin ya fiye zare Ido, shikuwa wadda suke Kira Modibo ya cika bata lokaci wajen mgn tamkar wani dan sarauta ko wadda mulki ya jiko ajikin sa, shikuwa wadda suke Kira Muftaho ya fiye kallo jaraba, irin wannan tunanin ne ya dauketa tsayon lokaci batare data sani ba, sallan mangariban da aka Kira ne ya dawo da ita cikin hankalin ta, alwala tayi tayi sallah sannan tai zaune nan kan sallayar tana rokon Allah abun da kullum ta saba roko tun bayan rasuwar Innawuro, shine mutuwa.
*******
Tafe suke kan titi, yayin da motocin su ke jere wannan nabin wannan har guda koma sha daya, yadda suke tafiya ajere yasa hankalin mutane ke dawowa kansu tare da kaucewa suna Basu hanya, Koda basu san waye cikin motar ba da gani kasan sun fitone daga wani gida me daraja.
Modibo kishingede abayan motar yayin da ya turbutsa hannunsa cikin kashin kansa yana yamutsawa, waigowa Magaji yayi ya kalleshi sosai, ganin halin da yake ciki ya yamutsa fuska tare da fadin, ” Modibo Yaya dai?”
Wani irin kallo Modibo yaiwa Mahgaji sannan ya lesa leben sa tare da ajiyan zuciya.
Kwayar idon Modibo Magaji ya kalla, ganin inda idon ke cike da wani farin ruwa yasashi lumshe idonsa yana fadin, ” karka sare Modibo, insha Allahu bazamu maimaita kwanakin da mukayi abaya ba, nasan kewa ke damun ka, idan kanajin kewan su ka kirasu cikin waya Mana.
Ganin Moddibbo be motsa ba yasa Magaji ya tsaida driver, sakkowa yayi ya koma kusa da Modibo cikin sauri ya turbutsa hannun sa cikin gashin Kan Modibo fuskanshi dauke da Murmushi.
Moddibbo be hanasa ba haka sukaita dafiya yayin da Magaji ya cika da farin ciki ganin halin da Modibo ya shiga, balakin kowasa yayi ya hadu da Magaji domin ya bashi labari, daker ya iya daure dariyar sa yace, ” na Kira maka su?
Tsaki kadan Modibo yaja sannan yace, Baya gamsar dani.
Murmushi Magaji ya sakeyi tare da kara yi masa susa cikin sumarsa, kula yayi Modibo har wani lumshe ido yake tare da kokarin boye dariyarsa yace, ” tafiya da gwani me dadi, idan har gwanin be lalace ba, kuma naji kana cewa ma me hikima bazai rance ba.
Ajiyan zuciya Modibo yaja me karfi sannan ya tashi daga kishin gid’an da yayi, gilashin dake aje agefen sa ya dauka ya daura Kan kyakyawan fuskar sa, sannan yayi gyara murya ahankali tare da fadin, ” to ai haka ne Magaji, ka iya ruwa kuma ka iya laka, inba hakaba ana komawa bangaren love sai a kunduma ka da ‘kasa.
Wani irin kallo Magaji yaiwa Modibo cike da dariya yace, ” Modobo wai bakaine kake cewa dashashshe yafi shukakke ba?
Lumshe Ido Modibo yayi tsayon lokaci bece komai ba dan haka Magajima be sake mgn ba.
Misalin biyu na rana suka isa kofar gidan Malam Baba kamar yadda suka saba, bayan sun shiga cikin kankanin lokaci ya duba Kafar tare da shafa sabon magani kamar yadda ya saba, addu’a yayi ya tofawa sannan ya sake daurewa Yana fadin”
Kafar taka Alhamdulillahi tana sabewa.
Eh ajikina ma inaji Malam, saidai jiyan nakasa bacci.
Wannan ai kewan gida ne Magaji ya fada fuskarsa dauke da Murmushi.
Kallon da Moddibbo yabi Magaji dashi yasa yai saurin kawar da idon sa.
Malam Baba kuwa Murmushi yayi yana fadin, ai kadan ya rage Modibo kafar tayi kyau ai, ka kara hakuri kafar tafi haka saina hada maka magani ka tafi dashi.
Allah ya kaimu lokacin Malam, sai mgnr maganin Yaddiko, muna da bakon da zaizo yau Malam yanzun haka Yana Kan hanya.
Toh ba damuwa, zan hada daga nan zuwa gobe da safe ka turo a karba, da wannan sukayi sallama da Malam suka fito, motar suka koma yayin da Modibo ya bada Umarnin a tsaya kofar gidan su yariyar.
Ahankali suka shiga gangaro da motar zuwa kofar gidan.
Magaji kuwa Nan danan ya kirne fuska dan beyi tunanin me irin hali da Modibo zai dinga bibiyar wannan yariyar ba.
Saboda tsabar haushi zama yayi amotar yaki sakkowa, Yana kallo Modibo ya sauka daga motar, mutum ne meji da karfi, duk da cewa kafarsa babu lafiya yana kokarin yin komai da kansa, ganin harya isa kofar gidan Muftaho ya sakko daga motar dake Gaban ta Modibo da Magaji yabi bayan Modibo yana wa Magaji kallon tuhuma.
*****
Tunda taji Karan motocin gaban ta ke faduwa, ko tantama batayi sune ta fada cikin ranta, sosai gabanta ke faduwa zuwa can taji ana kwankasa gidan, bugu na biyu ta mike ta isa kofar, har yanzun bugawa yake saidai bame tada hankali ba.
Ahankali ta zare sakatar tana samye da hijabin da nikabi, lekowa yayi tunkafin ta ware kofar, suna hada Ido tai saurin tura kofar tana kokarin mayar da sakata, hannunsa daya yasa ya tura yayin da itama take turowa, kafarsa me ciwom ta hanga dan haka tai saurin sakin kofar tare da saurin komawa da baya yayin data runtse idonta tare da daga tafukan hannun duk biyu kamar tana nunawa Modibo.
Murmushi yayi hakama Muftaho dake bayan shi dariya yake sosai.
Cikin zauren Modibo ya shiga, har yanzun tana nan yadda take, ahankli yace naji nahakura.
Sauke hannun tayi sannan ta wuce gaba zuwa cikin gidan.
Sallama Modibo yayi ta amsa sannan ya zauna inda ya zauna juya.
Muftahu kuwa shigowa yayi da wasu keji tsuntsaye guda biyu masu ban sha’awa Modibo ne ya nuna masa inda zai buga kejin.
Tunda aka shigo dasu suka damu gidan da tsuwwa, cikin sauri Unaisa ta juya bayanta, har Muftaho ya gama ya fice.
Ganin Bata juyoba Moddibbo ya shiga iban geron dake gefen gefen sa Yana watsawa a kasa nan danan tsuntsayen suka sakko suna tsinta, gyaran murya yayi tare da fadin, ” aunty na waigo ki gani.
Cikin sauri ta kara runtse idonta akaro na biyu, jin ya kirata da aunty, acikin ranta take fadin, wancen karon ya kirani da kanwata yau kuma yace min aunty, kila be sanin me yakeyi ya kirani da suna d’aya mana.
Aunty na magana nake fa, ki jiyo ki lallah tsuntsaye sun iya bada mishadi, musamman ake kirkiran wajen shakatawa azuba tsuntsaye, kallon yadda suke tafiyar da tasu rayuwar na kawar da dogon tunani da bakin cikin.
Har yanzun bata juyo ba dan haka ya sake cewa ko baki so in tafi da abina??
Ganin tana kokarin juyowa ya mayar da hankalin sa Kan tsuntsayen Yana cikaba da iban geron Yana watsa masu.
Kallon shi tayi yadda yake diban geron yana watawa tsuntsayen cikin kwarewa, kasunbarsa tabi da kallo tsayon lokaci idan ba gezo suke mata ba hatta kasubar su tsayon shi daya shida wadda suke Kira Magaji, amfani tayi da wannan damar taita neman wani alama dazai banbance mata tsakanin mutum biyun, wannan abun na tsananin bata Mamaki.
Tsinkayar muryan sa tayi yana fadin, “ai bazaki taba gane banbancin mu ba saidai idan nine nagaya miki da bakina koshi Magajin.
Cikin saure ta dauke idonta daga kallon shi, yayin da yacigaba da cewa watau dazon kin zata Magaji ne shine kikaso ki gutsure min hannu?, Shiru yayi zuwa can ya sake cewa, ” Aunty na ki zauna mana muyi mgn.
Bata motsaba idonta kawai yake hangowa suna motsaba dan haka ya juyo sosai ya fuskance ta, gysran murya yayi sannan yace, ” aunty, zaki bani aron hankalin ki?
Kallon sa tayi ta kawar da kanta.
Inaso kidauke ni Kamar d’an uwan da muka fito ciki daya, idan har kikamin wanan kallon ke da kanki zaki saki jikin ki dani, ni inason jin wani abu ne game dake kawai, nasan zakiyi tunanin soyayya ce takawo ni, a’a sam ba wannan, asali ma ni zuciyata a kulle take, inason na taimake ne, zan miki komai a rayuwa, zan saki makaranta idan kin sami miji na aurar dake, amma. duk hakan bazai yiyu ba sai kin min mgn sannan ki amince intafi dake cikin dangina, domin inda akasan darajar goro nan akan nema masa ganye, agogon dake daure ahannun sa ya kalla sannan ya dago ya maida idon sa kanta Yana fadin, ” Ina da bako, nasan yanzun ya iso, ki kula sosai bana son Ina nanata mgn, ina da sauki, Ina da sanyi, Ina da zafi Ina kuma da d’aci cikin idonta ya kalla tare da fadin kinsan Wahainiya?
Tunda ya fara mgnr binsa cikin dangin sa jikinta ya shiga rawa, bare yanzun da suka hada ido Lokaci daya taji duniyar na juyawa, hankalin ta nashi, cikin sauri ta dafe kirjinta tare da rike cikinta dake juya mata.
Kallonta yayi sosai da Mamaki shigarta cikin damuwa, gaba daya jikinta ya dauki rawa lokaci daya.
Mikewa yayi yana kokarin karasawa gabanta, amman abun da ya bashi Mamaki tsananin rawan da jikinta keyi yasa ta fara zamewa zuwa kasa.
Tsaye yayi ya kasa karasawa gaban ta, domin zuwa yanzun wasu tunanin sun fara darsuwa azuciyarsa game da ita, afili yace Yaya zanyi da ita?, Ya subuhanallah…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadeela Lamido
https://youtu.be/YErlnJjLv_U
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 13-14
Ahankali ya cikaba da takawa zuwa gareta, yayin da yake matasawa gareta yana hango yadda rawan jikinta ke dada tsanan ta.
Itakuwa Unaisa jin Karan karfen gigitata yake yi, dan haka tai saurin tura kanta tsakanin cinyan ta, sandan yazo gabanta kuwa jin kamshinsa take har cikin cikin ta.
Tsaye yayi agaban ta, a hankali ya jingine karfen sa daya na gefen dake da lafiya tare da fadin, ” menene ya same ki lokaci daya haka?
Jimmm yayi yana son jin wani kalma daga gare ta, ganin tsayon lokaci hakan ya gagara yasa Modibo ya sake fadin, ” ko na dame ki ne?”
Nan ma shiru babu amsa, kallo ya gama kare mata sannan yace”
Aunty! Na dameki in tafi?
Ahankali ta dago kanta, tacikin ni’kab dinta ta kalleshi suka hada Ido, cikin sauri ta maida idon ta kasa.
Waigawa yayi ya kalli gidan ko Ina da ina, ya mutsa fuska yayi sannan ya dauki karfen sa ya fara takawa, kitchen din ya leka sannan ya nufi makewayin dake gidan, tsaye yayi yana kare masa kallo tsaf yake babu wani datti ko alamar kazanta, bushe yake alamar an dade ba’a shiga ba, kofar ya saki ya dawo kusa da ita har yanxun tana nan yadda ya barta, kallo ya kare mata tsayon lokaci sannan ya nufi dakin ta, tsintan kansa yayi da tura kofar Yana daga tsaye fakin kofar, dakine irin na tsofi marasa karfi, babban gado da karamin gado gyare suke lukui, banda kamshin turaren wuta babu abun da dakin ke yi, komai na dakin kal, wannan ya tabbatar masa yariyar tana da tsafta, ahankali ya daga kafar sa ya shiga cikin dakin, wani hoto yagani guda biyu gefen filon ahankali yasa hannun sa ya dauka, wata tsohuwa ce ta bayyana daganin ta bafulatana ce saidai bakace bata da haske kwata kwata, bayan ya gama kare ma hoton kallo ya juya bayan sa, Innawuro yaga an rubuta cikin wani irin rubutu wadda Modibo ya bata lokaci wajen kallon sa, motsi yaji akofar dakin dan haka ya daga kansa ya kalli kofar yana jingine jikin babban gadon.
Hango kafar ta yayi ta kasan labulen dan haka ya maida wannan hoton baya ya tsaya kallon daya, tsoho ne shima, saidai wannan yafi kama da bahaushe ba fulani ba, bakine shima wadda saboda tsofa har ya rankwafa, cikin sauri ya juya bayan hoton inda yaga anrubuta Baffana da irin wancen rubutun dai.
Ido yasama hoton sosai Yana nazarin wasu abubuwa be ankaraba ya fara hangota hannunta rike da tsintsiyar laushi, tundaga kofar dakin ta dauko shara dan haka ya tsaya kawai ya zubawa sauratar Allah idanu.
Sosai take shara, kuma har yanzun bata tare da nutsuwarta, duk da cewa babu wani datti adakin, kallonta kawai Modibo keyi yana dan shafa gemon sa a hankali.
Duk dakin tabi ta share ko Ina, yayin da ta tsaya adaidai lokacin data kawo kurar gaban shi, ahankali ya sauke idonsa ya kalli kasa yana dan shafa gemun shi tare da Satan kallon ta, ganin ta dauki tsitsiyan tana Shirin cigaba da sharan yace, ” Aunty idan kika sake Kika daura tsintsiyar ki ajikina idan na tsinka miki mari saikin kwana biki farfado ba, duk wadda ya hadiye tabarya to kuwa zai kwana atsaye, izza na Kano, sarauta na Sakkwato, yaki na Zari’a, Karin magana na Bauchi, ba’a fini tsumma ba kar a badamin kwarkwata, idan kika fusatani abun bazai mana kyau ba.
Lumshe idonta tayi, cikin ranta take fadin, wannan wanni irin mutum ne, sosai ta kule dashi har babu misali, banda kafin hali me yakaishi shigowa har daki, har yanzun tsintsiyar na hannunta takasa matsawa kuma har yanzun jikinta rawa gake, kamashin Modibo kuwa tuni ya bade dakin, ko kamshin nasa gigitata yake yi.
Shikuwa Modibo gemon sa yake shafawa tare da dan lasan gemon sa, tsawon lokaci suka dauka ahaka kusan minti sha biyar sannan yace, ” ajiye tsintsiyar.
Ko motsi batai ba dan haka ya shafi gashin kansa yace, ” menene ya baki tsuro dazon? , kinga wani abune daya baki tsoro?, Koko nine baki son gani?
Har yanzun kanta akasa yake, ahankali ya maida idonsa Kan hannunta data rike tsintsiyar dashi bari tas tare da kyawawan yatsu, gyran murya yayi sannan yace, ” meyasa kike rufe fuskar ki amman hannun ki da kafarki a waje?, Suma ki dinga rufesu aunty na.
Batace komai ba dan haka yayi murmushi tare da fadin, ” kin yadda zaki bini cikin dangina ?
Kanta ta sake hadewa da guiwa dan haka ya hade hannunsa a kirjinsa cikin son ganu wani abu yace, ” amakaranta zan saki kiyi karatu.
Wannan karon zama tayi dirshen akasa zufa kawai ke karyo mata.
Kallo yaita binta dashi tsoyon lokaci zuwa can yace, ” kenan dan nace ki bini gidanmu kike rikecewa har haka, ko kin dauka ina Satan kawuna ne, idan Ina sata ai bazan tambayi ra’ayin ki ba, gafarsa ya daga, shikenan kisha zamanki, ga abokan hira Nan na kawo miki, duk sanda naxo gurin Malam kuma zanzo na dubaki, ko baki so??
Shiru tayi kanta akasa Dan haka ya kara cewa, aunty inason in diga zuwa muna gaisawa?
Kallo ya bita dashi zuwa yanzun ta dan rage rawan jikin dan haka yace, shikenan tunda bakison Ina zuwa gaya min me kike bukata nakawa miki shikenan bazan sake zuwa ba, Ina nufin abuwan bukata na amfanin kudin makaranta da kudin kashewa tun da kinkiyin mgn Dani inji matsalar ki.
Ganin babu amsa yasa hannun sa ya ya ciro kudi mai yawa ya aje bakin gadon tare da fadin gashi kiyi amfani dashi, karfen sa ya dauka sannan ya fara takawa yana kokarin fita dakin ya sake cewa bazan sake zuwa ba tunda bakison gani na, tsuntsayen ma nagene baki sonsu amman bazan kwashesu ba dole ki koyi zama dasu, ki kula sosai da Basu abinci, suna bukatar abincin kamar yadda mutum Kan bukata karki sake ki cututar dasu, Koda yake ma in kinso ki cutar dasu tsakanin ki da Allah ne.
Wanni irin kallo ta masa yayin da ya hangi akwayar idonta tana juyawa, cikin ransa yace bantaba ganin irin wannan kwayar idon cikin Nigeria ba saidai a kasashen waje, afili kuwa cike da kasaita tamkar an masa dole yace, ” naki ne Mana, mallakin kine kuma a karkashin ki suke, ina mgn ne kai tsaye da zuciyar ki, me ha’kori na sha’awar hura wuta me dasori ai saiya doba da ido.
Juyawa yayi ya fita yayin da yake ji ajikin sa tana binsa da kallo.
Sannu a hankali ya fito kofar gidan yana baza Ido, ganin babu motar sa sannan babu Magaji da Muftahu, wasu daga cikin abokan tafiyar nasu ne suka matso da wata motar daga cikin jerin motocin su, adaidai lokacin da Modibo ya karaso bakin motar wani ya bude murfin motar, kokarin shiga Modibo yake Yana fadin, ” Ina Magaji da Muftahu kuma?
Ranka ya dade bakon ne ya iso gidan kuma babu kowa.
Lumshe ido yayi tare dajan karamin tsaki, bayan ya zauna suka dauki Hanyar fita cikin Unguwar, saidai suna daf da fita, sukaga su Magaji na dawowo, ganin su yasa suka fara kokarin juyawa tare da kokarin saita motocin nasu domin subawa Motar su Magaji damar shiga tsakiyar tasu, bayan sun jera motocin sakkowa Magaji yayi ya bude motar da Modibo ke ciki tare da fadin, yace ka dawo nan.
Lumshe ido yayi tare da ajiyan zuciya sannan ya fara kokarin sauka, da taimakon Magaji suka shiga waccen motar, wani matashi ne zaune cikin motar cikin kanan kaya, ko kallon inda yake Modibo beyi ba ya zauna gefen sa yayin da bakon kebin sa da Ido cikin bakin gilashi bakin sa dauke da Murmushi.
Magaji da Muftahu ne agaban motar, har bayan sun hau motar babu mema wani mgn shiru kakeji, Magaji da Muftahu ko Satan kallon junan su sukeyi, yayin da Modibo ya murtuke fuska sosai, zuwa can Modibo ya dauki gilashin sa dake gefe ya sanya, Magaji dake hangen su ta mudubin motar dariya kwace masa tayi, ta mudubin gabanr motar ya hangi wani kallo da Modibo yai masa, dan haka ya hadiye murmushin sa.
Magaji kana mana dariya ne?, aboki nane bari ka gani zamu shirya, hannun sa yasa ya kamo na Modibo yana fadin kai hakuri nayi kuskure, kuma ai ka hukuntani tunda baka daukan waya ta tunda kuka taho banji muryan ka ba saidai inji halin da kake ciki wajen Muftahu.
Kallo daya Modibo yai masa ya sake kawar da kansa, yayin da Matashin yacigaba da cewa, Kai hakuri Modibo na, tsayawar ma da nayi beyi amfani ba domin har yanzun dai muna nan jiya I yau, kara ma lalacewa abon yayi.
Magaji dake Gaban motar suna saurasun kara baza kunne suka yi fuskokin su dauke da murmushi.
Modibo kuwa zame hannun sa yayi daga na abokin nasa Yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin, ” yayi kyau”
Haka ma zaka ce?
Fuskarsa daure tamau yace, “yayi kyau mana, idan bakasan yadda zakayi ba kazo a koya maka, amman ka tsaya kato dakai kana ta shirme har karamar yariya ta raina ka, kana bani takaici, wlh, idan ya riyar nan bata aure kaba takama da Kai.
Ta madubin motar Magaji da Muftahu ke Satan kallon yadda Modibo yake furta kalamin sa tamkar badaka bakin sa suke fitowa ba, kasancewar Basu taba jin sa Yana irin wad’an nan kalamin ba.
Shikuwa Bakon Ido ya zubawa Modibo tare da fadin, ” au ita cema zata aure ni…
Eh Mana, duk kabi ka susuce, karamar yariyar karasa ta inda zakabi da ita ka lankwasata cikin hikima, matsalan dake damun mutanen mu kenan, Abin kunya sai kaga mutu yaje wurin yariyar sa da niyyar yin awa uku sai kaga ko minti goma bai yi ba ya dawo, saboda rashin sanin makamar ta inda ya kamata ya fara zancen nasa, alhalin akwai hanyoyi da dama da zakaita jan hankalin yariya batare da kun gundiri juna ba, yazama cewa bata kaunar matsawarka kusa da ita sabo da dadin hirar da kakeyi da ita.
Sosai Magaji ya kara baza kunnen sa, domin daman acikin zuciyar sa Yana mamakin dadewar da Modibo ke yi idan ya shiga cikin gidan yariyar da ba mgn take da kowa ba, yana jimawa sosai, sannan yana yawan tuna kalamin Sulaiman da yace wani matashi yayi fin shekara yana bibiyarta amman betabajin ko kalma daya daga gareta ba, sannan kuma Sulaiman yace wannan matashin ta tazo zata bude gidan yake shigewa kenan mamayanta yake sai gashi Modibo kwankwasawa kawai yake ta bude har tana kokarin banbance tsananin na dashi, da alama ta fara yadda dashi, tambas Modibo yayi mgn da yariyar, kilama har fuskar ta ya gani, saboda ya kware wajen sarrafa harce, hakan yaji duk zuciyarsa ta jagule, lallai yanason ganin fuskan yariya domin idan akace yadda idonta da kafafuwanta suke dakyau haka fuskarta kedashi to lallai Allah yayi hallita.
Jin Moddibbo nacigaba da fadin wasu kalamin ya kara baza kunnen sa, gani yake kamar tukin motar na takura masa gara ya rufe idon sa ya saurara dakyau dan haka ya waiga ya kalli Muftahu yace, ” Muftaho kaina na sarawa ko zaka amshe ni..
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 17- 18
Bude idonta tayi adaidai lokacin da da Modibo yasa kafarsa acikin dakin, cikin tsananin mamaki take binsa da kallo, domin kuwa tasan karfi cire kofar nasa ne bane me muryan da da taji d’in ba, tambayan kanta tayi toh muryan kuma da taji d’azon d’in fa?
Kafin ta gamawa kanta wannan tambayan taganshi yana takowa abayan Modibo, hakan yasa tai saurin tashi zaune batare data sani ba, kallon sa tayi sosai sannan ta maida kallon ta gurin Modibon dake tsaye fuskarsa daure tamau babu alamar wasa”
Ganin inda ya tsare ta da kallon tuhuma ya sa tai saurin sunkuyar da kanta kasa, cikin kwalkwal da Ido, zuwa can tajin Modibo na fadin, ” ita ce ko?
Itace Mana Modibo, ai tunda muka shigo wannan Unguwar na shaida ita ce, domin babu wata yariya dake da d’abin daka lissafa.
Lumshe Ido Modibo yayi na tsayon lokaci zuwa can yace, “wani irin labari kaji akan ta?
Kawai dai ance iyayen ta sun rasu tana zaune ita daya kawai, kuma ni kaina ganau ne, domin bata mu’amala da kowa, sannan wani abun da zai baka Mamaki Modibo na dade Ina zuwa gidan nan wlh tak bata taba cemin ba, kuma duk wadda namai tambaya sai yace min tana mgn ba kurma bace, mgnr duniya nayi harna gaji, kai ta taba maka mgn ?
Matsawa Modibo yayi bakin gadon ya yaye mayafin data rufa dashi yana fadin, “abun da kazo dashi mata dashi ni bada shi nazo ba, wurgi yayi da bargon tare da cigaba da fadin, bance miki karki kara kin bude min kofa ba?, Ke! Kin sanni kuwa?
Ganin yadda ta sunkuyar dakai Suraj yayi yar dariya wadda bakai ciki ba, sosai ya kula mazoran Modibo yayi tasiri a gare ta, dan haka yai saurin fadin, “kai mata hakuri Modibo, anan gurin ita ta ganka, batasan wanene kai ba, daman hakane, wani tsutsu na gudun ruwa ne agwagwa kuma a ciki take kwana.
Afusace Modibo ya kalli Suraj Yana fadin, ” ai samun yarda ga dodo kesa ashiga ruwa lafiya, na sake zuwa na buga kofar baki bude wlh saina nuna miki wasan kokawa bana gurguwa bane.
Har yanzun bata dago kanta ba yayin da Suraj yabita da Ido yana mamakin yanayin ta ayau.
Shikuwa Modibo wayarsa ya daga Yana kiran Magaji domin tun Jan bargon da yayi ya gane da zazzabi ajikin ta, bayan Magaji ya daga ya shiga fadin, ” ka nemi wani asibiti mafi kusa ka taho min da likita, yariyar nan Bata da lafiya.
Sauke wayar yayi ya fice, yayin da Suraj ya bishi da kallo, bayan ya tabbatar da fitan sa ya hadiye yawon bakin sa Yana fadin, Kin gane ni?
Batare da tace komai ba ta juya kawai ta kwanta, domin zuwa wannan lokacin ta fara jiran tsammani kawai, Bata da wani abun yi dan haka tafi bukatan ta mutu kawai ta huta.
Fitowa Suraj yayi ya samu Modibo ya saki tsuntsayen yana watsa masu gero, yayin da fuskarshi take tattare da bacin rai.
Wad’an Nan tsuntsayen fah?
Saida Modibo ya had’iye yawon takaici sannan yace, ” nakawo mata ne dan ta dan dingajin motsi a gidan, amman na kula tun bayan dana kawosu Bata Basu abinci ba, Ina nufin Sam bata kula dasu ba, Suraj ina son dana gama amsan magani intafi da yariyar nan, Ina tunanin inyiwa Malam baba mgn akanta, domin musamu wani daga cikin dangin ta dazaiba ni ita intafi da ita, Ina son rayuwarta ta canza, bedace ace muna barin irin haka na faruwa ba, dan iyayen ta basa raye bashi dalilin zaman rashin galihu ba, kuma ba yana nufin rayuwarta ta kare haka bane, ba yadda za’ayi ace bata da dangi dan babu wadda yake fad’owa daga sama, duk wadda kagani acikin duniya mace da namiji ne sukai sanadin zuwan sa duniya ko da aure ko babu, dan haka nasan dole tana da dangi saidai ace ba asan in da suke ba.
Ajiyan zuciya Suraj yaja, Modibo mgn ta zahiri bata ta kowa, kota kofar gidan nan mutane basu cika biba, daukan ta suke kamar wata hallita ta daban, nikuma tunda naga yanayin ta awacen lokacin naso kawai ta bani hadin kai, naso ta bani hadin kai, har ga Allah aurenta naso yi, cikin wannan shigar na ganta kafarta da shatin idonta ya tabbatar min da yariyace kyakyawa wadda kowanni namiji zaiso ya kasance da ita, zaman da nayi da ita kuma na fahimce batason aga fuskarta hakama muryan ta bata mgn da kowa, tana ganin ita daya zata iya rayuwarta.
Afusce Modibo ya kalli Suraj ai da saika sanar da ita duk tsayon hannun mutum be iya cuda bayan sa, kuma ai ko agidan giya akwai babba.
Shiru kawai Suraj yayi domin duk yadda zai kwatanta masa bazai gane halin yariyar ba.
Zuwa can Modibo yaci gaba da cewa, ” kace baga taba ko jin muryanta ba haka kuma bakaga fusrkarta amma naji kace kaso auren ta?
Dakalin dake bayan Modibo Suraj ya zauna, sannan yace gani daya na mata zata tsallaka titi, nikuma nazo wucewa da mota ta, yanayin surarta taja hankali na harna biyo bayan ta, Modibo son ta naji har cikin raina, ban biyo ta da fargaban komai ba, domin juma’a mai kyau tun daga laraba ake gane ta, amman ban sani ba ko kana daja akan son da nace inai mata, nasan halin ka Sarai yanzun kana iya cewa ma bansan so bama gaba daya.
Wani irin dan murmushi Modibo yayi da yad’an bada sauti sannan yace, a’a taya zance baka san so ba, bayan Allah ne kadai yake da iya ikon sararafa zuciyoyi, ma abota iya kalamai suna cewa, so tsirone ko halitta ne a jikin dan adam , ni abin da nafi mayar da hankali akan so shine, So kaddara ce da ake haifar Kowanne dan adam da ita, haka yasa yake yanayi da bakan gizo, saboda kala kalar shi, sannan yake da siffa irin na littafi saboda shafi shafin sa, idan ya kasance so yana samun kulawa kullum sabon shafi ake bude masa, idan aka sami akasin haka ko rashin dace, to da zarar shafin farko ya cika fanni sa a sake wani, shiyasa ma abota soyayya suke cewa so tsuntsune”
Kallon Modibo yayi dake tsaye Yana mgnr yana watsa ma tsuntsayen gero yace, ” mhm me kake nufi da so tsuntsu ne?, nifa wani lakacin kalamin ka suna batar dani.
‘Yar dariya Modibo yayi kadan sannan ya hade fuska, Suraj ai bacewa acikin jeji karin ilimi ne, hakika so tsuntsu ne , tun da a bayan so babu tausayi, domin so yana tafe ne a kan doron sha’awa, burgewa, karka yi tsammani idan abu ya na birge ka ko baka sha awa ta fannin wani abu nasa kayi tsammanin zaka iya rayuwa dashi idan har ka mallake shi, wannan shi ake kira so da zarar abu ya baka sha’awa ko birgewa kaji kana son shi da zarar babu abin da yake birge ka ko baka sha’awa ya gushe ya disashe, sai a fara neman canji ko a jefar da shi, wannan shine yake jawo mutuwar aure yake yawa a wannan lokaci, numfasa yayi kadan sannan ya sake cewa, ” barin kuma in d’an banbace maka tsakanin so da kuma kauna.
Ina jin ka Suraj ya fada, adaidai lokacin da Modibo ke kokarin zama gefen Suraj, gyarawa yayi sannan ya amsa sanduna sa ina jinka.
A nazari na so shine ginshikin kauna, Idan babu so kauna bazata kasance ba kauna wani yanki ne na so, wadda masana soyayya suke cewa, so shine mafarin kauna, kauna tana tafiya ne a kan doron abubuwa guda uku, Sha’awa, Burgewa,Tausayi, idan ya kasance kanajin Tausayin wadda kake so ,. Zaka iya zubar da hawaye a domin ya shiga damuwa ko kunci Wannan shi ake kira kauna, Shi yasa idan kaga an gina soyayya akan doron gaskiya kauna take komawa, Wannan shi yake sa kaga aure ya d’ore koda wani daga ciki ya rasa wani abu da yake birge ko baiwa dan uwan zamansa sha’awa. Kyaun Surar jiki, Lafiya, Kudi, Da sauran su, Ina baka shawara, Kayi kokari ka hada so da kauna, domin yin haka shine zai baka damar rayuwa da Abin da kake so na har abada.
Ajiyan zuciya Suraj yayi sannan yace, mhm Modibo kenan toh naji, amman fa wani lokacin ka fiye mgn
Hmh, hakama zakace, to ai mgn jari ce.
Yanzun dai ba wannan ba Modibo Ina muka kwana akan yariyar nan?
Abun da nake tunani zan nemi wadda zai iya bani damar tafiya da ita, domin ina son tabar wannan rayuwar.
Allah ya taimake ka akan kudirin ka.
Ameen Modibo ya fada ahankali.
Ji yayi Suraj ya sake cewa amman nifa idan har Allah ya baka damar tafiya da ita Ina sonta zan aure ta.
Lumshe Ido Modibo yayi sannan yace, wannan tsakani ku ne, ni kawai Ina sonne ta zama mutum me yanci kamar kowa.
Shigowan Magaji da Suraj yasa su yin shiru daga inda Modibo ke zaune yabawa likitan Umarni, yayin da Magaji ya tsaya bakin kofar yana fadin, Wala Habaru taso a duba ki….
Baikai ga rufe bakin sa ba Modibo ya daka masa tsawa tare da fadin, karna sake jin ka kirata da wannan sunan banzan.
Modibo to dame zan kirata naga wannan sunan shine kowa ya santa dashi nikuma bansanta da wani suna ba vayan shi.
Unaisa da tun hirar su nad’azon tana sauraron su tai saurin cewa acikin zuciyarta, ji inda yake mgn kamar mutumin kirki, jiya da yazo shi d’aya ai ya kirani da wannan sunan, tsintan Muryan Modibo tayi yana cewa ka kirata da Afnan.
Afnan kuma, toh Modibo akan me zan kirata da amfan bayan kafi kowa sanin cewa Afanan jarabarbiyar yariya ce.
Wannan tsakanin ku ne, yanzun dai ka tashi a gurin kabashi guri yayi aikin sa.
Tashi yayi Kamar yadda yace, gefe suka koma shida Muttaho, itako Unaisa tsaye tayi ta jingina da babban gadon Innawuro, ta window take hango garaden maza hudu zaune a tsakar gidan nasu, wannan abun ba karamin daga mata hankali yake ba, gaban ta ta kalla taga yadda mutumin ke shirya kayan aikin sa sannan ya matso gabanta yana kokarin gwada zafin jikin ta, bayan ya gwada rubuce rubuce yayi sannan ya kalli fuskarta yace akwai ciwon kai?, da Kai ta amsa masa, jakar sa ya bude ya fara ciro allura Yana hada wa, sosai hankalin Unaisa ya tashi fiye da da, ganin ya nufata ta zabura ta haye can kuryar gadon tare da hada kanta da guiwa.
Ganin haka ya isa bakin kofar ya daga labulen yana fadin, ranka ya dade yariyar tana da gaddama, nasoma intaba goshin ta ganin ta rufe fuskarta tabarta, yanzun kuma na hada allura ta haye gado….
Suraj jeka, Modibo ya bada Umarni, shiga dakin yayi tsayon lokaci sannan ya fito yace Modibo Ina ganin kawai a Bata magani dan bazata tsaya ba.
Karfen sa ya mika hannun ya jawo, ya gyara masu zama a inda ya dace, sannan ya fara takawa zuwa cikin d’akin.
Tunda tafarajin Karan takunsa rawan jikin ta ya karo sosai, rawa kawai jikin ta keyi karkar har gaban gadon ya isa batare da yace kala ba, tanajin sa kusa da gadon ta dago kanta ta zuba mishi idanu, sandar sa daya ya aje jikin gadon sannan ya mika hannun ya rike kafar ta, jawota yayi harya iso da ita bakin gadon yayin da ganin Yana Shirin direta akasa tai saurin damukar gaban rigarsa cikin wata irin murya me kama da busan sarewa tace, ” Ayya Modibon su bafa Amin allura…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 15- 16
Kamar yadda Magaji ya bukata haka akayi, Muftaho na karbansa ya kwanta jikin kujerar motar ya rufe Ido tare da tattaro duk wata nutsuwa tasa ya maidata Kan hiran Modibo da abokin sa.
Hannun Modibo abokin nasa ya runtse acikin nasa tare da fadin, ” Modibo ninasan yadda nake bida yariyar, babu irin kallamar da ban furta mata ba, amman na lura duk abon da nake so bashi ne agaban ta ba, idan Ina gabas ne to ita tana yamma.
Waigowa Modibo yayi kadan ya dube sa, tsintan kansa yayi da Murmushi batare daya shirya ba, sannan yace, Suraj kenan, Har sharrud’a kake gindaya mata?
Jimmm wadda aka Kira da suna Suraj yayi sannan yace, ” eh to idan naga tana wani abu da beyi daidai da ra’ayina ba Ina mata mgn tare da nuna mata banso.
Lumshe ido Modibon yayi, batare da ya bude idon nasa ba yace, ” au haba?, kaji irin ta ko, to barin gaya maka wani abu, idan kaga an zuba miya cinikin tuwo ne ya kare, Kai da ba son ka ake ba, kabari harta kamo da son ka Mana, atashin farko kaje gurin yariyar da ka yadda cewa auren ta kake so, nuna mata kafita son abin da ka same ta akai, duk abun da zata yi ce mata burge ka take yi, Koda abun ba son shi kake ba, ka bita a sannu har ta shigo hannu, lokacin ne kake da damar gindaya mata sharrud’a tabi, ko nan gaba ka kiya Kada ka ce zakaje gun yariya ka fara da doguwar hira, misali ku fara da gaisuwa sai kuma ‘yan qananun tambayoyi wadanda basa buqatar doguwar amsa. Sannan sai a tafi masu buqatar doguwar hira.
Dariya Suraj yayi tare da shafo keyarsa kuma fa hakane Modibo, toni ko hakura zan da yariyar nan ne inje in sake shiri?
Ya rage naka, Modibo ya fada Yana gyara zaman gilashin sa dake manne a idon sa.
Muftaho kuwa Satan kallon Modibo yake ta madubin dake gaban sa, acikin ransa yake fadin, ” Modibo mu ya hadu ta ko Ina, ji inda yake furta kalamin Kamar ba daga bakin sa suke fita ba, shikanshi Modibo burgeshi yake yi, shikuwa Magaji idon sa arufe amman gaba daya kunnuwan su yana gurin hirar su, wannan karon jin Suraj din yayi yace, ” bazan boye maka ba Modibo nakosa nai aure akwai wata yayi saidai yanayin gidan su Ina ganin Bata dace dani ba, shiyasa ma na hakura da ita, kai nidai kamar ma banda sa’a
Babu wata mace wadda Bata dace dakai ba, sai in bata da tarbiya, barin baka misali, Mace dai ta kasance tamkar wata furen fulawa wanda idanun mutum suke sha’awar kallo a koda yaushe, ita fulawa ta kasance aba ce mai kamshi, Haka bayan kyawun kallo, tana da bukatar kasancewa a cikin inuwa, domin idan aka sanya ta a rana za ta yi yaushi, kaine zaka gyara komai domin gudun kar a samu wannan matsalar idan har ka sama mata farin ciki haka zata kasance a wajen sanyaya zuciya da farin ciki a zuciyar abokin rayuwar ta, ta wannan Hanyar ne shinfidar ku zata gyaru, ta gusar maka da tunanin ka ka gusar mata da nata, kallon Suraj din yayi cikin ido yana fadin, Ina nufin aji dadi tare
Waigowa Muftahu yayi ya kalli Modibo sannan yai saurin juyawa ya maida hankalin sa Kan tuki, fuskan sa dauke da fara’a sosai, zuwa yanzun Modibo ya fara bashi kunya, gani yake Kamar be dace yake cikin abokan guda biyu ba, Yana jin hirar su, saidai shi Modibo hankalin sa kwance yake zaro zancen, tsintan muryan Suraj din yayi yana fadin, ” gaskiya ne mutumina nidai yanzun nazama d’alibin ka.
Lumshe Ido Modibo yayi ni bani da lokacin wannan.
Hmmm lallai shiyasa Kai zaman ka cikin garin nan baka da wata damuwa….
Waye ya gaya maka, ai ba za’a hada nan garin da gida ba, baka inda na koma ba, kamar wani maraya.
Cikin dariya Suraj din yace har ka tuna min wani lokaci dana taba shigowa garin nan haka naita zaman bacin rai har nagaji na tattara ‘yan kayana nabar garin.
Cikin gajiya da zance Modibo yace ashe kataba shigowa, koda yake dama baka zama guri daya.
Ajiyan zuciya Magaji yayi idon da arufe har yanzun, ahankali ya bude idonsa tare da tattaro duk wata jarumta tasa adaidai lokacin da suka isa wani katon gida.
******
Zaman darshen tayi a tsakiyar dakin, tare da share hawaye, gaba daya tunanin ta baya aiki ayanzun, kuka tayi sosai idonta suka kunbura, tunawa da da tayi bata rufe gidan ba yasata mikewa da saurinta ta koma har ta isa zauren zuciyarta na ta farfasa bayan ta rufe gidan ta koma ciki, gado tahau tana cigaba da share hawaye, ji tayi komai bayya Bata dadi tare da rasa abun da zata tunu taji sauki acikin zuciyarta.
Agefe guda kuma kukan tsuntsayen ya dame ta sosai takejin sun takura mata, kasa tabuka komai tayi har dare sallah kadai ke tada ta.
Ko washegari idonta duk sun kunbura, kuma har yanxun bataji nutsuwa ta sameta ba Kamar da, dan haka taita addu’a cikin sallolinta inda take rokon Allah yacire mata wad’an nan mutanen cikin rayuwarta.
Haka ta wuni sukuku sannan babu wani abinci da tai tunanin ci ruwa kawai take sha, zuwa wannan lokacin kukan tsuntsayen ya ishe ta, tunawa tayi da zancen Modibo da yace karta barsu da yunwa, sosai taji cikin ta yayi sanyi saidai tunawa da tayi itama bata ciba bare tabawa tsuntsu, har dare Unaisa bata saka komai acikin ta ba dan haka ta fara galabaita ga tarin damuwa ga rashin cin abinci.
Washegari bayan tayi sallah daker ta iya komawa kan gadon ta kwanta babu kalmar ta dafi daga mata hankali Kamar cewa da yayi zai tafi da ita.
Misalin takawas da rabi taji ana kwankasa gidan, tunjin bugun farko tasan Dada ce, hankali ta sauko daga Kan gadon ta, wani jiri taji yana dibanta dan haka ta fara bin bango harta isa ta zare sakatar.
Unaisa Yaya menene ya faru?
Dada ke fadin haka lokacin da Unaisa ta fada jikin ta, rungume ta tayi tsam ajikin ta sannan ta jawota suka koma dakin suka zauna, yayin da Dada ta kurawa fuskar ta Ido.
Unaisa lafiya?, Meke damun ki?
Bakomai Dada, kwana biyu kawai banda lafiya ne.
Jimmm Dada tayi cikin yanayi irin na me tunani tace, ” baya ga cutar akwai wata damuwa a tattare dake Unaisa…..
Tunkan Dada ta rufe baki Unaisa tace, ” Babu”
Cikin takaici Dada tace hmmm Unaisa, nidin nan aihuwarki ce kawai banyi ba, kinga nan gurin, kallo Unaisa tabi inda Dada ke nuna mata gefen gado a kasa sannan ta koma ta kalli Dada ta d’aga kai alamar eh, Dada ce taci gaba da cewa, ” a nan gurin ni nadauke ki cikin jinin haihuwar ki, nina dafa ruwan zafi na kuma wanke ki, sannan naita gasa cibiyarki harta fad’i, ke komai ni nake miki har kika fara wayau, dan haka kibar boye min damuwar ki, banda abinki Unaisa yanzun ke har akwai wata damuwan da zaki boye min?
Sosai jikin ta yai sanyi, ga wani son Dada da taji ya kara zama daram cikin zuciyar ta, saidai koma menene bazata taba gayawa Dada kudirin mutumin ba, idonta cike da kwallah ta kalleta tace , nifa Dada babu komai banda lafiya ne.
Jimmm Dada tayi sannan tace, “shikenan, kullum Ina addu’a Allah ya karkato Mana da….
Batakai ga karasawa ba Unaisa tace Dada ni banso..
Kallonta kawai Dada tayi sannan ta lumshe Ido tana fadin, shikenan Unaisa ni yanzun banda ta cewa game dake, Amman Ina rokon Allah ya kawo mana mafita nidake gaba daya, tunda ke daga an kawo miki mafita saiki hau zazzabi, dan haka na zubawa sarautar Allah ido, duk abun da Allah yayi me kyau ne, kawai dai Ina rokon Allah karya kasheni batare da naga kin samu majingina ba, nakasa tare miki komai illah abincin da zakisa a acikin ki.
Cikin kwalkwal da Ido Unaisa tace, nifa Dada kinmin komai….
Batakai ga rufe baki ba Dada tace, ” wad’ancen tsuntsayen fa?
Mumunan faduwan gaba taji kafin tace sawowa nayi.
Wanni irin kallo Dada ta mata sannan ta zame kan Unaisa dake kafadarta ta sauko agadon ta nufi tsakar gida tana fadin, ” aina kika saya?
Bakin kasuwa.
Kallonta Dada tayi sannan ta kalli tsuntsayen tace nawa kenan?
Jimmmm tayi domin ita ko kudin kaza bata sani ba bare tasan na tsuntsaye, ganin kar Dada ta dagota tai saurin cewa dari bakwai.
Cikin Ido Dada ta kalleta, dari bakwai Unaisa?, daga kamar zasukai guda 20 kuma duk dari bakwai?
Daburcewar da tayi yasa ta kwarewa, tari ta shigayi dan haka Dada ta nufa kawo mata ruwa bayan ya lafa daki suka koma, Dada ce ta mata abun karyawa tasa ta taci dole sannan ta bata magani, sannan Dada ta wuce gida.
Dada na fita tunanin mutumin ya dawo mata, balakin haushi taji yana Bata, halinshi ya banbanta dana sauran mutane, bashine farkon mutumin daya fara bibiyarta ba, amman dabi’un sa sun banban ta, tana tsaka da wannan tunanin taji an sake buga mata kofar gidan akaro na biyu, ahankali ta fito cikin dakin ba haka Dada ke buga kofar ba, sannan wannan Modibo ma ba haka yake bugawa ba, saidai tana shiga dan karamin zauren nata tafara jiyo kamshin turen sa, hannun ta tasa ta dafe kirjinta sannan ta leka ta gefen kofar, sandunan karfen data hanga ya tabbatar mata da shine, bayan sa kuma ga motoci cen tana hangowa ahankali tasa hannun ta ta zare sakatar, shima zaman sudunan sa ya gyara a hakarKarin sa sannan ya fara takowa.
Tsaye tayi jikin bangon Kamar yadda ta saba masu, saidai wani kallo da taga Yana binta dashi yasa tai saurin kawar da kanta.
Gyaran murya yayi sannan taji yace, Wala Habaru.
Runtse idonta tayi jin ya kirata da wannan sunan.
Meyasa ake Kiran ki Wala Habaru?
Waigowa tayi ta kalleshi kadan sannan ta kara kawar da idon ta, gani tayi yau ya fiye murmushi sabanin da da yake mgn tamkar ana tilasta masa.
Ki budemin fuskarki kafin indaso in bude ta da kaina.
Kallon shi ta sake yi tana tuna wasu kalmomi daya fada abaya, ganin da tayi ya ya fara takowa gareta yasa ta fara ja da baya har suka isa kofar dakin, shiru tayi ganin yana nufota gadan gadan, wani irin mugun tashin hankali ne taji acikin ranta take fadin me yake shirin faruwa ne, wani irin dibara ne ya fado mata dan haka tai saurin angaje karfen ta nufa kitchen din aguje.
Daker ya iya tare karfe be ankaraba yaga ta fito da wuka daga cikin kitchen din.
Lailai yariyar nan baki da hankali, nine kika angaje kika wuce?, Hannun sa ya hada guda biyu suka bada sauti tare da fadin kinci bashi, juyawa yayi ya fice ba tare daya sake waiwayen ta ba.
Itako Unaisa tanajin tashin motar su cike da firgice ta zo ta rufe gidan sannan ta koma tasa kuka tare da tausayin kanta, gani take abubuwan na dad’a cakude mata
Acikin ranta tai alkawarin bazata sake bud’e kofsr ba ko wanni irin bugu kuwa za’ayi mata.
******
Modibo ne kwance awani tamfatsetsen gado na alfarma, rufe idon sa yake sai dai daganin kwanciyar sa kasan ba bacci yake ba, domin kuwa hannun wansa harde suke akan kirjin sa, yarin da ya dauki kafar sa me lafiya ya ratsata ta guiwar mara lafiyar, yana dan girgiza me lafiyan kadan.
Daganin irin kwanciyar sa kasan wani mutumne wadda yake ji da takama, kofar aka fara bugawa kamar bazai amsa ba zuwa can yace, ” waye?”
Muryan Muftahu yaji yana fadin nine.
Shigo, ya amsa masa duk batare daya bude idon ba.
Takowa Muftahu yayi har bakin gadon ya zauna, ahakali Modibo ya bude idon sa ya kalli Muftahu Yana fadin, ” Muftahu lafiya kuwa?”
Hankali yace, lafiya lau Modibo, Ina son ne nai mgn dakai.
Ok toh Ina sauraron ka, kokarin tashi Modibo ya fara yayin da Muftahu yace bama sai ka tashi ba.
Kishingila Modibo yayi yana me zubawa Muftahu ido.
Cikin kasa kasa da murya Muftahu yace, ” Modibo kasan me?”
Runtse Ido Modibo yayi batare daya bude ba yace tayaya zan sani bayan baka gaya min ba.
Yadda Modibo yayi mgnr adan fusace yasa Mutahu juyowa gaba daya, Modibo wannan yariyar ce naji ina son ta.
Dan jimmm yayi zuwa can yace wacce yariya kenan?
Yawu Muftahu ya hadiye sannan yace, wannan yariyar dake kin mgn d’inan
Komawa Modibo yayi ya kwanta akan gadon, sannan ya daga sandar hannun sa ya daura akan goshin sa dare da wani murmushi da yabada sauti Yana fadin, ” Abun dariya yaro ya tsinci ha’kori, kai kuma daga ganin sarkin fawa sai miya tayi za’ki?
Modibo nidai tsin tan zuciyata nayi ahaka.
Wani irin murmushi Modibo yai sannan yace, ” mhm, to naji, Muftahu kayi kyan kai, daman amfanin girma hankali, amfanin hankali kuma aiki dashi, karka wani damu.
Mikewa Muftahu yayi ya fita yayin da Modibo yabishi da kallon bayan ya tabbatar da fitansa ya maida idon sa ya rufe tare da maida kafarsa yadda suke.
******
Washegari ta kama alhamisa, taka ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzabi me zafi, hawaye ne yake zubo mata tanasa hannun ta tana sharewa, haka ta wuni kwance ko sallah zaune take keyi, bayan anyi sallar la’asar ne tafara jin ana buga kofar gidan, tun a bugun farko tagane bakin Malam Baba ne, saidai dama tayi alkawarin bazata sake bud’e masu kofar ba, tanaji akaita buga kofar zuwa can taji shiru dan haka ta lumshe Ido tana me sauke ajiyan zuciya.
Saidai abun Mamaki ji tayi ana dukan kofar Kamar yadda akayi wancen karon, Bata gama dawowa cikin nutsuwarta ba taji Karan takun sa dan haka ta runtse Ido, jira kawai take taji karshe abun da suke nima yau din Bata ta karfin gudu ko kare kan ta dan haka sunayen Allah kawai take kira cikin ranta, jiya yazo kuma yau ya dawo, saidai abun mamaki wani murya tafara jiyowa wadda bazata manta ta ba cikin kunnen ta, shine ya cire min kofar? kanta ta tambaya tare da kokarin tashi zaune…..
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4ohdpom4UjFUX3yaUb5Hl
BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 18- 20
Lumshe Ido yayi sannan ya bude su akanta ya kalli yadda ta cukuikuye rigar sa, idonta ya kalla inda yaga tsoro karara acikin kawayar idonta, har yanzun hannun sa na akan kafarta dan haka ya ida jawota, ittako Unaisa kara kama rigarsa tayi har ta kaiga buturan rigarsa budewa dan gaba daya ta cukuikuye rigar, idon ta yabi da kallo bayan kafarta sun dira akasa, wani irin dan kuka take sake bada sauti a hankali.
Shikuwa lukitan kallo ya bita dashi hango kawar idonta kwance da farin ruwa.
Dauke ido Modibo yayi daga kalon yace, ” me Kika ce?, maimaita inji,
Cikin sauri tayi kada da kanta, ganin haka ya kalli fararan hannun ta da take rike tam da rigarsa yace, ” kalli abun da kikai, wata kila kin manta hakan be dace ba.
Cikin sauri ta saki rigar tasa tare da kallon tafukan hannun ta, dan ita kanta ma San Bata san me take ba.
Juyawa yayi ya kalli likitan yace, bismillah.
Gani likitan na matsowa tafara dago hanun ta tana kokarin damkar sa Kamar yadda ta damki Modibo dan haka yai saurin dakatawa yana kallon Modibo”
Ke! Wuce amiki, Modibo ya fada cike da fada Umarni.
Ni ba’a min alura ai, ba’a taba min ba, ta yaya inaji ina gani in tsaya azurkud’a min karfe.
Jin tashin muryanta Modibo lumshe idon sa yayi, yayin da mutumin dake tsaye agefe yabita da Ido, sosai muryanta ta dauki hankalin sa, daker ya iya jurewa ya kalli Modibo yana fadin, ko za’a barta ne kawai sai a tsaya akanta tasha maganin?
A’a, lallai ne sai an mata alurar nan,
Babu inda ba’a ba mutum wuya ko a sa ya ji dadi a duniya, ko a lahira, akwai gidan wuta akwai Aljanna, dan haka ki ki matsa kusa tunkan raina ya baci.
Kuka ta fara sosai Yana kallon yadda hawayen ta ke jika ni’kabin dake fuskarta, idonta kawai yake gani yana jujjuyawa tare da hawaye, har yanzun bata motsaba.
Nine kikewa tsayayya?, Koda da yake Ina tunanin kin dauka ni tsaranki ne, tunda naji kin kirani da Modibo, wlh idan baki tsaya aka miki alluran nan ba nad’eki zanyi, domin Babu gidan Sarki da za’a ce babu mari da ankwa, ko babban Mallami mai tarbiya, idan ya fi karfin iyaye, sai mallamai ko Sarakuna, dan haka ki shiga hankalin ki.
Wannan lokacin Unaisa bata iya dagowa ta kalli Dattijo ba, hannunta tasa ta fara share hawaye tare da gumi, ahankali ta fara takawa har ta isa gabanutumin da ya riga ya gama saita allurat sa, hijabbin ta ta dan daga kadan sannan ta juya ta rike gadon tare da runtse idon ta, tunkan alurar ta shiga jikinta ta saki wani gitattancen kara wadda yasa Modibo dafe kansa, daker aka samu akayi daya, zuwa wannan lokacin Unaisa shashakar kuka take, daga waje suke jiyo dariyar Magaji da Muftaho, shiko Modibo da kallo ya bita kawai, harta haye gadon ta kwanta, dakin ya rage daga Modobo sai Unaisa, har yanzun dariyar kukanta Magaji keyi yayin da yake fadin, ” aina dauka Bata san inda ke mata ciwo bane take zama ita daya,
Modibo ko kukan ta yaji ya dame shi dan haka ya karasa gaban gadon kallo ya bita dashi yadda ta takure guri daya tana cigaba da kuka kasa kasa, sandarsa ya jingine jikin gadon sannan ya rankwafa kanta, ya isa, ya fada ahankali, ganin batasan yanayi ba ya sake cewa, sannu ko?
Wannan karon yi tayi Kamar me birgima Kamar dai irin ya dameta dan haka ya danyi murmushi kadan sannan ya kara rankwafawa sosai Ina jinki menene gaya min mgn.
Ni ku fita daga cikin rayuwa ta, wannan ai zallici ne, kune kuke sakamin rashin lafiya, da kun daina zuw zan warke, ban iya zama da kowa ba, kuma ni……
Hannun sa ya sa asaitin bakin sa yana fadin, shiiii, banson shirme da shiririta, mgnr ki ba yawa ba dad’i’ kije ki koyo mgn Hajiya, ko kuma kishirun kawai dan naka kamar Shirin ma yafi, kinfi hankali alokacin ba ki kayi shiru, kuma kinfi kama da mace me mutunci idan Kika rufe fuskar ki.
Itako Unaisa banda share hawaye babu abun da take, ahankali Modibo ya juya shiga bincike adakin, tana jinsa duk abun da take, bude budewa yai tayi komai saida ya bude bayan ya gama kallace sirrin dakin ya fara takawa ahankali har ya isa gaban ta, sandar sa ya jingine jikin gadon sannan yace, ” mgn zamu yi, aunty na, kinga abu na farko dai baki da lafiya, bedace abarki ke daya ba, kuma mu dukan mu maza ne, dan haka ki tashi muje dake inyaso idan kinji sauki saina maido ki.
Cikin sauri ta girgiza Kai, kallonta Modibo yayi sannan yace, ” to meyasa aunty, ganin tayi shiru ya daga kafadar sa tare da fadin shikenan, amman zan nuna miki kibiyar ajali sulke baya tare ta saita Kai, karfen sa ya dauka cikkin sauri ya fice adakin, Kai tsaye yai waje yayin da Suraj da Magaji suka leko fuskarsu dauke da dariya, kallon ta kawa sukayi suka wuce.
****
Unaisa shigo mana.
A’a Dada kizo muje waje kiji wata mgn”
A’a ki gaya min anan mana shigo zo zauna.
Waigawa tayi ta kalli bayanta nidai Kizo muje waje.
Tankad’en garin tuwan da take ta aje akasa tana fadin muje.
Karkashin wata bishiya suka shiga suka zauna sannan Unaisa tace, ” Dada wannan mazan ne na kwanaki suka dawo….
Da yaushe?, badai su tabaki b ko?
A’a Inna, amman ni banason suna shigo min suna takura min Dada suna sakani rashin lafiya.
Cike da damuwa Dada tace, dakata Unaisa, da wacce suke zuwa?, me maza balikai suke zuwa yi a cikin gidan mu, wannan Sam be dace ba, lallai akwai wani abun da suke shiryawa, su nawa ne unaisa.?
Cikin kuka tace ni fa Dada har bana iya kirga su, bansa daga inda suke ba, kuma suna da yawa sosai, mutun daya daga cikin su yana tilastani tare damin fada, dayan kuma yana hararana koda yaushe Dada suna sudani sosai, yau kuma sai na ganshi da wani mutum wadda shine ya fara shiga rayuwarta, Dada wai kinsan me?
Cikin tsabar damuwa tace saikin fada.
Dada wai wani acikin su cewa yayi zai daukini ya kaini cikin dangin sa, dan Allah Dada karki bari hakan ta kasance, wlh Dada bazan iya rayuwa da kowa ba, bare inshiga cikin wani dangi, ban iya mu’amala da kowa ba, kuma bana iya bacci a ko Ina, idan ba dakin Innawuro ba.
Jawota Dada ta yi ta rungume cikin jikinta, tana fadin, nima nan ai bazan iya bawa kowa ba ke Unaisa, ko zamu rabu ba irin wannan rabuwar zamuyi ba, rabowa ce zamuyi irin wacce zanyi farin ciki, bama niba har Innawuro da Baffa, bazan taba yadda arabani dake ba, inda wannan ne ki kwantar da hankali ki, akan me zan yadda a tafi da ke inda zaki zama baiwa, kiduba irin motucin da suke yawa aciki, ke da gani kinsan manyan mutane ne, kuma masu kudin nan ba wani kirki ne dasu ba, akan me zan turaki cikin wata Sabuwar duniya, da haka Dada taita rarrashin Unaisa harta samu ta wuce gida.
******
Modibo zaune saman wata kujara ta alfarma, shikadai ne acikin katon falon daya gaji sabo da haduwa, sanyin AC ne ke ratsa jikin sa, saidai jinsa yake duk zuciyarsa babu dadi, idon shi yariyar kawai yake hangowa tana zaune ita kadai cikin wannan kuntaccen gidan, iskan hadarine ya taso, duk da cewa shin falo yake amman be hanasa jin yadda iskar hadarin ke tada kasa ba, tunanin Muftahu ne ya fado masa da yace, Yana son yariyar, tuna kalamin Muftaho hankalin sa ya dauke daga jiyo iskan hadarin, acikin ransa yake fadin, idan har ya kasan ce da gaske Muftahu sonta yake toh Suraj kuma fah?, Jimmm yayi zuwa can yace zasu fi dacewa da Suraj domin shiya dade acikin sonta kuma harya iya jure tsayon lokaci na bibiyan ta sabanin Muftahu da bejima da sanin ta ba, duk cikin zuciyarsa yake wannan tunanin yayim da ya tsinci kasan da fadi afili, ” Suraj naso Muftahu na so, wa zan dakatar aciki? Koda dai bahaushe yace dan ganin bakin hadari ba’a zubar da ruwan buta, sai awannan lokacin yaji saukan ruwan saman tare da kankara, ruwa ne ake me karfi take yaji ya tuna da ita, afili yace Allah sarki, waigawa yayi domin neman daukan sandar sa, ganin bata kusa dashi ya dauki wayarsa yana kiran Magaji, saidai harta katse be dauka ba dan haka ya Kira Muftahu, Nan danan saigashi ya shigo hannun sa cikin aljihu.
Muftahu ka bani sadar nan inason zan fita.
Modibo ana ruwa ne fa”
Eh kabani da sauri.
Juyawa yayi zuw can sai gashi sun dawo tare da Suraj, Suraj din ne ke fadin, Ina zaka ne da yamma haka?
Suraj hankalina ya koma gidan yariyar nan, ji irin wannan ruwan da akeyi gashi Bata da lafiya ita kadai acikin gidan, ko wanni hali take ciki yanzun?
Ba dadi kam amma daka Bari sai gobe.
A’a Maftahu muje yanzun mu dawo.
Toh ai ni inda Magaji yasa kafar taka ce bansani ba, duk na duba bangani ba.
Lumshe Ido Modibo yayi, bangane baka gani ba, inashi Magajin yake?
Magaji yafita tun dazo fa.
Cike da bacin rai Moddibo yace, ina yaje??
Bansani ba yadai cemin bari yaje ya dawo.
Shiru Modibo yayi yana ciki da bacin rai, ba fitan sa bane ya bashi haushi illah karfen da yasan sune kafa agareshi amman be barshi kusa dashi ba, fushi da zafin zuciya yasashi mikewa…
A’a Modibo Yaya kuma ka taka kafar, bayan kasan ace karka taka ta.
Muftahu ya kalla batare da yacewa Suraj komai ba yace Muftahu muje kawai……
[11/20, 11:18 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 21- 22
Cikin dingishi yake tafiyan yayin da Suraj da Muftahu sukayi saurin kamashi, rikeshi sukayi yayin da Suraj yace, amman dai kasan yadda ‘kafar nan take maka ko?, yanzun ne fa aka samu aka samu kanta, kuma ya bada sharadin ko kaji dama kada ka taka ta….
Ganin Modibo yana kokarin d’ingisawa yasa su kara tareshi da saurin su, kowanne fuskar sa dauke da firgici, muftahu ne yai saurin zuwa ya dauko motar yayin da Suraj ya taimaka masa har suka fito harabar gidan, Nan danan Suraj ya bude motar yayin da Modibo ya shiga gaba, Suraj ma zagawa yayi ya zauna a mazaunin driver shima Muftahu bayan motar ya zauna domin yanayin Modibo a yau ya basu Mamaki, bayan sun dauki hanya ma kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Modibo ma rufe idon sa yayi kawai tare da kwanciya jikin kujerar Motar.
Sannu ahankali suke tafiya sabo da ruwan saman da ake shekawa, tafiyan minti 30 ta kaisu kofar gidan, ganin Modibo na kokarin sauka Suraj yace ka zauna bara na dubo ta, kafin Modibo yace wani abu Saraj ya hangi ta tana tahowa, dan haka ya rike hannun Modibo yana fadin kaga gatacan ma tana tahowa.
Acikin ruwan nan?, Modibo ya tambaya.
Sauka Suraj yayi da saurin sa, ganin Suraj yasa ta tsaya cak tana kallon sa, saidai shi ko kada batajin tsoron sa domin ya jima yana zuwa gurin ta, kuma be taba matsa mata da karfi da yaji saita bude fuskarta ba Kamar yadda wadda suke Kira da sunan Modibo ke yi.
Suraj ne tsaye agaban ta cikin tsareta da kallon yace, daga Ina kike?, Ido yabita dashi tsayon lakaci batace komai ba, ganin yayyafin da ake danyi a yanzun yana jika su yasa shi saurin fadin, ” toh kizo ga Modibo yazo duba ki hakawai yana zaune ganin wannan ba’kin hadarin ya matsa sai yazo ya ga halain da kike ciki, kinsan meye tunanin sa?, ganin ba amsa zai samu ba yaci gaba da cewa, ” be taba rayuwa cikin irin wannan gidajen naku ba, atunani sa be yadda da ingancin ginin ba, sannan kuma Yana ganin cewa ke kadai ce a cikin gidan dan haka yake tausaya miki, yau na tabbatar lallai Modibo na tsananin tausayin ki tunda ya fito a irin wannan lokacin, ni abun da nake so dake ki bashi hadin kai, ki zama karkashin kulwarsa, Ina me tabbatar miki zai kula dake fiya da tunanin ki domin yayi mun gani”
Idan akwai abun da Unaisa tafi tsana a rayuwarta be wuce mgnr tabar dakin Innawuro ba, dan haka ma wannan lokacin ji take Kamar ta make Suraj, dan haka ta shiga tafiya kawai tana kokarin kasarawa gida.
Bayanta Suraj ya biyo yana fadin toh kije Modibo na mota yana Kiran ki.
Cak ta dakata tare da runtse Ido acikin zuciyarta tace, me ya dawo yi?, Ba tasowan hadarin nan ya wuce ba, nagaji da wannan zirga zirgar gaskiya.
Ganin ta tsaya Suraj yace, Muji ko?
Ba yadda ta iya dole ta fara takawa zuwa gurin motar su daya tal da sukazo da ita, domin tasan ko Bata tsaya va kota hadin yaye ne indai wancen motunin ne saya shiga gidan, Suraj ne ya nuna mata gefen da yake dan haka ta zagaya ta tsaya gaban kofar da gilashin sa yake rufe.
Ahankali taga gilashin nayin kasa dan haka tai saurin yin kasa da kanta, ajikin ta taji kallon ta yake yayin da hakan yasa ta duk taji ta daburce.
Daga Ina kie?
Cikin dakarkiyar muryan sa yai mata wannan tambayan dan haka taji Muryan sa ta daki dodon kunnen ta, wannan karon ya dawo da takama, tafada azuciyar ta, kafin ta dago idonta ta kalle shi.
Ba kallona nace kiyi ba, kuma bana son shiru lallai yan Ina son kimin mgn, daga Ina keke cikin irin wannan yanayin kina awaje.
Wasa ta fara da hannun ta dan haka yabita da Ido tsayon lokaci sannan yace, ” Ina duka fa.
Cikin sauri ta kalle shi dan haka ya kara cewa eh da gaske Ina duka, idan na sake miki tambaya biki amsa min ba wlh saina dake ki, Ina jinki daga Ina kike?
Cikin sauri ta hada kanta da gefen window motar hakan yasa tai kusa da kunnen Modibo ahankali tace, Ni kaine ka bani tsoro.
Lumshe idonsa yayi jin muryanta cikin kunnen shi batare daya bude ba yace, meyasa nake baki tsoro aunty na. Sahima kasa kasa yai mgnr sosai, sai dai duk da haka suraj yaji abin da ya fada.
Bana son kacewa sai kaga fuska ta.
Lumshe Ido ya sake yi tare da fadin, sai kuma me?
Sannan kabar cewa zaka tafi dani.
Inajikin sai me kuma?
Kubar zuwa gaba dayan ku bana so.
Haba dallah?, da gaske mubar zuwa?
Eh.
Toh inajin ki sai kuma me?
Ni dai kubar zuwa kawai idai kuna zuwa ciwona bazai warke ba.
Hada dan Allah?, sabo dame?
Ni bazanbar dakin Innawuro ba, bazan iya bacci ko Ina ba inba gadon uwata ba, ban saba da kowa ba kuma bazan iya rayuwa da mutane ba.
Haba?, da gaske ko wasa?
Da gaske nake.
Toh Allah ya jikan ta, ya Kai haske kabarin ta, sannan nima zan sata cikin addu’ata, Allah ya jadda rahamar sa gare ta.
Lumshe Ido Unaisa tayi tare da fadin, Amin nagode
Ajiyan zuciya Modibo yayi sannan ya kara kasa da muryan shi tare da karkatowa gare ta, duk da cewa Yana zauna cikin mota, ahankali yace, ” barin inyi mgn biyu zuwa uku dake, ni ban tabajin Ina son ganin fuskarki ba, dan ni bashi ne agaba na ba, kuma kema dai banda abun ki inda Ina son ganin fuskarki da tuni nagani, dan cire wannan kyallen ba abu bane me wuya awaje na, Koda kikaga kwanaki nacewa Magaji ya danna minke ya cire, bayi hakan ne nagane kinajin mgn kokuwa kurma ce, ganin fuskarki bashi ne abun da ya kawo ni ba, nazo in taimake ki ne ko aya kike.
Shiru kawai tayi tana wasa da hannun ta, tare da addu’a Allah yasa karya kara mata duk abun data lissafa masa.
Jinsa tayi ya cikaba da fadin, kinsan mene?, Ina son ki fahimce ni da kyau, dan uwa nake son ki daukeni ba ba abokin gaba ba, idan Kika bani hadin kai komai duk abun da zanyi sai da yardan ki, Ina son kisa azuciyarki nima Innawuro ce mahaifiya ta, bana neman komai agurin ki, baki da abun da zaki bani, asalima zuciyata a kulle take, amman naji araina lallai Ina son in kaiki cikin mu, domin kishiga ciki wata rayuwa ta daban, barin kwad’aita miki wani abu, ki kwatanta inda zan kaiki da aljanar duniya, Amman bawai dan dukiya, kudi, mulki, ya ko saurauta ba, duk Basu bane hujar da tasa na Kira inda zan Kai da aljanar duniya, nakirashi da hakan ne saboda muna da soyayyar dangi, farar sura tare da farar zuciya, amman baxa’a rasa bata gari ba.
Sosai Unaisa taji ta samu nutsuwa ta kallin sa, babban abun barin cikin ta da yace komai saida yardanta, muryan sa ya sake dukan kunnen ta.
Aunty zaki bini muje??
Kanta ta kirkiza har yanzun bakinta Yana saitin kunnen sa.
Komawa yayi ya jingina da kujer motar tare da lumshe Ido sannan ya dago ya kalleta tare da fadin shikenan kije abun ki.
Juyawa tayi batare da tace komai ba, murmushi Suraj yaja tare da fadin, Allah yayi abin inji mafadin auren sa.
Wani ‘Kayataccen murmushin Modobo yayi, tare da fadin, “banda abin ka dawa Bata gama cin wutaba ai fara batayiwa ‘yar uwar ta barka.
Ai naga kamar tayi mgn ne yau.
Da gira Modibo yabawa Suraj amsa cikin sauri Suraj yace me tace ne?
A’a mgnr muce nida ita.
Dariya Suraj yayi har hakoran sa suka bayya domin aganin sa narasan Modibo nasarsa ce.
Har suka kamo hanya Suraj murna yake hakama Muftahu farin ciki fal cikin sa, afalo suka samu Magaji yayin da suke kokarin shigo da Moddibo dan kin yadda sukayi ya taka kafar Kamar yadda yaso.
*****
Ina kukaje nadawo ban sameku agida ba.
Zama Modibo yayi ya lumshe Ido Yana jin Suraj na fadin, “Ina ka aje masa sandarsa, sanin kane cewa dole dasu yake amfani, ko bazai fita ba ai ya shiga toilet, amman dan ranshin hankali saikai nisa dasu.
Kashhh, wlh na manta Suraj, na manta na kaisu dakin sa.
Muftahu ne yace ai naduba duk dakin bangansu ba.
Sunanan gefen gado mana, Modibo ya kalla sannan yace, Modibo Sorry wlh mancewa nayi.
Ko Motsi Modibo meyi ba, idonsa lumshe.
Mikewa Magaji yayi ya fito dasu ya aje agefen Modibo, saidai tunkan ya cire hannun sa akan karfen yaji saukan wani gigitaccen mari akan kumatun sa,
Sosai Marin ya shigeshi, rabon da amai irin sa ya manta.
Suraj da Muftahu ne sukayi saurin rike Modibo wadda banda huci babu abun da yake yi.
Ahankali Suraj ke fadin, haba Mana Modibo, ka koma ka zauna kodan sabo da kafarka, Muftahu ma hakuri yake bawa Modibo daker ya koma ya zauna, Magaji kuwa yana rike da kumatun sa saidai ya kafe Modibo da ido, tsayon lokaci suka dauka a haka sannan Magaji yasa kafarsa ya daki karafunan suka watse a kasa sannan ya dauki key din mota ya nufi fita a fusace.
Suraj ne da Muftahu suka fara fadin Ina zaka?, Modibo ne ya daga masu hannu dan haka babu wadda ya sake cewa komai.
Sunaji ya tashi Mota yabar gidan.
Lumshe Ido Modibo yayi sannan ya dauki wayar sa ya shiga typing, bayan ya gama ya aje wayar a gefen sa ya lumshe ido, befi minti minti goma da aji wayar tasaba saiga Magaji ya dawo hannun sa cikin aljihu ya tsaya a tsakiyar falon tare da fadin, ” Kai hakuri nayi suskure, daganin inda yai mgnr kasan tursasa shi akayi.
Adaren ranar ma Suraj ne da Modibo kwance wani dakin bacci, hira suke duk su biyun suna Kan gado, zuwa can Modibo ya daga waya ya kira Magaji da Muftahu, Nan danan sai gasu,
Tashi Modibo yayi zaune batare da ya kalli kowa ba yace”
Ina son in muku mgn akan yariyar nan ne, Ina son in dauketa muje da ita gida, abin da nake son kowa cikin ku ya sani, ni na dauki yariyar nan ne matsayi biyu kacal, kanwa ta jini sannan intaso Ina iya zama uba agare ta, idan nace uba, Ina nufin zan iya bada auren ta, sannan ni babu ruwana da fuskarta ko wani abu nata, rayuwarta kawai nake son taimakawa, dan haka banson wani cikin ku ya nunawarwa yariya irin wannan abun dana lisa.
Yauma kamar kullum motocin sune jare suke shiga cikin Unguwar su Unaisa, kofar gidan Malam Baba suka fara tsayawa yayin da Modibo ya fito, wannan karon cikin rakiyar Muftahu da Suraj suka shiga cikin dakin me maganin, Magaji kuwa daman har yanzun kunbure kunbure kawai yake yi.
Bayan an gama duba kafar tasa ne Modibo yace, Baba daman Ina son inma wata magana.
Toh toh inajin ka Ranka ya dad’e.
Kallon Muftahu da Suraj yayi sannan ya juya ya kalli Malam Baba, Baba akwai wata yariya ana tana makotaka da ita, na samu labari akan yariyar cewa bata da kowa, kuma ita daya take rayuwarta a inda naji ma duk cikin Unguwar nan babu wadda yake hurd’a da ita….
Gyara zama Malam Baba yayi sannan yace, ” Wala Habaru kake mgn akai kenan.
Eh haka akace sunanta.
Jimmm Malam Baba yayi sannan yace me kake so sani game da ita?
Ni kawai Baba Ina son in dauki yariyar ne inriketa sabo da naga bedace ace ‘yamace karama haka na rayuwa ita daya ba, inason kuyi min izini in tafi da ita, idan kuma tana dawani dan uwa duk inda yake zanje in nemo izinin tafiya da ita cikin dangi na.
Jimmm Malamin yayi zuwa can yace, ” ai wannan yariyar da kake gani dangin ta nanan fal cikin wannan layin da kake gani, jikan Malam Bawace, kodaga Ina ka tsaya cikin garin nan kace gidan Malam Bawa za’a kawo ka har kofar gida…
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16 59 91: BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 23-25
Cikin tsanini Mamaki Modibo ya kalli Malam baba, bama Modibo kadai ba har Suraj da Muftahu kallon sskabi mutumin dashi.
Modibo ne yace, ” Baba kana nufin tana kusa da ‘yan, uwanta to meyasa zuka banzatar da ita?
Jimmm malam Baba yayi tsayon lakaci sannan yace eh to, ba’aji abakina ba, Amman dai koma menene akwai Malam Ayuba shine karamin kanin Innawuro Yana raye shi yake da damar baka Wala Habaru ko ya haana ka, amman shawaran da zan baka ka rabu da yariyar nan inda ka ganta.
Meyesa kace haka Baba?
Toh nidai abinda nafi gani kenan, sabo da bama muba mutunan unwar nan ba, danginta ma gudun ta suke.
Jimmm, Modibo yayi zuwa can yace, ” nidai Baba banajin akwai abun da zai sani in janye kudirina, a takaice dai yanzun Baba ka hadani da iyayen ta.
Cikin wani irin yanayi Malam bawa yacewa Modibo toh shike Nan duk lokacin daka shirya kamin mgn saina kaika har gidan.
Aini Baba Koda yaushe shirye nake, ko yanzun ne ma muje.
Eh toh inaga Bari mu Bari zuwa gobe, dan yanzun da wuya a same shi agida wata kila ya tafi kiwo.
Dahaka sukayi Sallama suka wuce awannan karon Basu shiga gidan Unaisa ba, sosai hakan ya Basu Mamaki ganin Modibo bece su shiga ba.
*****
Washegari Kamar yadda malam baba yace, Modibo tare da mutanen sa suka sake shiga cikin Unguwar, gidan Malam Baba suka fara zuwa suka dauke shi sannan suka wuce gidan su Malam bawa.
Motocin sune jere kofar gidan Malama Bawa, Nan idon mutane da hankalin su ya dawo Kan motocin baki daya, kowa Mamaki yake me ya kawo wannan zuka zukan motocin kofar gidan Malam Bawa.
Jama’a da dama tsayawa sukayi domin ganin ikon Allah yayin da wasu ke tambayar lafiya, saidai Basu dame amsa masu.
Balam Baba ko Sallama yayi akofar gidan, wata yariya ce ta leko nan ya sanar mata tamai Sallama da Malam Ayuba.
Ba jimawa ya fitonganin manyan Motocin yafara binsu da kallo tare da bawa Malam Baba hannu suka gaisa.
Modibo ko wani mugun haushin Mutumin ne ya kama su, ganin tsakanin gidan su da gidan yariyar babu wani nisa amma aka barta ita daya.
Cikin gida Malam Ayuba ya koma ya dauko katowar tabarma ya shinfida ganin haka Modibo ya sakko shida Suraj suka zauna suka gurin.
Bayan sun gaisa ne Malam baba yaiwa Malam Ayuba bayani, saidai tun kafin Malam Baba yakai ga rufe baki Malam Ayuba yace mun bashi, ya tafi da ita daga nan har duniya ta shi.
Malam Ayuba beyi Mamaki ba jin wannan furucin daga bakin Malam a yuba , saidai Suraj da Modibo sunyi matukar Mamaki musamma da sukaji yace har Duniya ta tashi ma.
Nan danan idon Modibo ya kada yayi ja, yanzun ya fara fahimtan wani abu game da rayuwar yariyar, godiya yayiwa Malam Ayuba sannan yaciro kudi ya mika masa, godiya sosai Malam ayuba yayi sannan ya rakasu har bakin motar tare da tambayan Modibo yau zai wuce da Wala Habaru?
Zama Moddibo yayi sosai acikin motar tare da fadin” a’a bayau ba, Ina Amasa magani ne yanzun, dazaran nagana amsan maganin zan koma, amman insha Allahu duk randa zan tafi zan kawota tayi Sallama.
A’a basai kunzu ba kuje abin ku.
Sosai Modibo ya kara shiga Mamaki, tsintan kansa yayi da tamyan Malam Ayuba Yaya sunan yariyar ne, budar bakin Malam Ayuba sai fara dabur dabur daga karshe yace sunanta ya shige masa.
Jikin Suraj ne yayi sanyi sosai, dan haka bayan sun sauke Malam Baba yaso su tattauna zancen da Modibo saidai Modibon yaki hakan, nunawa yayi beson mgnr tare da komawa Kan kujerar ya kwanta, Koda suka koma gidama cewa yayi kansa na ciwo yake masa, dan haka Suraj ya shiga damuwa sosai, gashi yaso yasa idon sa akan yariyar sai dai Modibon yaki yadda hakan tsayon sati uku suka kwashe sai dai suke su amsa magani su wuce abun su, sosai hakan ya damu Suraj tun Yana boyewa har abun ya bafara gagaran sa, Muftahu ma can kasan ransa yake jin son sa yariyar a idon sa.
Magaji kuwa yanzun be cika biyo su ba saidai kullum su barshi a gida.
Yauma kamar kowacce alhamis Modibo zaune gaban Malam Baba bayan ya gama shafa maganin yace, ” Ina ganin yanzun kuna iya komawa gida.
Alhamdulillah Modibo yafada sannan
Sannan yace kenan Nan da sati daya Ina iya aje sandar?
A’a kadan kara riketa har bayan ka koma da sati biyu, lokacin ta cika wata biyar kenan da fara magani guri na, insha Allahu babu matsala da zata kara tashi.
Cike da gamsuwa Modibo ya amsa sannan suka masa Sallama suka wuce, yauma Modibo bece zasu gun yariyar ba, dan haka Suraj yace yau bazamu leka gidan Nan ba kuwa.
A’a kawai Modibo yace, sannan suka wuce gida, tun daga wannan ranar Shirin tafiya kawai suke tare da tattare duk wani abu da suke bukata.
*****
Muftahu ne zaune shi da Modibo saman Mota, suna hira ahabar gidan su, Magaji ne yace, gobe war haka muna gida, bayan dan hutun kwana biyu kowa ya kama harkokin sa, Ina tabbatar maka na koma gida bazan sake yin tafiya ba.
Mum fa zaunu, gashi wadda mukeyi Dan shi din ma besan munayi ba, Nina fara cewa zanyi jinyan sa amman ya iya daga hannun sa ya mare ni.
Ya sani Mana, Yana sane dakomai, kai ai laifi ka masa, kawai dai ranar ka vata masa rai ne ba wani abu ba, kuma ai kasan halin sa da fushi.
Duk fushin da zaiyi saiya mare ni?, kawai dai yaci albarkacin masu albarkan ne harna bashi hakuri, kuma bakasan wani abu ba?
Eh inajin ka.
Muna komawa gida zan dawo garin nan.
Me zakayi anan kuma ?
Wannan yariyar zan dawo gunta, idan har zata bani hadin kai auren ta zanyi.
Wacce yatiyar kenan.
Wala Habaru, Magaji ya fada Yana murmushi.
Runtse Ido Muftahu yayi, lokaci daya yaji wani zufa na karyo masa kenan Magaji ma sonta yake, Koda yake babu Mamaki domin yariyar daka ka kalleta ko cikin Hijjabi kasan zatayi kyau, duk da ciwa ta taso cikin talacin da yayi mata katutu, amman tafiyarta ma abun kallo ce, gata wani irin kyan sura na musamman, hakama tafukan hannun ta da kafarta kawai abun kallo ne, hakika ba namiji da zai kalleta beji Yana sonta ba, daker Muftahu ya iya fadin, ” ai da ita zamuje.
Ina zamu da ita?
Can gida Mana, tuni fa Modibo ya nemo izinin tafiya da ita gurin kanin maaifiyar ta, kuma ambashi daman tafiya da ita, sannan kuma nifa tuni na gsyawa Modibo Ina son yariyar.
Da sauri Magaji ya Mike kenan kuna min zagon kasa Kai da Modibo, akwai abun da kike shirya min, kuma ma tayaya Modibo zai dauki yariya ya tafi da ita batare da izinin kowa ba, nifa abun nan nasa ya fara isata, Yana yanke hukunci kansa tsaye batare da izinin kowa ba daga gida, cikin sauri Magaji ya nufi dakin Modibo yayim da Muftahu ya bi bayan sa, kusan atare suka shiga, Modibo waya yake adaidai wannan lokacin, Dan haka sukayi tsaye bayan ya sauke wayar kallon su yayi yace”, Lafiya kuwa?
Ahakali Magaji ya matsa kusa da Modibo ya zauna agefen gadon yayin da Modibo yake tsaye agefen gadon.
Ahankali Magaji ya shiga fadin, ashe ka samu an baka damar tafiya da yariyar nan?
Eh an bani, gobe insha Allahu zamu tafi da ita,
Kansa ya Dan shafa kada daga goshi zuwa keya sannan ya kalli Muftahu yace, ” toh meye kuma ka biyo ni, kaje Mana, mgn zamu yi.
Ni ba abun da ya dameni da kai.
Da kallo kawai Modibo ya bisu, gani yayi Magaji na hararan Muftahu dan haka yace wai meye haka?
Modibo wai biyoni yayi Dan nace zan gaya maka Ina son yariyar nan.
Murmushin Modibo yayi har hakoran sa suka bayyana sannan yace, ” shine kake koran shi?, abukin cin mushe fa ba’a boye masa wuka, taho ka zauna nan gurin Muftahu, tahowa yayi ya zauna kusa da Magaji, kamar yadda Modibo ya nuna masa sannan Modibo ya kallesu ya sake yin dariya yace, ” karkuyi fad’a dan kun hadu ason abu daya, inace da aure kuke son ta, kuma ai matar mutum kabarin sa, sannan akwai wani abo wadda duk ku biyun nan baku sani ba, idan baku manta ba antaba ce mana wani yayi nacin bin yariyar harna tsayon shekara daya amman bata saurare shi ba, toh ba kowa bane wannan mutumin illah Suraj.
Duk su biyon Modibo suka kallah, yayin da ya kara tabbatar masu da lallai Suraj ne, sannan ya kara da cewa, ” amman duk da hakan wannan ba wani abu bane, abun da ruwan zafi ya dafa idan akayi hakuri ruwan sanyi ma saiya dafa, domin Inda rabon kura a takobi sai a sayar asai mata akuya, ita mace Kamar allura ce acikin ruwa, me rabo ka dauka.
Cikin sauri Magaji ya tashi ya fice adakin, yayin da Muftahu yai saurin ruba masa baya, harabar gidan Magaji yaje ya tsaya, sintiri kawai yake tare da jujuye zantukan Modibo, kenan Modibo Yana nufin duk mu ukun muje mu taka rawar mu, kalaman Modibon yaita tunawa har tsayon wani lakaci, shima Muftau irin wannan halin ya shiga, yayin da Suraj ko bema san me suke ba.
Modibo ma zurfi yayi atunanin yadda zasuyi bayan sun koma gida, yayin da yake girmama farin jinin da yariyar ta samu agarin su Magaji.
Misalin farfe bakai na safe duk sun gama shiri, Dukkan su manyan kaya ne ajin su, na shadda yar gaske, wadda aka mata ado da aiki na zamani, kowane sanye da malum malum, amman banda Modibo sabo da kafar sa.
Mota uku kawai suka dauka domin yiwa Malam baba Sallama, sannan su dauko yariyar, gidan Malam Baba suka sauka bayan sunyi Sallama suka nufi gidan Unaisa.
Duk da cewa sunjima basuzo ba saida gabanta ya fadi, domin yanzun hankalin ta ya fara kwanciya, tahowa tayi ta bude kofar, Modibo kadai tagani, Ganin ta bude kofar yasa kafar sa ciki.
Jikin kitchen din ta tsaya Kamar yadda ta saba.
Sallama Modibo yayi bayan ta amsa yace, gaishe ni?
Daker ta iya bude baki tace Ina kwana.
Shima cike da takama ya amsa sannan yace, kin dade baki gammu ba amman kikasa tambayan ko lafiya, koda yake nasan murna ma zaki yi.
Kawar da kanta tayi, Dan haka Modibo ya bita da kallo sannan yace, ” kina jina na?, Kwanaki naje gidan ku na samu baban ki…..
Da saurin ta ta kalleshi tare ta katse shi da dan karfinta, ni bani da gidan da ya wuce wannan, sannan bani da wani baba da ya wuce Baffah kuma ni Baffana ya rasu.
Kallonta yayi sannan yai ajiyan zuciya tare da fadin, ” Allah ya jikan shi, amman bana son ina mgn a katse ni, ki saurareni kawai.
Nan danan yaga idonta ya koma launin ja jawur, duk da haka saiyaci gaba da cewa.
Baban ki Malam Ayuba yabani ke halak malak intafi dake ki zauna karkashin kulawata idan kin samu miji na aurar dake…
Bazani ba, kuma na gaya maka banda wani uba aduniyar nan, karka kara dangantani da wasu.
Ni kikewa mgn haka?, toh Bari kiji dole zan daukeki ko kinaso ko baki so, yanzun yanzun nan kuma ba sai anjima ba, dan haka nake shawartan ki da kifito da kafarki ko insa adauke ki aka.
Zamewa tayi zuwa kasa, ta rushe da matsanancin kuka, bude baki tayi da murya sosai tana fadin, ” saidai ka fitar da gawata, wlh bazani ba, da kanka kamin alkawarin kace saida aminceata yanzun kuma kace ko inaso ko banso ba, sabo da angani ahaka?, bani da wata daraja?, ganin yadda take kurma ihu yasa hannu ya riko hannun ta, wani irin rawa yaji jikin ta nayi yayin da tashiga kwalawa Dada Kira tana fadin Dadana kizo kigani, zasu tafi miki da amanar ki, Dada!! Kizo dan Allah ban iya rayuwa ko ina, kenake gani kamar uwar data haife ni, karki bari a rabani dake, Dadda!! Kizo fa idan Kika jinkirta zakiyi kukan bakin cikin rasa inda nake, za’a tafi dani wata duniyar Dada!!
Irin wannan surutan Unaisa keyi cikin ihu ta karaji, tuni Modibo ya fara fadin, ya isa kanwata ki dawo cikin nutsuwar ki, ganin Kamar batajin sa yasashi girgizata, daker ta dan fara nutsuwa lokacin harsu Suraj sun shigo cikin gidan sabo dajin ihumta.
Bayan ta nutsu ne Modibo yace Kanwata wacece Dada?
Hanakali tace Mama tace?
Jimmm yayi sannan yace mamanki?
Kai ta saga masa, Modibo na kallon cikin idonta yace tana Ina yanxun, nan kusa take?
Amsawa tayi da eh dan haka yace tashi ki kaini gurin ta.
Cikin sauri ta mike ta nufi fita, bata tsaya jiransu ba sauri taitayi yayin da suka shiga mota har tai nisa sannan suka biyo bayan ta, ko kafin su karaso ta karya kwana aguje dan haka Koda suka iso babu ita, saidai sun gane gidan dan waccen lokacin da suka biyota Nan tashiga,
Kofar gidan suka faka motar su saidai tunkan sukai ga fitowa Dada tafito hannunta rike da itatuwa biyu.
A hankali Modibo ya bude gilashin motar sa, Sallama yayiwa da Dada Sallama dan haka tamaida masifar ta tare da amsawa tana fadin, ” kune kuka biyo min yariya?
Sakowa Modibo yayi daga cikin motar yana fadin, banje da niyar tafiya da itaba saida na nemi izini, dan haka bana kallona a mara gaskiya, kuma banta sanin ki kojin sunanki ba sai yau abakin ta, dan haka nace mata ta kawo ni gurin ki, ni yanzun gunki nazo dake zanyi mgn.
Haka nan taji kalamin yaron sun shige ta, Nan ta bashi dama ya shiga zauren gidan duk kudirin sa ya gaya mata, sanyi jikin ta yayi sosai, sannan kuma ta yaba da dabi,un yaron saidai duk da haka bata iya bada Unaisa ba. dan haka tace, “nafahim ce ka Modibo, amman wannan yariyar tana dangi, na uwa dana uba, ni nan da kake gani mahaifiyar ta ce tasha nono tabarwa mahaifina…
Katseta Modibo yayi da fadin, ” Amman meyasa aka barta ahaka bawani kulawa?
Ai nike ciyar da ita kuma nabiya mata kudin makaranta zaman gidan ne kawai me gidan ya hana, sannan dangi kowa yaki ta sabo da wani dalili nasu.
Wanni irin dalili ne wannan Mamma?
Jimmmm, matar tayi, sannan tace, ‘ a’a wannan dalilin sirri ne da bana iya gayawa kowa face mijin da yazama nata na aure, banajin zan iya bude wannan saiga mijinta.
Jimmm Modibo yayi sannan yace ton Mama har yanzun Ina Kan bakana duk danaji kina tsaye akanta, ina son kibani ita, domin inje in daura daga inda Kika tsaya.
Wallahi yaro bana iya ba bada ta, ni nan da kake gani banga abun da zai rabani da Itaba, na tsallake matsalolin kala kala domin cika alkawari dana dauka, kuma Ina son in cikashi shi.
Lumshe Ido Modibo yayi batare daya bude ba yace Yaya sunan ta to?
Sunanta *RAHMA*
Bude idon sa yayi tare da fadin, _*Rahma* maganin zugi_, mama kibani ita inje da ita kema ki bimu kiga iyayena.
Modibo inajin kunyan sake sanar dakai bazan iya bada Ita ba, idan kaga abun da zai rabani da Unaisa saidai in aure, wannan nasan na sauke amanar dake kaina ne.
Jimmm Modibo yayi sannan yace Mamah kenan idan aure ne zaki yadda?
Me zai hana, aure babu inda bekai Mutum, Suraj Modibo ya kallah sannan yace, Muje mama zamu dawo.
Sallama sukama mama suka fito, saidai duk jikin Modibo yai sanyi, banda bad’uwan gaba babu abun da yake, dan haka ya kasa daukan kafarsa ya daura amotar, tsintan kanshi yayi da kwantar da kansa saman motar cikin wani irin yanayi da baya Ina tantance shi, lokaci daya yaji ya diri dirice…..
[11/20, 11:16 AM] +227 90 16
BA LABARI
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 26- 28
Gaba dayan su bin sa sukayi da kallo, Suraj ne yayi karfin halin dafa sa tare da tam bayan Yaya akayi ne Modibo?
Dagowa yayi tare da shiga motar ya zauna, kowa tambayan sa yake amman ya gaza yin mgn, Hanyar gida suka nufa yayin da suka tarar da tarin motocin su suna jiran su, kowa cikin Shirin tafiya duk an gama zuba komai cikin motar, cikin gidan Modibo ya nufa daka kalli fuskarsa kasan Yana da damuwa sosai.
Zama yayi cikin falo, gaba dayan su su tambayan ta suke waishin me yake faruwa ne?
Daker Modibo ya iya fadin, matar takin amincewa, dana dage mata saitace saidai in aure ne zai raba ta da yariyar, Ni ko azahirin gaskiya nafi son intafi da ita babu aure akanta domin ta samu kulawa ta data ammi mu, inason ta zamo wani abu, idan aka mata aure a yanzun Kamar an sata cikin matsala ne….
Me yasa kace haka Modibo?
Kansa tsaye yace saboda Batasan me rayuwa take ciki ayanzun ba, burinta kawai ta zauna ita daya tana ikirarin cewa adakin mahaifiyarta zata rayu harta mutu, nasan ko an mata aure yanzun bazata wani samu farin ciki ba, kaga fa inda take mgn daker Kamar intayi yankata za’ayi, naso na canza mata arayu amman matsawar ta tafi da aure akanta babu wani kulawa da zata samu daga gare ni.
Toh ai Modibo nima zan kula da ita sosai, Ina son yariyar kuma ko yanzun ashirye nake Dana aure ta, Ina da kyakyawan nufi akan yariyar.
Nasan haka Suraj amman duk da hakan dai nafi son tafi da ita ba auren kowa kanta.
Shikenan yanzun dai kana nufin gara mu tafi ba yariyar kenan?
A’a ba nufina kenan ba, Insha Allahu da ita zamu tafi, ko da auren ko babu, amman dai Kai me kake gani?
Nifa Modibo ko yau saina bada sadakin ta, wlh inason ta.
Shikenan, yanzun ina ga fasa tafiyan zamuyi, gobe sai mu koma, idan har zasu iya daura auren agobe zuwa jibi.
Afusace Magaji yace, ni gaskiya mutafi kawai, Abba nacen najira, kowa acikin gidan ya shirya wa zuwan mu, be dace suga bamu dawo ba.
Duk wadda ya tambayi dalili kuce masa Muftahu ne beda lafiya cewar Suraj, saidai tun Kan ya rufe baki Muftahun yace, a dai ce wani dan yawancin lokaci idan nai karyan ciwo toh ciwon yakan same ni da gaske.
Modibo da yasan me yasashi fadin haka yai saurin fadin toh ni ace nine banjin dadin
Magaji ne yai surin fita yayin da Muftaho ya rufa masa baya.
Modibo ko kokari yake kar Suraj ya fahimci su Magaji dan haka yace, ” su Kada suje gidam.
Da yamma Suraj ne ya shirya ya fita yayin da Modibo dasu Magaji suka zauna a gida, bayan fita Magaji ya samun Modibo cikin yanayi na tashin hankali yace, yanzun Modibo kana ganin ya dace mu tafi kawai da mata ba sanin iyayen shi?
Magaji ai tunda yace yaji ya gani babu matsala kenan.
Shikenan, yanzun daura auren za’ayi kenan?
Eh insha Allahu.
Tafdi lallai, Amman inda Abba mu ne kawai yaga anje masa da mata kawai ba BA LABARI yana iya tsinewa mutum, hakama ammi da Yadikko.
Ajiyan zuciya Modibo yayi sannan yace hakane Amman ai kasan kowa da ahalin sa.
Shikenan nadai kula kana karfafa masa guiwa.
Eh insha Allahu komai zaizo da sauki.
Shikenan Allah ya tai maka.
*****
Washegari sunje Kamar yadda Moddibo yace, maga ta fahimta sukayi da Dada inda suka yanke shawan gobe zasu kawo Sadakin ta sannan a daura auren nan take.
Bayan sun tashi zasu tafi Suraj ya nemi da Yana son mgn da yariyar, rokon sa Dada tayi akan cewa kwata kwata karya sako mata zancen aure domin Zazzabi na samunta da zaran taji zancen aure.
Modibo cikin mota ya koma ya zauna, Muftahu Magaji duk jikin su a sanyaye.
Sun jima suna jiran fitowan Suraj amman shiru, saida ya kwashe kusan awa biyu sannan ya fito.
Zuwa can ya fito yana share zufa, ya zauna acikin motar Yana sauke ajiyan zuciya.
Babu wadda yaiwa wani mgn har suka isa gida.
*****
Da daddare Suraj ne ya kasa bacci, dan haka ya tashi zaune tare dasa hannun sa ya Dan daki Modibo.
Tashi Modibo yayi zaune tare da fadin lafiya?
Modibo akwai abun dake damuna.
Meye shi?
Yariyar nan jiya naso ta bude min fuskarta ingani amman taki sam, duk zama da nayi gurin dazon ko kala bata ce min ba, gashi kuma ance da safe za’a daura auren.
Kashhh, Suraj kabar zancen ganin fuskarta, inace ahanta ka ganta kaji kana so?
Eh Amman gaskiya Modibo nafara wani tunani, idan ba ansan da wata akasa ba ta bude fuskarta Mana, kilama fuskar tata kesa jama’a ke gudun ta, ai Unguwar tasu cike take da samari kuma yariyar daidai da rana daya baka taba ganin ta babu ni’kabi, Koda ciwo take fuskarta rufe take ruf, kuma Modibo wani dalili ne zaiya dangin uwa dana uba su kitaa alhalin sun tabbatar ita d’in yar halak ce, kuma jinin su, sannan Modibo me zaisa mata da mazan Unguwar, yara da manya su dinga tsron wucewa Koda ta kofar gidan ne?, Dan haka nidai nafi ganin tana da swata siffa ne afuskarta me firgitarwa.
Shiru Modibo yayi cikin yanayi na sanyin jiki sosai, zuwa can yai gysran murya tare da fadin, ” Suraj kabar wannan tunanin, sheda ne kawai, kasa ma tana da wata hallita din, idan ka aureta kayi taimakon masulunci kuma zaka samu lada.
Kai ina gaskiya ni ina da ra’ayin auren kyakyawan Mace ne, dan haka inaganin gobe da safen kawai mukama hanyan.
Suraj karkayi haka, ka aureta inyaso saika aure wata inhar kaga Bata maka ba din, kuma ai mutane sun shaida yariyar nada kyau.
Toh ai kowa cewa yake ance, kuma kanajin abun da waccen matar tace, dangi sunkita saboda wani dalili, sannan daka bukaci ta gaya maka dalilin tace saiga mijinta kad’ai, dan haka nina lura wannan rufa rufa ne kawai ake, domin sai adaura auren afito ma mutum da mata tamkar dodonniya atunnin su dole mutum ya hakura, dan haka ni babu ni a wannan tafiyar nacire kaina aciki bazan auri gaibu ba.
Suraj nafi ganin ka tsaya ka nutsu kayi shawara da zuciyar ka dakyau, ada mun ce gobe da safe za’a daura auren mu wuce amman yanzun bari mu barshi sai zuwa jibi da safe lokacin ka kara nutsuwa da kyau.
Nifa Modibo kawai bani aciki, mikewa yayi yana fita daga cikin dakin yana surutai akan cewa shifa kawai ya janye.
Sabo da tunani ranar Modibo kasa bacci yayi, sosai ya kosa su koma gida kuma lallai Yana son su tafi da yariyar.
Washegari har misalin Tara na dare Modibo Suraj bece komai ba, Modibo ma bece masu komai ba har washegari, Magaji da Muftahu ko had’a Kai suka yi wannan lokacin, dan Basu san wani hali ake ciki ba akan mgnr, su dai kawai sunga ba’aje ba Kamar yadda aka ce.
Washegari da Safe misalin 9 Modibo ya fito falon, Suraj Magaji da Muftahu duk suna zaune, kowa da kalan tunanin sa, Tsaye Modibo yayi da sadar sa, sannan yai gyaran Murya tare da fadin, ” Suraj me ka yanke akan mgnr yariyar nan??
Batare da Suraj ya juyo ba yace, ” aina gaya maka bani awannan tafiyan.
Jimmm yayi na tsayon lokaci Yana nazari, zuwa can yace, Shikenan, Muftahu da Magaji ya kalla sannan yace, ” Suraj ya janye akan mgnr yariyar nan, acikin ko waye ya shirya auren ta?
Cikin sauri Magaji yace nine, Muftahu ko kallon yabi Suraj dashi tare da mamakin meye dalilin sa na janyewa.
Shikuwa Modibo ganin Muftahu bece komai ba yace, toh iyayenta mu su ke jira, idan har ka gamsu ba matsala ni zan karba maka auren ta.
Eh Ina so, nawa ne sadakin nata?, Modibo ya tambaya cike da zumudi.
Cikin da kwarin guiwa yace sai munje tukuna.
Shiko Muftahu tsintan kansa yayi da tambayan Suraj yace Meyasa ka fasa Suraj?
Muftahu haka kawai zan aure yariya ne banga fuskarta ba?, Kowa fa nata ya gujeta, kuma sun amasa yariyar jinin su ce, mezaisa su gujeta?, idan ba tana da sifar dodanni ba, kanaji fa wannan Dadar cewa tayi sai mijinta kawai ne zaisan dalilin kinta, Ni wlh ko inda take ban Kara zama.
Kuma fah haka ne Suraj ya fada tare da tsoro kara akan fuskar sa.
Idan hakane me zaisa ta bude fuskar tata kafin a daura auren?, Magaji ya fada cikin yanayi irin na wadda ya firgita.
Cikin sauri Suraj yace, ai taki ne Magaji, duk dad’ewar da nayi agidan shekaran jiya kala batace min ba, kuma duk nacin da nayi ta bude fuskar ta taki, nifa wlh ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba yariyar Nan tana da matsala afuskarta shiyasa kawai tacire tsammani da aure.
A’a bahaka bane, Ina son kusa zuya daya, acikin ku daya ya aure ta, ku maza ne kuma da daman kara aure.
Modibo wai babu kira me yaci gawayi, nidai bani aciki duk wadda yaga zai iya ga hanya.
Kama kugu magqji yayi sannan ya sauke hannun sa daya ya shara zufa tare da fadin, Modibo mu sama ma kanmu lafiya kawai mu kama gaban mu gobe da safe, dan wlh wani abokina ya taba bani labarin abun da ya faru agidan su, yariya ce yar islamiyya kullum cikin hijjabi, Yana murna yayi amarya sai adaren farko yaga ashe nono daya gare ta….
Dariya Suraj da Muftahu suka saka bayan Muftahu ya gama kyajewa yace, to kila ita duk biyun ne babu.
Modibo ne yai masa wani irin kallo Yana tsaye fuskarsa daure tamau Kamar be taba sariya ba, zuwa can yace, kuyi shawara Dukkan ku, acikin ku ukun dole wani ya aure ta.
Hada baki suka yi wajen fadin wlh bani ajiki.
Jimmm Modibo yayi zuwa can ya sake cewa, nidai nace muku ku kara nutsuwa, daga nan zuwa safe sannan ni Ina baku shawara kubi ahankali domin shi me rawar kai baya d’igirgire.
Da haka ya barsu afalon ya koma ciki, hira sukaci gaba duk akan yariyar, Magaji ne yace, kuna jin Modibo wai dole, shiya aureta Mana.
Washegari tun da sassafe suka haushi shiri, tunanin su Modibo zaice bayau zai tafi ba, amman Yana fitowa suka ganshi cikin shirin sa na tafiya, duk motocin sun sun hallara tare da yan rakiyar su, motoci goma sha daya ne jere, ahankali suka fara fita daga cikin gidan, saidai hanyar Unguwar su unaisa suka nufa kodar gidan Malam Baba suka tsaya, waya Modibo yai masa ya fito ya shiga cikin motar, tafiya kadan sukayi suka isa wani madaidaicin masallaci, cike da Mamaki suka shiga masallacin yayin dasu Magaji suke kuskus din ko sama da kasa zata jade bazasu yadda da auren taba.
Cikin suka samu masallacin bayan kowa ya zauna Modibo ya ciro kudi a aljihun sa ya mika, Malam Baba ne ya kalle shi yace dawa za’a daura ranka ya dad’e?
Suraj ya kalla yayin da Suraj yai saurin girgiza kansa, su kuwa su Magaji cikin sauri suka juyar da kansu, ganin haka Modibo ya kalli Malam Baba yace a daura dani.
Kabbara Malam Baba yayi sannan ya kalli Modibo yace, “wane sunan ka?
Ahankali Modibo yace *Fahat*
Nan take aka daura aure tsakanin Fahat (Modibo ) da Rahma.
Fitowa sukayi jama’a ne suka fara tambayan shi ongon wanene daga Ina yake? ganin babu me iya amasa masu sukabi abun da Ido kawai.
Daga nan gidan Dada suka wuce domin daukan Rahma, suraj Magaji da Muftahu sai kallon Modibo suke tare mamakin sa.
Magaji kuwa fadi yake, lallai, Ammi Afnan, Safna saidai kawai su ganshi da yariya BA LABARI.
Akofar gidan Dada suka jera motocin su, bayan an bashi damar shiga gidan, har cikin dakin Dada ya shiga ya zauna, babu kowa adakin zuwa can Dada ta shigo da Unaisa cikin shigarta kamat yadda ta saba, saidai da alama batasan me ake ciki ba, domin tana ganin Modibo ta fara raba ido, daker Dada ta zaunar da ita saitin kafar Modibo sannan tasa hannun ta ta roko na Modibo tana kokarin had’awa Dana Unaisa take fadin yau zan gaya maka wacece Rahma…
Alhamdulillah
Anan nakawo karshin littafi na daya.
3 comments
Comments are closed.