
BA BABARI BOOK 2
By
FadilaLamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 1
Bismillahir Rahamanir Rahim
Cikin tsananin mamaki Unaisa tabi Dada da Ido, ganin tana kokarin saka hannunta cikin na Modibo hankalin ta hai matukar tashi, kallon Mamaki take mata cikin ranta take fadin, ” ke da kanki Dada?, Bata cire idonta afuskar Dada ba taji hannunta cikin na Modibo ya rike ta ram dashi, kokarin kwacewa ta shiga yi saidai yadda ya rike hannun nata bata iya kwacewa, d’aga kanta tayi ta kalleshi ko kadan baya kallon gefen ta, idon sa da hankalin sa yana gurin Dada saidai yamata roko bana wasa ba, sosai take jin zafin rokon, ganin Bata da abunnyi ta tsaya kawai, sai a wannan lokacin ta tsinkayi Muryan Dada tana cewa,
” Yau zan gaya maka dalilin da yasa ‘yan uwa da mutanen garin nan ke gudun Unaisa.
Innawuro da Baffah ma aurata ne da sukayi matukar zaman mutunci da mutane, haka kuma zaman takewan su na aure gwanin ban sha’awa, tunda akwai auren nan babu yaji babu kuma wani mejin kansu, Innawuro bafulata nace shikuwa Baffah bakatsine ne, sana’a ta kawoshi nan Yobe sai kuma Allah ya nufa aure atsakanin su.
Sai dai tunda akai wannan auren zama yayi zama Innawuro ko Bari bata taba, hakan yasa suka shiga damuwa tare da neman magani, sosai Baffah ya kashe kudi amman shiru babu wani labari, adaidai wannan lokacin dangin miji suka saka Innawuro a gaba da surutu daga karshe suka matsa masa wai Baffah ya kara aure.
Itama wannan lokacin Innawuro taso yabi shawaran dangin sa ya kara auren, amman ya nuna bashi da wannan ra’ayi, inaworo tata karfafama masa guiwan yayi auren tare da nuna masa ita ta hakura, acikin nuna masa hanurinta ta roki mahaifi na Malam Ayuba cewa abata ni, nan take ya batani alokacin inada shekara goma.
Tunda Innaworo ta karbeni ta maida hankalin ta sosai akaina, hakama Baffa tamkar Uban daya haifeni, sun nuna min soyayya irin ta uwa da ‘yarta tare da toshe kunnen su akan duk wani surutun mutane.
Haka na rayayu da Innaworo da Baffah cikin zaman jin dadi, bazan iya cewa ga rana daya wadda suka musguna min ba, har nakai minzalin aure suka aurer Dani tare da min komai wadda iyaye keyi, bayan shekara daya da aurena na haifi da na miji, gidan Innaworo na koma nai zaman jego bayan nagama na dawo dakina, daga wannan lokacin shera goma na dauka ban kara haihuwa ba, wannan dalilin ya haifar da rigima a tsakanina da megidan hartakai ga ya sakeni.
Nakoma gida da zama kwana na Uku agidan na fahimci Ina da ciki, lokacin da Innawuro ta lura saita gayawa Baffah, ba ason rantaba ya gayawa mijina, lokacin yaso kwarai na koma dakina yayin da Dada ta rufe idonta taki amincewa, duk da cewa wanan lokacin girma ya kama Innawuro, sosai ta manyan ta harta dan rankwafa, hakama Baffah tuni ya rankwafa girma ya kamasu sosai kowa yacire rai da cewa zasu haihu, kwatan wata rana misalin shabiyu na dare naji kukan jariri adakin, kasa bude Ido nayi sabo dajin kukan, nidai nasan mukaid’ai ne agidan, cikina kuma be isa haihuwa ba.
Jin kokan yana kara yawa nasake curewa waje daya, sosai jikina ya fara rawa dan a tunanina ko aljanu ne, amman saina tsinkayi Muryan Innawuro tana fadin’ ” ke Aisha, Aisha tashi doba min me nasamu.
A firgice natashi, hasken fitilar da nake gani yayi kadan dan haka na dauki fitalan na nufi Inna wuro dake durkushe akasa, sai dai tunkafin in karasa na hangi jaririn dake shinfede akan zanin Inna wuro yana tsadara kuka.
Innaworo ke fadin yau Allah ya nufa na haihu Aisha dubamin me nahaifa.
Batare da wani bata lokaci ba na nufi Kanta, macece na fada Ina share zubar dake yanko min sannan na dauko wani zanin na dauki yariyar na rungume, gaba daya tunanina saida ya daina aiki awannan lokacin, ganin hakan bazai min ba na kwantar da yariyar a kangado naje na taso Baffa, shima ya nuna tsananin mamakin sa daga nan ficewa nayi a gidan na nufi gidan mu, da wannan daren, ina matsanancin haki nake buga kofar gidan, mahaifina ne ya bude kofar domin yaji irin Kiran da nake kwala masa, afirgice yake tambayana lafiya, Ina cike da hakki nace Innawuro ta haihu.
Mahaifina be boye mamakin sa ba, yace wanni irin haihuwa kuma, nikuwa fadi nake mace ta haifa katuwa.
Tare muka shiga gidan yana buga masu kufar tare da fadin wai kunji Ramatu ta haihu, gaba daya gidan fitowa sukayi kowa da Mamaki a tattare dashi, haka muka nufo gidan kowa na suratun shi be tabaji ba, annan gurin aka kirga shekaran su arba’in da doriya da aure muna shiga kuwa suka dire idon su akan na yariyar maza da mata, wasu kuwa kin shigowa dakin sukayi suna fadin, ko jiya nazo gidan nan banga Innawuro da ciki ba, idai ko Inna wuro ta haifita saidai in yar aljanu ce, mahaifina kuwa Innawuro yabi da kallo Yana fadin Ina Kika samu ‘ya?, Dan mu bamu da labarin kina da ciki sai kawai muji haihuwa kwatsam BA LABARI komai, a’a wannan akwai wata akasa.
Intakaici maka daga nan dangi sukaki amincewa da zancen, sai dai ganin jinin haihuwar da karnin jinin yasa wasu suka shiga tsoron innawuron ita kanta, da yawa Basu dauki Rahma ba domin abin ya basu tsoro kuma ga mahaifarta yashe akasa tare da rezar da aka yanke cibi, saidai kowa ya kasa saka hannu ya taba komai, nan sukaita zamewa suna guduwa ganin kowa ya fice awannan daren nasa ruwan zafi naimata wankan tare da saka mata kayan sanyin ta mekyau wadda Innawuro ce ta miko min, bayan na gama na juyewa Innawuro ruwan ka kafin ta fito na gyara dakin sannan na fito Inna wanke zannuwan Baffah nasamin albarka, bayan nagama komai na koma daki, nutsuwa nayi na dauki yariyar na zauna bakin karamin gado na zubawa yariyar Ido, nasancewa yawancin jarirai ana haifansu ne tamkar larabawa amman ban taba ganin jariri me kyayon wannan yariya ba, haka wasu daga cikin dangi ma da sukazo haka sukaita cewa wannan ai ba ‘yar bahaushe bace tambaya ba irin wadda Innawuro batashashi ba amman duk amsan dayace ‘yarta ce ita ta haifi abunta, dan haka suma suka maida tambayan su ga Baffa shima dai amsar dayace yake badawa, ranar suna ta zagayo Baffah ya mayar mata da Sunan Innawuro Ramatu nikuma nake kiranta Unaisa.
Wannan dalilin yasa kowa yake tsoron shigowa gidan, wasu daga cikin mokota duk sun shigo ganin yariyar yayin da kowa keshiga Mamaki idan yaga yariyar, awannan lokacin nonon Innawuro yazama fata dan haka sai Madara ake bawa yariyar, bayan wata biyu da haihuwar Unaisa na koma dakin Miji na, lokacin Unaisa tayi wayo, yayin da kyayunta ke dada fitowa, bayan wasu watan ni nahaifi ya mace, Innawuro ta nunawa Unaisa kauna sosai suka shaku soayya gata babu irin wacce Basu nuna mata ba saidai harta fara takawa dangi da mutanen Unguwa kowa tsoronta yake tunda aka haifi Unaisa banajin akwai wani da yace Allah ya raya bayan ni da iyayenta lokacin da Innawuro tafara zuwa da ita Unguwa kuwa tsangwama babu irin wadda bata gani ba ita kanta, itako Unaisa ta taso dason wasa da dariya amman yanayin tsangwaman data fara lura dashi daga wajen kowa ya maida ita wata kala, hankali na bekara tashi ba sai vayan rasuwar su Innawuro yariyar duk ta zama wani iri daker ta yadda nasata amakaranta itama makarantar saida muka neme ta nesa da gida, domin ni kaina ayanzun jama’a basa sakar min jiki sosai sabo da Ina mu’amala da ita, haka mijina sabo da yadda yaga Ina kula Unaisa ya rabani da ‘yar da nahaifa zainab yabawa dangin sa ataikace dai Modibo wannan shine dalilin wannan tsangwama da jama’a kewa Unaisa, idan zan tsaya faiyace maka komai sai mu kwana mu wuni a’a gama ba.
Ajiyan zuciya Modibo yayi tare da shafa sajen sa, daga karshe ya sauke kansa akan Unaisa data takure guri daya, hannunta rike cikin nasa banda sheshshekar kukanta bakajin tashin komai, ahankali ya maida hankalin sa Kan Dada tare da gyra murya sannan yace’ ” me Kika fahimta game da haihuwar ta?, Ina nufin kina ganin su din ne suka haifeta kokuwa kina tunanin akasin haka?
Toh nidai Kawai abun da nasani, Innawuro mutuniyar arziki ce, kuma tabbas na farka naga jaririya akasa tare da nahaifa ga kuma rezar da aka yanke cibi a agefe, sannan Innawuro tace min Aisha tashi na haihu dan haka Innawuro ita ta haifi Unaisa.
Shiru Modibo yayi tsayon lokaci da alama nazari yake, zuwa can ya dago kansa ya kalli Unaisa dake kuka har yanzun sannan ya sake maida kansa kasa tsayon lokaci, ahanli ya sake hannun ta dake cikin nashi sannan ya kalli a agogon dake daure a hannun sa tare da fadin, ” Mama Bari muje kar muyi dare.
Kallon Unaisa tayi wadda zuwa yanzun ta koma gaban Dada tace, ” Unaisa ki daina kuka kinji ko, karki tsinkar min da zuciya, in ga Kamar na miki rashin adallaci, nasan baki son aure ba tun yauba amman dole auren shine mutuncin ki da martabar ki, kinga wannan bawan Allah.
Modibo ta nuna mata da hannu, dan gaka tai saurin girgiza Kai tana fadin, niba auren da zanyi Dada kibari dan Allah.
Ai aikin gama ya gama Unaisa, Modibo Mijinki ne, da safen nan aka daura miki aure dashi…..
Nashiga Uku Dada, me yasa kikamin haka, kingaji Dani ko Dada, kuka ta rushe dashi sosai tare da jayewa tana kokarin shiga bayan Dada.
Dada ko fadi take, kiyi hakuri Unaisa kawai na fawalawa Allah komai ne yasa na amince da auren nan, dan babu wadda ya taba nuna yanason ya taimake ki Kamar sa, kiyi hakuri ki tashi kuje, nima amanar ki na bashi Kamar yadda aka bani amanar ki, insha Allahu kuma bazaici amana ba.
Sosai jikin Unaisa ke kerma mikewa Dada tayi ta nufi bude fuskar Unaisa hannunta tasa ta dafe fuskarta ta dan haka Modibo yace, ‘ rabo da ita Mama tadai taso muje kawai.
Daker ta dago Unaisa dake kurma uban uhu jikin ta na matsanancin kuka, Dadama tana kuka take Jan Unaisa har suka iso kofar gidan da Motocin su ke jera, Muftahu Suraj da Magaji ne suka bode Motar, Modibo ya shiga ya zauna yayin da Dada take kokarin daga kafar Unaisa, da’ker tasata Motar tana matsancin kuka yayin da har yanzun Unaisa ke yanga Ihu tana roko Dada.
Magaji ne ya zauna a mazaunin driver har sukai nisa suna hango Dada sai share hawaye take, itako Unaisa kuka kawai take tare da fadi kasa kasa taci amanar Innawuro, tuni subar layin domin da mugun Gudu Magaji ya fincike motar.
Hanya suka dauka tun tana gane gurare har tazo Bata ganewa, kuma har yanzun bata bar kuka ba, Modibo kuwa goran ruwa ya bude yana kurba bata ankarama ba taga har ya shanye yayi jifa da goran, zuwa can taga ya kara daukan wani, shima kurba yaitayi harya kaishi rabi sannan taga ya waigo ya kalleta, wani irin fad’uwan gaba ta taji ganin irin kallon da yai mata goron ya mika mata cike da bada Umarni yace amsa ki shanye kibani roban
Amsa tayi domin yadda yayi ba ta yadda zatayi ta iya Musa masa, Kamar yadda yace haka tayi sannan ta Mika masa goran ruwan, jefa yayi dashi sannan ya mika hannun sa yana kokarin dauko wani tare da fadin Magaji saukar da motar nan gefen hanya.
Dani tayi Magajin na gangarawa dan haka ta shiga tsananin tsoro, dajin Allah suke ba gida gaba ba gida baya, me zasu min a dajin Allah?, Waishin Dada tamasan su din daga Ina suke, ta tambayi wani gari zasu kaita?, Sosai ta rikice ta fita hayyacin ta…..
11 comments
Comments are closed.