
BA LABARI BOOk 2
by
Fadila Lamidi
page 12
Afnan ya hango tana tahowa fuskanta dauken da Murmushi, har ta iso gare su, Unaisa ta runguma ajikinta yayin da duk da haka Modibo keta mata fadan kukan da take.
Ahaka Afnan din ta wuce da ita yayin da suna tafe tana tambayan ta menene ya sata kuka.
Abangaren Modibo har suka fita amakarantar waigen su Afnan din yake tare da fada.
Shiru Suraj ya masa bece komai ba har suka dauki hanya, ganin yanata fadan shi daya yaja bakin sa yai shiru.
shiru motar ta dauka tsayon lokaci sannan Modibo ya kalli Suraj tare da fadin, ” Me kake tunani game da kiran Baba?”
Juyowa Suraj yayi ya kalli Modibo yace Ina ganin mgnr auren ka ce.
jimmm, Modibo yayi zuwa can yace, ” wai tsohon nan meyasa ya saka min Ido ne ni daya.
Wata kila saboda Kaine jikan sa na farko, kuma yana son ganin ‘ya’yan ka.
Yafini son ganin ‘ya’yan nawa ne?, komai fa lokaci ne.
Hakane, amman tunda ka amsa tun farko gara ayi kawai, ko bakason kama Madam kishiya ne?
A’a, Sam, Namiji mijin mace hudu ne, shi Mai martaba yanason inyi aure ne kawai dan yaga har yanzun Safna bata haihu ba, abun da nake son ka gane shine, bana son na gida Karin auren akan kawai Ina da mata bata haihu ba, banson wannan yazama shine hujar, idan ma zaizamanto hujja toh nafison inji ni akan kaina inason karawa ba a dinga jujjuyani ba.
Hmmm, Modibo kenan, ya naga kana kokarin kaucewa bayan ada ka amsa, kuma da kake wannan mgnr aiko rashin haihuwa Hujja ce.
Eh, Amman ni akan kaina banji na ‘kagu ba, ba’a fini son inga d’ana ba a duniya, iyaye suna wani kuskure, da sun ga ‘yar wata matsala agurin yariyar da d’ansu yake aure, sai subi su data hankalin su, wancen Yana Kara aure, wancen ma na cewa Kara, daga karshe sai azo abata goma daya bata gyaru ba, akwai wani Muhimmin abu da yakamata ace iyaye suna duba dashi, shin d’an nasu yana lafiyar dazai kara rike mace sama da daya?
Cikin tsananin mamaki Suraj yace,” ban gane ba?”
Komawa Modibo yayi ya kwanta jikin kujerar motar, sannan ya daura kafarsa daya kan daya tare da cigaba da fadin,” Ina nufin hakkokin da suke kan mijin akan matan sa banda magar ciyarwa dan wannan a bayyane yake, mukoma mgn irin ta mu’amala ta mata da miji, wani na mijin bashi da koshshiyar lafiya, mace daya ma da ana iya rabata abashi rabi, me kake tunani idan aka matsawa irin wannan mijin Karin aure?
Wani irin murmushi Suraj yayi sannan yace, ” kana nufin kai ma kana daya daga cikin irin wannan mazan?
Haka nake koba haka nake ba wannan abune wadda ya shafeni nida iyalina, saboda kasan ance gani ya koriji, wannan tambayar da kamin Safna kadai yafi cancanta ta amsa maka ita, Amman kash shi aure sirri ne, ni kawai Ina nunar maka ne da cewa, abari mutum yai ra’ay da kanshi ko kuma abashi shawara, amman tursasawa kamar ana jefe mutun cikin halaka ne, karka manta lokaci Safna haka aka matsamin lallai sainayi aure wannan karon ma sai a matsa min ?
Okay yanzun ne kasan da wannan yancin kenan, karkace min saboda wannan yariyar kake wannan mgnr.
wacce yarinya kenan? Modibo ya tambaya bayan ya tsare Suraj da Ido.
Wannan wawiyar yariyar Mana, wa take da suna, oho da alama yanxun kam ka fara sonta, sabo da ita kake kokarin zillewa Maganar maimartaba.
Wani irin yalwataccen murmushi Modibo yayi wadda ya fito da kyaun fuskarsa sannan ya dauke kansa tare da shafa keyarsa , juyo ya sake ya kalli Suraj akaro na biyu.
Wannan karon ma irin Murmushin dai ya sake saki, sai dai na wannan karon ya bada sauti, wadda har yaso tunzura Suraj.
Ciki da Bacin rai Suraj din ya kalli Modibo adaidai lokacin da Modibo ke gyara zaman gilashin sa tare da fadin, ” Idan na fahimceka kana mgn ne akan *RAHMA* bazan ce maka Ina sonta ba bazan kuma iya cewa bana sonta ba, abun da yake tsakanina da ita kuma Allah ne ya kulla, zanyi zaman aure da ita ko bazanyi ba shima dai wannan na Allah ne, nayi Alkawari acen baya zan gina rayuwarta, kokarin da nake kenan yanzun. sannan akullum Ina farin ciki tare da gode ma Allah da yasa min ita akarkashi na.
Ban fahimceka ba?
Idan ka nutsu zaka fahimce ni.
Ta Yaya zan gane, bayan ka’ki gaya min abun da ke cikin ka, komai akace kace Allah. Suraj ya fada afusace.
Shikuwa Modibo wannan karon idon sa akan hanya cikin kwanciyar hankali yake cewa, ” kaga laifina?, ruwa na Allah, kifi na Allah, masu cima aina Allah ne.
Sai ayanzun Suraj ya kula da fusatan da yayi dan haka ya shiga kokarin saisaita kanshi, Amman can karkashin zuciyar shi akwai damuwa sosai.
****
Modibo Magaji Muftahu da Suraj zaune agaban kakan su, Yana zaune saman kujerar sa ta sarauta, kamilin mutum me mutunci, manyantaka zai nunawa Abban su Modibo, kama suke sosai, gyaran murya yayi sannan yace, ” idan kunfi karfin iyayen ku ni bakufi karfina ba, kune manya kuma maza kowane cikin ku ya gama karatu kuna da aiki me kuke jira?
Shiru Babban falon yayi, yayin da Sanyin AC ke ratsa su kota ina, Magaji da Muftahu naman dake gaban su suke ci tare da korawa da ruwan lemo suna sauraron Dattijon kakan su, cigaba yayi da cewa.
A’a kawai kun zauna agida gabza gabza daku kuma iyayen ku zun zuba muku Ido, ban sani ba ko girman ku ke basu tsoro?
Magaji ne yai karaf bakin sa cike da nama yace, ” Baba, kamar ka fara rikecewa, idan ba haka ba ai babu Modibo a wannan Kiran naka
Kara kishigidewa tsohon yayi tare da shafa gemon sa Yana kallon Magaji da ya maida hankalin sa Kan naman dake gaban sa.
Modibo kuwa kallon yadda tsohon ke shafa gemon sa yake yana murmushi tare da jiran jin amsan dazai bawa Magaji.
Tsinkayan Muryan Kakan nasu yayi Yana cewa, kerr nake kallon ku, ka fara gayawa Ubanka wannan kalmar kafin kazo ka gaya min.
Gaba dayan su fashewa sukayi da dariya yayin da Kakan nasu yacigaba da cewa, ai alamun rikicewa yana wajen Abban ku, tunda ya rasa yadda zai daku kunfi karfin shi, Modibo da kake mgn kuma har yau be aje komai ba, bashi da komai, dan haka karku yadda in sake muku Kira na biyu, kafin nakira inji mgn me dadi.
Amsawa sukayi gaba dayan yayin da Ya juya ya kalli Modibo yace Kai kuma ya mgnr mu?
Baba yadda Abba yace tun baya kawai acigaba.
*****
Unaisa kwance saman gadon Ammi cikin tsananin damuwa, bata wani saba da Modibo ba amman tafiyan sa ya dameta sosai, duk tambayan da Ammi ke mata ta kasa gaya masu dalilin damuwar ta, hakama Afnan tayi tayi tun suna makaranta taki gaya mata, dan haka kawai suka bita da Ido.
Haka ta kwana batai wani Baccikin kirki ba, washegari ma har suka dawo makarantar ahaka take jinta, misalin sha biyu na rana taji motoci na shigowa hakanan jikinta ya Bata sune.
Jin Ammi tayi tana fadin sun iso.
Wani irin sanyi taji cikin ranta lokaci daya taji damuwar ta tafi, mikewa tayi tabar daki domin tana ganin Nan zasu shigo, Bata sake komawa ba Saida ta tabbatar duk sunbar dakin Ammi.
Nutsuwa taji Yana shigarta burinta kawai tasan Yana cikin gidan, domin shi kadai ne tasan zai iya sadata da dada wadda ayanzun tafi muradin ganin ta fiye da kowa a duniya.
Tundaga wannan Ranar Unaisa da Afnan suka maida hankali sosai akan makaranta, sosai suka saba da afnan duk wani abun su kusan iri daya ne, tsayon wata uku kenan suna zuwa makaranta jikinta ya murje sosai tayi kyau, daka kalleta sai kayi tunanin wani Babban gida ta fito me daraja, Basu cika haduwa da mazan gidan ba yanzun domin duk sun koma bakin aikin su, sai yamma suke dawowa gidan, yawancin lokacci sai dai Afnan tacewa Unaisa Hamma yace yana gaida ki.
amsawa take ko ajikin ta, wani lokacin kuma sakon turaruka ne ko takalma zatace gashin Hamma Modibo yasai mana
Shima amsa take tayi godiya.
Saboda yadda Rahma keda kyau kaya sukafi karban ta fiye da Afnan duk da cewa itama ba baya bace tun, ba’aje ko Ina ba Rahma ta cika sosai.
Sosai Ammi ke ganin wautan Modibon da yabar Rahma ahaka matare da tana dakin ta ba.
Ayanzun hira suke sosai da Afnan babu abun da suke boyewa juna.
*****
Modibo ne tafe ke kokari tura kofar Ammi, daga daga dakin Afnan yajiyo wata murya na kyalkyalar dariya, jimmm yayi domin jin muryan bana aFnan bane, bakuma ya tunanin Rahma ce, dan haka ya fara kokarin wucewa abun sa, adaidai wannan lokacin ya tsinkayi Muryan Afnan tace Ashe shi adole sona yake.
Dariya ya sakeji da irin wannan dai muryan ta dazon, zuwa can yaji an tsaita da dariyar ana fadin, ” ninaga mutum nata kwambarewa yana yanga ashe duk wannan kwambarar takice, dan Allah gobe musake saka driver din ya wuce ya barmu mubi ta wajen.
Tabbatarwan da yayi muryanta ce yasashi ya shiga Mamaki, tare da maimaita kalaman nata cikin ransa, juyawa yayi yabar wajen da saurin sa, dakin Ammi ya shiga yaso yai mgn da Ammi ganin Magaji na gurin be wani zauna ba ya fice.
Shi ko Maji sosai yake son ganin yariyar, saidai kwana biyu duk jimawar da zaiyi adakin Ammi har yabar dakin Baya ganin ta.
ya riga ya gama shiryawa tsaf ganinta kawai yake son yi.
*****
Modibo kuwa kwana yayi da tunanin hirar Afnan da Rahma, saidai ya rasa taya zai bullo wa abun, baya son mgn makamanciyar wannan tana shiga tsakanin sa dasu, idan ba dole ba, kasa cire abun da yayi aransa yasa shi ya nufi dakin Ammi bayan ya fito masallaci sallah asubu.
Saida gaban Ammi ya fadi jin sallamar Modibo, domin ba dabi’ar sa bace, ko Magaji da beda aure baya zuwa irin wannan lokacin.
Dan haka bayan sun gaisa tace Lafiya kuwa Modibo?
lafiya lau Ammi, kawai jiya da daddare naso in miki wata mgn ne sai kuma na manta har natashi banyi ba.
Jimmm Ammi tayi sannan tace lafiya dai ko?
Lafiya, daman cewa zanyi Afnan Aure zakunmata data kare Secondary?
Modibo toh ai kafi kowa sanin halin Abban ku, mutum ne meson karatu.
nima Ammi nafiso tayi karatu ai.
yanzun wani abu ne ya faru?
A’a, kawai dai cewa zanyi, kidinga mata fada banda kula samari, idan kuma aure take so ta fada sai amata
Sai amata kuma Modibo?
Eh Mana Ammi, idan auren suke so da su dauko Mana mgn ba gara a masu ba.
Jimmm Ammi tayi cikin rasa inda mgnr sa ta dosa, iya saninta dai Yana mgn ne akan Afnan, kauda mamakinta tayi tace, kokaji wata mgn ne?
A’a, kawai inaso ne a dinga tunasar dasu.
toh Allah ya taimake mu, saidai Afnan Amman ita Rahma ai da aure akan ta.
batare da ya bawa Ammi amsa ba ya juya yana kokarin fita tare da fadin, tana nan kuwa?, na kwana biyu ban gan ta ba.
Bayan sa Ammi tabi da kallo tare da fadin, ” makaranta ne ya boye ta.
*****
Misalin 07:30am Modibo ya nufi dakin Ammi cikin Shirin sa na zuwa aiki, zama yayi sannan ya shiga gaidata, saidai tun kafin ya su gama gaisawar yakejin dariyar Afnan da Rahma dan haka bayan sun gama gaisawa yacewa Ammi waddan cen kuma me suke yi haka?
Cike da Murmushi Ammi tace hirar su ce can suke yi.
Shine suke ihu haka kamar suna gidan kallon kallo
Rahma ce, kasan bata dariya saitaji mugunta, Afnan kuma kasanta da hira har da karya ma saita had’a, ita kuma taita dariya.
Tsaki ya ja afili, sannan ya juya ya harari kofar dakin Ammi, wata zuciyar kece masa tashi kaje ka same su yayin da wata zuciyar ta hane shi da yin hakan.
Zaman kusan minti miyar yayi sannan ya mike da nufin tafiya abun sa, Sallama yama Ammi sannan ya mike cikin sauri ya bude kofa, timmm yaji akirjin shi babu zato, cikin sauri yasa hannun sa ya dago ta tana dafe da goshin ta tare da fadin, Washhh Allah na Ammi kaina.
Cike da tsawa yace, Dallah gafara can baku da nutsuwa iskancin banza kawai.
Nan danan jikin ta ya shiga rawa tabbatar da cewa jikin Modibo ta fada, duk zaton ta kofar ce, gefen sa tabi ta rabe tana kokarin wucewa ciki, adaidai lokacin da Afnan ta iso kofar, kallon Afnan yayi sannan yai saurin juyawa ya kalli Rahma domin afarko ya dauka Afnan d’in ce.
gani yayi gaba daya ta canza masa, har ya fara tunanin idan ma a hanya ya ganta zai ganeta kuwa?, akwai sauyi sosai, kan dogon hancinta ya hangi wasu taurari na walwali har suna kokarin kashe masa Ido, cike da mamaki ya bita da kallo tare da fadin, ” Ke!! hannun sa ya daga Yana mata alamar ta matso.
kasa motsawa tayi, daga inda take taji ya sake fadin, ” Ke ! wai hanci kika bula ne? cire gilashin idonsa taga yayi tare da fara takowa zuwa cikin dakin….
4 comments
Comments are closed.