
BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 2
Gangarawa yayi Kamar yadda Modibo yace, saidai shiru da yaji na tsayon lokaci yasashi juyowa ya d’an kalli Modibo sannan ya kalli Unaisa data d’an juyawa Modibo baya tare da fadin, “wani abu ne”
Cike da bada aumarin Modibon yace, ka sauka ka bude mata motar.
Bude motar Magaji yayi sannan ya bude motar yana bin Unaisa da kallo wadda har yanzun kuka take.
Batare da Modibo ya kalleta ba yace sauka ki wanke fuskar ki, karkuma ki dawo min da kuka.
Cikin sauri Unaisa ta fita tana fadi cikin ranta, “idan banyi na fili ba nayi na zuciya, nisa tayi sannan ta tsuguna ta wanke fuskar ta, saidai ta kasa tashi a gurin, ji take kamar ta mike tabi cikin dajin aguje, acikin ranta taci gaba da fadin, “idan na gudu shikenan na tsare masu, yadda wannan Magajin kemin kallon tsana ba bina zaiyi ba, shikuma wacen anacen Modibo ba kafa ne dashi ba, daga can bayanta taji Muryan Modibo Yana fadin, ” Magaji bata gama bane?
Batare da Modibo ya rufe baki ba Magaji yace, ” ke! dallah tashi kina bata mana lokaci.
Mikewa tayi da sauri tabi cikin motar ta zauna, irin zaman dai na d’azon shita kuma yi, bayan nata ya kallah ya tabe baki sannan ya dauki wayar shi ya karata a kunnen sa, zuwa can taji yana fadin, ” Muftahu kagaya masu mun taso ne?
Zuwa can tace ya cigaba da cewa yauwa karka gaya kaji.
Magaji dake tukim yanajin sa, acikin ransa yake fadin, “dole kace kar a gaya mana, tunda kasan baka shuka abun arziki ba, koda yake wannan ba aure bane ba shiririta ne, babban abin bakin cikina ayanzun, kawo mana mutum Mutumi cikin gida, haka zamuyi ta faman ganinta tana biya biya da hijabi, sosai takejin zafin Modibo da har ya yadda aka taho da yariyar nan.
******
Muftahu da Suraj su biyu cikin motar, dukan su abaya suke, sunyi jugum jigum, Suraj ne keta sauke ajiyan zuciya wadda ya rasa Kona menene, sosai takejin tashin hankali, gashi Koda na minti daya tunanin yaki barim sa wai Modibo ne ya yadda ya aure wannan wulakantacciyar yariyar wadda Bata da galihu”
Bayan sunci rabim tafiya sannan Muftahu ya saki ajiyan zuciya tare da fadin, Suraj akwai matsala ba, Su Abba sunci buri akan auren Modibo, shikuma gashi ya tashi yaje ya karbi aure babu shawaran su, kana ganin bacin ransu bazai shafemu ba kuwa, haka fa ba waccen karon Abba har saida ya kusa tsine Mana.
Cike da haushi Suraj yace zaidai shafe ku, ni idan naga dama ko gidan bazam shiga ba zan wuce gidan mu, saidai inaji auren jeka nayi ka ne Modibo yayi, tunda yace karka fada kila bazai gaya masu bane.
Shiru Magaji yayi tsayon lakaci zuwa can yace, ikon Allah nifa wannan lamarin har yanzun daure min Kai yake, Ni kuma bana tunanin Modibo zai boye auren, amman gara yai shiru sabo da idan Safna taji wannan mgnr bansan wani hali zata shiga ba, shida ya karbo auren yasan yadda zai dashi.
Kawar dakai Suraj yayi cike da takaici, sannan yace, ” Allah ya kauta, ai wannan ba aure bane yayi, kawai dai yayi ne dan ya taimaki yariyar ya baro da ita daga garin, amman fa duk da haka Modibo yayi ganganci, saidai Ina a Ina faruwar wani abu.
Wani abu kenan Muftahu ne ya tambaya.
Nasan idan har Ammi taga yariyar dole ne ta bude fuskarta
Bude fuskarta ai na banza ne tunda danta ya karbo auren dodanniya ko tantama banayi yariyar naka sassiya ce.
Cikin tarin takaici Suraj ya juyar da kansa kan titi Yana kallon yadda shuke shuke suka girma wannan be kadai yake rage masa radadin da yake ji cikin zuciyar sa.
******
Magaji ne keta kallon zaman Modibo da Unaisa ta mudubin dake gaban sa, kusan, juya masa baya tayi yayin da lokaci bayan lokaci take Satan kallon Modibo, bayar da kallon sa yayi ga Modibo dake danna waya ga Dukkan alama bashi da wata damuwa, bubu wani canjin yanayi a tattare dashi, kur ya masa Yana son ya gane wanni halin yake ciki, bakin ciki ko farin ciki, saidai duk iya kallon sa da yake ya gaza gane hakan, dan haka ya maida hankalin sa atunanin gida.
Unaisa kuwa banda raba ido ba abun da take, ganin ana keta dajuka ya daga hankalin ta, tafiya kawai ake Bata da masaniyar garin da za’a kaita, wannan ya wuce ace za’a wani gari saidai ace za’a shiga wata kasa, lisaffin garuwan ta shigayi tuntana iya rike kirgan harta kagara, ahankali ta juya ta kalli Modibo, juyowa yayi ya kalleta kadan sannan ya maida kansa kasa tare da daukan gilashin sa ya daura a idon sa, agogon take daure a hannun sa ya kalla sannan ya daga Ido ya kalli Magaji tare da fadin, lokacin sallah yayi, idan ba gari a kusa ka tsaya muyi sallah.
Amsawa Magaji yayi tare da kara gudun motar, cikin tafiyan dabefi na minti goma ba suka isa wani dan kauye, sakkowa sukayi kusan a tare suka nufi Dan karamin masallacin dake bakin hanyan, cikin motar suka barta ko kala babu wadda yace mata cikin su, gurin ta babu kowa sai motocin dake zuwa suna wucewa aguje, tarin damuwa ne acikin ranta, tunani ta shigayi, yayin data tsinta kantan tana fadin, ” afili Ina zasu Kaine, ya rabbi ka kubutar Dani, Dada kema yau kin gojeni, wayyoni wannan wacce irin ranace, Innawuro kintafi kin barni cikin bakin rayuwa da wahala, wlh nagaji Innawuro, kizo ki dauke ni Nima na huta, juyawa tayi ta kalli kofar yayin da wata zuciyar ke Bata shawaran ta fice kawai tabi daji, kila taci karo da wani naman Dajin ya cinyeta ta huta, sai duk karfin da take nunawa kofar taki ta bude, ayanzun tana daidai inda Modibo ya tashi, bata Ankara sai ganin su tayi suna tahowa, kasa motsi tayi tana binsu da ido, Modibo ne yasa hannun sa ya bude kofar, ganin ta agurin zaman sa yasa shi binta da idon kawai, kokarin sauka ta fara dan haka ya kauce ya Bata hsnya tare da fadi a hankali, aunty Ina zuwa haka?
Da saurin ta ta sunkuyar dakai tare da lankwasa yatsanta daya tana wasa dashi yayin da hawaye ke sakko daga idon ta.
Motar ya mayar ya rufe sannan ya shiga zagawa daya gefen ya zauna har yanzun kallonta yake yayin da Unaisa duk tabi ta daburce.
Magaji kuwa banda Satan kallon su babu abun da yake,tafe suke babu me cewa kala illah Modibo da yake yawan dannan wayarsa tare da bada hankalin sa sosai akan wayar, Unaisa kuwa tun tana kuka har idonta ya fara bushewa saija da sukayi tare da kumburi, magariba a hanya ta same su, babu sallar data wuce Modibo da Magaji lokacinta nayi suke tsayawa su gabatar sosai ta shiga damuwar bashin sallah hud’u, har akayi sallar isha’i tafiya suke
Idonta akan hanya kawai Bata da masaniyar inda zasu kaita, ko anan suka barta Bata san yadda zatayi ta koma gida ba, zuwa can ta fara hango haske fitulo kota Ina, gara bude Ido tayi nan ta shiga hango wasu lafiyayyun titina masu kyau da ban sha’awa, saidai kuma tana tare da tarin damuwa daga can ta fara hangowa arubuce cikin manyan baki *ABUJA*
CIKIN garin taga suna shiga, wannan ya tabbatar mata anan din zasu tsaya, gudu Magaji yake sosai kan lafiyayyen kwaltan, zuwa can taga ya tsaya, sai yanzun ta kula da motocin sun dake tsaye agurin, Basu jima da tsayowa ba wasu motocin suka tsaya bayan tasu, da alama hada kansu suke, itadai Unaisa sarautar Allah ta zuba Ido dan wannan rana Bata da masaniyar inda zata kwana.
Muryan Modibo ta tsinkaya yana fadin Magaji muje mana.
Jira nake su tashi ai Magaji ya bashi amsa, saidai Kan ya rufe baki motocin suka tashi, cikin garin suke shiga ajere, zuwa can taga motocin sun fara tafiya sannu hankali dan haka ta bude Ido domin taga abun dake faruwa, wani tamfatsetsen gate taga suna shiga yayin da megadin keta daga masu hannu.
Gidane katon gaske nagani na fada, fitolune kota Ina cikin gidan can gefe kuma shuke shuke ne na zamani masu ban sha’awa, zagaye gidan yake da gini kallon tsayon benen gidan take daga can sama taji muryan mace cikin ihu take fadin, ” Oyoyo Hamma Modibo!! Nan danan gidan ya dauki ihu tare da guje guje tare da Kiran sunan Moddibo dan haka Unaisa ta rikice gaba daya ta fice hayyacin ta.
Fitowa suka farayi daga cikin motocin, Moddibo ne ya sauke karfen sa sannan ya sauko fuskarsa dauke da fara’a yana kokarin gyara zaman karfen a hakarKarin sa wata buduwar yariya ta kwaso aguje tare da Kiran Hamma Moddibo!! da karfin tsiya ta fada jikin sa.
Sakin karfen sa daya yayi ya fadi kasa sannan yasa hannun sa ya zagaye ta ajikin sa tare da sumbatan kumatun ta.
Gurin ne ya cika gaba daya da mata da mazan, kuma har yanzun mutane fitowa suke, wani Dattijo Unaisa ta hango Yana tahowa da Sadda a hannun sa wadda tafi kama data takama tare da daurin rawani akan sa, sosai suke kama da Modibo da Magaji, idonsa cikin farin gilashi, sosai kasunbarsa tafi dasu Moddibo yawa, wata kyakyawar Dattijowa ce gefen sa tasha adon gwala gwalai, da alama matarsa ce dan sosai suka dace da juna.
Ganin su yasa Modibo ya saki yariyar yayin da ya rungume Dattijon, shima rungumeshi yayi tsam ajikin sa na tsayon lokac, kamar bazai sake shi zuwa can ya dagoshi ya sunba shi sannan ya kamo hannun Dattijowar yas ka mata hannun Modibo, cikin saurinta ta runtse hannun sannan ta rungumeshi ajikinta, kasancewar ya kere mata tsayo ya farajin saukan hawayen ta akan kirjin shi.
Itako Unaisa har yanzun tana zaune cikin motar, sosai ta saki baki tana kallon irin wannan soyayya ga dukkan alama iyayen Modibo ne, gaba daya mantawa tayi da inda take, Bata hankara ba ta hango tawagar mutanen sun juya sun nufi cikin gidan batare da mutum ko daya yayi saura a gurin ba…
8 comments
Comments are closed.