Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 23

Posted by

BA LABARI BOOK 2 PAGE 23

 

BA LABARI BOOK 2

  BY
FADILA Lamido

EXQUISITE WRITER’S FORUM.

Page 23

Afnan ta samu ita da Ammi afalon suna hira, tana shigowa suka dago atare sunan kallon ta, dan haka tai saurin sunkuyar da kanta kasa.

Saida taji ajikin ta Ammi ta kauda idonta akan ta sannan ta dago ta sake kallon Ammi tare da zafgawa Afnan harara Domin dagani ta fada ne.

Wannan lokacin Kan tv sukafi maida hankalin su saidai jifa jefe suna d’an satan kallon Unaisa.

 Ganin dare nayi Ammi ta tashi, gefen Abba su take da niyyar zuwa dan haka ta nufi dakin ta domin kara kintsa jikin ta, domin ita Ammi har yanxun Koda yaushe cikin gyara jikin ta take Bata duba yara dake gare ta bare har ta tsufar da kanta.

Ganin Ammi ta nufi dakin ta kalli Afnan dake dauke kanta tace, ” kin gaya mata?

    Mene?

   Mgnr da muka yi.

 Ai bakice in gaya mata ba, kuma madai ai ke yafi cancanta ki gaya mata bani ba.

Cike da haushi Unaisa tace, ” Saboda me?”

Sabo da mgnr ba tawa ba ce, idan kin lura da Ammi da Hamma Modibo so da yawa idan zasu yi mgn dake irin baka cewa suke in fita, idan kin gaya da bakin ki zai fi….

Afusace Unaisa ta mike komawa dakin tayi ta sake kwanciya ruf da ciki yayin da ta shiga tuna ta gata ga Modibo daki daya wai kuma haka zasuyi Bacci.

Mikewa tayi aguje ta koma bayin amaita sake yi kamar zata fitar da kayan cikin ta, bayan ta gama jikinta amace ta fito, kokarin kawar da damuwar take Amman ta kasa.

Sai can dare Afnan ta dawo, tana kallon yadda Unaisa keta sintiri tun tana Bata dariya harta koma Bata Tausayi dan haka yanxun data fito jikin ta ba karfi tace”

Aunty Unaisa dan Allah ki kwantar da hankali, ba wani guri bane fa za’a kaiki cikin gidan nan ne, wai dan Allah meye abun tada hankali, narasa abun dake baki tsoro kishiya koko Mijin?

 Kallon ta Unaisa tayi, ayanzun idonta ya bushe bubu hawaye tace, ” nifa ba tsoron kishiya nake ba, kema kin sani, idan har zakiji tsoron kishi to zanji tsiron ta.

Toh Hamma Modibo ne baki so kenan?

Wanni irin kallo Unaisa tai mata sanan tace shima bakin sa nake ba.

Toh dan Allah mezaisa ki firgice har haka?, Ni wlh ji nake Kamar na jawo ranar.

Ai ke daban Afnan, kun saba sosai da Kabir, idan kun had’u daker kuke rabuwa, nikuwa fa?, ban saba dashi ba, bana sakewa Sam idan Yana gurin.

Jimmm Afnan tayi sannan tace, ” na fahimce ki, Amman wlh hamma na baida matsala ko kadan, shima harda laifin sa, amman kwana kadan zakiga kun saba.

Nifa Afnan dan bakisan abun da nakeji bane, yin rayuwa da wadda kake ganin sa kamar mahaifin ka.

Yaudaran kanki kikayi Wlh, amman shi tuni yake nuna miki da auren shi akan ki, kece dai Kika dauki abun ahaka, ni ki barni inyi bacci gaskiya kema ki kwanata dan Allah.

Wanniirin kallon Unaisa ta mata sannan ta dauki wayatta ta fara Kiran Dada saidai harta gaji da kiranta bata daga  ba.

 Washegari da Safe Afnan tare suka shiga dakin Ammi ita da Unaisa, kallon su tayi vayan sun gaisa tace Unaisa yanaga kin fada, idon ki a kunbure kinyi kuka ne?

Da saurin ta ta sunkuyar da ka ta tare da fadin, a’aT

Tabwlh Ammi ni bamma tunanin tayi bacci, daga kuka sai amai kawai take cikin dare.

Oh ni, wannan amai naki Allah ya raba ki dashi, toh me yayi zafi?

Wasa Unaisa tafara da hannunta, Afnan  ne ce tace, ” tunda Hamma ya gaya mata zata tare shikenan ta birkice, dariya Afnan tayi tare da fadin, Ammi tace wai ita Uba ta dauke shi.

   Dariya Ammi tayi tare da kallon Unaisa dake lankwasa hannun ta tace, ” ai daman wani lokacin miji Uba ne, ki kwantar da hankalin ki Babu komai, banajin Modibo.

    Hawaye ne yazobo Kan ciyarta yayin da tai saurin saka hannun ta ta share murya kasa kasa tace, Ammi toh akara tsayon lokacin, ranar auren Afnan da ace yayi kusa.

Toh shikenan Bari ya shigo hakan za’a yi, zanyi mgn dashi.

                      *******

Misalin 7 na safe Modibo da Magaji ne gaban Ammi, aiki zasu fita suka shigo yin sallama da Ammi, Modibo ne ya fara fita Ammi dai saurin Kiran shi tare da fadin, inason yin mgn dakai kuwa.

Dan dawowa da baya Magaji yayi Yana fadin Ammi Nima in tsaya?

 Kana iyawa, kallon Modibo tayi tana cewa, ” yariyar can jiya batai bacci ba, Afnan tace ta kwana ne tana amai, kai waye ya aikeka ka gaya mata zata tare, nasan halin ta shiyasa nai shiru da bakina, anufina idan abun yazo ta ji.

Cikin rashin Fahimta yace amai me take toh?, akan me zata damu?

    Ai tace ita Uba ta dauke ka.D

DariyaMagaji yayi shiko Modibo daure fuska yayi sosai kamar be taba dariya ba sannan ya shafa sumar sa tare da juyawa yana fadin, saina dawo Ammi.

A’a zonan Ammi ta fad’a, har Magaji yayi gaba jin Ammi ta Kira shi yasashi dawowa da baya shima.

Kararrashe da dan Allah kasan ita vata iya damuwa ba damuwarta saitaita amai…..

  Toh Ammi zanyi haka din.

Juyawa yayi Yana hararan Magaji da yaga Yana kokarin biyo bayan shi, Ammi ce ta Kira Magaji dan haka Modibo ya wuce Abun shi.

Bayan fita Modibo, Ammi ta dubi Magaji cike da takaici tace, ” ya kamata kasan me kake yi, kaiba karimin yaro bane ba, nagaji da halin ka, Rahma zata tare agidan Modibo ranar auren Afnan, Ina gargadin ka babu ruwan ka da ita.

Ammi tace na mata wani Abu ne?, nifa tuni na fita hanyar ta.

Kara gaya maka nake yi, yanzun wannan binsa da kake abaya ya dace ne ? ya tafi ka bishi ya sake dawowa kaima ka dawo, Kai karamin yaro ne? ko kuwa dole ne sai kaji me za’ace?

Cikin rashin jin dadin Zancen Ammi yace, Ammi wasa ne nake mishi, kuma shima yasan wasa ne.

Toh kudai kuka sani, nidai yanzun Ina mgn ne akan matar shi, kar inji kar ingani, domin akan mgnr yariyar nan Saida Abban ku yai mishi da gaske tuncan baya, domin baya son ganin fada a tsakanin ku, fadan ma akan mace ai be dace ba sam.

Nima ai Abban yamin mgn, kuma tundaga lokacin ni babu ruwa na da ita kwata kwata ban mgn da ita.

Ai bazai yiyu ace bazaku yi mgn ba, yanzun Safna ai duk cikin gidan nan Kaine mutumin ta, amman Bari ka gani akan Rahma bazai yadda da wannan ba, sabo da abun da ya faru baya, dan haka na gaya maka ka ka kiyaye.

                         *****

Washegari, da yamma bayan Modibo ya dawo aiki, wayar Unaisa ya Kira, sai data kusa katsewa tukuna ta dauka.

   Murya kasa kasa ta gaidashi.

Amsawa yayi yana Lumshe idon sa, zuwa can yace

“Ya amai din naki ya tsaya kuwa ko har yanzun?

    Eh kawai tace.

  Daxon muyi mgn da Ammi tace kinason adan kara miki lokaci ko?

   Eh tace ahankali.

  Baki shirya bane?

   Nan ma eh ta sake cewa.

Toh shikenan nakara miki lokacin, niba bakon zafi bane, ki shirya ahankali baki da matsala.

  Can kasa sosai tayi da muryanta tare da fadin, sai yaushe?

Duklokacin da Kika shirya kimin mgn kawai, ni ashirye nake ke nake jira kawai aunty na

  Dagode ta fada ahankali

  Bakomai kanwata kisaki jikin ki kiyi harkokin ki.

Godiya take kokarin yin taji yace, me kike bukata wadda zakiyi amfani dashi da bikin?

   Ammi ta sai min ai.

  eyeeee ‘yar gatan Ammi, me dame ta saya miki?

   Cikin kosawa da hirar tace, ” Komai”

 lallai Ammi toh ni kuma inason nasai miki wani abu.

Ka barshi Ammi ta saiya min.

Idan ban banki ba bazanji dadi ba, kyauta ce irin ta uba da ‘ya, ko ni ba baban ki bane??

   Can kasa kasa tace Babana ne.

Yauwa ko kefa, kuma ko a haka nasan keba ro’kak’kiya bace, daman Bahaushe nacewa ro’ki ro’kakke kaga bakar ruwa, nasan duk ranar da narokeki bazaki min rowa ba ko?

 Eh, ta sake fada, domin ba wani fahimtan sa take ba.

Murmushi yayi tare da sauke ajiyan zuciya sannan ya sake cewa, ‘ ban tabajin kin kira sunana ba sai sau daya, inason inji kina Kiran sunana, Koda Baba ne ki kirani zan amsa, tunda dai nasan shekaru basa faduwa akasa sai ajiki, ballanta ma Saniya ko ta lalace ai ta d’au ‘kahon ta, nan gaba zamu yi kuwwa tun da haka akafin so ko?

Nan ma eh ta sake cewa tare da nazarin kalaman sa cikin ranta.

Dariya yayi har ya bada sauti, lumshe idon sa yayi sannan yace, toh karki damu, ai kowa yayi kuwwa gudummawa yake so, kuma inda Zaki yasan zai samu abincin sa cikin sar’kakiya da bai fito sarari ba, ko ba haka ba?

Hakane ta sake cewa, sannan yace, ” shikenan ki saki jikin ki, ko anji mu ai banji kunya ba, tunda dai barawon kaka’ki ai bashi da ikon busa shi, zan bawa Afnan sako ta baki.

Amsawa tayi da toh sannan ya kashe wayar sa.

Kallon wayar taita yi duk kalaman nasa batasan me yace ba, kawai dai tasan ya kara mata lokaci.

                         ******

Momy ranar yaushe zaki taho bikin toh?

Kai Safna, duk kinbi kin data hankalin ki yanxun yau ba saura kwana sha uku bikin ba?

TohNan dai da kwana goma ki tsumaye mu, meke damun ki ne?

Momy nifa Kamar aaure Modibo zai yi.

Kashh, nagaya miki babu wannan mgnr,  ba yadda za’a yi akai sadaki batare da sanin mu ba, duk iyayen da suke Kai kudin auren dama nemo auren kansu muna nan tare, banji wannan labarin ba.

Ammibaki tunanin kila auren sirri zaiyi, tunda ga Abu  da yake faruwa?

Jimmm Momy tayi sannan tace banayin wannan tunanin Safna ki kwantar da hankalin ki.

Momy nakasa wlh, hankalina yaki ya kwanta, inason Modibo sosai bazan iya zama dashi tare da wata ba, hawaye Safna ta share tana cigaba da fadin, Momy yadda ake gyara gurin nan jikina na bani aure zauyi, mace zai saka aciki  dakin nan

Safna tunda kin sa azuciyar ki aure zai yi dole ki kasa kwanciyar hankali, yanzun abun da za’ayi ki tambaye shi cikin siyasa.

                        ****

Shirye shiryen biki nata kankama, tundaga ranar da sukayi waya da Modibo ta saki jikin ta, shirye shiyen biki suketayi ita da Afnan duk wani shiri da akema Afnan anawa Unaisa, komai iri daya Ammi ke cewa amsu, dan haka ha yau daya rage sauran kwana shidda bikin shiri su kawai suke yi, Afnan  rawar Kai ita da Kabir dinta sai abun da yai gaba.

Babu wadda ya sake mata mgnr tarewan ta kwata kwata cikin gidan, batayi mamaki domin Bata taba ganin Modibon yayi Alkawari batare daya cikasa, abun daya kara kwantar mata da hankali tun daga ranar be Kara kiranta a waya, ko dakin Ammi basa wani had’uwa.

Da Unaisa ko Afan wani ya gifta ka zaji wani uban kamshi na tashi sabo da iri gyaran da ake musu.

Yarage saura kwana biyar bikin aka Kai kayan Afan gidan mijinta, Yadikko da Safna ne zasuje domin a jera komai a gaban su.

Misalin biyar da yamma suka dawo, Yaddiko ce ta fara shigowa Safna nabin ta abaya cikin yanayin dake nuna agajiye take.

Adaidai lokacin da Unaisa ta mike zata fita tana fadin, Yadikko barin je in dawo kiji, Kamshin daya daki hancin Safna yasata kallon ta, wani irin kyawun fuska da cikar sura tagani, rabon dataga yariyar tama manta, duk yadda ake son cikar budurwa ta cika buleliya komai yaji, kyallin da ta hango saman tsinnin hancin ta ya dauki hankalin ta, nan danan taji wani irin bacin rai, wani abu ne me azabar radadi ya tsaya mata a wuya, ganin Unaisa na Shirin gota ta ga wani maya taccen Kamshi  da yake dukan hancin ta, yasa tai karaf tasha kwalar Unaisa tare da fadin, Ke!! ni kika bangaza?

Cikin Ido Unaisa ta kalleta sannan tace, ni?, ayaushe na bangaje ki?

   Tambaya ta kike yi?

Dole in tambaye ki tunda bansan lokacin da nagogi jikin ki ba bare har na bangaje ki.

Toh nace kin bangaje ni ko zaki dake nine?

Akan me zan dakeki tunda ba dukana kikayi ba, kince na bangaje ki toh ki sakeni in wuce Allah ya baki hakuri.

Ammi da Yadikko ne suka mike suna musu tsawa tare da karasa wajen.

Safna ce tace Yadiko bakiga abun da take ba Kamar zata dake ni.

      Jin Anturo kofar duk suka maida hankalin su ga kofar, Modibo ne da alaman yazun ya dawo aiki, kallon Mamaki yabi su dashi, Safna rike da kwalar Unaisa.

Ammi ce ke fadin yawo toh shigo ka gani.

Bakin kofar ya tsaya yayin da Rahma tau saurin dauke kanta daga kofar ta mayar kan Safna tana fadin, ” ki sake ni in wuce?

Bazan sake kin ba ko akwai abun da zakiyi?….

Tun kafin ta rufe baki Unaisa tasa hannun ta ta ture na Safna da karfin tsiya saidai tana kokarin gyara wuyar rigar tata taji ta daura mata mari yayin da taji Ammi da Yadikko sunai mata tsawa, tare da cema ma Moddibo kai baxaka mata mgn bane?

Saidai Basu Ankara ba suga Unaisa tasa hannun ta tasha kwalar rigar Safna tare da daga hannun ta da nufin kai mata mari saidai jin tsayawan su Ammi yayi yawa yasa ta kallon su sannan ta juya ta kalli Modibo daya kalmashi hannun sa akirjin sa Yana kallon su kawai, sauke hannun ta tayi a hankali tare da  kallon cikin idon Safna da duk ta fito da idon cikin yanayin dake nuna taji Mamaki tace, ” kinci darajar mijin ki.

Harta nufi kofar ganin Modibo agurin ta koma can bayan Ammi ta zauna, itako Safna wani irin kallo tabi Unaisa dashi sannan ta nufi kofar da Modibo ke tsaye……

8 comments

  1. Pingback: Herbalife business
  2. Pingback: more tips here

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *