
BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido
Page 4
Mikewa Dattijon yayi da saurin sa tare da kama kafada Unaisa ya dagata yana fadin wacece wannan?
Adaidai lokacin Modibo ke shigowa ya tsinkayi Muryan Ammi tana fadin, ” wai matar Modibo ce.
Matar Modibo?, Dattijon ya tambaya da tarin Mamaki a tattare dashi, ahankali ya maida kansa gurin Modibo yana fadin ban fahimta ba Modibo?
Kawar dakai yayi can gefe, zuwa can ya juyo ya kalli Ammi yace, ” Ammi inace jiya mun gama mgn?
Kan ya rufe baki tace jiya ban fahimta bane, Saida Magaji yazo ya warware min komai, bazai yiyu ba Modibo, wlh bazan amince da wannan ba.
Ku dakata ku cireni a duhu, har yanzun bana fahimtan ku fah, Modibo zo ka zauna”
Karasawa yayi ya zauna ransa ahade daganin sa kasan yana cikin bacin rai.
Shima Abban nasu komawa yayi ya zauna yayin da ya zaunar da Unaisa saitin kafar sa.
Gurin zama ya nunawa Ammi tare da fadin, maman yara kwantar da hankali ki kizo ki zauna.
Afusace ta zauna tana tsananin huci.
Abban ne yace inajin ki wani bayani Modibo ya miki.
Kamar yadda Modibon ya gaya mata haka ta gaya ma Abban su sannan ta gaya mata abun da Magaji kuma yace.
Shiru Abban yayi tsayon lokaci sannan ya kalli Muftahu da Suraj dake tsaye yace da gaske mgnr Magaji haka ne??
Tabbatarwa da Abban suka karayi, tsayon lokaci Abban ya dauka yana nazari zuwa can yace, ” abu daya ne zaisa nace banji dadin wannan abun ba Modibo, shine rashin shawara, Ina da hakki da yadace ace ka sanar dani, har yanzun da tsufan nan nawa banayin komai saida shawaran mahaifina naso ace kafin ka zartar da wannan hukuncin ka gaya min shima ya sani bayaji daga sama ba, abaya fa yata mgnr ka kara aure amman Sam kaki, sai yanzun da ya riga ya nema maka aure da kansa sai yaji mgn daga sama kawai.
Ahanki yace Abban wai wannan Shirin Allah ne ba shirina bane….
Tunkan Modibo ya rofe baki Abba yace, “kwarai kuwa shirin Allah ne Modibo, ta wani bangaren naji dadi da ka zabi mata da kanka dan waccen ma bakaine ka zaba va.
Alhaji wannan ba zabin shi bace, yafi karfin yariyar, kuma kwata kwata babu gaskiya acikkin wannan lamarin, Magaji ya tabbar min yariyar nakasheshiya ce, tarasa wani abu, bama wannan ba, yace halittan na firgitar wa gareta, ban Dana abun Modibo menene nashi na auren yariyar da betaba ganin fuskarta ba?
Cikin saurin Abba ya dauki gilashin sa ya maida a idon sa yana fadin, maman yara ni duk abun da Modibo ya kawo shi Ina daraja shi, batun yariya kuma ko Yaya take tunda yace yaji ya gani wannan ba matsala bace, karfa ki manta anyi daya ba’aji dadi ba, dan haka mu yanzun mun gaji da kyau hali muke nema, juyawa yayi ya kalli Modibo yace ko Malam?
Sunkuyar dakai Modibo yayi adaidai lokacin da Ammi ta bude baki da nufin yin mgn.
Abban ne yai saurin daga mata hannu tare da fadin, ” nifa vana son kana nan mgn, duk wadda ya raina tsayuwar wata sai yahau sama ya gyara.
Shiru falon yayi babu me mgn kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Ammi kuwa ajiyan zuciya take ta saukewa tsayon lokaci.
Abban ne yayi gyaran Murya tare da kallon Unaisa yace, ya sunan diyar tawa?
Cikin sauri ta kara kasa da kanta tana wasa da hannunta ta cikin hi ijabin .
Tunda Modibo yaga Abba na mgn da ita ya daga kai ya kalli ta, ji yayi Abba ya sake fadin yariyana mene sunan ki?
Ganin abun da take ya sani Sarai bazatai mgn ba dan haka yaji ya kule da ita cikin tsawa yace, Ke! bakiji ana mgn dake ne?
Cikin siririyar Muryan ta tai saurin fadin Rahma, adaidai lokacin da Abban kema Modibo fada akan tsawan dayake mata.
Ammi kallon yariyar kawai take cike da takaici sannan ta kalli Modibo da yaketa mazurai.
Suraj Magaji da Muftahu kuwa ba haka ransu yaso ba dan haka gaba dayan su idon su yake akan Unaisa.
Yawun takaici Ammi ta hadiye, domin Abban su ya toshi duk wani abu da tai kudiri, dan haka ta tsinta kanta da cewa, ” shikenan, tunda ka goya masa baya, yanzun ai saita bude idonta muganta ko?, mgnr boye boye kuma ta kare, tabude mugani.
Cikin sauri Modibo ya daga kai ya kalli Unaisa da ya hangi rudewa a tattare da ita, gaba daya kallon su Magaji gurin Unaisa ya koma, lura da Ammi tayi yariyar ta firgita yasa ta nufeta gadan gadan.
Ahankali Unaisa tafara ja da baya saidai Ammin tafe take da sauri dan haka ta cin mata cikin sauri ta Mika hannun ta da finciki ni’kabin tare da daura idonta akan fuskar yariyar.
Ya subuhanallahi shine kalmar da Ammi ta fada da karfi bayan ta daura idonta ya tabbatar mata da fuskar yariya.
Cikinfiriki ce suka mike tsaye har Abba, sl nufu su sukayi Domin Ammi baya ta Basu.
Modibo na zaune inda yake be motsa ba, sai dai hankalin shi da idon su gaba Yana kan su, kokari yake shima ya daura idon sa a Kan fuskar ta.
Abban ne ya daura hannun sa akafadar Ammi tare da matsar da ita gefe, kusan atare suka daura idon su akan fuskar Unaisa, lumshe Ido Modibo dayayi batare da ya shirya ba. Tsintan Muryan Magaji yayi yana fadin, Kutumelesi 😬, Suraj kuwa fadi yake lahaula fisha’atillahi.
Shikuwa Muftahu yama kasa mgn gaba daya, idonsa akan Unaisa fuskar sa dauke da Mamaki karara.
Ammi ma kasa mgn tayi saidai ta kalli fuskar Rahma sannan ta kalleta har kasa tana kwantanta tsayin ta, ganin duk wanan abun bazai yiwuba tai saurin daga Unaisa dake sunkuye da kanta akasa ta mike tsaye, hannu tasa tana kokarin yayi hijjabin Rahma, ganin abun da take Shirin yi Abban yai saurin cewa a’a karki haka, saidai aikin gama ya riga da ya gama dan Ammi tana rike hijjabin yaye shi tayi, ganin haka Abba yai saurin komawa ya zauna.
Unaisa tsaye take gaban Ammi ta sunkuyar da kanta, dogowar rigace jikinta ta atamfa, baza’a ce ta kamata ba dan bata fitar da Surar jikinta sak ba, kanta babu dankwali dan haka kalabar dake kanta ya sauka har gadon bayanta, kasa daina kallon ta Ammi tayi hakama Magaji Suraj Muftahu da duk sukayi suman tsaye.
Zufa Ammi ta share sannan tace, tirkashi, shagalin buga tsalle da jijjaga hawa katanga bana me ciki bane, kuga ikon Allah.
Abba ne yayi dariya tare da Mika hannun sa ya shafa kan Modibo tare da fadin, ” a toh wannan shine dalilin da yasa bana daukan duk wani abun da Modibo zai kawo da wasa.
Har yanzun Ammi Rahma take kallo yadda ta sunkuyar dakai tsinnin hancin nan kamar zai shige baka, suturar jikinta ammi ta kalla duk da ba wata suturar arziki bace sun mata kyau ajikinta, gashi kunnenta ko dan kunne babu, cike da mamaki ammi tace cikin zuciyarta, ji yarinya babu kwalliya ko daya afuskanta ta zuba uban kyau.
Abban ne yace toh ya isa haka duk kuzo ku zauna.
Ammi ce ta mayarwa Unaisa da hijjabin sannan ta zauna saman kujera tare dabawa Unaisa Umarnin ta zauna.
Zama tayi saitin kafar Ammi.
Gyaran Murya Abba yayi sannan yace, ” abun da nake son ku gane yanzun anan shine komai nufin Allah ne, yanzun addu’a daya ce zamu rakashi dashi shine Allah ya bashi ikon rike su da amana.
Jin Abba na mgnr adalci Magaji yai saurin ficewa Afusace, ganin fitan sa Suraj yace Modibo saika fito, bayan Magaji yabi dan haka shima Muftahu ya rufa masu baya.
Abba da Ammi Basu lora da komai daga gare su ba, Dan tunatarwa yaiwa Modibo sannan ya sashi agaba zuwa wajen Mai Marta ba dan kada yaji daka sama.
Ammi kuwa tana rike da hannu Unaisa ta suka koma part dinta.
Binta da kallo take yi har suka isa, cikin kankanin lokaci ta hada mata ruwan zafi, har cikin toilet din ta bita tana nuna mata yadda zata yi ammafani da wasu abubuwan, acikin ranta take fadin yariyar kuma Bata da kyauyanci.
Zuwa can ta fito tana sanye da hajjabin ta yayin da take share hawaye.
Rahma, har yanzun bazaki bar kukan ba?, ki saki jikin ki kibar dardar, zama ne me tsaye ya kawoki nan ba gutun zama ba, sa’anan Allah ya sakoki cikin zuri’a me yawan gaske, dole sai kin saki jikin ki, Modibo mutumin kowa ne, kema sai kin rike kowa ya zama naki.
Hawaye kawai Unaisa take sharewa
Wasu kaya Ammi ta Mika mata tare da fadin, wannan kayan Afnan ne, kisa kafin asawo miki naki, wannan karon Batai masu ba karba tayi saidai tana saka kayan taji tana yawo aciki, babban burinta kawai a kawo mata ni’kabin ta, tunda matar ta cire batasan inda ta cilla matashi ba, sai tanajin ta tamkar tsirara take, hakama hijjabin ta dan haka taji duk hankalin ta ya tashi tunda ta fara nunuwa har bacci da hijjabi take yin sa komai zafi,
Duk abincin da akaita jera mata kin cin sa tayi, Ammi nata mgn harta gaji tai shiru falo ta koma tabar Unaisa cikin dakin, kuka take sosai dan har yanzun zuciyarta ta kasa sukuni.
Misalin kaefe biyu na rana Modibo suka shigo tare da Ammi, kallo d’aya ya mata ya dauke kai tare da fadin, Ammi saikin dinga zare mata Ido, tana da rainin wayau.
Kallon Unaisa tayi tace a’a rashin sabo ne, abinta a hankali, gatanan kasata taci abincin. Juyawa tayi ta fita, kallo d’aya Modibo ya sake mata sannan yace, dauki abincin nan kici.
Da saurinta tace, “nina koshi, dan Allah ka maidani dakin Innawuro, jiya ban banci, ban taba Kona ko Ina ba, ni nafison naganni ni daya, nagode da taimakon ka hakama ya isa.
Shiiiii🤫 maza ki rufe min baki, kuma ki dauki abincinan kicinye shi, mikewa yayi fuskarsa daure tamau yana cigaba da fadin, ” zankira Ammi awaya inji kinji ko bakici ba, sannan kuma zan gargade ki, kada na sake ganin ko labarin Ammi na miki mgn kina mata banza, ke bama Ammi ba, kowa Kika gani ki gaisher, inba mara hankali ba waye ake mishi mgn Yana barin mutane?, da hankalinki kinaji kina gani, toh na sake ji, kuma gidan nan kin shigo shi kenan har abada kicire azuciyarki zaki barshi, kinyi na farko kinyin na karshe karki sake kallon idona kicemin in maidake gida, bari kijima na gaya miki ni bana wasa duk ranar da Kika kara min zancen gidan sawa zanyi a rusa shi
Idonta ya gani awaje, sosai yaga wani sihirtacen kyau a tattare da ita, duk da beson ya cika kallon ta Amman ya tabbatar wa kansa
Tafiya ya fara yayin da yaji ta fashe da kuka tare da fadin, ” toh ni Ina ni’kabi na ?
Batare da ya juyoba yasa hannun sa ajikin karfen sa ta kasa yana me nuna mata ni’kabi dake daure jikin karfen, tafiya yacigaba dayi bayan ya tabbatar tagani.
Wahawaye Unaisa ta share bayan ya fice sannan ta hadiye wani abu daya tokare mata akirji ki gaba yaki ba,
*****
Bango yake duka iya karfin sa, zuwa can ya tura hannun sa cikin gashin kansa tare da zagayo tashi Kan fuskarsa ya share hawaye, kasa kasa yake fadin, nashiga Uku, zuciyata zata dauwama da bakin ciki, Allah mena maka?, kenan ni bani da sa’a a rayuwa ta?, Modibo ne me sa’a?, Buga kofar da ake yasa shi saurin fadawa toilet yanawanke fuskar sa tare da bada Umarnin shigowa.
Yajima ciki sannan ya fito yana goge fuskarsa,
Suraj ya gani shida Muftahu, idon Suraj jawur yace Magaji zan wuce gida Modibo yayi abun da yayi ya malle yariyar nan, wannan shirine, Ko shakka banayi ya taba ganin ta ne, kuma shine ya hanata ta bude idon ta.
Ajiyan zuciya Magaji yayi sannan yace, ” ni kuma bana ganin haka, idan ka kula dashi ba son yariyar yake ba, taimakon ta kawai yake son yi ni yanzun na shiga rudani bazan iya juran ganin yariyar ba wlh, nikadai nasan menakeji wlh harna gammace damun barta acen kowa ma ya rasa.
Suraj ne ya kalle Muftahu yace, Kai kuma mene tunanin ka.
Hmmm aini banda ta cewa, amman tabbas nayi Dana sani, abu daya kawai zanyi yanzun.
Meye shi Magaji ya tambaya?
Addu’a, Allah karya daurawa Modibo sonta…
****”
Modibo ne zaune cikin wani katon falo, wannan karon babu karfe akusa dashi, kwata kwata, tv ya zubawa Ido fuskarsa babu wasa.
Idon sa akan Tv yace, fushin me kike?
Kyakyawar matshiyar dake zaune agefen sa ce tace, bakomai
Murmushi yayi kadan tare da gyara zaman kafafun sa yace zonan.
Mikewa tayi tana zunburan baki ta isa Kan jinyarsa me lafiyan ta zauna, saidai har yanzun cikin yanayin fushi take.
Hannunta ya rike duk biyun sannan yai saurin tura kansa wuyanta, wani irin sihirtaccen sumba yakai mata wadda yasata lumshe Ido tare da saurin ture kansa.
Dagowa yayi ya daura mata shanyayyun idon sa tare da fadin, wani abu ne?
Cikin yanayin shagaba tace, ” kanafa ganin nama kwalliya bakace koma ko kallo na bakayi saima Tv daka zubawa Ido.
Kallon ta yayi sama da kasa sannan ya mika hannun sa yaja dan guntun siket din dake jikinta tare da fadin, wannan ne kwalliya?
Idon ta sauke a nasa tare da fadin, ba kwalliya bace?
Hannun ta ya sarki da nashi Yana fadin, ” kwalliya ce amman fa ni mafiyawan lokaci nafison na bude da kai na, kin san bahaushe na cewa in zaka huta toh ka huta a babban inuwa, sa hannun ki ki taba jikin kiji…
6 comments
Comments are closed.