Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 page 5

Posted by

BA LABARI BOOK 2 page 5

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido

Page 5

Hannun nata ta tura acikin jikin sa yayin daya bita da Ido tare da fadin me kikaji?

‘Dumi.

Toh dole wata rana inason inji jikin ki ahaka, wannan suturar da kike sawa ni dai Kamar nagaji da ganin su.

Turbine fuska tayi da sauri sannan ta tashi daga jikin sa ta koma gefen sa ta zauna.

Hannun sa ya kara mikawa ya rike nata, ke har yanzun baki da wayau, ban son yawan fushi nan

Toh Hamma Modibo bakaine komai ka dinga nuna mutum bemaka daidai ba.

Ai saiki tsaya ki saurareni ko?, Idan nagama wadda be miki dadi ba saiki min mgn akan sa.

Toh Ina jinka.

Dauke kansa yayi daga gareta sannan yace, nina fison komai ya dinga juyawa bana son ana abu kullum ana maimaitawa, karki dauka kawai kullum kisa kananan kaya shikenan ki motsamin sha,awa a’a dole wata rana akwai bukanar canjin launi, akwai hirarraki na jawo hankali da abubuwa da dama, ke macece ki fad’ad’a tunanin ki domin ki dinga yin abin da ya dace.

Hmmm, kai dai kawai kace min ka had’u da karuwai acen sun bude maka Ido.

Ko danan cen idona a bude yake, kuma ni agidan ustazai na sauka, kurame Babban hijjabi da ni’kabi, nasan bayau na fara gaya miki bancika son wannan shigar ba, wannan gidan akowanni lokaci ana iya fad’owa, ke ko ajikin ki ko?

Shiru kawai tayi dan ya saba mata irin zantukan da ba fahimtan shi take ba, mikewa tayi afusace ta nufi daki, murmushi yayi Yana bin bayanta da kallo, acikin zuciyar sa yake fadin naga ranar da yariyar nan zatayi hankali, mikewa yayi yabi bayan ta, wannan karon be dauki sandarsa ba dan yanaji ajikin sa zai iya taka kafar domin sosai ya gaji da karfen.

Samunta yayi ta kwanta ruf da ciki, tsaki yaja jin tsakin sa yasa ta tashi zaune da sauri tana share fuska.

Hannun sa yasa a aljihu sa duk biyun sannan bazai yiyu ace kinyi wani abu bazan gaya miki ba, juyo ki kalleni da kyau, juyawa tayi ta kalleshi manyan kaya ne ajikin sa shadda da babban riga tare da hula akan sa, tajima tana kallon sa shima kallon ta yake zuwa can taji yace, ” yadda nake a haka sai ashigo ke a ganki ahaka?, kinga abun ya miki tsari?

Aina aje hijjabi afalon in naga bako Ina sakawa.

Jimmm yayi, zuwa can yace, toh yanzun Umarni kawai zan baki tunda ke baki do fahimta, kisa irin kayan nan iya daki kawai, ko Ina nan ko bana nan.

Amsawa tayi kawai da toh, dan ta lura fitinan shi ne ya motsa, ficewa yayi adakin batare daya sake cewa komai ba.

Hawaye ta share sannan ta dauki wayatta ta danna ta kara akunnen ta, zuwa can ta kara karfin kukan ta, Saida ta dan jima tanayi sannan tace, Momy

Na’am safna, yau ninaga ikon Allah har an fara ko?

Momy tunda ya dawo aburkice yake fa.

Hmmm Safna kema bakijin mgn, d’azon na acemin sunje sunje gidan Baba, meke faruwa agidan?

Rasa ta inda zata fara tayi daker ta iya daurewa tace Momy wai dan tsabar wulakanci namai kwalliya wai beson irin ta.

Hmmm Safna Modibo kutson Mutumi ne, idon shi bude yake, yaron na bani tsoro fiye da tunanin ki, halin shi na daga min hankali, gashi idan ya kafe akan abu ya kafe kenan, halin su daya da yariyama komai nasu iri daya ne babu inda ya baroshi, shiyasa ma tasu tafi zuwa daya.

Momy ba halin su daya da Abba ba Abba ai yafi Hamma Modibo kirki.

Ke kike ganin haka, lokacin da muke yara sai mun gama shirya Shirin mu tsaf rana daya Yarima zai wargaje shi, inda Kika San Yana gani har hanci, to haka wannan dan nasa yake Modibo, shikadai ne ya dauko uban shi, yanzun ingaya miki wata mgn zaki iya jurewa?

Cikin sauri tace Eh Momy

Ashe su Modibo da zasu dawo sun taho da bakuwar yariya?

Cikin tsananin faduwan gaba tace, ” a’a”

Ya zakice min a’a, bayan an tabbatar min yariyar nan gurin Ammin sa.

Momy Basu dawo da kowa ba, har gaban motar naje taryan su lokacin su kadai suka dawo.

Allah sarki Safna, har kin ban Tausayi, Modibo ya raina miki hankali, toh ki bude kunnen ki kijini da kyau, naji kishin kishin din Modibo ya dawo da mata.

Cikin sauri ta tafe kirjinta tare da fadin, Momy? kirjin ya buga dagaske ko wasa?

Ina wasa dake ne?

Momy wacce irin mata, kina nufin aure yayi ne?

Safna, Modibo yayi aure, tun da labarin ya sameni naita jiran inji wayarki yanzun ma na dauka zancen da zaki min kenan.

Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un, Momy waye ya gaya miki?

Safna magana dai ta karad’e Babban gida nidai babu wadda ya tare ni da zance.

Mikewa Safna tayi zufa na karyo mata Momy yanzun meye abun yi?

Ai ki nutsu kawai, Safna, wannan mijin naki Yana da matsala, gashi da zurfin cikkin tsiya…

Momy bashi da zurfin ciki kana masa wani abu yake gaya maka, idan mgn ce ma kafin ka gama fada ya baka amsa.

Safna bakya fahimta ta, amman Modibo ba inda ya baro Ubanshi, yanzun saidai mu zura Ido muyi kallo dan gudun kada nakiya ta tunu garma, karkice zaki tareshi da mgnr ko ya fada miki karki nuna tashin hankalin ki, basai na koya miki yadda zakiyi ba, ki dake sosai ni kuma zan nuna miki kina da gata.

Cikin matsanancin kuka Safna tace, Momy Allah bazan iya ba, yanzun Nan ma kirjina zafi yake min.

Nace ki kwantar da hankali ki, iri irin mu basa zama da kishiya.

Daker suka sauke wayar sosai Safna ta kara shiga damuwa sai dai tana ta kokarin daurewa Kamar yadda mahaifiyarta ta fada.

Har dare ya raba ta kasa zuwa dakin Modibo, shikuma be nemeta ba da safe ma bata iya lekawa ba, duk da tana cewa tana tantama amman balakin haushin sa take ji, tsintan kanta tayi da son zuwa part din Ammi saidai wata zuciyar na hanata zuwa domin tana kwashe sati daya zuwa biyu Bata leka part din Ammin ba.

Shikuwa Modibo har Sallah asuba yau yaje da kafar sa, saidai yana dingishi kadan, ganin har goma na safe bega Safna ba yai tunanin fushi take har yanzun saidai ya dau alkawarin bazai rarrasheta ba dan bega abun fushin ba.

Misalin goma da rabi yunwa ta isheshi, dole ya mike har ya nufi falo wata zuciyar tace masa yaje yaga lafiyarta dan haka ya juya zuwa dakin, tura kofar yayi da Sallama a bakin sa.

Zaune ya sameta kan gado ta mike kafarta tare da hade hannunta Kan kirjinta, kallo d’aya ta masa ta dauke kanta har ya karaso gaban ta, batare da ta kalli ko gefen sa tace Ina kwana?

Lafiya lau, lafiya kike kuwa yau?

Lfy Lau ta sake fada tana dauke kanta.

Toh yayi, ganin ya nufa kofsr ta tsinta kanta da cewa, Ina zaka.

Gurin Ammi ya Bata amsa a gajarce

Wani irin kulolon abu ne ya tokare mata awuyan ta adadai lokacin da yake shirin sakin kofar tace, Hamma Modibo?

Juyowa yayi kad’a tare da zuba mata idon shi.

Itama idon ta ta daura anashi Hamma wai da gaske ne kayi aure?? karake mgnr tayi da tsiyayowan hawaye

Dawowa yayi da saurin sa fuskarsa dauke da Mamaki dan beyi tunanin zata iya jin mgnr ba, zama yayi gefen ta tare da saka hannun sa yana share mata hawayen dake zubo mata tare da fadin Safna menene haka?

Hamma aure fa akace kayi? Kara fashewa tayi da kuka dan haka yai saurin jawota jikin shi ya rungume tare da daura kansa anata yana fadin, yi hakuri kinji, kwata kwata ban tsammaci haka daga gareki ba, ganin shekara uku da suka wuce kinata matsa min nayi aure.

Amman Hamma hankalin yanzun ya tashi sosai bansan me yasa ba, yanzun Hamma da gaske ne kenan?

Shafa kanta ya shiga yi ahankali tare da fadin, Da gaske ne Safna, kuma abun da yasa ban gaya miki ba yariyar karama ce sosai, auren ma Allah ne ya kawoshi kawai, amman yariyar kankanuwa ce Ina tunanin Afnan ma tana iya girman ta.

Daker ta iya hadiye yawu tare da fadin, ai ta girma Hamma.

Sumbatan ta yayi tare da fadin, a’a da saura, tana gun Ammi na bar mata ita.

Wani irin Safna taji duk kokarin ta na ta daure ta kasa, duk da cewa ko ada tana balakin son Modibo amman sai take ji Kamar ada ba son shi take ba yau ne ta fara son shi, wani balakin kishi ne ya taso mata, gashi wai yariyar ma dan gata ya mata yawa dakin Ammi aka barta, ahankali tace a’a ta tare kawai anan inaga zaifi, babu amfanin zamanta acan din

A’a sam ba yanzun ba..

Hamma zaifi.

Safna! Wannan ba hurumin ki bane, abun da nake so kawai dake ki kwantar da hankali ki, karki ce zaki tashi hankalin ki, shekaran mu biyar muna tare yakamata ace kin san halina.

Shiru kawai tayi Bata sake cewa komai ba tana kwance jikin Modibo Yana shafa bayan ta amman ji take kamar ama hura mata wuta azuciyarta.

******

Rahma kin gama ne.

Eh ta ce ahankali.

Yauwa to kwashe kayan ki kaisu kitchen.

Mikewa tayi ta kwasa kayan Kamar yadda Ammi tace, kofar dakin ta bude ta fito, tafiya kadan ya sadata fa Babban falon gidan, gaba daya saita rasa Ina ma zata bi, tafiya ta fara tana tafe tana waige waige harta gota wata kofa taji Kamar kamshi na tashi kadan kadan dawowa tayi da baya tare da sa hannun ta ta tura kofar, wata dattijuwa tahanga tana girki dan haka ta isa in da taga Kamar Nan ake ajewa ta aje sannan ta juyo.

Dakin Ammi ta sake komawa tana kokarin zama a kasa Ammi tace zonan ne Rahma.

Ahankali ta karasa gabanta ji take kamar tsirara take gefen ammin ta zauna ahankali Ammi tace,

” Rahma kinga dai zama ne Allah ya sakoki kiyi acikin mu, to kibar takura kan ki, ki saki jikin ki, domin ki samu canjin rayuwa, ni Ina son ki daukeni uwa, duk abun da kike so aduniyar nan indai be sabawa addini ba zan miki shi, gani kinki sakin jikin ki damu yasa na tura adauko Afnan, idan kina ganin ta kyafi jin dadi, kuma da hutun makaranta ya kare tare zaku tafi, daidai kike da kowanni d’a na cikin gidan nan, kuma nasan halin yarana bazasu taba nuna miki banbanci ba, duk abun da kike so naci Kona sakawa duk kimin mgn ko wacce irin damuwa kike da ita ki gaya min kinji ko?

Kaita daga yayin da Ummi ta bita da Ido tana fadin Kamar da mgn abakin kiko?

Sunkuyar Kai tayi ahankali tace dan Allah kice mishi karya yasa a rusa mana gidan mu.

Jimmm Ammi tayi sannan tace hauka yake? ai bazai ma fara ba, ko haka yace da ke?

Ni inason na koma gida ne, shine yace idan na kara mgnr gida zaisa a rusa mana gida, karake mgnr tayi da kuka cikin sigar lalashi Ammi tace,

Karki kara ce masa toh, ni duk sanda kikaji son gidan ni ki gaya min, Umarni kawai zan bashi.

Amsawa tayi cike da gamsuwa sakin ta Ammi tayi ta fita adakin.

Bata jima da fitaba taji an turo kofar tare da fadin Ammi!

Da firgice Unaisa ta waigo sukayi Ido hud’u, Magaji ne tagani saidai yau fuskarta daure take.

Tsakiyar dakin ya tsaya sannan ya sake kwalawa Ammi Kira.

Jin Ammi Bata amsa ba yabi Unaisa da Ido yana kallon wani kallon raini da take masa, dama ya saba ganin tanama Magaji irin wannan kallon saidai shi bata taba mishi ba sai yau Dan haka abun ya daure masa Kai.

Fuskar shi dauke da kallon Mamaki yace ke bakiji Ina Magana ne Ina Ammi??

Yadda yayi mgnr yasa ta amsa masa da Dan karfi irin na wadda aka tilas ta masa tace, Bata nan!

Zaro Ido yayi tare da fadin, ” ke! nine kikewa mgn haka.

Kara juyawar da kanta tayi tare da zunburo baki.

Afusace yayi kanta adaidai da Ammi da Magaji suka shigo yayin da Unaisa ta saka kara.

A’a Modibo Yaya haka kuma?

Jin Ammi tace Modibo tai saurin kallon kafar sa, dingishi takula yanayi, nan danan ta dawo hankalin ta hannun ta tasa tana kare fuskarta tare da fadin yi hakuri na dauka d’ayan ne?

Ammi ce ta fashe da dariya yayin da har yanzun Modibo ke kokarin rike kunnen ta, cikin matsanancin dariya Ammi tace, “Modibo bari kaji ita ta dauka Magaji ne,

Hannu Magaji yasa ya riko na Modibo suka koma suka zauna, Satan kallon su take sosai sike daburta ta, Ammi ce tace Rahma ashe baki iya banbancewa tsakanin Modibo da Magaji, shikuma Modibo ya zage karfi da yaji taka kafarsa yake, kuma suna fa da banbanci sosai, taho ki zauna in nuna miki banbancin su.

Ahankali Unaisa ta karasa ta zauna kusa da Ammi, saidai idon ta akasa yake.

Kalle su in nuna miki, Ammi ta fada fuskarta dauke da dariya.

Ahankali ta d’aga idonta ta kallesu yau fuskar su iri daya ce duk sun kirni fuska dan haka suka kara rikitata.

Ke idan Kika kallemu saina fasa miki Ido, Modibo ya fada idon sa akan Unaisa.

Fashewa Ammi ta sake yi da dariya tare da fadin kallesu barjin tsoron sa.

Dagowa tayi kadan suka hada Ido da Modibo, irin kallon nan kisake kallo na ki gani yai mata cikin sauri ta sunkuyar da kanta, yayin da jikinta yadau rawa.

Jinan Rahma kallesu in nuna miki…

 

 

 

 

 

5 comments

  1. Pingback: top cams
  2. Pingback: Mostbet
  3. Pingback: situs toto

Comments are closed.