
BA LABARI BOOK 2
By
Fadeela Lamido
Page 6
Kasa dago idonta tayi yayin da takeji ajikinta gaba dayan ita suka zubawa Ido.
Rahma dago idon ki Mana ki gani.
‘Kasa ta kara da kanta sosai tare da wasa da yatsun ta.
Ammi ce ta dago ta kalli Modibo sannan tace, wai me kake ma yariyar nan ne take tsoron ka har haka?
Dan murmushi yayi ma Ammi, itako Unaisa gaba daya diriricewa tayi tare da ‘kosawa su fita, amman saitaga am kawo musu abincin sun fara ci, wani abu data lura dashi tsakanin Magaji da Modibo Kamar basa jituwa sosai abincin ma kowa nasa daban aka kawo masa.
Suna tsaka da cin abincin ne Ammi tace ya kamata yau kuje ku Kara gaisawa da Mai martaba, Abban ku yace gobe zasu koma.
Nikam ya sauka lafiya Ammi bazani ba, jiya yata min fada karmar wani ubana.
Ai dole yayi fada Modibo ka bashi hakuri ko?
Bakan na masa Ammi har ya gama.
Lallai kanajin rashin kirki ka kasa bashi hakuri?
Juyawa Ammi tayi ta kalli Magaji tace kaiko yau lafiya kake!?
Kaina ne yake min zafi Ammi.
Zafi kuma?
Eh Yana ciwo ba.
Toh sannu Allah ya sauwa ke.
Amin yacez yayin da Modibo ma ya d’an karkata yace, ” sannu idan ka gama ka nemi magani.
Amsawa yayi ta toh sannan yaci gaba da juya cukali har Modibo ya gama Magaji ya kasa saka komai a bakin shi.
Ammi ce ta sake matsa matsu akan cewa lallai suje suyi Sallama da Kakan su dan haka suna gamawa can suka nufa.
Suna fita Unaisa taji Kamar an zare mata ‘kaya har wani sanyi taji jikin ranta.
Zaman su sukayi ita da Ammi yayin da Ammin ke yawan janta da mgn dole take amsa mata sabo da tsoron karta gayawa Modibo.
Sai dare take komawa dakinta wadda take wuni a na Ammi, dakine Babba kusan girman su daya dana Ammi, komai na dakin mekyau ne, duk da shaida haduwar dakin amman komai baya burge ta, abu daya kawai yake sawa taji sanyi idan ta tuna yadda Ammi ke kokarin jawota jikin ta, afili tace wanccen Modibon kuwa yanzun ya canza hali, ko kirki bashi da.
Tun daga wannan rana bata bari su sake haduwa dasu Modibo adakin ba, dakin da aka bata take cin abincinta sai misalin daya take komawa dakin Ammi ranar da ta cika kwana 4 agidan Afnan ta dawo, sai alokacin ta lura dakin Afnan ne aka bata, murna sosai Afnan tayi da ganin Unaisa duk da cewa bata Santa ba, wannan dalilin yasa har tayi sati biyu agidan basu hadu da Kowa cikin su Modibo ba.
Saidai ta lura da Afnan basa shiri da Magaji sosai, domin tana yawan yin waya Modibo tana kai masa karan Magaji tare da yawan kiran sunan sa.
Yau Afnan tana idar da sallah asuba ta wuce dakin Ammi sai misalin goma na safiya ta dawo hannunta rike da manyan ledoji ajewa tayi tsakiyar dakin tare da fadin, Rahma tashi ki gani.
Tashi tayi zaune ta kalli kayan alokacin da Afnan ke fitowa dasu, kayan sawa ne na mata dinkakku nau’i daban daban, d’inkuma ne na zamani basu kyan gaske, duk da cewa din kunan sunyi kyau amman cike da mamaki take kallon rigar tare da fadin, ” kuna da karamar yariya ne agidan Nan?”
A’a me Kika gani?
Kayan ne naga kamar na yara.
Kut lallai kayan ki fa, ranar nan mukaje da Hamma Modibo muka sawo su, sannan muka bada dinkin su.
Ni?, Wannan ai bazasu min ba.
Zasu miki tashi kigani kuma.
Kai a’a basai na gwada ba.
Mikewa Afnan tayi da riga daya a hannun ta tana fadin wlh saikin gwada
Ganin Afnan ta tunkaro ta ta fara kokarin kare kanta tana fadin toh Bari da daddare saina gwada.
Bayanta Afnan ta koma cikin sauri ta bude zif din rigar har kasa, ganin wuyan rigar na kokarin zamewa kasa tai saurin sa hannun ta ta dan ne kirjin ta.
Bayan ta Afnan ta kalla sanan tace lah ! baki sa bra bane?, Ina bra dinki dauko?
Jimmm Unaisa tayi sannan tace ni ban sawa.
Cike da mamaki tace me yasa?
Haka nan kawai, gurin kayanta tai saurin isa ta fara fito da bra dinta wasu sabi ta fito dasu guda uku tare da fadin gwada ko zasu miki?
A’a bazama suyi ba Afnan maida abun ki ni bana so ne.
Wlh sai kin saka, dariya ce ta kubuce mata adaidai lokacin dataga Unaisa ta zauna tana fadin nifa banso.
Yanzun bra din ma gudunta kike?, wlh sai kin saka, kanta nufa yayin da tai saurin zagawa ta bayan ta tana kokarin daura mata yayin da Unaisa ke tureta, sai dai ita Afnan sosai takejin dariya gani Inda Unaisa keyi kamar wadda za’a daura mata wani mugun abun.
Da dambe ta saka mata sannan ta zame rigar jikin ta kasa.
Cikin sauri Unaisa tasa hannun ta ta danne kirjinta tana fadin, haba Mana Afnan wanni irin iskanci ne hakan.
Babu wani iskanci ai Dukkan mu mata ne, gani tayi kokon bra din ya mata kad’an yayin da kuma fadinta yayi mata yawa kad’an.
Har yanzun Afnan dariya take tare da fadin, cire kawai ta ba saze dinki bace.
Zama Unaisa tayi ranta duk a bace sannan ta cire bra din ta wurgawa Afnan tare da da mayar da tata rigar, ita ko Afnan har yanzun dariya ne kecinta zuwa cen ta dauko ledan kayan data shigo dashi ta aje akan gado, sannan ta dauko kwalin waya ta mikawa Unaisa gashi wayar ki inji Hamma Modibo, ta aje a gefenta, itako Afnan kofa ta nufa tana fadin Ina zuwa barinje in dawo kinji.
Dakai Unasisa ta amsa mata, har takai kofa ta juyo tana fadin, yauwan yace wai akwai Number Dada aciki.
Tanajin an amtaba Dada taji wani sanyi har karkashin zuciyarta ahankali ta bude wayar ta fito da ita fara ce sol duk da cewa komai baya burgeta hakika idan tace wannan wayar Bata burgeta ba tayi karya, duk da cewa bata san kudin wayar ba taji dai ajikin ta me tsada ce, Bata taba rike wayar ba dan haka batasan inda zatabi ta kunna ba, Dada nada waya amman irin yar karamar Nan ce
Ajiye wayar tayi dan batasan inda zatayi da ita ba, ahankali ta jawo daya ledan takalma ne masu dan karan kyau da masu tsayo da marasa tsayo har guda takwas kowanne da jakar sa, kallo tabi kayan dashi sosai acikin ranta take fadin yanzun wannan kayana ne, ban taba tunani ko ganin irin su gurin wani ba takalmi saikace bana takasa kasa ba, kwalla ce ta cika mata Ido alokacin da tafito da wasu mayafai kala kala, kwalla taji Yana zubo mata wadda ta rasa na menene, hannu tasa tana sharewa Amman duk da haka zubowa suke, kallon kayan take tana sake lallo Mamaki take wai itace zata zuba duk wad’anan kayan ajikin ta hawayen ta ta share sannan ta bude daya daga cikin jakun kunan, nan taci karo da yan kunnaye da sarka har da agogo, nan wani hawayen ya sake zubo mata.
****
Aunty Safna Ina Hamma Modibo?
Batare da ta kalli Afnan ba tace ki kirashi awaya mana.
Tunkan Safna ta rufe baki Afnan ta daga waya zuwa can tace Hamma na kana ciki ne?
Jimmm tayi zuwa can tace tam sannan ta nemi guri ta zauna.
Dauke Kai Safna tayi tsayon lokaci ba wadda yace kala tsakanin ta da Afnan.
Modibo ne ya fito cikin farar jallabiya da alama wanka ya fito, zama yayi kusa da Safna tare da fadin Afnan yaya akayi?
Wata mgn nazo na gaya maka.
Okay toh ga kunne na.
Kuce kawai na tashi, Safna ta fada tare da kokarin mikewa.
Hannun sa ya mika ya roko na safan a daidai lokacin Afnan ta isa ta gefen sa ta rankwafa ahankali tace,
” Rahma Bata da bra ko daya”
Lumshe idon sa yayi sannan ya bude fuskarsa dauke da Murmushi yace, Haba?”
Allah kwata kwata.
‘Yar karamar dariya yayi sannan yace yanzun meye abun yi?
Muje mu sawo, Afnan ta fada tana kallon fuskar Modibo.
Key motar sa ya mika mata tare da fadin Muje.
Karba tayi sannan taiwa Safna Sallama ta fice, kusan minti 10 da figanta sannan ya fito, mazaunin driver ya zauna sannan ya fice agidan.
****
Juya wayar Safna keta yi ta rasa yadda zatayi da ita, tsintan kanta tayi da balakin son Afnan ta dawo dan haka da tadanji motsi motsi d’auka take itace.
Sai misalin shabiyu na rana ta taji an turo koro kofar da sauri tana daga Kai sukayi Ido hud’u.
Wata lada ta Mika mata tare da fadin, gurin Hamma Modibo naje muka je sawo miki bra gashi nan duba ki gani.
Jimmm tayi domin jin sunan Modibo data kira kawa da zancen tayi da fadin nuna min yadda zan Kira Dada da wayar nan.
Amsa wayar tayi ta dannan sannan ta mikawa Unaisa.
Ciki da ajiyan zuciya ta amsa wayar tasa a kunnenta zuwa can taji Muryan Dada tana Sallama, kasa amsawa tayi yayin da kwalla ta cika mata idonta.
Sallama Dada take ta rangadawa ta gaza amsawa tsoron kar Dada ta yanke wayar cikin kuka tace Dada.
Zaro Ido Dada tayi dan Bata tsammaci jin Unaisa ba.
Arude tace Unaisa Yaya kike?
Cikin kuka tace lafiya Dada.
Allah sarki Unaisa kina Ina ne cikin mutane kuke ko daga ke saisu?
A’a Dada ya kaini gidan su.
Unaisa bar kukan kimin mgn, muna waya da Modibo saidai Ina tason inji daga gare ki, yace min kina wajen mahaifiyar sa ko?
Unaisa tana kuka sosai tace eh.
Toh kobar kuka, ko akwai matsala ne, suna kyaran ki ne?, Ko suna gudun ki?
A’a Dada kawai dai nafi son dakin Innawo.
Unaisa, ashe bazakibar zancen Nan ba bakiso hankalin ya kwanta ko?, ko ana takura miki ne?
Hawaye Unaisa ta share sannan tace a’a, nidai a takure nake.
Unaisa ki saki jikin ki, yaron nan dan mutuncine Allah ya hadaki dashi dan Allah ki kwantar da hankalin ki, Ina Kika samu waya?
Cikin shashakar kuka tace shine ya bani.
Allah sarki kinsan me nakeso dake?
A’a
Ba yanzun kina da waya ba, duk wata matsa ki gaya min, muna tattaunawa, idan karshen wata yayi sai nazo mutafi gida amman fa saikin kwantar da hankalin ki.
Dada da gaske kike?
Da gaske nake Mana, Nan da karahen wata zanzo amman fa sai naga kin saki jikin ki, idan baki saki jikin kiba ko zuwa ma ni bazanyi ba.
Zan saki, amman fa kizo karki min wayo.
Ai daman zanzo inga guri Unaisa Allah yai miku albarka.
Daker suka rabo tsakanin Dada da Unaisa.
****
Misalin karfe hudu na yamma Afnan ce ke daurawa Unaisa dan kwali, bayan ta gama ta matsa mata domin ta kalli madubi, tsaye Unaisa tayi tana kallon kanta cikin madubin cikin sauri ta mika hannun ta tacire dan kwalin tana fadin ni gaskiya bazan iya fita da wannan kayan ba Kamar wata yar tsana
Aiko wlh dashi zamu tafi meyasa kika kwance?
Daukan dankwalin tayi ta nufi ta, tare da fadin, ” mufa fitafa mota zamu hau kuma can ma muka sauka gisa zamu shi.
Toh kibani hijjabi ne.
Babu hijjabi ta data amsa a takaice.
Badan ranta yaso ba ta amsa gyalen da Afnan ke Mika mata, shima ba wani girma ne dashi ba, aka ta daura yayin da Afnan ta rataye nata a kadanta.
Wani irin masifaffen kyau Unaisa tayi, Saida Unaisa tai masu hotuna sannan tace muje.
Jerowa sukayi, su biyo, Satan kallon da Afnan ketayi tare da fadin, ” yau Yadikko zatai farin cikin ganin ki nasan, daman tuni take cewa Hamma Modibo ba aure yayi ba.
Cikin sauri Unaisa ta dafe kirjin ta tare da fadi kibar Kiran sunan nan gabana na fadi.
Yar dariya Afnan tayi adaidai lokacin suka isa dakin Ammi.
Ammi naganin Unaisa ta saki fara’a tare da fadin, Masha Allah, kinga inda kika fito kuwa.
Rasawa tayi tana wasa da hannun ta tare da dan murmushi kadan, acen kan kujerar Ammi dake gefen gadon ta ta hangi wani rike da kofi.
Kallo daya ta masa ta dauke kanta domin a zaune yake bata iya gane Magaji ne ko Modibo ne, sai dai tunda Amma ta fara yaba kyaun da tayi yake Satan kallon ta tare da kurban abun da yake hannun sa, ahankali ta ce Ina wuni dan har yanzun bata gane ko waye ba.
Dauke kansa yayi tare da hade fuska sosai yace Lafiya lau.
Koda yake amsawa baza kunnen ta take ko zata dau murya as amman vabu abun data gane.
Afnan ce tace Hamma munyi kyau?
Tun Kan ta rufe baki yace kun yi.
Cikin rawar Kai ta sake cewa Hamma kalli Rahma…
Haba Mana Afnan kin daman kuje kawai ya fada ransa abace.
Tabe baki Afnan tayi sannan tace Ammi mun tafi.
Toh adawo lafiya.
Fita sukayi yayin da Unaisa tabarwa zuciyarta Modibo ne agurin acikin ranta take cewa ya baci da fada.
Saidai abun da ya daure mata Kai suna fitowa harabar gidan ta hago sa Yana tahowa cikin dingishi ciwon kafarsa.
Ja tayi ta tsaya yayin da Afnan tace muje mana. Lura tayi da in da Unaisa take kallo kallon gurin itama tayi tare da fadin, “Hamma mun tafi”
Ciki sauri Unaisa ta sunkuyar da kanta tare da wasa da hannun ta tace Ina wuni.
Wani irin kallo take mata idon shi a lumshe sannan yace, Lafiya
Kara kasa tayi ta ganta domin tanaji ajikin ta ita yake kallo, wucewa Afnan tayi tana fadin muje.
Kokarin wucewa take taga ya kara d’ingisawa tare da fadin karku dad’e,
Ke ku tsaya ma na kaiku kawai.
Har ya zauna amotar kallon sa take, badan dingishin da yake ba da tace wannan ne Magaji waccen na dakin Ammi kuma Modibo, sosai ta shiga rudani, Jan motar ya fara ahankali har suka fita agidan sunhau titi sosai ya waigo ya kalli Afnan yace, idan mun isa gidan Muftahu zaki karbo ma ya dikko sako sai driver ya karaso dake gidan yadikko…
7 comments
Comments are closed.