Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 7

Posted by

BA LABARI BOOK 2 PAGE 7

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido

Page 7

Cikin sauri Unaisa ta kalli Afnan dake amsa masa.

Cikin ranta ta fara tunanin yanzun sauka zatayi ta barni kokuwa tare zamu.

Shiru motar tayi har sukayi tafiya me nisa, zuwa can taga sun karya kwana sannan sukaja suka tsaya.

Afnan taga ta bude motar dan haka itama ta fara kokarin sauka.

Kausasiyar muryan sa taji abayan ta cikin fada yace ke koma ki zauna.

Cak ta tsaya, yayin da taga Afnan ta sauka ta rufe motar, figar motar yayi da karfi har Saida ta kusa faduwa.

Tafiyan kusan minti goma sannan taga sun shiga wani makeken gida, saidai tunda suka shiga gidan yai zaman shi amotar babu almar zai bude motar.

Itama zama tayi illah Satan kallo sa da take.

Zuwa can taga ya bude gilashin sun gaisa da wani, batace zata fitaba dan koka ta fita batasan Ina zatabi ba dan babu wadda ta sani agidan ko hanyar da zai kaita cikin gidan ma Bata sani ba.

Zuwa can ya bude motar ya fito, kusa da ita ya dawo ya zauna dan haka tai saurin matsawa.

Wani irin kallo ya wurga mata wadda yasata ta kara firgita, wannan karon yinkurin bude motar tayi saidai tajita gam.

Kallo ya bita tashi tamkar zai cinyeta sannan taga ya Yana kokarin miko hannun sa jikin ta.

Cikin sauri ta dago idonta sunayi idon hud’u dashi, jawur taga idon nasa ya kafeta dasu tamkar zai cinye ta.

Ganin tambas jikin ta yake tahowa da hannun yasashi saurin bige hannun nasa tunkan ya karaso jikin ta.

Wanni irin kallo ya mata ke! Ina wasa dake ne?

Ni karka taba ni.

Meye amfanin ki to?.

Hawaye ne sukai saurin zobo mata sabo da tashin hankalin da take ciki batai yin kurin sharewa ba.

Hannun sa taga ya mika ya rike kanta tare da zubawa fuskarta, ita cikin wani irin kallo idon da a alumshe.

Kina da kyau ya fada cikin wata irin murya wadda batai kama da tashi ba, duk irin kokarin da take na ta kwace fuskarta tagaza yin hakan.

Kina da kyau, ke kyakyawa ce haka yaike ta cewa Yana rike da kan Unaisa itako hawaye ne ke kara jika fuskarta.

Ranta kuwa fadi take ni bazan iya zaman nan ba, Bata hankara ba taga ya saki kanta yayi saurin yaye mayafin ta kirjin ta ya bayyana, cikin sauri ta kalli kirjin ta, nonon ta tagani sun kara wani cukal cukal tamkar ba kirjin ta ba dagowa tayi ta kalli inda ya kafe kirjin nata ta Ido har yana lasan bakin sa, rasa abunnyi yasata waigawa tana kallon cikin gidan, ga jama’a can kowa harkokin sa yake yi, bana ankara ba tajin ana shafan kirjin nata azaburi ta daki hannun sai dai dukan beyi wani tasiri ba ganin yana kokarin zagaye hannun shi ya jawota gareshi ta saki wani irin gigitattacen kara.

Ko ajikin sa Kara rungumeta yayi tsam ajikin sa tare da sauke ajiyan zuciya a jajjare.

Duk cikin cikin da take na ta kwace kanta ta gaza yin hakan, daga ita saishi amota yana rungume da ita yanata faman sauke ajiyen zuciya zuwa can taji ya fara kokarin laluban bakin ta kokarin tura bakin nasa yake cikin nata saidai taki barin haka, dabe suke sosai cikin motar, inda take jin duk ya sossoketa da gemon sa, suna cikin haka taga ya saketa lokaci daya, lokacin gaba daya gyalenta baya jikin ta, gyalen ta fara tattarowa nan takula motar su Afnan ce ta shigo shiyasa ya sake ta.

Jikin ta na matsancin rawa sosai ta hangi Afnan din ta nufi cikin gida.

Sai a lokacin ya bude motar ya fita yana fadin ki nutsu ki dawo cikin hankalin ki.

Kuka ne ya kwace mata, ita Sam Bata saba da irin wannan rayuwar ba gaba daya ji tayi ta tsana garin da abun dake cikin sa, kuka tayi tare da kara gyara mayafin ta, duk ya tattabe mata nono Sam baxan iya zama ba ta fad’a a fili.

Zuwa can ta sake hango Afnan ta fito tana dube dube tare da daga waya zuwa can taga ta kallo motar tare da tahowa ta bude.

Ganin Rahma tana kuka tai saurin fadin lafiya ?

Ba komai Unaisa ta fada tare da sauka a motar

Hawayen ta fashe yayin da Afnan ke binta da Ido kawai.

Hannun ta Afnan ta rike tana fadin, wai me ya faru?

Kawar dakai kawai tayi cike da takaici , cikin gidan suka nufa har yanzun idon Unaisa cike da kwallah.

Haka sukayi ta ratsa gidan har suka shiga cikin falon gidan, Basu tsaya nan ba Kara kutsawa sukeyi har suka isa wasu kofofi guda biyu na gefen Dana Afnan ta kwankasa tare da sallama.

Muryan tada amsa sallaman ne tasa gaban ta faduwa lokaci daya, tura kofar sukayi suka shiga wani rantsatsen gadone makeke ya dauki hankalin Unaisa, wani ta hango zaune abakin gadon Yana matsa Kamar matar dake kance akan agadon

Afnan ce tace Hamma Suraj Yaddiko bacci take?

Eh, jikin ta ya motsa jiya, bamuyi bacci ba, juyowa yayi ya kalle su, gaidashi Afnan tayi tare da tambayan sa jikin Yadikko dan haka itama Unaisa ta gaidashi tare da yimasa ya me jiki amsawa yayi cikin yanayin rashin walwala.

Zuwa can matar ta motsa, ahankali Suraj yace Mama?

Ahankali ta amsa.

Tashi Kisha magani ga Afnan taxo ma

Kokarin tashi take zaune Suraj din ya taimaka mata ta zauna, Afnan ce ta karasa kusa da ita tare da saurin zaunawa kusa da ita tana fadin, Sannu Yadikko ya jikin.

Jiki Alhamdulillah, ta fada tana kallon Unaisa dake tsaye, Afan ta kalla sannan tace wannan fa?

Rahma kizo ki gaida Yaddiko mu Afnan ta fada tana miko ma Rahma hannu, cikin rawan jiki ta karasa gaban matar kokarin tsugunawa take akasa matar tai mata nuni da gefenta tare da fadin zauna anan.

Batai musuba ta zauna, sannan ta dan sata kallon Suraj da ta lura baya cikin walwala da damuwa sosai a fuskar sa.

Gaidata tayi sannan Yadikko ta sake tambayan wacece wannan?

Yaddiko wannan itace matar Hamma Modibo da suka taho da ita.

Cikin sauri ta zura hannunta cikin na Rahma sai awannan lokacin Unaisa ta d’aga Ido ta kalli Yadikko Kamar sudaya da Ammi kamar ma harta baci, saidai Ammi ta danfi Yaddiko girma ko ba’a fada ba tasan Yaddiko kanwar Ammi ce, saidai kuma Yaddiko idonta duk akunbure suke daga ganin ta kasan ba wani kosheshen lafiya ne da ita ba.

Yadda take kallon Yaddiko haka itama Yaddiko take kallon ta, ganin kallon da Yaddiko take mata yayi yawa tai saurin sunkuyar da kanta kasa.

Suraj ne ya jawo wani galan ya bude tare da cikashi da ruwan magani ya mikawa Yaddiko tare da fadin, Mama gashi kisha maganin da Moddibo ya taho miki dashi ne.

Bazan shaba Suraj kutatara maganin ku.

Meyasa mama?, Amman da da kina sha ai kina samun sauki. banajin dadin wannan abun da kike Mama, zankira Ammi ingaya mata halin da ake ciki, zaki kashe kanki ne?, tabbatarwan da yayi basha zatayi ba yasa shi fita afusace.

Afnan ce ta dauki ruwan Maganin tana share hawaye tace Yaddiko Kisha dan Allah.

Afnan nagaji da shaye shayen maganin ne kawai wadda nasha ada sun isa haka.

Hakanan Unaisa taji hawaye na zubo mata, ko meyasa matar take gudun magani, Tausayi ta Bata, sosai ranta take fadin kenan matar ta gwamace mutuwa da rayuwar duniya, maganin dake hannun Afnan ta kalla tsintan kanta tayi da amsan maganin ta kalle shi sannan ta kalli Yaddiko tace, Yaddiko dan Allah kisha. Gani tayi Yaddiko tabita da Ido dan haka ta nufi bakinta da kofin, bude baki yadikkon tayi ta shanye tass, bayan ta tabbatar ta shanye tace sauke kufin adaidai lokacin da Suraj ya dawo wani Dattijo biye dashi.

Tsaye sukayi yayin da tsohun yabawa Suraj Umarnin ya zuna maganin, Afnan ce tace ai munbata tasha.

Dattijon ne ya kalli Yaddiko yace haka nake fama da ita gurin shan maganin saina matsa take sha.

Cikin fushi sosai Suraj yace Baba wlh sai in bar garin tunda banda amfani agurin ta, ai wannan ma rashin adalcine na lura so take ma ta mutu, bata damu Da wani halin zan shiga ba ni, juyawa yayi afusace ya nufi kofar, yayin da mahaifin nasa ya bishi da kallo, ita ko yadikko Kiran sunan shi ta fara saidai ya riga yayi zuciya beko waigo ba.

Sai kusan mangariba suka fito domin komawa gida, suna fitowa Unaisa ta fara rawan jiki, jikin ta be gama daukan rawa ba saida taga sun nufi motocin dake gidan, dan haka tai saurin rike gyalen Afnan tare da fadin, ” amman ba tare da wannan Modibo zamu tafi ba ko?

‘Yar dariya Afnan tayi sannan tace, ai Hamma Modibo bezo gidan nan ba bare ma ya maidamu, driver ne zai kaimu.

Wani irin tunani Unaisa ta shiga, tare da rasa gane Kan abun, har suka shiga motar sukai nisa tunanin da take kenan kuma ta kasa yin tambayan dake cin ranta.

Misalin karfe shidda na yamma suka isa gida, suna sauka acikin motar suka hangi shi Yana tahowa cikin tafiyan dingishin da ya zamar masa tamkar gayu, da alama masallaci zashi.

Kallon su yayi sau daya ya kawar dakai yayin da jikin Unaisa ya dauki rawa sosai.

Rike ta Afnan tayi tana fadin ga Hamma tsaya yazo, kasa kasa da murya murya tayi tana fadin muje dan Allah.

Karasowa wajen yayi saidai be tsayaba Kamar yadda Afnan taso kokarin wucesu yake Afanan tace Hamma mun dawo.

Tagefen idon sa yake kallon su tare da fadin, kinyi kokari sannun ku da zuwa, Ina Yaddiko na.

Daga murya tayi dan harya riga ya wuce su tace, ” Hamma yau bata da lafiya daker ma Tasha maganin.

Kai dan Allah? !!

Allah kuwan!

Toh daga masallaci can zan wuce in dubo ta!

Tam Hamma na.!

Kokarin juyawa take taji ya sake fadin, Afnan babu sabon labari ne?

Akwai fah Hamma!

Bayan sun gama mgnr ne ta juya wayam taga babu Unaisa cikin sauri ta nufi cikin gidan, a part din Ammi ta same ta

Bayan sunyi Sallama Nan sukayi kwanciyar su, hira suke yawancin hirar Afnan ce da Ammi suke, ita ko Rahma tana kwance gadon Ammi tayi rufda ciki, babu abu da take tunawa sai abun da yai mata d’azon, wani abun dake daure mata kai Modibo yacika tsare gida, amman dazon taga ya tabe mata jiki, yanzun kuma yayi Kamar bashi bane, Yana wani tafiya Yana dingi shi, tunawa tayi da kalmar Afnan da tace ai Hamma Modibo bezo gidan Nan ba bare ma ya Mai damu, wata zuciyar ce tace mata kila tana nufin be shiga gidan ba, yayin da wata zuciyar kece mata ki tambaya kawai dan ki tabbatar.

Har misalin 10 na dare tana akwance rufda ciki yayin data Zoro kanta tare da hade hannun ta biyu ta daura habarta akai.

Ammi ce ta kalle ta tace, ” Rahma yau Kamar kina cikin damuwa ko?

A’a Ammi.

Hmmm duk dadai baki gama sakin jikin ki ba kam akwai damuwa yau atattare dake.

Ammi babu.

Shikenan Ammi ta fada tare da cigaba da hira da Afnan, sai dariya suke, zuwa can Ammi ta mike ta fita dakin ya rage daga Unaisa sai Afnan, kasa hakurin da tayi yasata kallon Afnan tace, Afnan dazon da zamu fita waye muka samu acikin nan dakin?

Kai tsaye Afnan tace Hamma Modibo.

Wani irin fad’uwan gaba taji ya sameta da karfin tsiya ya buga.

Afnan wadda fa yake zaune acan da kofi a hannun sa sanda zamu fita?

Wannan kalma ta Unaisa a kunnen Ammi ya sauka, dan haka ta tsaya cak bakin kofar tana sauraron su.

Afnan ce tace eh Hamma Modibo ne.

Tashi Unaisa tayi ta zauna cikin rikicewa tace toh wadda ya Kai mu can kigidan fah waye shi?….