Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 page 8

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido

Page 8

Wannan Hamma Magaji ne.

Cikin tsananin tashin hankali Unaisa ta tashi zaune wai ba Modibon bane ke dingishi?

Eh shine Mana.

Toh ai dashi muka tafi, wadda muka Bari anan shine Magaji.

Dariya Afnan tayi sosai, sannan tace, “waike an gaya miki ban sansu bane?, Hamma Modibo shi muka Bari anan da Hamma Magaji muka tafi.

A’a toh wadda muka tafin ma dashi ai Yana dingishi.

Kara fashewa da dariya Afnan tayi sannan tace baya wani dingishi kafar sa lafiya kalau take.

Wlh Yana dingishi Afnan.

Toh badai Hamma Modibo bane wlh ka ke kiga yana dingi dai.

Tana daga zaune take share hawaye, to me zaisa yayi dinshin alhalin bashi bane maciwon kafar, wata zuciyar ce tace ai tabaki yake son yi shine yasa, take taji kabanta ya fadi, shigowan Ammi yasa ta maidon da hankalin ta jikinta fuska daure ammi ta shigo, ke wacce irin shasha ce, Ammi ta fada alokacin data suka hada Ido da Unaisa, Mijin naki ace baki sani ba?, Ni banga Kamar da suke dashi ba, wadda har za’a rasa gane su, Afnan ta kalla tace ke kiramin su suzo maza.

Cikin tsananin dariya Afnan ta dauki waya kiransu tayi daya bayan daya tare da sanar masu da kiran Ammi, cikin kankanin lokaci suka shigo.

Sannu da gida suka ma Ammi, itako Ammi nuna Unaisa tayi tare da fadin, Kiran ku nayi in banbancewa Rahma ku, Bata gane ku sam, yanxun na sameta tana tambayan Afnan wai ita tunanin ta da Modibo sukaje gidan Yaddiko ku.

Cikin sauri Modibo ya daga idonsa ya kalle ta cikin Ido, dan haka ta sunkuyar da Kanta kasa.

Ammi ce tace Rahma ga Magaji ga Modibo, ki kallesu da kyau suna da banbanci sosai, sai wadda be sansu bane sosai yake ganin tsananin Kamar su.

‘Dagowa tayi ahankali ta sauke idonta ana nasu, yayin da gaba dayan su suka mata kur da Ido.

Kallon su take kasa kasa sai dai iya ganin ta bataga wani banbanci ba.

Ammi ce ta sake cewa, ” Rahma ki kyalle su da kyau, kinga Magaji garin jikin gareshi, amman su d’in ba ‘yan biyu bane, shekara daya Modibo yabawa Magaji, kinga kuma Magaji yafi Modibo haske shi kuma Modibo yafi Magaji idanuwa.

Afnan ce ta tintsire da dariya tare da fadi, Ammi ba haka zakice mata ba….

Cikin sauri Modibo ya nuna Afnan tare da cewa yauwa Ammi ga Afnan bari ta banbance mata tunda ita bata wayau.

Juyawa Ammi tayi ta kalli Afnan fuskar ta cike da Murmushi, yayin da Afnan ta shiga fadin, ” Rahma shifa Hamma Modibo Ustazu ne, kama kadan sukeyi da Hamma Magaji, hancin Hamma Modibo dan ziriri ne, yana da kirki sosai, wadda kina kallon fuskar shi zakiga hasken kirki ya baibaye shi.

Modibo zaune Yana kallon guri daya tare da shafa gemun sa kadan kadan tare da sauraron Afnan fuskarsa babu alamar wasa, tsinkayan muryan ta yayi tanaci gaba da cewa, ” amman fa duk wannan kirkin nasa kinayin abun da ba daidai ba zai rufe idon sa ya cafalaki babu ruwan sa…..

Tunkafin Afnan ta rufe baki ya sauke kafarsa daya daura Kan daya tare da fadin, Allah yai miki Albarka Afnan.

Amin Hamma.

Ammi ce tace to kin gaya mata halin Modibo saura na Magaji.

Ta gefen Ido ta kalli Magaji sannan tace ai shi Hamma Magaji d’an nanaye ne….

Cikin sauri ya dago ya kalli Afnan fuskarsa cike da fushi, mikewa yayi ya nufe ta, Ina wasa dake ne?

Dariya Ammi tayi tare da fadin karka taba ta.

Ammi bakijin me take cewa ne?, Koda ai ba laifin ta bane, abakin ki taji.

Had’e Fuska Ammi tayi sannan tace Afnan tashi kuje ku kwanta.

Mikewa Afnan tayi tana satan kallon Magaji ta yafito Unaisa suka fice.

Ammi ce ta kalli Magaji bayan fitan su Afnan tace, ” wai Kai kwana biyu meke damun ka, kullum fuska daure tun da kuka dawo baka da walwala.

Toh Ammi aini gani nayi duk gidan an tsane ni.

Ban gane an tsaneka ba?, Wacce irin mgn ce wannan, akwai bare ne nan?

Ammi kinaji fa abun da Afnan take fada yanzun, ni babu memin shaidan harziki agaban wannan wulakantacciyar yariyar takece min ni dan nanaye.

Kallon sa Modibo yayi sau daya ya dauke Kai yayin da Ammi take tambayan sa wacce yariyar ce wulakantacciyar?

Kofar ya nuna tare da fadin wacce yariyar mana.

Mikewa Modibo yayi tare da fadin, Ammi zanje in kwanta, gobe in Allah ya kaimu zan koma gurin aiki na

Amsa masa tayi yayin da Magaji ma yace masa mukwana lafiya.

Allah yasa ya fada a hankali sannan ya fice.

Ammi ce ta maida hankalin ta sosai kan Magaji, ” waikai Magaji Anya kuwa baka fara shaye shaye ba?, Ta yaya zakazo ka zauna agaban Modibo ka dinga cewa Matar sa wulakantacciya, wanni irin cin fuska ne wannan, karfa amanta idan ada kana mata wannan kallon yanzun Allah ya daga darajar ta matarsa ce abun ikon sa, akarkashin kulawar sa take duk hakkokin ta yana Kan dan uwanka, idan har zaka kirata wulakantacciya toh zaka Kira Modibo wukantacce, kuma sanin kankane cewa Modibo ba wukantacce bane, ya rike girman shi da mutuncin sa ko bashi da sisi ya wuce akirashi da wannan sunan, banda tsaurin Ido da rashin kunya agaban shi kake zagar masa matar auren sa.

Ammi wannan wani aure ne?, wlh badan Yana sonta ya yadda ya aure ta ba, kawai ya yadda ne dan yana so ya taimake ta, kuma muna nan dake nan gaba kadan zaki gane haka, kwata kwata babu sonta azuciyar sa, wannan matar tashi ma yaushe zasu barshi yayi wani aure, ninasan wlh Ammi ba zaman aure zai da ita ba.

Jimmm Ammi tayi cikin yanayi irin na me damuwa sannan tace, meyasa kace ba son auren yake ba Magaji?

Ammi idan Yana son ta meyasa yabarta anan?, ai kunfi kowa sanin halin shi, ita kanta Safna daker suka Kai matakin da suke ayanzun.

Cikin wani irin yanayi Amma ta dubi Magaji, idan na fahimceka kana nufin bazai iya zama da mata biyu ba kenan?

In ma dai zai iya Ammi ba wannan yariyar ba, cikin mu fa babu wadda bema tayin auren ta ba, har rana yasa mana tare da Karin lokaci akancewa mu yanke shawaran, Suraj da Muftahu sunso su aure ta saidai rashin bude idon ta yasa suka janye, ammi Koda mukaje masallacin agurin Saida ya sake bamu dama, sai dai duk rashin ganin fuskarta yasamu wani tunani daban, shikuma yana son saiya taho da yariyar kawai kota halin kaka, saiji mukayi yace wai a daura dashi, dan haka kinga nan gaba yana iya sakin ta, dan wlh ba sonta yake .

Dagowa Ammi tayi ta kalli Magaji, Aiko bazan ji dadi ba idan haka ta faru, yariyar ta shiga raina, sannan gashi Safna shekara biyar kenan shiru, ko be dawo da mata ba daman aure zai kara, Ina son su zauna tare sosai, dan haka zan sameshi muyi mgn akan ta, inji ta bakin shi…..

Ammi karki tuntubeshi, kibarshi ki zuba masa Ido kawai.

Jimmmm Ammi tayi zuwa can tace shikenan, kuma naji kace Suraj ma yaso yariyar?

Eh Ammi Suraj din ma shine ya fara sannin ta tun kafin Shi ya santa.

Shiru Ammi tayi cikin yanayin dake nuna ta shiga damuwa.

****

Afnan?

Na’am

Yanzun kenan wadda mukaje amotar sa shine Magaji ba Modibo ba?

Wallahhi Magaji ne Rahma.

Wani irin bakin ciki taji ya kuleta tare da wani irin zuciya daya taso mata wadda batasan tana shi ba, rawa jikinta keye lokaci daya idonta yayi jawur.

Rahma lafiya kuwa?

Idonta aguri daya tace lafiya lau.

Da kallo kawai tabita yayin data kula hawaye na zubo mata, abu daya ke mata bakin ciki yadda yaita dingisa kafar sa, kallon wani kasurgumin munafuki ta fara masa, sosai takejin zafin sa, wani irin tafarfasa zuciyar ta ke yi.

Ganin abun da yai mata take tamkar fyade dan babu wadda ya taba mata haka kuma ko Modibo ne yai mata haka saitaji tsanar sa bare Magaji, wata zuciyar ce take ce mata ta gayawa Ammi abin da yai mata, saidai bazata iya fadi ba, haka ta kwana juyi akan gadon, gaba daya ta kasa bacci yayin da tsanan magaji yai kwance acikin zuciyar ta tsintan kanta tayi da balakin son yasan tagane abun da yai mata din, sosai dan gudun kada ya sake kwatanta hakan.

Misalin takawas na safe ta nufi dakin Ammi, tana daf da fita taji muryan sa yana gaisawa da wani, sakin kofar Ammi tayi ta nufi kofar da zata sadata da harabar gidan, bude kofar yayi daidai ta tsayuwar sa jikin motar tare da kallo kofar.

Ganin ta tsaye awajen yayi wani yalwataccen Murmushi, kallon sa tayi daga sama har kasa, uban kwalliya yaci da shaddar data dauki guga sosai, juyawa yayi yana kokarin shiga motar.

Ganin haka Rahma tai saurin kallon gefenta, wata roba tagani me ciki da dutsen kwangila cikin sauri ta dauki daya yana kokarin shiga cikin motar yaji saukan abu akeyan shi, wadda saboda rad’ad’i dauka yayi ko harsashi ne.

Waigowa yayi ya kalleta sannan yasa hannun sa ya shafa keyan sa tare da dawo da hannun ya kalla, jini ya gani a hannun nasa dan haka ya fara takowa cinki fushi tare da tarin Mamaki.

Ganin ya fara takowa itama ta fara takawa zuwa ciki gidan, dakin Ammi ta shiga tare da mata sannu sannan ta wuce bayanta ta zauna.

Tana zama Yana shigowa, ganin shigowan shi babu Sallama Ammi tabi tsayon shi da kallo tana fadin, Modibo lafiya?.

Jin Ammi ta ambaci Modibo ta tai saurin mikewa tana raba Ido, gani tayi Yana tunkaro ta, batasan yaya akayi ba tadaiji wani Kara wadda yai mata kama katse jijiyoyin dake kai jini ajikin ta.

Mgn takeji sama sama Bata game me ake cewa, zuwa can ta farajin muryan Ammi cikin fada take cewa, ” ka dawo cikin hankalin ka, bakajin tace ta dauka Magaji ne?

Muryan sa sama sama yake cewa, “nace kibani ita daga yau zata fara banbance mu.

A’a baza’ayi haka ba, ka wuce kabani guri.

Gaba daya fuskarta ji take Kamar an daura mata dutse sabo da nauyi, duk kokarin ta na ta bude idon ta gaza yin haka

Muryan Ammi kawai takeji cikin fada tana janshi tare da fadin ya fitar mata adaki.

Karan kofar taji da karfin tsiya, zuwa can taji Ammi ta dawo kusa da ita ta zauna, hawayen dake zubo mata take sharewa ga uban kunburin da fuskar tayi sabonda azaban Marin daya zafga mata.

Duba fuskar Ammi take tana matsawa tare da fadin, sannu, kema baki kyauta ba Rahma, narasa menene wanna, shi Magajin yayi miki wani abun ne?

Kuka kawai Unaisa keyi Ammi na rarrashin ta, zuwa can ta sausauta da kukan sanan ta bude idonta, kadan, gani tayi duk jinin sa ya didiga akasa dan haka taji hankalin ta ya kara tashi, duk dakin digon jinin sa ne tsintan kanta tayi da fadin, Ammi Ina yake?

Cikin damuwa tace yana dakin shi.

Ammi Afnan tazo ta rakani in bashi hakuri”

Toh, zata rakaki amman karkije yanzun, Yana cikin fushi.

Cikin matsanancin kuka tace,zani a haka Ammi.

Jimmm Ammi tayi sannan ta kalli tayi sannan ta juya ta kalli jinin dake digo akasa ko Ina, daga gefen gadonta ta hangi inda yai jifa da wayar sa tare da key din mota, mikewa tayi ta dauka sannan ta kwalawa Afnan Kira.

Bayan ta shigo wayar Modibo ta mike mata tare da key din tana fadin, ” raka Rahma gefen Modibo

Fuskar Unaisa ta kalla tace Ammi menene.

Kuje dai ki rakata, Modibo ta jefa kanshi ya bashe, wai ta dauka Magaji ne.

Zaro Ido Afnan tayi sannan ta koma bakin gadon tare da fadin Ammi tsoro nake ji.

Tashi kuje da kin kaita saiki dawo.

Har suka isa part din idonta Bata iya budewa

Babu kowa afalon dan haka Afnan taita rafka Sallama,

Jin ba’a amsa ba ta nufi kofar da zata Kai mutum dakin baccin sa ta fara bugawa, wani irin tsawa ya buga wadda tasa Afnan komawa da baya, a matukar firgice tace, ” nice Ammi ce tace in rako Rahma.

Shiru sukaji, yayin da tsayon lokaci, jikin Afnan rawa yake itako Unaisa duk jikinta ya gama sanyi.

Ji sukayi ana bude kofar Safna ce, tsaye tayi tana kallon su saidai Bata iya ganin fuskar Unaisa domin ta dan jawo karamin hijabinta gaba ya rufe fuskar ta.

Safnace ta kalli Afnan tace, yace ke ki koma, ita tashigo, cikin sauri Afnan ta mikawa Safna wayarsa tare da key din ta juya tana gode ma Allah.

Itako Safna kallo ta karewa Unaisa daga sama har kasa tace, ” biyo ni”

Bin bayanta tayi cikin sanyin jiki sosai, wata kofa taga ta bude ta shiga dan haka itama tashiga, Bata da wani nutsuwan tantance me yake cikin dakin abu daya kawai ta iya gani mutum sambalele kwance ruf da ciki tsakiyar gadon dagashi sai gajeren wando.

Safna taga ta zauna gefen sa tare da fadin gata.

Batare da ya motsa ba yace tasa min guiwoyinta a kasa.

Juyawa Safna ta sake yi tare da fadin, ” ai kinaji….

Kallonta tayi kadan ta zame tare da dire guiwoyin ta akasa tare da sunkuyar da kan ta.

Kallo Safna tabita da shi, Bata ganin fuskarta amman tana kallon yadda hawaye ke sakkowa daga idonta yana diga akan hijjabin ta saitin kirjin ta….