
BA LABARI BOOK 2
BY
Fadila Lamido
Page 10
Arikice Ammi ta mike cikin tashin hankali, tasan Modibo da fushi amman bata taba ganin fushin sa cikin dare haka ba.
Bakin window ta isa ta yaye labule, tamkar rana haka gidan yake sabo da hasken fitulun, daga inda take tsaye tana iya hango inda yake dukan kofar Magaji da duk kafar sa guda biyu, tsoro ne da firgici ya shigeta lokaci daya, kada kafar ta sake ‘ballewa, cikin sauri ta bude gilashin window afirice tace, “Kai Modibo!! Modibo! Fahat menene haka?
Be amsa ba, bema san tanayi ba, megadin gidan taga ya fito daga can ta hango ma’aikatan dake gidan suna fitowa, gani tayi Abban su ma ya bude kofar sa yana fitowa tare da kiran sunan Modibo cikin tsawa, adaidai lokacin da Magaji ya bude kofar Modibo ya cakumeshi tare da kai masa wani gigitaccen mari.
Cikin tsananin rikicewa ya dafe wajen, jawoshi Modibo keyi Yana Kai masa duka yayin da Magaji ya shiga karewa tare da fadin,” ya ishe ka haka karka kara dukana.
Modibo kuwa dukan yake kaimasa tare da hucin bacin rai.
Duk Mutanen da sukazo gurin babu wadda ya iya rike Modibo da mutun ya kawo masa hannu yake turesa ganin haka Ammi ta fito kawai.
Ahannun Abbasu ta samu Modibo saidai duk da hakan kokarin kwacewa yake, yayin da Magaji ke zubar da miyon bakin sa yana fadin wlh bazan yadda ba.
Abban su ne ya kalli Modibo dake rike a hannun sa yace, ” Modibo menene yake fauwa?
Kawar da kansa yayi can gefe cikin huci.
Modibo mgn nake menene ya faruwa?
Kawar da kansa ya sake yi sannan ya sake hannun sa cikin aljihun sa yana fadin, shikenan kawai Abba bakomai.
Kallon sa Abban yayi, haka ma Ammi sannan ya juya ya kalli Magaji dake zubar da miyon tare da jini abakin sa Yana fadin wlh bazan yadda ba karfina yafi?
Mayar da kallon sa yayi ga Modibo tare da fadin Muje, juyawa yayi ya kalli Magaji yace kaima wuce muje.
Gaba suka shiga yayin da Abba yacewa ma’aikatan kowa yaje ya kwanta wannan ya wuce.
Falon sa suka nufa su biyon suna gaba tuni Ammi ta fara share hawaye sosai abun ya daga mats hankali, rabon da taga ya daki wani anjima sosai, saidai yaita fada tare da zaro zance.
Zama sukayi afalon yayin da Abba yaishiru tare da hade hannun sa gurin daya Yana nazari, daka gansa kasan Yana cikin damuwa.
Ammi ma tagumi tayi tana kallonsu daya bayan daya.
Zuwa can Abba yayi gyaran murya batare da ya kalli kowa ba yace, Modibo menene ya kawo haka?
Sunkuyar da kansa yayi da sauri tare da yin ajiyan zuciya.
Juyar da tambayan Abba yayi zuwa ga Magaji kai me ka meshi?
Abba nifa kawai ji nayi ana buga min kofa, Ina budewa kawai ya rufeni da duka, haka ake yi? ubanane shi dazaizo ya sameni kawai ya rufeni da duka Abba?
Jimmm Abba yayi zuwa can yace wani abun ka mishi, Kai Modibo me yake faruwa ne gaya min?
Bakomai Abba, kawai kuje ku kwanta ya wuce kawai, Modibo ya fada yana kokarin mikewa.
Ammi ce tace koma ka zauna, babu wani baccin da zamu iyayi yanzun kuma, mene me ya maka ne?
Ya wuce Ammi kubar mgnr, raina ne kawai yake abace bansan na fito ba, awaje na ganni.
Shiru sukayi daga Ammi har Abba kallon Modibo suke, zuwa can bayan Ammi ta gama ‘karewa Modibo kallon tace, ” Fahat ko akan Rahma ne?
Kawar dakai Modibo yayi yayin da Abba yace wacece Rahma?
Matar shi Ammi tafad’a tanabin Modibo daya maida kansa cen gefe da kallo.
Abba Ma Modibon ya kalla sannan ya kalli Magaji tare da fadin, ” a’a ya kuke wasa hakane?, matar auren sa ce fa ba budurwa ba, wanni irin shirme ne wannan?
Ninafiganin hakan Alhaji, acikin Daren nan Modibon ya Kira Rahma banjin me yake cewa Amman najiyo amon fad’an sa cikin waya, dakaina na amshi wayar na kashets sabo da yariyar bata ma da lafiya.
Ni Ina ruwana da ita Ammi? me ya dameni da ita, ita din……
Kai karka gaya min mgnr banza, Modibo ya fad’a Yana nuna sa da yatsa,
Kafi kowa sanin abun daka aikata alakacin daka sauke Afnan ahanya, ita kuma ka tafi da ita
Menayi? aiketa din da nayi laifi ne?, Sabo da tana tare da yariyar shikenan bazan aiketa ba, zarkina kake kenan?
Ya wuce zargi, Abu daya zan gaya maka yanzun shine karka kara, na gaya maka karka kara, Idan anacin baure a kiyaye tauna cikin sa, dan wata rana za’aga tsutsa
Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un Ammi ta fad’a ta yayin da Magaji ke fadin, ” lallai ita yariyar tace na mata wani abu ne?, Ina yariyar take akirata mana, wlh sainayin maganin ta, zaman gidan Nan saiya gagare ta
Abba ne ya daka masa tsayawa tare da fadin, ” ya isa haka, ka shiga hankalin ka.
Abba babu abun da nasan nayi ne, kuma shi ai an bashi dama yayi mgn nima abari nayi mana, Ina ruwana da yariyar ko mgn inayi da ita ne?
Jabir!!
Na’am
Jabir
Na’am
Jabir
Na’am Abba
Saunawa na kira sunan ka?
Sau uku Abba
Sau uku ko?, toh kafita idona in rufe, nasan halin kowanne acikin ku, nasan abun da kowannen ku zai iya aikatawa nakuma San wadd bazakuyi ba, karna karajin irin wannan ya sake faruwa.
Cikin kawar dakai Magaji ya amsa tare da Satan kallon fuskar Modibo da take daure tamau.
Abba ne ya maida kallon sa gurin Modibo tare da fadin, Fahat banson akara tayar da wannan mgnr.
Ajiyan zuciya yayi sanan yace toh Abba.
Ya wuce ko?
Eh yasake fadi tare da mikewa, murya ciki ciki yace Saida safe.
Agogo Abba ya kalla karfe uku da rabi yagani, bayan Modibon yabi da kallo Yana fadin Allah ya tashemu lafiya.
*****
Lokacin da Ammi ta koma dakin ta har hudu ta buga, zama tayi bakin gado domin idon ta ya riga ya bushi, damuwa ne azuciyarta sosai, Afnan da Unaisa ta kalla zuna zaune kowanne daure da tagumi, afili tace yau dai Modibo ya hana kowa bacci agidan nan.
Washegari tu da sassafe ta nufi Asibiti da Unaisa sabo da tun Marin da Modibo yai mata jini ne ya kwanta cikin idon ta gashi kukan da take yawan yi ya kunbura mata fuska.
Daga Asbiti gidan Yaddiko suka nufa, bayan sun gaisa Ammi take bata labari jifan da Rahma taiwa Modibo.
Murmushi Yadikko tayi tana fadin yau ga shirmamma ke mijin naki kuma kike kasa ganewa ba mgn kuwa, jawo Unaisa tayi tana kallon cikin idonta tare da fadin Sannu ko, Modibo be kyauta ba.
Lafewa tayi akirjin Yadikko tanajin yadda yadikko take shafa bayanta cikin sigar lallashi, sai alokacin hawaye suka zubo mata tun dare jiya hawaye ya daina zubo mata
Tsinkayan muryan matar tayi tana fadin, ” Hajiya Modibo yayi mata, ga kyau ga nutsuwa, wlh tunda naimata gani daya ta tsaya min arai.
Murmushi Ammi tayi tare da fadin abun dama bata shaida mijin nata.
Itama Yaddiko dariya tayi tare da fadin, Bata sansu sosai bane amma basa wani kama, kuma harda rashin zaman su tare yau da gobe, da ace tunda yazo da ita ta tare kawai da yanzun…..
Unaisa Bata bari Yaddiko takai ga karasawa ba ta zame ta miki tare da kokarin ficewa adakin.
Bayanta sukabi da kallo Saida ta fice adakin Ammi ta maida kallon ta ga Yaddiko tace, wlh yariyar ta kwanta min sosai nake son Modibo da ita, saidai auren Kamar ya karba ne kawai, nakula yana tausayin yariyar, sunce iyayenta sun rasuwa suka barta a yadda sukace tana da karancin gata.
Wayyo Allah sarki, Allah ya jikan iyayenta, shi kuma Allah yashi ikon rike amanar dake kansa.
Da Amin Ammi ta amsa mata sannan ta mata fadan Shan magani, sai misalin hudu na yamma suka dawo gida.
Tundaga wannan ranar Unaisa Bata sake Bari sun hadu da Modibo ko Magaji ba, tsayon sati biyu aka dauka, gaba dayan su taji bata kaunae ganin su, saidai tanajin shigowan su gurin Ammi harma da fitan su wani lokaci.
Ranar da suka cika sati uku bata sasu cikin idonta ba Afnan ta shigo hannun ta rike da ledoji.
Gaban Rahma ta zube su tare da fadin, gobe zaki fara zuwa makarantar mu,
Jimmm Unaisa tayi zuwa can tace Inji Wa?
Injin Hamma na yace dole ki koma baya domin ki samu karatu mekyau, Rahma kinsan me?
A’a
Ammi so tayi ki tare sai yace sai kinyi karatu, Ammi taita masa fada, amman ya dage.
Kasa cewa komai tayi, saidai cikin zuciyarta dadi taji ba kadan ba, mgnr makarantar ma yaimata dadi domin zaman gidan ya fara isanta
Afnan keta surutunta ita daya wani tasa mata baki wani ba tasa ba labri dai take ta bata saidai yawancin labarin da Afnan take badawa na dariya ne dan haka taketa dariya, duguwar rigace ajikinta mara nauri dakadan ta wuce guiwanta irintace ma ajikin Afnan, dukan su kansu babu kallabi, yatsun hannun su Dana kafarsu dauke da jan lalle na zamani, babu kwalliya afuskarsu amman sosai sukayi kyau, Afnan da Rahma kusan kansu daya sai dan kauri da Afnan tafi Rahma dashi Dukkan su fararene saidai farin Rahma bariin da Afnan bane, balari Afnan takebawa Unaisa itako dariya kawai take.
Saboda yadda take dariyar har aka turo kofar bata sani ba, jin Afnan tayi shiru yasata waigowa, dif ta hadiye dariyar tata tare da binshi da kallo, sunkuyar dakai tayi da sauri tare da kamo daya hannunta ta shiga wasa dashi.
Tsaye yake cikin kananan kaya shigar da Bata taba ganinsu acikin ba gaba dayan su, gilashin sa ya cire tare da sakin kofar ya karasa shigowa.
Jikinta na bata Modibo ne saidai har yanzun bata gama tabbatarwa ba.
Afnan ce ta ce Hamma Ina wuni.
Lafiya lau Afnan ya gida?
Amsawa tayi tana kallon yadda Rahma ta takure.
Shiru gurin ya dauka tsayon lakaci, be sake cewa komai ba, bayan kusna minti goma Modibo yace, ” aunty na kina lafiya?
Kasa amsawa tayi ahankali ta rike rigar Afnan ta gefe.
Itako Afnan dariya ce keson kubuce mata jin Modibo ya kira Rahma aunty.
Zuwa can taji ya sake cewa, jimana aunty minti 1
Cikin sauri Afan tasa hannuta duk biyun ta toshe bakinta dashi, saidai duk da haka ta kasa danne dariya, fashewa tayi da dariya sosai tana kallon Unaisa.
Modobo ma dariya yayi irin wadda be taba yinta gaban Unaisa ba sannan yace, ni kike ma dariya ko?
Hamma Auty fa kace mata?
Toh saime kuma umhum, tashi kije kicewa Ammi Ina gaisheta….
Mikewa Afnan tayi da sauri bakinta cike da mgn, adaidai lokacin data bude kofar taga Modibon yana karasawa cikin dakin nasu
14 comments
Comments are closed.