Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tayar da ƙura a Kannywood
Advertisements
Jama’a da dama a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram nata ce-ce-ku-ce kan wasu kalamai da ɗaya daga cikin ƴan wasan Kannywood ta yi na cewa ana biyanta naira dubu biyu zuwa dubu biyar a duk lokacin da ta yi fim.
A hirar da BBC ta yi da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita, Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ta kasa mallakar muhalli shi ne tun daga lokacin da ta soma wasan kwaikwayo a zamanin mulkin Yakubu Gowon, ba ta taɓa samun kuɗi a dunƙule dubu ashirin ko talatin ko hamsin idan ta yi fim ba.
Wannan batu nata ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta inda jama’a ke ta zargin daraktoci da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar cewa ba su kyautata wa ƴan wasa.
Advertisements
Jarumi kuma mai shirya fina-finai a Kannywood Ali Nuhu yace,
“Bai taɓa biyan Ladin Cima ƙasa da Naira 40,000 ba Saɓanin yanda tace suna biyanta Naira 2,000 zuwa 5,000 bayan yin fim.
2 comments