
WATA FITSARA*🤔
By
Fadeela Lamiɗo
PAGE 10
Wata mota ya hango can kofar da zata adaka da gidan Inna Yalwa dan haka ya karasa bayan motar sannan ya fito”
Jimmm yayi hango Khadija tsaye ta gaban motar yayin da wani ke tsaye kusa da ita”
Tsintan kansa yayi da karasawa wajen, ido biyu sukayi da Khadija, saurin dauke idonsa yayi akanta ya maida Kan wadda take tare dashi”
Alhaji Kabiru?🤔
Na’am Ahmad ya garin”
Hannnu ya bashi suka gaisa sannan wadda ya Kira da suna Alhaji Kabiru yace”
Ya aiyuka ya kwana biyu?
Alhamdulillah Ahmad, ya fada sannan ya kalli Khadija ya shige cikin gidan zuciyarsa cike da Mamaki”
Dakin Khadija ya shiga ya zauna bakin gado, zuwa can ma ya kwantar da bayansa Kan kadon, yayin da kafafunta ke zube akasa”
Afili yace Khadija na nufin Alhaji Kabiru zata aura?, Tsohon saurayinta, lallai Khadija nawasa dani, yatsansa ya ciza sannan yace”
Yaune karshe duk abun da zanyi Khadija ta fahimceni nayi, Amman taki ganewa shikenan zan barki, zan barki Khadija”
Tagefen idonsa ya share hawaye sannan yai ajiyan zuciya”
Da Sallama Khadija ta shigo dakin daker Ahmad ya iya amsawa”
Kwanciya kayi halan bakajin dadi ko??
Lfyta lau ya fada yana kokarin tashi zaune”
Amman saina ganka wani iri??
Eh mana toh a ya kike son ki ganni bayan kekika birkitani”
Kaidai ka birkita kanka Ahmad”
Hakane?
Eh mana”
Meyasa kikace haka?
Hakane mana zuciyarka tana tunanin abun da bazai yiyuba”
Eh bakiyi karyaba daman zuciya da buri akasanta”
Hmmm Kai komai aka Gaya maka kana da amsan da zaka bada😏
So kike in miki shiru ki gayamin abun da kikaga dama?
Ni a’a yanzun dai mubar mgnr ma kawai, aurena saura sati biyu yau, akwai abubuwan da bani dasu nawa zaka bani insaya??, Karasa mgnr tayi cikin zulaya tare da tsaresa da ido domin taje me zaice, ya hakura kobe hakura ba?
Ido ya tsora Mata sannan yace”
Kiyi lissafi kawai Khadija konawa ne indai har idashi zan miki”
Dadi taji sosai, insha Allahu ita da Ahmad an wuce gurin……
Wai Alhaji Kabiru Zaki aura?
Wannan tambayan ita ta katseta daga tunanin da take, ahankali tace eh”
Murmushi yayi kadan sannan yace”
Ashe kuwa zaki tabka kuskure”
Cikin sauri tace, nidai babu ruwanka dashi”
Shikenan na bari,
Mikewa Khadija tayi ta cire Hijjabin jikinta ta ninke sannan ta ajiye adaidai lokacin da Ahmad din ya mike”
Zabura tayi tajingina da bango yayin da Ahmad ya karaso yai Mata runfa sannan ya tsareta da ido”
Inajin ki ya mgnr mu dake?
Kwalkwal tayi da ido Ahmad ba yanzun mukayi mgn ba ai kasan mgnr aurena nanan”
Ainace miki ki janye ko?
Ni bazan janyeba Ahmad Aure zanyi, kuma na gaya maka bar tunanin aure tsakanin mu dannni ba tsarar ka bace”
Hmmm ke ba tsarata bace ko?, Shekarun mu daya Amman ke kina da Samha ko?, nikuma ko auren fari banyi ba dan haka kikejin kanki tare da wahalar dani, ke kin girma ni kuma ban girmaba har yanzun kallon yaro kike min ko?
Shiru tayi tana jikin bango haryanzun yayin dayai mata runfa ya tare ta da hannunwansa babu hanyar wucewa”‘
Ahankali yace shikenan, tunda ke girma kikeso zaki samu, shikenan saikin ji sakona……
Wani sako ne wannan Ahmad kana tayar min da hankali fah wlh zan zageka Ahmad”
Toh ki zageni mana, ai bayau kika faraba, kinsha zagina amman kisan irin zagin da zakimin dan idan kikai min wadda be daceba zakiga yadda zan dake adakin nan”
Me zaka min ne, Ahmad Kanata ikirarayin idan naki amincewa dakai zanga abun da zai biyo baya me kake niyar yi ne?
Wannan ba matsalar ki bace ba”
Hmmm Ahmad wlh Kai hankali Dani, nace bazan aureka ba, nacin meye wannan?
Hannunsa ya dago yayin da tai saurin cewa karka tabani”
Akan me zan tabaki?, Niba haka nake ba, niba haka nake ba, ni kike dakawa tsayawa ko?
Toh wanene Kai?, ninama goge number ka awayata domin aurena zanyi wlh babu fashi”
Ni ban goge number kiba Khadija, saidai bazan kara kiranki awayata ba, kuma ko kin kirani bazan dauka ba”
Daka taimakeni kuwa, ni bazan ma kiraka ba bare kaki daukan”
Hmmm, Khadija kenan, Nina San anjima zaki kirani, zakiso kiyi mgn dani nikuma bazan saurareki ba”
Juyawa yayi ya fita yayin da Khadija ta saki ajiyan zuciya tare da fadin”
Me Ahmad yake shiryawa ne?🤔”
Gaba daya ranar haka ta karasata bata da walwala kwata kwata koya ta motsa Ahmad take gani, a yadda ya fita ta figita sosai”
Dataji Karan wayarta sai taga kamar ce mata za’ayi Ahmad ya dake Alhaji Kabiru”
Misalin 9:30pm taji Muryan Alhaji tare da Baba cikin gidan, sosai gabanta ya fadi Dan kafin Alhaji yazo gidan su Saida wani Babban dalili, abu biyone acikin zuciyarta take tunanin zai iya kawo sa gidan, kodai ace Mata tayi hakuri ta aure Ahmad ko kuma Alhaji Kabiru ne ya kawo Karan Ahmad akan ya tare da fada, vata tunanin akwai wani abu wadda Ahmad zaiyi Wanda ya wuce wannan”
Amman me har 10 ta buga babu wadda ya kirata, saidai tanajin alamar Hira sukeyi cikin farin ciki da Annashuwa da alama kusan gaba daya gidan sun taru ne adakin Baba, afili tace wata kila nikadai ce bana wajen, abun kunya waini Ahmad zaice yanaso yanzun shikenan kowa yaji, aikuwa ko sama da kasa zata hade nikam bazan Aure Ahmad ba……
Kiran da Inna Yalwa ke kwala mata ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, tare da mikewa da saurinta”
Lokacin gani tayi matan gidan nata fitowa daga dakin Baba kowa fuskansa dauke da fara’a”
Shiga ciki tayi ta zauna yayin kanta akasa, wannan karon daga Alhaji sai Baba acikin dakin”
Khadija taji Alhajin ya fada”
Na’am”
Bakiji gidan anata murna bane kika kule daki??
Bacci nake Alhaji Farkawata kenan”
Masha Allah Alhajin ya fada sannan yace”
Kinaji Khadija, wani abun arzikine ya tunkaro
Mu ko nace yake Shirin tunkaro mu”
Tunda Alhaji ya fara mgn gaban Khadija ya fara faduwa yayin data kasa kunne take jiran taji me za’a Mata”
Alhaji ne yacigaba da cewa, koda nasan kila kina da lbr tunda Ahmad mutumin kine, ko ya gaya miki??
Cikin sauri ta girgiza kai”
Tam dazon Mahaifin sa yazomin da wata mgn data sani farinciki matukar gaske, naji dadi sosai kuma insha Allah zan jajirce sai inda karfina ya kare”
Sosai gaban Khadija ke dukan uku uku tai matukar kosawa taji meye”
Yariyar wajen ki Fatima Ahmad ya neme da aneman masa auren ta”
😳😳😳 Hannu tasa ta dafe kirjinta jitayi tamkar numfashinta zai dauki saboda tsabar razana datayi, zufane ya fara karyo mata kota ina”
Yayane Baba ya fada bayan ya lura da yanayin da Khadija ta shiga”
Nufarfashi ta sauki sannan tace”
Alhaji wasa yake yi wlh, Samha ai karamar yariya ce bata isa aure ba”
Wanni irin wasa kuma Khadija?, Mahaifinsa ne yazo min da mgnr dazon nan, babu zancen wasa aciki”
Alhaji ai bata isa aure ba, ta yaya aure zai kasance tsakanin Ahmad da Samha aj yamata girma”
Hmmm Khadija kenan wannan ba wani abu bane, tunda ba haramun bane ba, intakaice miki mgnr tsoho me shekaru na ma sai ya auro kamarta, wannan wani zumunci ne Ahmad zai kara kulla mana wadda komu bamuyi tunanin hada ‘yayan mu ba……
Hawayene suka zubo Mata tare da fadin”
Alhaji wannan ba zuminci bane ba, wannan ai WATA FITSARA ce kawai, wulakantani Ahmad yake shirin yi😭
Gaba dayansu bude baki sukayi cikin fada Baba yace”
Dan yace yana son ‘yarki kike kiransa Fitsararre🤔, dama akwai wani takun sakane tsakanin ku??
Jimmmm tayi zuwa can ta girgiza Kai hawaye na tsiyayo mata😭😭
Babane yace”
Fatan alheri mukesom kiyiwa abun, shekaranta nawa ne yanzun?
Kanta akasa yayin da hawaye kecigaba da sakkon Mata tace”
Sha shidda ne”
Jammm sukayi zuwa can Alhaji yace”
Wannan ba wani abu bane ba, idan har ubanta ya amsa zaibashi saiya dan jirata kadan, idan kuma zaibamu haka din mu ai muna so, Ahmad nada hankali da nutsuwa nasan zai riketa da kyau”
Alhaji nasan Abbanta bazai Mata aure yanzun ba, kuma ko zai Mata bazaibawa Ahmad ba Dan ba shiri suke ba😔😭
Wannan ba matsalarki baceba Khadija, ni abun da nasani matar mutum kabarin sa Dan haka bana ko dar, indai matarsace toh aure babu wadda ya isa ya hana”
Jimmm tayi tana Kara nanata zancen nan sannan tace”
Toh shikenan😔
Mikewa yayi ta fita daker take iya ganin gavanta, cikin dafa bango ta isa dakinta tana fitowa taji duk gidan zancen ake dan haka taji kamar ta hadiye zuciya ta mutu, kodata shiga dakinta cikin bango tasa kanta tana share hawaye take fadin”
Nashiga uku,😭 tsakani da Allah ya Samha zatayi da Ahmad?😭 Ina zata kaishi ya jama’atul musulmi😭 nashiga uku, memakon ya gaya min yaje ya furta kowa yaji😭, Ina bazan bari ba, wlh bazan taba barin ayi wannan abunba, wannan ai iskanci ne, Banda shi bashi da kunya dazon ya gama cewa na aureshi yanzun kuma yace, Samha?😭
Kuka ta dingayi yayin da kirjinta yadau zafi sosai, ji take kamar zai fashe saboda tsabar tashin hankali”
Kuka taci ta koshi sannan ta fara neman mafita, wayarta ta dauka ta dannan masa Kira saidai harya katse be dauka ba sake Kira tayi har sau 5 amman ba’a daga ba, afili tace Inna Ahmad ya shiga ne?😭
Kasa hakuri tayi dan haka ta tsinci kanta tura masa sako”
_Ahmad idan kaga sakona kakirani inason mgn dakai_
********
Ahmad kwance Kan gadon sa yayin da Hajja ke fesansa tana fadin”
Banda abunka meye kuma na damuwa, indai Fatima ce insha Allahu rabonkace batun yauba nake maka sha’awarta saidai idan kana da wata damuwa daban kuma”
Himmm nidai Hajjah kimin addu’a kawai bani da nutsuwa kwata kwata Ina bukatar addu’arki, ki rokarmin Allah yasamin nutsuwa acikin zuciyata”
Cikin tausayawa take kallonsa tasan be taba furta yana son Wata yariya ba wata kila shiyasa yaudin ya daburce, shafa kansa tayi sannan tace”
Ahmad, gobe kaje ka ganu Fatima wata kita kila kadan samu nutsuwa, yau farin ciki ya kamata kayi amman naga Kai kamar wani abu na damun ka”
Hajja ainagaya miki danaje gidansu taki mgn dani”
Toh ai kaikuma ba beye Mata zakayi ba, anya kuwa ma zaka iya da ita kuwa🤔, karamar yariya ce fa sosai dole saika kwantar dakai tare da jawuta jikin ka”
Mezai Hana Hajja…… Shigowan sakon Khadija shiya katse masa zancen da take”
Yadda yaba wayar hankali yasa Hajja barin dakin tare da ja masa kofar”
Bayan ya gama karanta sakon Khadija murmushi yayi, wani kwari ne yaji yazo masa har ya tashi zaune bebar murmushi ba”
Gyara zama yayi sosai sannan ya fara typing…
_Kin manta kince kin goge number ta_???
Cikin kanganin lokaci yaga ta maido masa”
_Wasa nake maka, ka kirani zamuyi mgn_
Kafin yayi wani wunkuri kiranta ya sake shigo masa, tsayawa yayi yana kallon sunanta harya katse sannan ya rubuta mata”
_Nibazanyi waya dake ba kamar yadda kikace yafi, Saida safe_
Batare da wani bata lokaci ba ta sake turowa…..
_Wani lbr naji dazon, Wai kace kana son Samha da gaske ne_??
Ataikace ya aika Mata da _eh_
_Saboda da Allah Ahmad WATA FITSAR ce kuma wannan_??
Murmushi Ahmad yayi wannan karon beson ya amsa Mata dan haka yaita kallon sakon har wani ya sake shigowa”
_Tsakanin ka da Allah Ahmad ya Samha zatayi dakai, haba dan Allah kaiko kunya ma bakaji_
Wannan karon ma murmushi yayi afili yace”
Meya shafeki badai girma kike so ba gashinan kin samu sai hankalin ki ya kwanta, wani sakon ya sake gani….
._Ka dauki wayata muyi mgn ko kazo da safe, Samha ai saita rainaka tamaka kankanta Ahmad, banji dadiba danaga duk anji zancen_
Kashe wayar yayi baki daya sannan yace”
Kin ma rainamin wayau ke kin min girma ita kuma kince tamin kankanta zaki gane baki da wayau, tsaki yaja sannan yai jifa da wayar”
Itama Khadija ganin yabar amsa mata ta Kira layin sa wannan lokacin akashe taji shi, can Kan gado ta aje waya sannan tai lamo yadda taga rana haka taga dare dan haka washegari ta tashi da tunanin zuwa gurin Samha amakaranta domin taji kotasan wata mgn akai🤔
Duk yadda akayi Samha tasan wani abu, idan ko har hakane zataga bacin raina, haka kawai Ahmad bazayi haka ba, da irin wannan tunanin ta shirya ta nufi makarantar, saidai batasan yadda Ahmad keyi abarshi yaganta ba”
Shima Ahmad yau da shirinsa ya tashi, domin akwai yadda yakeson abun ya tafin masa dan haka dole yaje ya ganta sannan yacire Mata haushin shi azuciyarta
7 comments