Advertisements

Screenshot 20220215 220638 1

HANYOYIN SARRAFA KWAI KALA KALA, SA ME GIDAN GYANGYAƊI

Posted by

HANYOYIN SARRAFA KWAI KALA KALA, SA ME GIDAN GYANGYAƊI

 

Advertisements

 

HANYOYIN SARRAFA KWAI KALA KALA SA ME GIDAN GYANGYAƊI

Abubuwan bukata

Advertisements

Kwai
Nama
Curry
Maggi
Gishiri
Tumatir

Ki dafa kwanki, daidai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, kisa maggi, curry, gishiri, ki kada ya kadu sosai, ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai.

 

Advertisements

SUYAR KWAI MAI NAMA

Abubuwa Bukata

kwai
Nama
Maggi da gishiri
Curry
Albasa
Attarugu

Ki tafasa namanki da maggi, curry, thyme, albasa, ki daka shi sosai, ki fasa kwai ki yanka albasa, attarugu, ki zuba dakakken nama, ki karo maggi da gishiri daidai yadda kike so, ki kada sosai, ki soya kamar wainar kwai.

 

NAMA CIKIN KWAI

Abubuwan bukata

Kwai
Nama
Gishiri da Maggi
Albasa
Attarugu
Mai

Ki dafa kwanki daidai yawan da kikeso, kowanne ki yanke kasansa wajen fadin kadan ki kwakule kwanduwar a hankali ki cire ta, ki tafasa namanki da curry, thyme, maggi, gishiri. Idan ya dahu ki zuba attarugu kadan ki daka naman, sannan ki dinga debo dakakken naman kina turawa cikin kwai, idan ya cika sai ki debo kwanduwar ki toshe bakin kwan da ita, haka zakiyi tayi har ki gama, sannan ki dinga tsoma kwan a cikin ruwan kwai kina soyawa, idan ya soyu sai ki kwashe, wannan nama cikin kwan yana da dadi.

 

WAINAR KWAI MAI ALAYYAHU

Abubuwan bukata

Kwai
Hanta
Alayyahu
Curry
Maggi da gishiri
Albasa da Attarugu
Manja ko Mai

Ki yanka alayyahunki kanana, hantar ki daka ta, bayan kin dafe ki fasa kwai ki zuba hantar, ki zuba alayyahunki, curry, maggi, gishiri, da albasa, idan kina so, ki soyata kamar suyar wainar kwai.

 

WAINAR KWAN VEGETABLES DA KODA

Abubuwan bukata

Koda
Kwai
kabeji
Peas
Green peas
Carrot
Maggi da gishiri
Curry
Albasa da attarugu

Ki yanka vegetables naki ki soya su sama-sama, ki fasa kwanki ki zuba maggi, curry, gishiri, ki tafasa kodarki ki yanka ta kanana, ki zuba akan kwan, ki zuba vegetables ki soya.

 

DAFAFFEN KWAI MAI DADI

Abubuwan bukata

* Kwai
* Albasa da Attarugu
* Curry
* Maggi da gishiri

Ki fasa kwanki ta samansa amma fasawar yar karama zakiyi, ki zaggaga kwan a kwano, ki yanka attarugu da albasa ki zuba a kan kwan, ki zuba curry, gishiri da maggi daidai yadda dandanon zai yi miki, ki zuba mai kadan ki kada kwan sosai, sannan ki duddura kwan a cikin kwansonsa da kika juye, ki kawo solitef ki nannade kwan dashi sosai sai ki zuba ruwa a tukunya, ki jajjera kwan ki rufe ya dahu sannan ki sauke, zaki bare kamar yadda ake bare dafaffen kwai, bayan kin warware solief din. Akwai dadi sosai.

 

KOSAN KWAI

Abubuwan bukata

Kwai
Busasshen burodi
Attarugu
Maggi da gishiri
Curry
Albasa
Mai

Ki daka busasshen burodi, ki fasa kwai, ki yanka albasa, attarugu, maggi, gishiri, curry, ki zuba busasshen burodi ki juya yayi kwauri kamar kwabin kosai, ki dinga dibar kullin kina sawa a mai kina soyawa kamar kosai, idan yayi ja ki dinga kwashewa kina tsanewa da kwadanda.

 

ALALAN KWAI / AWARAR KWAI

Abubuwan bukata

Kwai
Kifin gwangwani
Albasa da attarugu
Maggi da gishiri
Man gyada ko butter

Ki bude Kifin gwangwaninki, ki dagargaza shi ya murmushe sosai, ki fasa kwan daidai yadda kike son yawan alalan, ki yanka albasa, attarugu, carrot, ki hada da peas ki zuba akan kwan, kisa gishiri, maggi, curry, ki zuba kifin akan kwan, ki buga sosai, ki zuba mai kadan ki shafa butter ko mai a gwangwani ki zuzzuba, ko ki kukkulla a leda, za ki iya ci haka idan ya dahu ko ki yayyanka kisa a ruwan kwai ki soya ta zama awarar kwai *

 

WAINAR KWAN DANKALI

Abubuwan bukata

Kwai
Dankali
Nama
Albasa
Curry
Maggi da gishiri
Mai

Ki dafa dankalinki ki marmasa, ki tafasa nama, curry, maggi da gishiri ki daka, ki tafasa kwai ki zuba dakakken naman da dankalin akan kwan ki yanka albasa, kisa gishiri, maggi da curry ki kada su hadu sosai ki soya kamar suyar kwai, ko ki gasa a oven

57 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *