IMG 20220121 WA0314

WATA FITSARA PAGE 13

Posted by

WATA FITSARA PAGE 13

 

WATA FITSARA

     By
Fadeela Lamido

                         Page 13

Gaskiya mgnr ka sosai take min irin ta Uncle, har dariyar kuma iri daya, saidai shi Uncle kafin kabashi dariya aiki ne, bakoda yaushe yake dariya ba, Amman fa duk ranar dayai dariyar saiya burgeka”

       Dan Allah, Anya kuwa kodai kece baki iya bada dariyar ba?

    Niko na iya bada dariya tunda inabawa Abbana dariya yaitayi inajin Dadi shima kuma yanason yaga Inna dariya, amman Uncle barshi dai da murmushi Amman da wiya kaji yayi dariya, bafa ya Wasa da yara dani kadai yake wasa mutane tsoronsa suke Amman ni yana mgn Dani”

     Himm lallai Fatima kice taku tazo daya dashi”

   Sosai kuwa, Ina sonshi sosai azuciyata saboda shima yana Sona”

     Dan Allah?

     Dagaske, kasan shi Uncle din……

   Ina zuwa dan dakata Malama, daga hannun sa yayi kamar yana gabanta yace”

      Haka ake yi?,  nakiraki muyi Hira kuma kinata min zancen Uncle din ki, har kinsa nafara jin kishin sa”

    Jimmm tayi sannan tai murmushi to ai Babana ne tun da dan uwan Mamana ne”

      Cikin lumshe idonsa yace nagane, amman uwa daya Uba daya suke da Mamar taki??

     Kai tsaye tace A’a

   Jim yayi fuskarshi ciki da murmushi zuwa can yace toh aiko akwai aure atsakanin ku”

     Cab lallai, Babba ne fah🤔

     Jimmm yadanyi sannan yace”

     Ai ba’a girma a aure, zai iya auren ki”

     Jimm tayi cikin yanayi irin na tunani, jin shirunta yayi yawa ya Kira sunanta”

          Fatima”

     Na’am

    Yanaji kinyi shiru”

    Ni bacci nafara saida safe”

     Katse Kiran tayi yayin da Ahmad ya tsaya yana kallon wayar dariya yayi sosai sannan yace”

     Toh ita Fatima ashe da kore samarin zata dinga yi da lbrn Uncle,🤣 jifa lbrn Uncle kawai tabani takuma kashe wayarta tabarni🤣

      **********

  Itako bayan ta kashe wayar tunani ta shigayi, sosai take son ganin Uncle dinta Amman zancen Mamananta nata dawo mata, duk da haka batabar son jin muryarsa ba, wayar hannunta ta kallah ga waya ahannunta Amman babu damar yin waya da Uncle tunda bata da Number sa”

    Daker vacci ya dauketa ko tuna wani Moh’d batai ba”

         ***********

Khadija zaune gaban Hajjah duk ta rame idonta ya zurzurma, gefenta aunty saude ce wato yayar Ahmad”

      Hajjah ce tace”

  Ina jinki Khadija, abun yaban Mamaki, keda Ahmad beci ce kuna haka ba, yace kinata zagin shi har kina neman dukan sa, me yai zafi haka?

    Hawaye Khadija ta share sannan tace”

     Hajjah bakiji WATA FITSARAR da ya bullo da ita bane?, Ina Samha Ina shi dan Allah Hajjah sa’a nane fa, Ina zata kaishi ma”

    Baki Hajjah ta rike zuwa can tace”

    Haba Khadija, wannan ai tunanin yara ne, dan Allah kibar wannan mgnr, Ahmad yana son Samha tun tana ‘yar karamarta fahimtane bakiyi ba”

    Hmmmm Hajjah bakisan wani abu ba”

    Menene shi Gaya min?

    Hajjah Ahmad bashi da kunya kowacce irin mgn fada yake gabana sannan yazo yace Wai Samha zai aure😭😭

    Hannu Hajjah tasa ta fara share Mata hawaye tare da fadin”

   Karki damu da wannan, idan kin tuna Ahmad bashi da aminiyar data wuce ki adah, kuntaso tare kamar tagwaye dan kinsan wasu kalamai nasa ba wani abu bane ba”

    Sosai Hajjah take rarrashin Khadija bayan tayi shiru ta tashi tabarsu da aunty saude”

      Kallon Khadija aunty Saude tayi tace”

     Amman kinbani Mamaki Khadija, yanzun dan Ahmad yace yana son ‘yarki harsai an lallashe ki, meye da Ahmad din?, Yana da wani mugun haline da kike gudun sa haka??

    Aunty Saude Ahmad fah cewa yayi yana sona kawai Dan naki amincewa ya tsoro da wannan zancen, ba har zuciyarsa yake fada ba”

     Haka kike tunani Khadija?, Su Daddy fah har sunje sun nemar masa izzini gurin Babanta kuma yabashi dama”

    Ba gaskiya bane, na tabbatar Usman bazai bawa Ahmad auren Samha  kamar yadda kikace ba, kwata kwata basa shiri”

     Ai saikiyi Khadija, Amman nasan baki isa kija dayin Allah ba”

   Insha Allahu Aunty aure bazai kasance atsakanin su ba”

     😳😳 Agabana Khadija? Wanni irin wulakanci ne wannan, ke kin kisa, yayi yayi kinki ya hakura yace ‘yarki, kina nunawa muraratan bakya so?

     Cikin kuka tace Aunty Ahmad Dan uwanane daidai darana daya bantaba masa kallon wadda zan iya aura ba, kuma abun da yasa banson auren sa da Samha, Ahmad bashi da kunya Dan iskane babu irin kalmar iskancin dabe Gaya min ba, sabo da tsabar raini yace kuma Samha zai aura, aunty wlh zuciyata zafi take sosai

      Cafdi lalai, yauzun Khadija kika iya kallon tsabar idona kice min Ahmad dan iska ne?, ‘yarwa aka taba kamashi da ita?, Inason ki gayamin wani abun mara kyau da Ahmad yake aikatawa”

    Shiru Khadija tayi tana share hawaye yayin da Aunty saude ta tsareta da ido, ganin Khadija bata da niyyar mgn yasa fadin”

     Shikenan, ke kin kishi, kuma kince baki yadda ya auri ‘yarki ba, bari yazo indai shima ba maye bane yabar miki ‘yarki, idan ko har ya dage ni banu ruwana akan zancen banson wannan auren kin gama nuwa Ahmad kiyayya duk da tun kina ‘yar karama yake nuna miki kyauna”

   Afusace Aunty Saude ta mike, ciki ta shiga tawa Hajja sallama ta wuce Khadija tana share hawaye”

    Sosai jikin Khadija yayi sanyi, bakin Ahmad da Samha take ba, amman abun  tsare ne babu Kwata kwata, tunawa da tayi Abban Samha bazai badataba yasa ta saki ajiyan zuciya, sannan ta daga hannunta sama tace”

     Allah kasamin nutsuwa nabarwa zuciyata Usman bazai bawa Ahmad aure ba idan matsalar ta bullo daga wajen Babanta babu wadda zai zargeni”

     Da wannan tunanin tadan samu nutsuwa agidan ta wuni da Yamma harta mike tawa Hajjah Sallama saiga Ahmad ya shigo”

      Kusan cin karo sukayi yayin da yai saurin kyaucewa ya bata hanya”

      Afusace ta fita ranta bace,  yayin da Ahmad yabita da ido yana fadin”

    Ina wuni?

   Ko waigowa bataiba bare yasa ran zata amsa”

    Juyawa yayi ya shiga gida inda Hajja ke sanar masa sun gama mgn da Khadija”

     **********

  Tundaga ranar Khadija ta daina cewa komai akan zancen ko taji acikin gidan anayi tashi take dabar wajen yayin da kwata kwata Ahmad ya dauke kafar sa daga gidan”

       ************

    Abba ni gaskiya bana son shi😔

    Jimmm yayi yana kallonta zuwa can ya mika hannunsa ya zaunar da ita Kan cinyan sa tare da fadin”

Moh’d din??

     Kaita daga alamar eh”

    Murmushi yayi har yanzun bebar kallon ta ba, toh Mamana da kike wannan mgnr kin tava ganin sa ne??

     Girgiza Kai ta sake yi sannan yace”

   Ni banson na ganshi”

      Shiru ya sakeyi sannan yace”

     Gaskiya Ummee kina da matsala, tayaya mutumin da baki gansa ba har kika fara cewa bakison sa, nikuma kinga sau biyu mukayi waya dashi naji ya kwanta min, yaron nada wayau kamar ki?

      Shirin kuka take tana fadin”

     Nidai Abba kace yabar kirana  bana so😔

    Jimmm ya sakeyi sannan yace”

    Toh yanzun abun da zamuyi, ki daure kibari yazo din kafin kice wani abu akansa, idan baki sonshi bazan takura miki ba, kar ki yadda ki bata min rai akan wannan kiji na gaya miki”

        ********

  Khadija ce tsaye gaban Alhaji Babiru yayin da yana daga cikin motar sa ya zuba tagumi”

     Zuwa can ya dago yace”

   Kinga Khadija nagaji da wulakancin da kike min, yau sati daya kenan idan na kiraki baki dauka, narasa gane kanki, yanzun kinzo kin tsaya inata mgn kin min shiru akarshe kin kama kuka, niba Yaro bane ba, nasan duk take taken ku namata idan kuka canza ra’ayin ku, da wannan abun da kike kifito fili kicemin kin fasa’

   Niba fasawa nayi ba kaje kacigaba da harkokin bikin ka har adaura aure, amman kabar kirana waya ko zuwa wajena, inada damuwa azuciyata sosai banajin Dadi shiyasa zaka ganni ahaka”

    Haka komai bemin Dadi”

    Ahakadin ne zan aure ki Allah ya kiyaye aini ba wahalalle bane, anayin aure ne dan aji dadi ahaka zan aureki kina min kunci, tsaki yaja sannan ya rufe motarsa harsaida Khadija ta zabura yabar layin

     Koda ta shiga gida rasa inda zata saka kanta tayi komai ya daina Mata Dadi, yayin data karajin tsanar Ahmad cikin ranta”

         *********

      Ranar da ya rage saura kwana 6 daurin auren Khadija aranat Ahmad ya ziyarci makarantar su Samha”

     Tundata zauna acikin motar take zunburan baki, cikin kunkunai take gaida shi”

    Samha yaya ne?, Inace mun shirya kona sake miki wani abu ne?

     Kawar dakai tayi yayin da yace”

   Ina jinki meyene kuma??

     Kawar da kanta tayi sannan tace”

    Uncle meyasa ka zagi Momy na??

   Jimmmm yayi tare da runtse ido, zuwa can ya bude tare da roko hannunta yace”

     Ni?, Haka tace miki na zageta??

     Eh mana, nakirata ta bani number ka shine tace min kana zaginta kuma so kake ka cutar Dani injita”

    Subuhallahi😬 ya fada afili, sannan azuciyarsa yace ya Ina tufka zata dinga warware min?

    Hannunta ya kama cikin wasa da yatsun yake fadin”

     Fatima, nasan kin yadda Dani ko?

    Kaita daga idonta ciki da kwallah”

    Toh inason ki Kara yadda dani fiye da da, ni ban zageta ba, nasan darajar ta, kuma idan zata fada miki gaskiya bana tunanin nataba zaginta ko cikin wasa, kinsan menene Khadija?

     Kaita sake girgizawa”

  Yana Cigaba da wasa da yatsunta gace”

    So take ta rabani dake saboda nabata shawara akan auren da zatayi, shine kawai Amman wlh ban zageta, kuma ni bazan cutar dake ba

     Sosai ta yadda dashi dan haka tace shikenan Uncle Amman tace karna sake maka mgn, kabata hakuri saboda ta dinga bari na Ina hira dakai”

     Jimmm yayi cikin lumshe ido sannan yace”

     Ban miki alkawari ba Fatima daga nabata shawara saikuma nabata hakuri”

   ..Kwalkwal tayi da idonta kamar zatai kuka”

   Kawar da kansa yayi tare da yamutsa fuska, kusa dashi Fatima ta Kara matsowa ta rike hannunsa, Uncle karkai fushi kabata hakuri kaji👏🏻

      Hannunsa yasa ya zame nata daga jikin sa sannan yace”

   Naji to, yanzun meye lbr?

    Yauwa Uncle, kaga Abbana ko?, Wai wani yabawa number ta ya kirani Wai idan mun daidai na aure shi”

    Wani wa?, Ya tambaya atakaice”

    Uncle sunan sa Moh’d munyi waya dashi sau biyu”

   Kenan aure zai miki?

    Eh Uncle Amman ni koransa zanyi ban son sa”

Dariya yayi har hakuransa suka bayyana sannan ya sake roko hannunta yana kallon cikin idonta yace”

     Karki koresa Fatima, kibari yazo ki ganshi mana”

     Banson ganinshi Uncle ni ko awaya banso yake kirana, kasan ma abun da yasa nake daukan wayarsa”

     A’a

   Muryan ka da nashi sun kusa iri daya🤗

      Cikin murmushi yace Dan Allah?

   Allah kuwan harma nagaya masa sannan nabashi lbrn ka kasan me yace min?

       Sai kin fada”

    Cewa yayi Wai nidaiai zamu iyayin aure tunda ba mmn ku daya baba daya va da Mamana ba”

    Cikin murmushi sosai yajawota jikinsa sannan yace”

     Kwarai kuwa zan iya auren ki”

   Cikin dariya tace, Haba dai Uncle bazakaji kunyata ba?

     Cikin ido ya kalleta sannan yace, kunyar me?

   Jiba fah Uncle Kai kato ni ‘yar karama”

    Hmmm toh meye aciki?, Ke yanzun idan na aureki saikiji kunyata??

       Kanne Kai tayi tare da shigewa cikin sa tace”

     Nidai Uncle banson Moh’d din”

    Yana shafa bayanta yace, nikuma nace kibari ki gansa bakinci muryansa irin nawa bane???

     Eh”

    Yauwa toh idan akai sa’a kamar tamu ma tazo daya, ai kila kisoshi”

     Caf ai wallahi kamar ku bazata taba zuwa daya ba”

      Waye ya gaya miki, toh idan mukayi kama koda ace irin gemuna yake dashi Zaki soshi??

     Dagowa tayi ta kalleshi sannan tace”

      Toh dan yana da irin gemun ka kawai saina kama son shi?😩

      A’a inace ranar nan cewa kikayi gemuna ke burgeke??

     Ai Uncle ajikin kane yake da kyau basan ko idan na ganshi agurin wani zai burgeni ba”

    Sosai yayi Mamakin wannan kalami na Fatima kenan duk abun da take tana sane, cikin ido ya kalleta sannan yace”

    Nidai nace miki kibawa Moh’d daman yazo ya kanki, in kuma dani za’ayi toh”

    Duka takai masa akirji yayin dayai saurin tarewa cikin kukan shagwaba tace ai Abba na bazai yadda ba”

     Yana rike da hannunta duk biyun yace kefa zaki yadda???

    Cikuikuye kanta tayi cikin dan karamin  hijjabin makarantar ta, mamayansa tayi ta finceke hannunta ta fita aguje,  harta shiga makarantar bata waiwayo ba, murmushi yayi yashafa sumar sa tare da kara kallon gate din, yana kokarin dauke idonsa yaga ta leko ta na daga masa hannun cikin murmushi”

   Kara fadada murmushin sa yayi sannan shima yadaga Mata hannun”

   Cikike da farin ciki ya koma gida,

    Washegari wuni yayi da ita cikin ransa, kome yake ita yake tunawa dan haka washegari yai nufin Kai kansa gidan Alhaji Usman”

     Wayarta ya Kira daker ta dauka ya sanar Mata yau yana tafe”

    Daker ta yadda yazo din sannan ya shirya cikin kananan kaya da suka dace da jikin sa, ya nufi Gidan su Khadija”

    Akan hanyarsa ne Aunty Saude ta kirasa bayan sun gaisa tace”

   Kana inane yanzun?

   Ina hanya zani gidan su Fatima yau, Aunty kimin addu’a kinji”

    Kafin kaje inason ganin ka”

   Aunty idan na dawo zanzo nariga nakama hanya”

    Ahmad kazo nace k…….

   Aunty Dan Allah kiyi hakuri indawo namatsu sosai inganta”

   Lumshe ido tayi sannan tace shikenan Ina jiran ka………

8 comments

  1. Pingback: remisolleke
  2. Pingback: cam coins
  3. Pingback: 1win Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *