Advertisements
HATTARA IYAYE, CIKAKKEN LABARIN KISAN HANIFA.
Abdulmalik Muhammad Tanko Malamin makarantarsu Hanifa, yayi garkuwa da Dalibarsa ya bata guba ta mutu kuma ya nemi karban kudin fansa kafin aka kamashi saboda tsabagen cin amana
Hanifa karamar yarinyace, bata wuce shekaru 5 ba, bata masa laifin komai ba amma saboda son zuciya da rashin imani ya sace ta ya kasheta kisan wulakanci
Advertisements
Ina yawan fadawa makusanta na wannan maganar cewa ita wannan rayuwar da mukeyi a yanzu amana tayi karanci, batun yadda da mutane yayi wahala, mugun mutum macuci da makiyi bai da kama
Kana mu’amala da mutum yana maka murmushi zaka dauka masoyinka ne, amma a cikin zuciyarsa inda wani babban dutse zai fado maka a tsakiyar kanka ka mutu nan take zai so hakan,
Da wahala wannan Malamin ya iya sace Hanifa ba tare da ya samu shakuwa tsakaninsa da ita ba, mugayen mutane irin wannan suna kokarin jan yara a jikinsu kafin su kai ga cutar da su
Advertisements
Don haka iyaye mu dauki darasi, lokaci yayi da zamu dinga tsoratar da yaranmu ta hanyar jan kunnensu akan su dena yadda da kowa, ba yara ba har mu kanmu manya yanzu ba lokacin yadda da mutane bane, idan za’ayi zumunci ko abota to ayita daga nesa ba ma sai an hadu ba
Akwai addu’ah da Manzon Allah (SAW) Ya karantar wadanda ake neman tsarin Allah da su daga sharrin miyagun mutane da Aljanu, a dena wasa da addu’ah da ake tofawa yara idan gari ya waye zasu fita waje
Allah Ka karemu.
5 comments