
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 51
Moh’d ne daga can cikin wayar aka bata amsa.
Mamaki ne ya kamata tare da jinjina rashin kunyan Moh ɗin.
Cike da haushi tace inaji yaya aka yi?
Yanzun Umma take gaya min labarin da gaske ne wai?
Wani guntun murmushi Ammi tayi wadda bekai ciki ba sannan ta katse kiran tare da ganin rashin hankalin Moh’d, wato saboda Rashin kunya har yana iya ganin zai kirani yai min wani tambaya, toh murna yake ko bakin ciki Ammi ta tambayi kanta.
Washegari tunda suka tashi sallar asuba suka hau hira tsakanin Ammi da Yadikko, da kuma Unaisa, sakin jiki tayi sosai tana basu labarin irin rayuwar da tayi a baya, yayin da wani Yadikko tai murmushi wani kuma ta share hawayen tausayin Unaisa.
Hira sukaita yi gwanin ban sha’awa, yayin da Unaisa tai zaman durshen a kasa.
Misalin 7 na safe Modibo da Safna ne suka shigo, kujera daya suka zauna tunda Safna taima Unaisa kallo daya ta dauke kanta, ganin tsinin cikin jikinta yasa taji wani haushi cikin ranta yanzun wannan cikin Modibo ne?
Modibo ko bayan ya gaidar dasu Ammi Unaisa ya kalla yayin da itama ta mishi kallo daya ta dauke kanta tana fadin, Ina kwana?
Lafiya ya kike?
Lafiya lau ta fada a hankali.
Yayi kyau taji ya faɗa.
Muryan Safna taji tana ma yadikko murna cikin sakin fuska da fara’a yayin da Ammi ta amsa mata.
Bata wani jima ba tamike ta fita.
Ranar haka gidan yaita samun baki masu taya murna, misalin sha biyu tsohuwa yasmeen ta iso ita da tawagar ta.
Mata Uku ne beye da Ita dattijai sai kuma Samari guda biyu yayin da budurwar yariya ke biye dasu.
wannan karon Afalon Ammi aka zauna, Modibo ne yabi budurwar yariyar da tsohuwa Yasmen tazo da ita da kallo, tabbas sunyi kama sosai da Unaisa, kamar har ta ɓaci, saidai kamar ta fi Unaisa shekaru, ɗaga Murya Modibo yayi ya nuna yariyar yana fadin, Ammi kallah.
Gaba daya kallon inda Modibo ya nuna akayi, inda kowa ke fadin tsananin kamar dake tsakanin su da Rahma da yariyar.
Yasmeeen ce tace jika ta ce
Wani daga cikin Samarin ne ya kalli Unaisa yana fadin ina ‘yar uwar tamu kadai itace na gani kwanaki asabiti?
Ammi ce tace itace, cikin sauri Yasmeen ta isa kusa da Unaisa ta zauna tare da jawota jikin ta tana sumbatar ta cikin kwalla tare da share hawaye tana fadin, Muhammad yaji kunya, kuma Moh’d yayi asara, kara rungumar Unaisa take tana fadin, ” Allah yai miki Albarka kuma Allah ya sauke ki lafiya.
Sosai Unaisa ke jin son tsohuwar yana shigarta, yariyar ce ta taho ta rungume Unaisa adaidai lokacin da Ammi ke fadin, ” lallai Allah me hikima”
Magaji ne yace wlh sunyi kama sosai kuwa.
Wata taga cikin matan da sukazo tare tace ai jinin kenan, ai dole ne sai anga wata alama, aini da ace naga yariyar nan tuni dole zan gane jinin muce, duk yaran mu maza da mata su aje kafar su ku gani, yatsun su iri ɗaya ne, ku duba kafar su ku kalli Tata.
Ikon Allah kowa ke ta fada, Yasmeen ne ta fara gabatar da mutanen da tazo dasu ga Unaisa, bayan an tunana masu duk shedun da aka samu Unaisa dasu, mata Uku ta nunawa Unaisa tana fadin, wadɗa nan duk iyayen ki ne, sune kannen mahaifin ki, amman sun fishi hankali, maza biyu ta nuna sannan ta nuna mata ɗaya daga cikin mata da su ka zo tare tana fadin wanan itace mahaifiyar su, duk yayyen ki ne kizo kuyi zumunci ku karki biwa halin Ubanki , akwai ‘yan uwa da yawa suna can Sudan, karki saurara Moh’d sam bashi da zumunci.
Haka Yasmeen taita ma Unaisa bayani yawan dangin da take dasu, sai taji dadin yadda sukaita nan nan da ita.
Ganin suna kokarin tafiya Magaji ya matsa kusa da Modibo yana mashi kuskus, Sarai yake jin abun da yake cewa, amman sai yai shiru dan besan amsan da zai bashi ba, ganin Modibo yaki kulasa shi yasa ya daga murya yace Ammi ina da mgn.
Wanni irin kallo tamai sannan tace ina jinka.
Sunkuyar dakai yayi sannan yace, “Ammi ku neman min auren wacce yariyar, idan ba’a mata miji ba zan aure ta.
Kallo kallo aka shiga yi inda idon su ya sauka akan wannan yariyar me kama Unaisa.
Ammi ce tace yau na shige su , Magaji haka ake nema aure?
Dariya akayi gaba daya banda yariyar data sunkuyar da kanta kasa.
Tsohuwa Yasmeen ce tace Gara da ya faɗa, indai Fanan ce gata nan Allah ya daidaita ku, amman fa bazawara ce ta taɓa aure harda ‘yarta daya.
Duk falon mayar da hankalinsu sukayi gurin Magaji inda cikin sunkuyar dakai yace bakomai.
Balakin mamaki ne ya kama Modibo dan haka yaita kallon Magaji yana murmushi.
Itako yariyar gaba daya taji duk ta takura tunda taji zancen Magaji.
Suna kokarin tashi Moh’d na shigowa shida wani abokin shi, sosai yakejin kunya dan haka ya sunkuyar da kan shi, Abokin nashi ne yai gyaran murya sannan yace, da farko dai mu masu laifi ne, mun amsa laifin mu, sannan kuma munzo mu nemi yafiyar ku gaba ɗaya, Ni abokin Moh’d ne, bakocin sa ne kuma amini sa, be taba gaya min wata matsala tasa ba sai wasu watanNi da suka wuce bayan na fahimci yana cikin damuwa.
Yabani labari akan inda ya dauki jaririn yakaishi wani guri, duk da cewa bantaba tunanin akwai wadda zai iya aikata hakan ba amman na tausaya mishi, kuma naga wautan shi, tun farko dabe matsa da bincike ba, duk da haka na bashi shawaran yacigaba da bincike nima kuma zan taya shi, idan aka samu tsofaffin unguwa ana iya dacewa, cikin ikon Allah kuma jiya cikin dare ya kirani yace min ace anga yariyar na tambaye shi bakace namiji bane, sai yace min wai shima gaskiya be duba ba. toh wannan abun Allah ne ya aiko dashi dan haka mukazo mubaku hakuri.
Ammi ce tace wanni hakuri zai bamu yanzun kuma ai yabawa kanshi, mudai mun gode Allah munga yariyar, sauran ya rage nashi, yayi abinda zai yi in yaso, Modibo ta kalla sannan tace kabashi hoton Baffan ya duba.
Hannu Modibo yasa a aljihun jallabiyar cikin shi ya dauko ya mikawa Mohammed yana kallon hoton yana hawaye, tabbas shine mutumin, idon shi cike da hawaye ya mike yana kallon Unaisa sannan ya kalli Fanan yaga tsananin kamar da suka yi da yariya dake da tsohon ciki, kwalla ce ta sakkowa masa, Yana daga tsaye ya kalli Unaisa yace zonan ‘yata inji dumin jikin ki ko zan samu sassauci raɗaɗin da nake ji cikin zuciyata.
Wanni irin kallo Unaisa ta mishi sannan ta kawar da idon ta
Kizo dan Allah Moh’d ya sake faɗa yana kallon Unaisa da matsanciyar soyayyar ta azuciyar shi.
Mikewa Unaisa tayi ta koma bayan Yadikko ta zauna yayin da duk mutanen gurin suka bita da kallo.
Mohammed ne ya sake cewa, idan kinzo gurina ba yana nufin kin yafe min bane, dan Allah ki taimakeni kizo in ganki.
Tausayi sosai yabawa Modibo hakama Ammi dan haka Ammi tace Rahma bakiji ne.
Cikin sauri ta dauke kanta daga gurin Ammi dan haka Modibo yace, bakiji ne ana miki mgn?
kara kawar da kanta tayi can gefe nan danan hawaye ya fara zobo mata.
Taso kizo mana, Modibo ya sake faɗa.
Girgiza kai tayi dan haka Modibo yace, ki taso karki bari rai na ya bacci.
Suraj ne yace ka rabo da ita mana Modibo dole ne sai taje?
Afusace Modibo ya mike ya isa inda take ya kamo hannun ta ya isa da ita gaban Moh’d sanan ya dawo.
Sosai Moh’d ɗin ya rungume Rahma ajikin shi tare da sun batan ta yana fadin, ki yafe min dan Allah, karki bari in mutu da bakin ciki wannan abun dakai cin da na aikata, inajin kunyan ki ‘yata.
Bata iya cewa komiai ba, tanajin yadda yake fitar da hawaye bayan tsayon wani lakaci ya sake ta.
Gurin Yadikko ta koma tana me zunbura baki sabo da yadda Modibon ya bata haushi, haka Moh’d ya fita yana matsanancin kuka karkashin zuciyarsa da tarin nadama wadda besan ranar daina wa ba.
Bayan tafiya sa su Yasmen suka tafi bayan sunyi musayar no da su,
Misalin biyu na rana tawagar sarki suka iso domin taya farin ciki, kowa ka gani yana fara,’a afalon Abba aka sauki mai martaba, kwana biyu sukayi suka koma, hakama Dada kwanan ta uku kenan ta koma, bayan Su Ammin sun haɗa mata sha tara ta arziki.
Yau Yadikko zata koma gida, Suraj ne yazo daukan ta lokacin da suka fito harda Unaisa da Ammi, bayan Yadikko ta zauna a motar Unaisa tace, gobe zanzo.
Murmushi Yadikko tayi sannan ta lumshe ido tana fadin, ” me zakizo yi karki zo ke ko nauyin jikin ki bakyaji?
Toh ke yaushe zakizo?
Yar dariya Yadikko tayi sannan tace, duk lokacin da kikaji kina son ganina ki kirani awaya.
Zakizo?
Eh, sai insa Suraj ya kawo Ni.
Cikin sauri Suraj ya kalle su yana fadin, Mama kidaina min irin wannan.
Yar dariya Yadikko tayi, lokacin taji Suraj na fadin, ke wuce kiba mutane waje, mara kunya kawai, sai In tattakaki, yanzun ina da damar da zan miki duka wlh, ki shiga hankali ki, idan ba haka ba har gaban mijin ki zanzo in zane ki, idan yai min mgnr banza in haɗa dashi.
Cikin dariya Yadikko ta rike hannun Unaisa tare da faɗin, rabo dashi, wanne shi, haka yake masiffafe ne, muyi waya kinji.
kaita daga tare dama Suraj wani irin kallon ta wuce abun ta.
Ammi ce ta kalli Suraj tace, Me yasa kake mata haka? bakajin tausayin ta?
Mama gaskiya kina nuna fifiko, daman nasan za’ayi haka, kinfi sonta a kaina.
Ba haka bane Suraj, tausayinta nakeji, gara Kai, kasha nono na itako Bata shaba, Bata San daɗin uwaba sam, gashi tana shirin zama uwa, dan Allah ka rungume kanwarka, ka ganta ta, musa mata farin cikin data rasa a baya.
Kawar da kai yayi tare da fadin, nifa bata min mgn Mama, ko gaidani bata yi, sabo da kawai na kara aure, wai ita Sumayya take tayawa kishi, kuma Ni yanzun lafiya lau muke da Sumayya amman ita sam bata min mgn.
Dariya Yadikko tayi tare da fadin yanzun na ganu inda Rahma ta gado bakin kishin nan, haka Ubanta yake.
Dariya Suraj yayi sannan yace, ” toh Yadikko indai kina son muyi shiri ni da ita ki mata mgn barmin kallon raini, ta kuma bini sauda kafa, ayanzun na wuce kallon da take min na abokin mijin ta.
Cike da Murmushi Ammi tace kai zaka rike girman idan ka kama girman har Modibo sauya girmama ka.
Murmushi Suraj yayi tare da jin sanyi a ransa jin Yadikko tace har Modibo ma saya girmama shi.
Yau suka koma part dinsu ita da Modibo, duk da tana da tsohon ciki be hana Modibo nuna mata yadda yai rashin ta na kwana huɗu ba, sosai ya kula da inda walwala Rahma ya kararu.
Tundaga wannan lokacin Rahma ke samun kulawa daga dangi, kowa soyayya yake nuna mata sosai dangi suka kosa ta haihu.
Magaji kuwa babu wadda yasan yadda yayi yaje gidan Yasmeen saidai idan ya dawo ya kawo ma Unaisa leda inji kakarta sosai Modibo yake jin mamaki Magaji domin ayanzun bashi da zance saina aure.
Saboda yadda ya matsa su Abba sukaje masa neman auren Fanan batare da sanin kowa ba, saida suka gama tsaida magana sannan Abba ya sanarwar Ammi.
Fushi Ammi tayi sosai tare da korafin haka aka mata da auren Afnan ba’a neman shawara gurin ta sam.
Nan Abba ya shiga rarrashin ta tare da nuna mata wannan ba matsala bane tayi hakuri nan gama zava kiyaye.
Rigima Ammi tasa cewa ita bata son irin dangin su Moh’d Bata son ta hada iri dasu.
Dariya Abba yayi sosai sannan yace, ” yanzun kece kike fadin, haka” ai iri kun riga kun haɗa, tunda aka haifi Rahma, sannan ga Rahma nan zata haifar miki jika, wannan ba wani abu bane, matar Magaji Allah ya riga ya zaba masa, idan ya aurenta daman matar sa ce dan haka dan Allah kiyi hakuri.
Haka Ammi ta hakura badan ranta yaso ba wata biyu aka saka ranar auren Magaji da Fanan.
Ganin haka, Muftahu ma ya hanzarta tsayar da mata, cikin kankanin lokaci akayi komai aka gama
Safna kuwa wannan lokacin duk tayi baki ta rame ta lalace, rigima taketaba Modibo wai ita saiya saketa saidai duk yadda take mishi nacin ya saketa yaki yin hakan daga karshema yace idan ta sake masa mgnr saki sayya mata duka.
Dole ta daina mgnr, sa idai wasu abubuwa ratshin jin da ta tsiro dashi duk dan ta dinga bata masa, saidai ko kadan baya kallon komai da take yi domin yasan abun da take so, saki ne shi kuma bazai bata ba.
Yau kwana Uku kenan Unaisa naji ciwon mara, kullum sai sunje asibiti amman sai ace da sauran lokaci wannan ya fara saka Unaisa kuka domin cikin balakin nauyi yake mata har takan rasa inda zatayi dashi.
Sati Daya kenan tana ciwon amman har yanzun shi, waya Afnan tama Unaisa cewa gata a part din Ammi, farin ciki ne ya kamata tana sauke wayar ta kira Modibo.
Hamma Modibo”
Na’am Unaisss
Inje gurin Ammi?
kiyi me keda kikecewa baki da lafiya?
Zanje Afnan ce tazo fah.
Ok, kice zaku ku ishe ta da surutu?
A’a fa hira zamuyi.
Lumshe ido yayi badan ransa yaso ba yace Allah ya taimaka.
****
Tirtse tirtse da ciki sukayiwa Ammi adaki suna hira, Afnan ce tace wlh ban dauka zan dawo gidan nan baki haihu ba.
Nan danan Unaisa ta hade rai kamar zatai kuka tace, ” har na wuce inda aka saka min a asibiti, wlh duk nagaji, kilama an manta ne.
Ammi dake sauraron su a agefe ne dai dariya sannan tace, waye ya manta ki Allah?
Afnan ma dariya tayi yayi da Unaisa tai saurin tuba adaidai lokacin da Ammi ke saki faɗin zaki gayawa me garin ku ne.
Afnan kuwa dariya ta sakeyi sannan tace duk na kosa ki haihu sannan nima nasaka rai nifa sai watan gobe ma suka samin.
Irin hiran da sukaitayi kenan har yamma sannan Afnan ta tafi gida tams Rahma Dariyar yadda cikin duk ya sukurkutats.
Unaisa ce ta kalli Ammi tace Ammi kina ganin ta dai tana min dariya ko.
Rabu da ita itama nata ai zai tsufa kwantar da hankalin ki kyau rama.
Bayan tafiya Afnan gida Unaisa ta koma daker ta iya daura girki
*****
Misalin shabiyu na dare Unaisa kwance akan kirjin Modibo yayin da cikin ta yai kwance a tsakiyan su, wayarsa ce tai kara ganin Ammi ce yai saurin dauka, ji tayi yana fadin Masha Allah barka Allah ya raya.
Da sauri Unaisa ta tashi zaune tare da fadin, ” waye ya haihu?”
Cike da farin ciki yace, Afnan ce ta haifa ɗa namiji yanzun nan saura ke ko.
Kanbuuuu Unaisa ta faɗa tare da tsayawa tai shiru alamar ta shiga tunani, zuwa can tace, toh ne dai ko bazan haihu bane?
Kallo yabita dashi sannan yace zaki haihu mata.
Hawaye ta share sannan tace, Allah kuwa cikina ya riga na Afnan gashi harta haihu Ni ina nan.
Ganin inda ta fara hawaye Modibo yasa dariya, tun abun da bashi dariya har ya koma bashi haushi domin kuka Unaisa take sosai bana wasa ba, rarrashin ta yayi harya gaji gaba daya ta hanashi kwanciya daker yai mata wato yace ta kwanta da safe idan bata haihu ba zai kaita asibiti acire mata.
kwanciya tayi duk da haka Bata runtsa ba dan haka kukanta ya hanashi bacci.
Misalin bakwai na safe suka nufi part din Ammi tana ganin su tace, badai ganin jaririn zakuba da Sassafen nan.
Ammi wanni ganin jariri, ki kalle Rahma tunda bagaya mata Afnan ta haihu tasamin rigima wlh kuka ta kwana yi dagani har ita babu wadda ya runtsa.
Ikon Allah Ammi ta fada sannan ta dubi Rahma tace yanzun ina zaku?
Modibo ne yacewa Unaisa ana miki mgn.
Sunkuyar da kanta tayi tare da fadin ai kai take tambaya.
Dariya Ammi tayi yayin da Modibo yace toh ki zauna anan barin je inyi wanka in dawo.
Tunda Modibo ya fita be sake dawowa ba sai yamma, cewa yayi tai zamanta gurin Ammi domin gurin Safna yake, haka Ammi taita rarrashin Unaisa har akayi sunan Afnan bata haihu ba.
Bayan sunan Afnan da kwana biyu tashi da matsanancin ciwon mara, Modibo ya riga ya fita dan haka takira Ammi, Ammin ce tace tazo amman saitace bazata iya tafiya ba, wannan yasa Ammi tasowa da sauri tare da kiran Modibon awaya.
Magaji ne yakai su asibitin da Unaisa ke zuwa suna isa aka tabbatar masu da haihuwa ca, Bayan kusan awa daya da zuwan su Unaisa ta haifa kyawawan yaranta maza guda biyu koda Modibo da Suraj suka iso saidai suka samu daddaɗan labari.
****
Yaran ne duk biyu a hannun Yadikko hawaye ke zuba a idonta tana kallon yaran tare da tofa musu Addu’a, Modibo ma dake tsaye a gefe kallon yaran yake sannan ya kalli Unaisa cike da zallar farin ciki yana tuna yadda yayi ya fito da daga wannan gidan mekama da akurki.
Safna ko tana daga gefe saidai duk wadda ya kalleta yasan akwai damuwa a tattare da ita, sanyi tayi kalau duk rigimar da zata ma Modibo be kulata saidai idan ya gaji yace zai mata duka balakin tsoronsa takeji dan haka yanzun tai sanyi, saidai bataki ya saketa ba akida yaushe.
Ranar suna ta zagayo akayi suna nagani na fada yayin da aka hada mutane daban daban duk yan Kano sunzo suna mai martaba yayi farin ciki mara misaltuwa, mutanen Yobe duk sunxo suna tare da iyalan Yasmeen, Moh’d ma yazo ganin yaran sai dai bayan ina kwana da Rahma tace bata sake kallon inda yake ba.
Sai ranar sunan tasan cewa Modibo Suraj Magaji da Muftaho duk a kamfanin Da Maimatar ba ya bodewa Modibo suke aiki.
Ammi ce ke kula da Unaisa har tai arba’in sannan ta koma part dinta yaran duk sunyi Dumi Dumi gwanin ban shawa’a.
Bayan kwana ashirin da sunan akayi bikin Magaji da Muftahu sosai akai shagali har da Unaisa saidai acikin gidan kawai Modibo ya amince mata ta tsaya.
Yadda Modibo ke nuna soyayyar sa ga yaran yasa Safna ta sake data balaki saidai Modibo ya kara zare mata ido tare da nuna mata shi baya saki garama ta kwantar da hankalin ta.
Lokacin da Hassan da Hussaini suka cika wata Uku sannan Unaisa ta zaga dangi ba inda bataje ba sai gidan Moh’d, dan haka Modibo ya dubeta yace, yaushe zakije ki kai ma Baba Hassan da Hussaini ya gani?
Wanni Baban?
Babaki mana.
Baban ya rasu ai?
Hmmm Unaisss kenan ki shirya gobe zan kaiki gidan shi,
Ni bazani ba.
Dole kije Unaisss.
Dole fa kace?
Eh dole, indai na isa dake zakije, ko Allah muna masa laifi kuma mu nemi gafara ya yafe mana, mezaisa ke bazaki yafe mishi ba?, karki manta shine yai silar zuwan ki nan.
Ni bashi bane, idan kuma shine ya maidani ba’a so…
Wani irin kallo Modibo yai mata, wadda yasata hadiye ragowar mgnr dake bakin ta sannan yace, ” kina hauka ne, duk lalacewa naka dai naka ne, kuma daman hannun ka ya taba rubewa ka yanke ka zubur?, dan haka kiyi hakuri mahaifi ki ne, ya tabina Office kullum mgnr daya ce in baki hakuri, daman bai masa alkawin zan kawo ki, gobe zamu je dan Allah komai ya wuce.
Badan ranta yaso ba ta amsa saidan irin yadda take daraja Modibo batason ta tsallake mgnr sa.
Bayan shekara Goma.
Modibo ne danne da Unaisa yayin da take haki tare da fadin nabari wlh na bari…
Yadda ake buga kofar yasashi sakinta tare da fadin, yanzun haka Mamace…
Tunkan ya rufe baki sukaji muryan ta dakwai tana fadin, Daddy kaga Khalifa ya nausheni ko?
Kama kugu Modibo yayi tare da fadin, jeki gayawa Ummin ku.
Muryan cakwai ta sake cewa Daddy Ummee tace nice banda gaskiya fa.
Cikin fada yace, bazan yadda ba, Ammin tawa har ake cewa bata da gaskiya, rigarsa ya saka sannan ya bude kofar inda ya dauki kyakkyawar yariyar kamar Unaisa tayi kaki ta tofar ya daura a wuyan sa sannan ya nufi part din Safna.
Safna ce a tsakiyan Hassan da Hussaini yayin da Khalifa ke tsaye yana kara mgnr Tv Modibo ya shigo yana fadin waye yace Ammi na bata da gaskiya?
Yar dariya Safna tayi sannan tace, wlh wannan Ammin batayo halin ne sunan ba, duk ta damemu ta tsokani wancan ta tsokani wancen nina hana Hassan bugun ta.
Juyawa yayi ya kalli Hassan ɗin yace akan me?
Ahankali yace Daddy wuyana take hawa.
Haransa Modibo yayi tare da sauke Mamma daga wuyan shi yana fadin jeki hau wuyan Husaini daman Hassan ya faye masifa.
Juyawa yayi abinsa yayin da Safna ta bishi da kallo, yazun kam tacire rai da haihuwa dan haka ta rungume yaran da Safna ta haifa guda 4.
Modibo ko dakin ya koma ya rofe kofa tare da jawo Unaisa take kokarin guduwa, buga kofar aka sakeyi dan haka Modibo ya dan dakata yana tambayan waye.
Muryan Khalifa sukaji yana faɗin, Momy kinga dai Hassan ko?
Cike da faɗa Unaisa tace dukan ka yayi? kiramin shi.
Modibo ne yai saurin fadin, a’a Khalifa jeka gayawa Ammi…
Alhamdulillah anan na kawo karshen labarin BA LABARI, kuskuren da nayi aciki Allah ya yafe min, abun da na fada daidai Allah yasa ya amfanar, sai kun jini a sabon Littafina me suna DAGA DAJI
6 comments