WATA FITSARA
Advertisements
By
Fadeela Lamido
Page 12
Kana Ina yanzun?
Advertisements
Ina Kan hanyata ta zuwa gidan Hajjah”
Shikenan mu hadu acan din”
Dan danan ya isa gidan Hajjah har yanzun bebar huci ba, Hajjah na kallon shi tace Yaya akayi?
Advertisements
Zama yayi gefenta cikin tsananin bacin rai yace”
Hajjah, meyasa ne Wai Khadija ta tsaneni?
Meya faru?
Yanzun Hajja ke bakisan bata Sona ba?, Ta dade tana wulakantani”
Shiru Hajjah tayi zuwa can yace”
Yanzun dai meye ya faru?
Mun hadu da ita amakarantar su Fatima?, Bansan meta gayawa yariyar ba amman naga tanata Mata fada harda jah Mata kunne, sannan tabiyini ta gaya min abin da ranta keso, bayan na kaita gidan Baba ta sake haukace min tana jifana da kujera tare da zagi iri iri, Hajjah daker na iya daurewa…..
Gara daka Daure Yaro, karka biye mata, yanzun bada bane, ko itama din ai rashin hankali ne wannan, karka sake ma tanka Mata, aini atunanina dadi ya kamata taji da wannan al’amari dan Allah Ahmad kar inji ka kuma tanka mata har ace kana mayar Mata da mgn, nima din zan nemeta”
Sanyi yadanji cikin ransa, yayin da Galadima nazuwa suka shiga dakin Ahmad din”
Komai Ahmad yabawa Galadima lbr fiye da yadda ya gayawa Hajjah”
Dariya sosai Galadima yayi sannan yace”
Dole ta haukace Ahmad tafasan halinka kaff, tana ganin idon ka ya bude da yawa, tasan kalamin ka kace kana sonta kagama tsiyaya Mata rashin kunya kuma kace ‘yarta kake so, Wai!!! agaskiya ka goge mata Haddda narantse da Allah”
Murmushi Ahmad yayi sannan yace, kasan wani abu Galadima?
Saika fada”
Naji Dadi sosai danaga hankalin Khadija ya tashi fiye da tunanin ka, kuma naji wata ‘yar nutsuwa ta fara shigata, jiya danaje gurin Fatima kamar karna dawo, tunda nake bantaba mata kallo irin na wannce zan iya ma’amala irin na aure da itaba sai jiya, jiyane kadai namata irin wannan kallon kuma na hango wasu abubuwa acikin idon yariyar, ko ayanxun nafahimci Fatima tafi Khadija kwazo, kuma Fatima bazata iya furta min kiyayyaba kamar yadda Khadija ta nuna min’
Naji Dadi daka fahimci haka, daman ni banson ka da Khadija ba, akwai wasu abubuwa da zaka rasa idan ka aure Khadija, duk da cewa itama din ba baya bace, Amman zakafi more ma yar, Amman fah gaskiya naso agoge raini, wlh”
Murmushi Ahmad yayi bar wannan zancen Sani, kasan yazon dole nasawa bakina linzami, ta rufe ido Wai nama ‘yarta girma, Khadija na nufin ni babu tsarata?, Ita namata kankanta ‘yarta kuma na Mata girma, naso intambayeta wayakama yayi jarumta tsakanin Babba da Yaro, ninasan zan cikata tab har in wuce inda akajemata, amman tace namata Yaro, kawai dan muna dashekara daidai, kaga wannan wani ra’ayintane na daban, ita kanta tasan nafi karfinta wlh, kasan me yanzun, gani take kuma zan cutar Mata da yariya, Sani Dan Allah idan manya sunji tsoro basai subawa yara waje ba suyi kallo, ni nasan gani take kawai nafi karfinta’
Sosai kuwa, Ahmad toh yanzun Ina labarin Babanta kuma”
Gobe su Daddy zasuje, saidai Ina fargaban sa sosai, dole nasan zaice bazai bani ba, Amman abun da nakeso kawai ace yariyar nasona idan har ta yadda tokam nasan Babanta nasonta sosai”
Ajiyan zuciya Galadima yayi sannan yace”
Abokina akwai matsala fah, duba da yadda kukaita rigima dashi”
Hakane amman kasan me, tunda naga Fatima yau nasamu nutsuwa sosai azuciyata kuma inaji ajikina zan aureta”
Jimmm Sani yayi sannan yace Amman Khadija zata damu sosai”
Ita tasani Sani, idan har nace zanyi ne”
***********
Ashe baki da hankali Khadija?, Ahmad din kike wulakantawa har kina kokarin danbacewa dashi, Ina tunanin ki ya tafi dan Allah?
Inna ku bazaku gane bane, wlh da biyu yake wannan abun, duk fadan da kikaga munayi dashi cewa yayi yana Sona nikuma nace banson shi, yanzun haushin nace aure zanyi yasa shi tsiro da wannan zancen”
Koma dai mene kibar wannan zancen, ai be furta nakin ba na ‘yarki ya furta wannan abun kunya ne kike yi Khadija”
Inna ni kinsan abun dake dagamin hankali?, Wlh Inna Ahmad bashi da kunya ko kadan da kike ganin sa, mgnr rashin kunya ko wacce tazo bakinsa fadamin yake, mijin diyata ace nasan fitsararrsa, ya furta min Inna aiko kinga dole bazanso ba, Wai ba ance Daddy yayi masa Mata ba??
Babu ruwanki da wannan Khadija, Shi Mahaifin nasa da kansa yazo yai mgn dan haka naki ido, Ahmad da iyayen sa ba abun da basu miki ba, tun bakisan meye duniyaba suke kula dale haka shima Ahmad ya wahala akanki, inason daga yau karki Kara nuna baccin ranki akan zancen Auren nan”
Amman Inna ‘yar karamar yariyar za’a bari da katon namiji kamar Ahmad…..
Ke karki kawomin iskanci kinji ko, Ina ruwanki da fitsar sa yaran zamani yanzun wanne ba fitsarrene ba, wadda ma kike ganin sa kamar na kwarai bakisan me yake aikatawa ba aboye, shiko Ahmad tun yana karami dan gar da gar ne, yanzun intakaice miki mgn ki duba wayoyin yaran zamani kika badala ba fitsara ba, ni Ina ruwana da WATA FITSARAR sa indai bake yawa ba?🤔
Cikin sauri ta girgiza Kai tare da fadin A’a
Toh karna sakejin, babu ruwanki, Banga dalilin daga hankalin ki haka ba, wannan idan iyayen sa sukaji ai bazasuji Dadi ba”
Shikenan Inna mikewa tayi ta nufi dakinta, tunani ta shiga me zurfi komai baya Mata Dadi haka ta kwashe tsayon kwana uku duk tabi ta rame saboda tsabar damuwan datayi, afili tace nashiga uku, ni bawai sone banai Ahmad ya aure Samha bane ba, matsalar tayi karama shikuwa idonsa asoye yake kuma ya dade beyi aure ba, nadade da gane shidin jarabarbe bane, ace kuma wai Samha zai aura, ai akwai tashin hankali, zuwa daya zai Mata ta gamu da yoyon fitsari shikenan ya lalata Mata rayuwa”😭😭😭
Hawaye ta share tare da fadin, koda nasan Usman bazai taba vashi auren ‘yarsa ba toh meyasa ma zan damu, tsaki taja ta mike tanufi yin alwala bayan ta dawo ta tada sallah, damuwarce ta sake bijuro Mata dan haka ta koma ta zauna daker ta iyayin sallan duk inda taso ta kawar da tunanin ta kasa datayi shiru zancen ke fado Mata”
*********
Ranar data cika kwana biyar da faruwan wannan lamarin tana kwance tana aikin tunanin taji wayarta nakara, Alhaji Kabiru tagani dan haka taki dauka, tana kallo harya karaci kiransa yagaji ya bari, zuwa can ya sakejin Kira, kallon wayar tayi cikin harara, bakuwar number tagani kamar bazata daukaba sai kuma ta dauka”
Na’am, Samha kece?
Nice Umma, Ina wuni”
Lafiya lau wayarwa kika samu?, Ko yabaki waya ne?
A’a na auntyna ce”
Ummhimm toh sannu me Aunty yaya akayi lafiya ko”
Lafiya lau Umma”
Ya gida ya karatu kinayi sosai dai ko”
Inayi mana sosai ma”
Toh yayi kyau, yaso hajiya kina zuwa”
Muna zuwa Amman tare da Abbana kuma baya barina yanzun fah acan tare muke zuwa mukuma dawo tare kinsan me Umma”
Saikin fada min”
Abba cewa yayi wai dole yasamin ido tunda ya fahimci bakaratu bane agabana”
Yana da gaskiya ai Samha, keda kike ce masa amiki aure dole ki dinga bashi tsoro, kema ai shirme ne kike wanni zaman aure zaki iya??
Toh Mommy bashi bane yake cewa baya son boye boye indiga gaya mishi komai nake so”
Toh ke kuma dan yace miki haka saikice aure?, Kema nasan bakisan abin da kike cewa ba kina dai fadane kawai”
Hmmmm ni Umma shifa yake cewa in fada abun da yake raina”
Dum taji gabanta ya buga cikin rufe ido tace”
Yauzon dai kina gayamin gaskiyar abun dake ranki kika fada ko?
Shiru taji Samha tayi wayar ta ciro akunne ta kalla sannan ta maida tace”
Samha?
Na’am
Waike meyasa baki da kunya ne Samha?
Cikin kukan shagwaba tace Ina dashi fah,
A’a Ina kika ganta, ni bansan yadda akayi kika zama haka ba, kinaji na?
Eh”
Banason ki Kara bude baki kiyiwa Baban ki mgnr aure ba dabiar kwarai bace kinji ko?, Baki Kai wannan matakin ba inaga dai rashina kusa dake ne, yanzun koni na bude baki nace amin aure bare ke?, daya sani ya make bakin ki, yanzun meye kika kirani kina da wata mgn ce ko gaisuwa ne kawai”
Ni number din Uncle Ahmad Zaki bani”
Kiyi uban me dashi??
Cikin turo baki tace”
Kiransa zanyi fah?
Ya miki uwar me?”
Umma nifa mgnr mu kawai zamuyi”
Baki Khadija ta rike Samha mena gaya miki?
Shiru tayi dan haka Khadija tace”
Wai banace miki ko makarantar ku yazo karki fito ba?, Kinaji, Samha, ki daina kulasa ki fita harkansa babu ruwanki dashi indai kinason mu shirya dake kibar kulasa”
Cikin kuka tace sabodame Umma”
Au tambayanta kike yi?, Kinaji, munyi fada dashi zagina yayi, har yana neman dukana, komai kikaga yana miki neman hanyar wulakantani yakeyi Fatima, so yake yaga karshena, hawaye Khadija ta share sannan tacigaba da cewa”
Samha zuwa wajen ki da yakeyi da biyu yakeyi badan Allah bane so yake ya lalata miki rayuwa”
Sosai jikin Samha yai sanyi, wayarta ta kashe ta aje gebenta tare da tunanin uncle dinta meyasa zaiwa Momy haka”
Kuka taci sosai idonta sukai jawur Waini irin haushin uncle din taji ya kamata lallai uwa uwa ce akan me zai zagi Mamanta😭😭
*********
Daddy da Alhaji tare da Baba ne zaune agaban Alhaji Usman cikin mutunta juna suka gaisa sosai Usman yakejin kunyarsu yakasa dago idonsa ya kalle su rabon da suyi irin wannan zaman tun yana auren Khadija
…Dan haka sosai yau din yakejin nauyin su”
Alhaji ne yace”
Nasan zakayi Mamakin ganin mu agidan ka, toh wanannan ba wani abu bane duk da cewa Kun rabu da Khadija akwai ‘ya atsakanin ku, kafin incigaba da mgn akan abin da ya kawomu anan inason kasan cewa komai mukaddari ne daga Allah mekyau ko mara kyau”
Jinjina Kai Usman yayi tare da fadin”
Hakane”
Alhajine yacigaba da cewa”
Yauwa naji Dadi daka fahimci haka, kamar yaune mahaifinka ya zauna kamar haka lokacin da yazo da mgnr neman auren ka, saigashi yau Nima nazo da tawa bukatar awajen ka, wakr haka Banda Allah”
Sosai Alhaji Usman ya baza kunnuwa yana son yaji me suke shirin fadi acikin wannan babbar tafiya me mahimmanci wadda akayi ta harda Babban mutum kamar Daddy🤔
Mgn ce take tafe damu muhimmiya, akan ‘yar wajen ka Fatima”
Cikin sauri Usman ya dago ya kallesu sannan yace”
Wani abu ne Baba??
A’a wani danmune yake son auren ta, nan daka ganmu izini mukazo Nima”
Dariya Alhaji Usman yayi yayin da yabawa dukkan su Alhajin dariya kowa ya dara sannan yace”
Wai Nima auren Ummee kenan kukazo?🤣
Suma cikin dariya suka hada baki wajen fadin”
Dan mu keso, Dan haka mukace bazamuyi kasa aguiwa ba”
Sunkuyar dakai Usman yayi zuwa can ya dago cikin dariya yace”
Yanzun dai Baba duk bakwa kishi kenan
Dariya aka sake yi gaba daya falon sannan Alhaji Usman ya sunkuyar dakai yace”
toh Alhamdulillah, wannan ba wani abu bane matsalar kawai Ummee karamar yariya ce sosai, wadda in ason zuciyata ne bazanso naimata aure a waannan matakin nataba”
Munyi wannan tunanin daman, shi yaron ba kosawa yayiba zai iya Dan dakatawa kadan ya jirata, idan kuma kabamu yanzun duk muna so, munyaba hankalin yaron zai kulla da ita yadda ya kamata, kuma Dan zamani ne inada tabbacin karatu sai inda tace ya isheta haka, bukatar mu kawai ka amsa kamu dama”
Sunkuyar da kansa yayi sosai yace”
Naji dadin wannan yabon da kuka ma yaron, kuma tunda naganku anan nasan mutuncine agabana, tunda nasan ku, nasan daga irin wani gida kuka fito, kuma da ba’a badawa nima da baku bani ba, amman ni kai tsaye bazamce nabadata ba saidai nace yazo ya nemi so gurin yariyar, idan tana son shi ni abun da take so shi zan Mata”
Toh Alhamdulillah ai ko hakan ma kamar Ka bamu ne, insha Allahu zasu daidaita ma mungude da wannan karancin”
Bakomai Usman ya fada sannan yace”
Toh yaron Dan wani gida ne?
Baba ne ya nuna Daddy yace Dan wajen Alhaji”
Masha Allah Usman ya fada sannan yace to ya sunan sa?
Daddy ne yayi karaf yace Moh’d, zan bashi number ka zai kiraka ku gaisa baya gari ne “
Da haka suka tashi kowa fuskanshi dauke da murmushi, Fatima aka turo ta gaisa da kakanninta bayan sun tafi Alhaji Usman ya wuce da Fatima falon sa inda suka samu Aunty zaune tana kallo”
Bakin sun tafi Alhaji?
Sun tafi, yafada yana kokarin zama bayan ya zauna ya jawo Fatima jikin sa yace”
Ummee an girma kinga su Baba Wai neman auren ki sukazo🤔
Aurena Abba dawa??
Idonta ya kalla yace”
Wai sunzo nimarwa Dan gidan Daddy izzinin neman auren ki kinsan wani Moh’d??
Cikin turo baki tace”
Ni ban sanshi ba, toh me kace musu???
Hancinta ya kama yace”
Nace yanemi so wajen ki?
Abba ni banson shi wlh”
A’a kul kibari mana ki ganshi, idan be miki ba ai shikenan ni bazan miki auren dole ba”
Karyar dakai tayi cikin baccin rai, tare da share kwallah, Yi yayi kamar be ganta va zuwa can yawaigo ya sake kallonta yace”
Kina min kuka ne?, Nifa wannan ba ra’ayina bane ra’ayin kine, inda Banga take taken kiba ke bakima gama zama mutum ba”
Toh Abba ai cewa kayi saina zaba kum😩……
Dakatar da ita yayi domin yasan halin ta yanzun ta yanko masa wani zancen Dan haka yai saurin cewa”
Ko yanzun zaban zakiyi, wuce kibani guri”
Jin tsoron karya taso da fadansa yasata saurin komawa daki yayin da anty ke tambayan sa yanzun Kai aure zaka Mat
Wani irin kallo yai Mata sanan yace wannan ba matsalar ki vace, idan Ina mgn da ‘yata kibar samin baki”
********
Washegari da Daddare Daddy yavawa Ahmad no Alhaji Usman, tare da gaya masu yadda akayi”
Dakinsa ya koma yana tunanin yadda zaiyi ya Kira Alhaji Usman, karon farko dayaji gabansa na faduwa Dan zaiwa Alhaji Usman mgn, daker ya iya cijewa ya Kira”
Kasa kasa Ahmad yayi da murya, cikin girmamawa ya gaida sa Dan shiru ya biyo baya daga can Ahmad yace”
Abba Moh’d ne
Toh madallah Moh’d ya gida”
Lfy lau”
Yayi kyau, ai daman ance min zaka Kira, shekaran ka nawa ne??
Jimmm Ahmad yayi Dan be tsammaci wannan tambayar ba, shekaruna 30 Abba”
😬😬 Wai Ashe babba ne, kana da aure ne?
A’a tukuna”
Toh🤗 toh yayi, karatu fa koda ance baka gari ko?
Eh Ina wajen aiki”
Toh yayi kyau, wani irin aiki ne kake yi”
Likitane ni Abba”
Masha Allah to badamuwa Allah yai mana zabin alheri kaji ko”
Ameen ya fada, sannan ya sake cewa Allah kuma ya daidaita ku”
Cikin daga murya Ahmad yace Ameen ameen Abba nagode”
Jim suka dan sakeyi sannan Ahmad yace”
Abba tayi bacci ne?
Murmushi Usman yayi sannan yace Ina zuwa zan nuro maka numbarta yanzun nan”
Godiya yayi sannan ya kashe wayar, tashi”
Alhaji Usman na sauke wayar yace”
Kajimin Yaro Wai ameen ko kunyata bayaji, shima dai inaga irin Mamana ne zanso naganshi, sosai nake son naga mijin Ummee domin akwai wasu abubuwa da nake hangowa cikin idonta”
Ahmad zaune akan gadon sa, ya cire rigarsa yana sauke ajiyan zuciya”
Wai yau shine yake kiran Usman da Abba, tuna Khadija yayi cikin sauri ya kawar da tunanin ta”
Sosai yaji nutsuwa tana shigarsa yadda ya dace sannan ya fara shafa gashin dake kwance agirjinsa yana me lumshe ido, cikin su wacce tafi sani nishadi idan natunuta?🤔 Cikin sauri ya kawar da tunanin”
Shigowan Number yasashi bude ido ya kalla shidai yasan Fatima bata da waya, bebata lokaci ba wajen Kira, saida ta kusan katsewa ta dauka, cikin sallama”
Shiru yayi yana sauraron sautin ta tare da cigaba da shafa gashin kirjinsa, shikadai yasan wani irin nishadi yake ji”
Kasa amsa gaisuwar yayi daker ya iya amsawa, tare da tambayan ta karatu”
Yadda take mgn daker abun ya bashi Mamaki har wani dankwasa murya take”
Sosai sallon da take amfani dashi yafara saka Ahmad shiga wani irin shauki wadda beyi tunanin zai nunasa yanzun akanta ba, shima canza salon muryarsa yayi batare daya sani ba”
Lumshe ido Fatima keyi tare da sauraron muryansa”
Fatima yanaji kinyi shiru?, Fatima Ina mgn kinyi shiru?
Ina jinka”
Shafa kirjin sa ya sake yi sannan yace”
Nace kibani lokacin dazan sameki agida”
Nidai basai kazo ba”
Bangane basai nazo ba, me kike nufi?
Nifa Ina da irin wadda zan aura bawai kowa ba”
Jimmm Ahmad yayi sannan yace”
Aishine nace kibani dama muga juna ko?, kinga Nina sanke, ke kuma baki sanni ba”
Cikin muryar dake Kara rikita Ahmad tace”
Ni bandamu da in gankaba muyi waya kawai, wayar ma kasan meyasa zan bari muyi???
Cikin Mamaki sosai yace”
A’a sai kin fada”
Saboda muryan ka tayi shigen ta Uncle dina”
Lumshe ido Ahmad yayi tare da fadin”
Dan Allah?
Toh kibani dama mana inzo ki ganni, Nima”
Nidai a’a muyi waya kawai”
Ahaka za’ayi auren?, Shikenan toh bani labari”
Jimmm tayi zuwa can tace”
Toh ni wani lbr zan baka?, In baka lbrn Uncle dina?
Dariya sosai Ahmad yayi sannan yace, ton Ina Jin ki……..
3 comments