
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 17
Kuka Samha tacigaba da rairawa Khadija cikin waya yayin da Khadija tai shiru tana sauraronta zuwa can tace”
Yanzun meye amfanin wannan kukan da kike?, Bashi da amfani Samha ninafi bukatar kiyi wayau ba kuka ba, kisan inda yake miki ciwo duk yadda Abban ki zaiyi dake karki yadda da auren amman kiran Ahmad ba mafita bane, ya iya shirya makirci kala kala”
Koda Khadija tagama waya da Samha itama jinta tayi kamar tace wayyo Allah, irin son da Usman yakewa Samha batajin zai iya Mata irin wannan auren dan haka tadan saki ranta, zuwa can kuma damuwa ya sake bijiro Mata, fuskan Usman ce tafi Bata tsoro duba da irin kalaman da da alama fah da gaske yake yi”
Ranaku nata tahowa har ya rage saura kwana biyu, Samha duk ta rame ta fita hayyacin ta, sosai Momy ta bada hankalin ta gurinta duk wani rawan Kai yanzun babu shi saidai ta zauna cikin tunani, tuni kallon da takewa Ahmad ya goge azuciyarta yayin da kalmar yana son Mamanta yafi komai tsaya nata arai, be tsaya anan ba harda karin wasu kalamai wadda batasan ko meye su ba”
Yatsanta tacija tare da fadin, insha Allahu auren bazai taba yiyuwa ba, taya zai ce yana son Mamana kuma ya dawo yace ni, Ashe daman Uncle dan iskane amman yake Yi kamar mutumin kirki, har fada yake min ashe munafuki ne me fuska biyu, inba iskanciba taya zaiso uwata kuma ya soni kuma yana Dan uwanta nikuma yana Uncle dina?😭😭, Koke koke taitayi yayin da tagaji zaman tai lamo bisa gadon Momy”
Momy kuwa shirye shirye taitayi duk da cewa jikinta asanyaye yake kuma itama bata goyon bayan ama Samha aure awannan lokacin saidai kuma tundataga Usman ya dage ta hakura domin kuwa me daki shiyasan inda yake masa yoyo”
Itama bangaren Khadija tana cikin damuwa sosai duk da cewa Ahmad yabar zuwa gidan amman shirye shirye su Inna keyi gida duk ya dauka gobe auren Ahmad”
Inna Yalwa ce ta kirata bayan sun nutsu tace”
Toh Khadija gobe daurin aure banga kina wani shiri ba?🤔
Allah ya kaimu Inna ni Shirin me zanyi??
A’a inace Zaki dan saya wani abu kikai duk da Ubanta nadashi Amman zaiji dadi kuma ita ‘yar ai dadi zataji”
Inna munfayi mgn dashi yace karna wahalar da kaina yagama komai”
Toh Masha Allah, amman bazaki gayyato kawayen ki ba?
Ni bani ba kawaye gareni ba Inna Safeena ce kuma Bata gari”
Toh ai shikenan Allah ya kyauta Inna ta fada sannan ta dauki tsintsiya tahau shara”
*********
Ahmad da Galadima zaune falon Hajjah yayin da Hajjah ke fadin”
Inason Inga Yaro yayi aure shima yaji dadin rayuwarsa, wani lokacin sainaga kamar bazanga auren nasaba duba da inda yai girma babu aure, idan naso na matsa masa yayi auren
Babansa cewa yake, kar amatsa masa aure lokaci ne, intaice maka Sani harshi kanshi yagaji ya nemo yariyar Amman Yaro yaki, ni bantaba tunanin akwai abun da zaisa Ahmad shiga damuwa irin na wannan lokacin ba, bafa ya wani baccin kirki daya kwanta zai tashi ya zauna”
Kallonsa Galadima yayi sannan yace ai gashinan duk ya rame Hajjah, kuma nasan Khadija ce take zuge mana Mata”
Baki Hajjah takama sannan tace Wai har yanzun Khadija kuke kiranta??🤔
Juyawa tayi ta kalli Ahmad sannan tace kai Ahmad kaima Khadija kake kiranta???
Cikin kawar dakai yace a’a”
Me kake ce Mata toh?
Ni nabar Kiran sunanta ne gaba daya hajjah”
Hmmm, dole zaka Kira sunanta Ahmad garama ka shirya tun wuri”
Cukin kawar dakai yace dan Allah Hajjah ki bari, sunanta Khadija azuciyata afili kuma zamyi shiru kawai”
Babu ma abun dazaiyyi dalilin hakan”
Murmushi kawai Hajjah tayi”
Babu wani shiri me karfe da akeyi, domin Ahmad jikinsa sanyaye yake, Galadima ne kawai yasan me ake ciki, aranar Aunty Saude da wasu daga cikin ‘yan gidan su Khadija sukakai Laifen Fatima gidan Momy”
Wannan kawo kaya shiya Kara gigita Samha, tana kwance cikin dakin tanaji ana koda kayan, tare da tunanin ta shiga gidan manyan mutane bisaga lakari da tsadar kayan da suka zobo, daga can cikin falon taji yayar Abbanta nafadin”
Harna matso naga sirikin nawa, da alama sosai yake son ‘yata”
Tsaki Samha taja wadda duk wadda ke falon Saida ya waiga, dakin Mama Aisha ta kalla ko tantama baitai Samha ce, juyawa tayi ta sake kallon jama’ar tace”
Da banso amata aure yanzun, amman ganin kayan nan raina yayi fari fess, Hira suke cikin raha yayin da suke ta darrar raku amman sai jiyo tsakin Samha take”
Mikewa tayi ta nufi dakin, Samha na zaune bakin gado sai ajiyan zuciya take sauke wa”
Zama tayi tana kallon cikin idon Samha tace”
Samha mu kikewa tsaki?🤔
Kaita girgiza alamar a’a
Mune mana, ai bakiyi da saida kika fara Jin hirar mu, wato haka zakije ki dingawa mijin tsaki🤔
Hawaye ne suka zobo mata, cikin kawar dakai tace ni bansan lokacin da nayi ba”
Eh ai bazaki sani ba tunda kinajin rigima”
Karyar dakai tayi, sannan tace”
Mama ni kiyiwa Abbana mgn banson shi fah😩
Jimmm tayi tana kallon ta sannan tace”
Samha bakin alkalami ya bushe, kinganni nan tunda Mommy ta Gaya min zai miki aure kince bakiso Amman shiya dage, shiru nayi Ina nazari domin nasan ko giyan wake yasha bazai miki auren dole ba, haka na nufi gidan sa, bayanin da yayi min kece baki da gaskiya, domin yace min kedin nan kin fada masa da bakin ki kinason shi”
.Rana daya kika dawo kikace mishi wai kinfasa, sannan yagaya min wata mgn dayasa ni nai tsam da daraina, yace tuni kike cewa ya miki aure??
Hawaye ta share sanan tace ni Mama Wasa nakeyi, fada kawai nake yi😭😭
Toh shi be dauka Wasa ba, yace tsoro kike bashi, sannan shi wannan da kikace kina so din yanzun din ma yace baki da watahujjah ko dalili, a tunanin sa zugaki ake yi?
Ni ba wadda yake zugani Allah Mama😩
Toh shikenan naji yanzun share hawayen ki muyi mgn, banson kuka”
Cikin sauri ta shiga share hawayen yayin da Mama Aisha ta karasa share mata wasu sannan tace”
Inajin ki meyasa baki son sa??
Hannun Mama takama sannan tace”
Mm Karki gayawa Abba👏🏻
Eh, nayadda ko zan fada Saida yaddan ki ai, mafita ake nema ko, Ina jinki”
Sunkuyar dakai tayi tace”
Mamana yakewa rashin kunya”
Mamana ki??, Inace Kaninta ne??
Eh Dan uwanta ne”
Jimmm, Mama tayi sannan tace toh Banda abun ki Samha Ina ruwanki?, Ina dan uwantane?, ai irin wannan rigimar na zumunci ba’a shiga zasu shirya ai”
Cikin kuka tace Allah Mama bazasu shirya ba”
A’a Samha wannan ma ba hujja bane, kinga akwai abun da Abban ki yasani shiyasa yake cewa anzigaki, ki kwantar da hankalin ki, ki nutsu, karki bari Abban ki Yaji sunan Khadija akan wannan mgnr”
Rashin mutunci fa yake mata Mama😩😭
Yanzun ai bazai Mata ba Samha, ko banza ta haifa ya aura, yanxun haka tsohon zance ne aka rike, koma dai menene, Allah ma muna saba masa, kuma mu rokeshi ya yafe mana, bare dan Adam, zamanin nan nayanzun waye me kunya Samha?, Duk rashin kunyan shi bana tunanin yakai ki”
Cikin kuka tace”
Mama Allah kuwan bana son shi, ni kallon Babana nake mishi wlh, ba wani miji ba, ni Mama dan Allah abar mgnr auren nan, dan ko anyi shida kanshi zaiji wuya zai maidoni gidan Abbana”
Wata irin dariya Mama tayi wadda batakai ciki ba sannan tace”
Da alama dai so kike sai anyi rigima dake sosai, toke guda nawa kike dahar kike cewa yaji wuya?, Kuma da kike cewa Baban ki ne kicema kakanki ne dole dai kizauna dashi, au kenan gani kike Wai wuyan ki ya isa yanka🤔? Wannan muka barki kika dade agida bansan abun da Zaki zama ba🤔, mikewa Mama Aisha tayi ta fice tana fadin”
Momy ai bakiyi kallo ba, Samha sai munyi da gaske zata zauna agidan miji”
Jin haka ta sake dasa sabon kuka, zuwa can ta share hawayen ta tare da fadin”
Shikuma d’an menacin jira yake daura akai masa ni, ya koma gefe yai mukus shinan tantiri, wlh yaji tsoron haduwan sa Dani, wata zuciyar ce tace me zaki masa?, Mikewa tayi tana fadi Oho😏
Khadija kuwa yau bata iya mgn, yayin da dayawa daga cikin mutanan gidan suka tafi gidan Hajjah”
Ganin abubuwan nata kankama tafara tunanin kodai marfaki take yi ne?, Wai Ahmad ne zai auri Samha🤔
Daddare kasa bacci tayi, ji tayi ada ba damuwa tayi ba, yanzun ne take cikin damuwa”
Hakama Fatima daren kasa bacci tayi hawaye yaki daina zuba, Abban kawai take tunawa meyasa yanzun yabar jin tausayin ta😭😭
Alhaji Usma zaune dakin sa ya daura kafa daya Kan daya yana girgizawa, mutum biyu ne acikin zuciyarsa wadda daya bangaren ke tausayin Samha sosai, saidai yana hangota nan gaba tana dariya, damuwa yayi sosai, harya tsinta kansa da Jan tsaki, Karan wayarsa yaji yana kallo yaga sunan Samha ne”
Cikin sauri ya dauki wayar tare da yin shiru”
Abba??
Na’am Umme bakiyi bacci ba?
Nakasa bacci Abba dan Allah kayi hakuri”👏🏻😭
Jimmm yayi sannan yace, Nima nakasa bacci mamana, kiyi hakuri ki kwanta”
Abba dan Allah kar ayi gobe👏🏻😔
Ummee kiyi hakuri nace, wata rana zakiyiwa kanki dariya fah🤔
Wlh Abba bazanyi ba, indai aka daura auren mutuwa zanyi, Abba zaka rasani”
Jimmm yayi, sannan yace duk wadda ya mutu kwanan sane ya kare, kiyi hakuri kima mijinki biyayya”
Cikin toshe baki tace, Abba bashi bane mijina dan Allah kayi hakuri….
Katse Kiran yayi tare da kashe wayarsa baki daya, hannun yasa ya cire hawayen agefen idonsa tare da ajiyan zuciya”
Washegari tun asuba Khadija ta kasa barin Kan Sallayanta addu’a take kada Allah ta tabbatar da auren”
Misalin daya na rana dubban mutane suka shaida daurin auren Ahmad da Fatima wadda aka daura Abban masallacin juma’a”
Kowa kagani yana fara’a Amman Banda Alhaji Usman da Ahmad, fuskan su babu walwala sosai, yake kawai sukeyi”
Labarin na samun Khadija ta rufe dakinta, itako Samha idonta bushewa yayi”
Babu wani shagalin biki da akayi, acewar Ahmad da Hajja saidaga baya za’ayi”
Gidan Momy kuwa babu wani armashi domin zuwa yanzun duk dangi sunsan Samha Bata so auren”
Karfe 8 na dare Abba ya shigo gidan fatan alheri akaita masa yayin da ya zauna yacewa Momy”
Ashirya min Fatima dakaina zan kaita gidanta”
Toh Amman baka bari ‘yan uwa su rakata ?
Momy inace ‘yan uwa suka mata jere, wadda bejeba daga baya yaje ya gani, nidai yanzun ashirya min ita in dankawa Mijinta…..
Mmn Yazeed
7 comments