
WATA FITSARA
By
Fadeela Lamido
Page 25
Dagowa tayi ta kallesa, sai yanzun ta tuna kalmarsa ta jiya”
Wani irin taji cikin ranta domin tasan Fushin Abbanta babu kyau, tunawa tayi da cewan da tayi batason auren Uncle ta fasa shine dalilin yasa Abbanta ya dauke ta daga gidan ya maidata gidan Mommy tun ranar Bata sake takowa gidan Abbanta va sai kuwa yau”
Cikin kwalkwal da ido takalleshi sannan ta nufi hannunsa takama bayan ya sakko cikin motar”
Uncle kayi hakuri dan Allah karka hadani da Babana”
Zame hannunsa yayi tare da nufan cikin gidan”
Tsayawa tayi tana kallonsa, can baya ya nufa hanyar da zata sadashi falon Abbanta Kai tsaye da alama sunyi waya😔
Zagayawa tayi tabi bayansa yayin data shiga har sun gama gaisawa da Abbanta yana zaune kansa akasa”
Tsaye tayi abakin kofar idonta cike da hawaye tana wasa da yatsunta”
Kallo Alhaji Usman yabita dashi sannan yai murmushi yace”
Mamana baki da gaskiya zo karaso”
Kasa daga kafa tayi illa Satan kallon sa da take”
Ahankali ya sake cewa Mamana zo mana bakya daukin ganina??
Hawaye ne suka zubo Mata ganin haka Alhaji Usman ya mike ya kamo hannunta sannan ya dawo ya zaunar da ita kusa dashi yace”
Nayi kewan ki da yawa Unmeen gashi kinxo kina dardar dani”
Kallon Ahmad tayi ta sunkuyar dakai toh ai Abba shine yace zai kawo maka Kara ta”
Kinyi wani abu kenan ko??
Kaita girgiza tare da fadin A’a”
Kinyi mana, tunda gashi alamu sun nuna baki da gaskiya”
Shiru tayi dan haka Usman ya dago ya kalli Ahmad yace”
Ahmad me yake faruwa ne??
Gyaran Murya yayi sannan yace”
Daman nakawota ne adan jamata kunne, tanayin wasu abubuwa wadda banajin dadin sa”
Dagowa yayi ya kalli Ahmad sannan yace bangane ba Ahmad??
Eh Ina nufin tana nuna batasan nauyin da yake kantaba ayanzun, nasan karamar yariya ce Amman yakamata ace tasan akwai hakkina akanta ayanzun ko dan yaya ne, nasan dole inyi hakuri dawasu abubuwa amman ita abun nata narasa gane kanshi, ranar nan cemin tayi idan zata iya kasancewa dani toh zata iya kasancewa da Ab……
Hannu Usman ya daga masa tare da runtse idonsa, dole Ahmad yai shiru, zuwa can ya dago kansa yace”
Mamana wannan kuma WATA FITSARA ce Haka??, mijin ki kike gayawa irin wannan mgnr da bata da dadin ji Sam”
Hannu tasa ta share hawaye”
Hannunsa yasa ya fara share mata hawayen yana fadin”
Dan Allah kidawo da hankalin ki jikin ki Mamana, Ahmad ayanzun mijin kine, shyafi cancanta ki gayawa kalami masu dadi, sannan kiyi mishi biyya, idan irin haka nafaru tsakanin ku hankalina bazai kwanta ba, na yadda nabashi kene dan Ina tunanin zakiji dadi, me zaisa kiki kwantar da hankalin ki?
Abba bazanji dadi ba indai dashi ne wlh, bana son shi jiya ma duka na yayi”
Cikin sauri Usman ya kalli Ahmad irin kallon tuhuma”
Kawar dakai Ahmad yayi sannan yace”
Bansan lokacin da nayi haka ba raina ne ya baci, nabarta amota nashiga Office kafin na fito batanan tafita tayi tafiyanta, lokacin dana fito nata nemanta har dare Ashe takoma gida wannan abu ne ya tunzura ni”
Ajiyan zuciya Usman yayi sannan ya juya yace”
Karki sake yin haka kinji ko idan kin sake nima zan taya shi dukan ki, sannan karki yadda ya sake kawo min karanki, idan ya sake kawo min karanki abun bazai mana kyau ba”
Hawaye ta share sannan tace Abban ni bana son shi……
Runtse Ido Ahmad yayi Kona barta anan zuwa wani lokacin?
A’a, karka barta kayi hakuri, kuruciya ce take damun ta, juyawa yayi ya kalli Samha yace kije ki tsuguna kibashi hakuri”
Cikin kuka sosai ta mike tsunawa tayi kamar yadda Abbanta yace tace kayi hakuri”
**********
Tunkafin su fito gidan idon Samha ya bushe kamar ba itace take kuka ba”
Shi kansa Ahmad gani yake kamar ba Fatimar da bace, wani irin rashin kunya yake gani cikin kayar idonta
Daure fuskansa yayi sosai domin yana ganin dolenta ta dawo cikin hankalin ta”
Nisa suka yi da alama gidan Hajjah zai maidata ahankali tace”
Kadan kaini Inga Mamana”
Mamanki??, Tsaki yaja idan kinason inbarki kiga Mamanki cikin hankalin ki, niba sa’anki bane Amman kina min abun da kika dama, sabo da kin raina ni yanzun baki ganin darajata kika gayawa Abbanki na dake ki ko??
Ai Kaine kafara kaini Kara, dan Allah ka kaini”
Wlh ba inda zan kaiki, kuma tunda kin rainani zan dauki mataki, niba karamin yaro bane dazaki dinga min abin da kikaga dama”
Nidai ka kaini gidan Baba dan Inga Mamana dan Allah”
Babu inda zaki sai kin dawo hankalin ki, da anyi mgn kice wani Mamanki Maman ki, yanzun ke matar aure ce kina karkashin ikonane ko kinki ko kinso, yanzun idan nace zan matsa miki sai aga rashin hakuri na, Amman inason ki sani aurena dake kanki yana nan daram duk ma abun da zakiyi ki kula da wannan”
Kuka Samha ta fara domin balakin so take taga Mamanta cikin turo baki tace ni idan bazaka ba ka saukeni intafi”
Sosai ran Ahmad yabaci tsayawa yayi cak yace sauka”
Sauka tayi ta fara tafiya waigawa yayi yaga ta aje Jakarta, cikin tsananin fushi ya sauko ya zagaya ya bude barayin data sauka ya finciko jakar makarantar ya wurga mata”
Timm taji ta daki kafarta ta fadi kasa, wani mutumine dake tafe agurin ya tsaya ya kalli Samha sannan yajuya yaga inda Ahmad ke huci yana kokarin komawa cikin mota yace Kai Yaro dakata”
Zama Ahmad yayi cikin motar yana kallon mutumin dake daukowa Samha Jakarta akasa yace ya mika mata tare da fadin”
Wanene wancen??
Cikin kifta ido tace uncle dina ne”
Korin tashin motar Ahmad keyi yayin da mutumin ya sake dakatar dashi akaro na biyu”
Meyesa ya sauke ki anan?
Nace zani gurin Mamana ne shi yace a’a”
Kallonta yayi dakyau sannan yace toh muje”
Batai musuba ta biyoshi yayin da yake ce mata mijin ki ne?, Ko an muku aure ne?
Girgiza kanta tayi tare da fadin A’a”
Hakan yayi daidai da karasowar su gurin motar Ahmad, kallon sa mutumin yayi yace”
Haba yaro ya zaka saukita akan hanya….
Ita ta zabi haka Baba”
Hucin da tsohon ya kula Ahmad nayi yasashi fadin”
Aiba biye Mata zakayi ba yaro tace gurin Mamanta zata”
Shine aina ajeta taje tun da abun da take so kenan”
A’a baza’ayi hakaba yaro kayi hakuri, ke mijin ki ne ko??
Tsare Samha yayi da ido yayin data sunkuyar dakai, tsuhon ne yace”
Karki karayin haka kinji ko? Yanzun akarkashin ikon sa kike idan kika bishi ahankali wata rana zai kaiki da kanshi”
Kallon Ahmad yayi yace Yaro kayi hakuri kaji”
Baba daka barta taje tun da Bata da hankali”
A’a bazayi haka ba kayi hakuri, zaga kishiga motar ku tafi”
Tsohon dakansa ya bude Mata kofar sannan ya bata Jakarta”
Godiya Ahmad yama tsohon sannan yaja motar batare daya kalli inda Samha take ba”
Haka suka isa gida kuka kawai Samha keyi yayin da Ahmad yaki kallon inda take, suna isa gidan Hajjah ya fice yabarta amotar”
Sakkowa tayi itama ta nufi gidan tana me share gutun hawayenta”
**********
Misalin misalin 5:00pm Ahmad ya fito yayi wanka ya canza kaya, hannun sa takardune birjik tare da wayoyin sa da laptop”
Hajjah ce ta kalleshi tace Ina zuwa haka??
Zama yayi adaidai lokacin da driver ya shigo, hanyar dakinsa Ahmad ya nuna masa bejima ba ya fito da kwati da wasu takardun ya fice”
Hajjah ce ta kalli Ahmad tace Wai lafiya kuwa?, Ina zaka aketa fita da kaya”
Hajjah ya kalla sannan ya kalli Samha dake Kan cinyar Hajjah tana Mata tsifa yace”
Gidana zan koma Hajjah”
Gidan ka?, Ita Fatima fah?
Ta zauna anan zanturo mata driver da zai dinka kaita makaranta yana daukota, ki gaya Mata Hajjah banyadda taje ko inaba bayan makarantar ko kofa ta fita bada izinina ba ban yafe ba, bare ma aje ga mgnr zuwa unguwa makaranta kawai na amince mata taje”
Amman Ahmad ka tsaurara da yawa fah, me yake faruwa ne??
Mikewa yayi ya fice
Yana fadin Hajjah Saida safe muyi waya kawai
Bayan Samha Hajjah tadan daka sannan tace”
Fatima tashi kidan rakashi mota kinji😔
Mikewa tayi Dan bazata iya cewa Hajjah bazata ba……
Mmn Yazeed
6 comments