Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 13

Posted by

BA LABARI BOOK

 

 

Tsintan kanta tayi da zamewa ta zauna akasa, ya kusa isa kusa da ita ya daga kansa ya kalli Ammi tare da cewa, “Ammi yariyar nan wai bula hancin ta yi ne?

Eh, ai kwalliya ce Modibo.

kwalliya?

Amsa Ammi ta sake bashi amsa da eh, ta tambayeni ta bula tace yana Bata sha’awa ni kuma na bata dama.

juyawa yayi ya kalli Unaisa da saurin sa tare da tabi baki tare da fadin, ” toh Allah ya kauta, tashi muje in sauke ku.

Ficewa yayi yayin da Afnan ta shiga yiwa Unaisa dariya, daker ta mike suka fito jikin duk yayi sanyin

Har suka fito duk a d’arare take, Afnan ce ta shiga gaban Motar yayin da ita ta zauna abaya, har suka isa tanajin yadda Afnan take hira da Modibo saidai yawancin hirar Afnan din ce ke kawowa yayin da yake binta da, haba, eh, Ashe haka akayi.

Sosai abun ya kule Unaisa yadda Afnan din ke zuba kamar an kunnan Radio shiko yana ta wani basarwa, suna isa ta bude motar ta fice, domin taga har yanzun Afnan Bata gama surutun ba.

Daga nesa ta hangi suna kallon ta suna mgn, dan haka tai saurin dauke kanta har motar ta tashi agurin Bata waigo ba.

Bayan ta tabbatar da Motar ta tashi ne ta juya ta tana kallon Afnan tare da fadin, ” me yace miki akai na?

Dariya Afnan tayi sannan tace, ” Meyasa baki gaishe shi ba?

Mancewa nayi, shine ya rudani, kamar fa da dukana zaiyi, dan dai kawai Ammi ta sa vaki ne.

Mamaki Kika bashi yace ai, yace wai ko gaidashi baki yi yanzun.

Yau dai na mance ne wlh.

Ya kamata ki dinga zuwa har part dinsa kina gaidashi fah

taf wlh bazani ba, akwai matar shi me Harare harare me zai kaini.

Toh ba dole tai Harare harare ba, Nima tana min haka kila tasan abun dake tsakanin ku keda Hamma, kuma ita kishin tsiya gare ta, ana zargin ita take Hanna Hamma aure, bayan ya aure ta akwai wata yariya da Hamma yaso ya aura sati biyu ya rage bikin aka fasa, irin haka ko sau uku anayi, sannan kinga ciwon kafar Hamma ma Ammi na zargin Safna da sune sanadin ta.

Tabe baki Baki Rahama tayi tare da fadi Allah ya kauta, saidai harta aka tashi daga makarantar ta kasa goge abun cikin ranta.

Bayan sati biyu suka samu hutun makaranta, dan haka suka samu damar zuwa gidan ya dikko ita da Afnan, sosai Yaddiko take nunawa Unaisa kauna, saidai har yanzun Yadikko Bata da wani kosarsiyar lafiya, abakin Afnan take jin Suraj ne kawai d’an daYadikko ta haifa, sai kannen sa wadda suke yan Uba mata ne su biyu, sabo da yawan zuwa gidan da suke sufa saba sosai dasu, sau daya suka hadu da Suraj, gaishi sukayi ya amsa yayin da ya wuce su cikin sauri.

Hakama gidan su Muftahu suna zuwa kadan kadan sabo da kannan mufhahu duk maza ne, Abba Muftahu kanin Abban su Modibo ne, dagani ma basai ka tambaya ba, satin su biyu da yin hutu Ammi ta fara fadan yawon su, kullum basa zama agida, yayin da tashiga yiwa Afnab fada Kiri kirinta daina zuwa Islamiya.

Cikin yanayi irin na wadda fadan ya shige ta tace, Ammi to ai bama dawowa makaranta ne da wuri shiya.

Zangawa Abban ku mgn komai yamma kuka dawo ku wuce makaranta ko a d’ako Malamin da zai dinga maku da daddare.

Washegari tana zaune adaki da yamma Afnan tace Rahma kizo inji Hamma.

menene?

Nima shigata kenan dakin yace min in Kira ki.

Mikewa tayi aranta tanajin ba alheri bane, yanzun haka fada zai yi.

A Hankali ta tura kofar sannan ta isa bayan Ammi ta zauna tana gaidashi kasa kasa.

Lankwasa Hannu ta tafara zuwa can taji yace”

Kishirya gobe da zamuje YOBE.

Tsintan kanta tayi da fadin, Alhamdulillah, tare dasa hannunta ta rufe fuskan ta, cikin yanayin dake nuna tana farin ciki.

Dariya Ammi tayi tare da fadin, yau sai farin ciki abun nema ya samu.

Modibo ma murmushi yayi tare da binta da kallo, rasa inda zata saka ranta yasata mikewa tana rufe da Fuska tabar dakin.

Ammi ce ke fadin bude fuskar dai karki fadi.

ta fita ba jimawa shima ya mike ya fita.

Misalin karfe 08:00pm Unaisa da Afnan zauhe gaban Ammi, wasu ledoji Ammi ta Mika mata wai tsaraba ce inji Modibo, sosai taji dadi saidai kuma duk kayan na Dada ne.

ai duk ita daya zakima tsarabar.

Adaidai wannan lokacin Modibo ya shigo Ammi ce tace yauwa Dama Rahma na tambaya wai kwana naza zata yi?

Daya, ya fada Yana kokarin zama.

Daya tal?, Modibo ca nake zaka barota acen tayi ko sati ne.

Haba Ammi, har sati, kwana dayan ma Dan karta gaji ne da aranar zamu dawo.

Juyawa tayi ta kalli Unaisa tace, ” to ke ki ji, dauko akwatin kisa tsarabar tare da Kaya kala daya ai zai yi.

Kallo Unaisa yayi yace a’a Ammi basai ta dauki akwati ba, kayan ma ta bar su aledan.

Ammi kallon Unaisa tayi tace ai ta hada kayan tunda tace Dada kadai zata kaiwa.

A’a, ta gyara su yadda ta gan su, daya na Dada, dayan kuma takai gidan kanin Maman ta.

Cikin sauri ta yamutsa fuskar tare da juyar da kanta adaidai lokacin da Ammi kecewa hakama yayi ko, kallon Rahma tayi data jiyar da kanta can gefe tace, ” gyara kayan inda suke kinji, kije ki kwanta dan kisamu goben kitashi da wuri.

Cikin kasa kasa da murya tace Ammi ni fa Dada kadai zan kaiwa.

Juyowa yayi ya kalleta, Sarai yaji abun da tace, tare da bacin rai afuskan ta, gani yayi Ammi na rarshsshin ta kasa kasa dan haka ya mike tare da fadin, Ammi barta tai yadda take so.

Ficewa yayi abin sa, har bayan ya koma dakin sa Maki take bashi, gani Yake kamar ba ita bace, ko canzo ta akayi, nasan daman taganin mutane dole zata saki jiki, amma beyi tsammanin abun zaikai har haka ba, gogewan ta lokaci daya abun har tsoro yake bashi, dan haka ko yanzun ma dayai kwance saman gadon sa ya kasa bacci tunanin ta kawai yake yi.

Ahankali Safna tura kofar ta shigo, saidai har ta isa bakin kofar be dago ya kalleta ba ganin haka abun ya Bata Mamaki kuma idon sa biyu abude ba bacci yake ba.

Gefen shi ta zaune tare daura hannun ta kan kirjin sa tana fadin, Hamma lafiya?

Dan zabura yayi kadan tare da fadin, Lafiya lau *Rahma*

Runtse idon tayi zuwa can ya bude tana fadin” Hamma Rahma kuma?, wacece Rahma?

Tashi yayi zaune karon farko data hangi diri diricewa agurin Modibo, kasancewan abun bakon yanayi ne yasata taji damuwa sosai.

Ganin inda yake kokarin hade fuskarsa tasata kawar da zancen ta hanyar fadin, Kace gobe zakayi tafiya Ina zakaje toh?

Sai yanzun zaki min wannan tambayar?, kin gama fushin kenan?

Jimmm tayi zuwa can tace Eh nagama.

Meyasa Kika gama?, bayan alokacin da nake rarrashin ki baki saurareni ba.

Hamma Raina ne ya baci lokacin, kuma duk macen da akazo mata da irin wannan mgnr dole taji zafi indai tana son mijin ta, yanzun dai mubar mgnr.

Ai inaji Kika Kira Momy Kika gaya mata.

Jimmm ta sake yi zuwa can tace, nidai kayi hakuri, Koda na gaya mata ma addu’a tamin nima tace in dinga yi.

Shikenan, ya fada Yana kokarin dauko wayarsa dake gefen gado.

Amman Hamma badan na bata maka rai bane zakayi tafiyar ko?

Akan me?, Ina hauka ne?, kawai sabo da kin Bata min rai sai intashi inbar gari?, nifa ba wahalalle bane nan da kiga ganin, ba macen da zan zauna tamin iskanci, duk abun da kikamin kiga nayi shiru be zafe ni bane, amman inhar ya zafeni kema sai ranki ya baci, duk wadda ya kwana lafiya shi yaso.

Shiru dakin yayi tsayon lokaci zuwa can tace’ ” toh Ina zaka?

Yobe zani.

Yobe kuma me zayo acan?

Zankai Rahma gidan su.

Rahma?, Jimmm tayi domin ita har ta fara mantawa akwai ta agidan nan, wani irin Mummunan tashin hankali Taji ya same ta lokaci daya dazon ma fa da Rahma ya kirani ta fada azuciyar ta, afili kuwa cewa tayi.

Cikin sanyin jiki tace, Hamma ni abun yamin yawa, ga wanannan ga waccen da wanne zanji?

Kallon ta yayi tare da fadin mena gaya miki dazon, duk abun da Allah ya jarabceka dashi ka amashi hannu biyu saika zauna lafiya, yadda rayuwar tazo min haka nake karbanta.

Hawaye ta share Hamma yanzun shikenan ni bazanji dadin gidan aure na ba, Hamma har mata Uku zakayi ko kunya bakaji, Suraj fa har yanzun beyi aure farko ba, haka zan taso cikin matan su ni Ina baibaye da kishiyoyi shikenan fa rayuwata a wahala zata kare, ni bazanji dadin duniyata ba.

Safna!!

Juyowa tayi suka hada Ido, yayin da yaci gaba da cewa, “waye ya gaya miki jin dadi mukazo yi a duniyar, Umhum Safna?

Hawaye tacigaba da sharewa, kare mata kallo yayi sosai sannan yaci gaba da cewa, ” ki maida hankalin ki kiyi hakuri, Aure ibada ne kuma Allah ne ya bamu wannan damar, kisa azuciyarki ibada kizoyi ba jin dadi ba, karki biyewa rudin duniya, duniya me halin d’an mangoro,kana tsotsun ta saita subule maka.

Hmmm, ai Kaine mangoron, dole kace min haka mana tunda kana Shirin tara mata, ka taba waccen ka taba waccen, yanxun ne burin ka zai cika, dama ai aikin ka kenan, duk irin takura min din da kake yi be isheka ba saikaje ka mana kwashe kwashe.

Ji Mana hajiya, mubar mgnr nan zoko kwanta.

NI bazan kwanta ba, kajirasu suzo ka kwanta dasu.

Murmushi yayi kadan sannan yace, kiyi hakuri toh

Wlh ka jirasu har suzo.

Ai basu riga sunzo ba yanzun kam kece agaba na.

kokarin tashi take dan haka ya mika hannun sa ya rikota tare da fadin, ki daina rantsewa, ki hau gado hakkina zan amsa, bude baki tasakeyi yayin da yai saurin sa hannun sa a baki ta Yana fadin, shiiii, Raina nason dole kibani.

 

******

Washegari tunda sassafe Unaisa ta gama shiryawa, misalijn 06:00am Modibo yai Sallama da Ammi ya fice, Ammi da Afnan ne sukama Unaisa rakiya har gaban motoci uku da za’ayi tafiyan dasu, kowa ya kalli Unaisa saiyasan tana cikin farin ciki.

Modibo ne ya taho hannun sa cikin na Safna, suna karasowa ta rusna ta gaida Ammi dake rike da kayan Unaisa motar da Modibo zai shiga aka bude ya shiga baya ya zauna, zagayawa Unaisa tayi ta shiga gefen sa ta zauna.

Fatan sauka lafiya Ammi ta masu sannan ta wuce cikin gida, itako Safna har aka rufe motar tana gurin yayin da take dagawa mijinta hannu.

Shima hannu ya daga mata cike da Murmushi, Unaisa ko ita da Afnan suke dagawa Juna hannu yayin da Afnan tayi raurau da Ido itako Unaisa Murmushi take mata.

Kokarin ficewa daga gidan suke Motar Magaji na shigowa, daga cikin motar sa ya gaida Modibo tare da fadin, Lafiya kuwa fita da sassafe?

Lafiya lau Yobe zamu.

Yobe? Kallon Unaisa dake gefen Modibo yayi da wani irin duba, yace adawo lafiya.

Allah yasa, baka kwana agida ba kenan ko?

A gida na kwana, kawai daga masallaci ne naje gurin Muftahu.

Hmmm shikenan.

Motocin ne suke kokarin gotawa yayin da ya gallawa Unaisa harara, itama wani irin kallon tsana ta jefa masa wadda ya kara kullar dashi, tunda Modibo ya gaya mata Magaji nada tabo bata taba ganinsa ba sai yau.

Hanya suka kama sosai, babu mema wani magana, saidai fuskar kowannen su da walwala mgn ce dai babu tsakanin su.

Misalin hudu na yamma suka iso, sosai taga garin ya canza mata suna daf da isa kofar gidan Malam Ayuba ya waigo ya kalleta yace, Zamu fara sauka anan ne ku kaisa kinga agidan Dada saiki huta gama day….

Cikin sauri ta muskuta ni bazani ba.

meyasa?

Ni dai ka kaini gidan Dada in gaidata sai ka kaini gidan mu.

Ina ne gidan ku?

Gidan Innaworo.

Tsaki yaja tare da fadin, baki da hankali, Umarni ya bada a tsaya nan kofar gidan Malam Ayuba suna tsayawa yace sauka ki shiga.

Jimmm, tayi zuwa can ta bude ta fita tare da gyara mayafin ta, ledan jiya taga ya miko mata wadda ta hada duk domin Dada yace amsa ki Basu.

Idon ta kasa tace na Dada ne.

Nace kije ki Basu.

Tsaye tayi tana mutsu mutsu da baki yayin daya tsare ta da Ido zuwa cen yace ai banjin ki me Kika ce?

Cewa nayi ko Ina tafiya kud’i na zuba ajikina bazan Basu ba.

Cikin tsananin Mamiki ya bude motar ya fito, kallonta yayi ya kawar dakai sannan yace, sai kibari idan kin sami naki kudin da gumin ki sai ki hana.

Kawar da Fuska tayi cike da haushin sa, kasa kasa tace, ” tunda kudin ka ne ka Basu da kanka to.

ke!! zagina zakiyi ne?, rashin kunya zaki min??….

Tunkafin ya rufe baki ta finciki ledan fuuuu azuciye tayi cikin gidan.

Bayan ta Modibo yabi da kallo sannan ya bada Umarnin ashiga da buhunan abincin da suka taho dashi.

Tsaye yayi yana jingine cikin motar, befi minti biyar da shiganta ba yaga ta fito, matan gidan ne duk abayanta suna fadin, mungude fa Allah yi albarka ko wacce fara’a dauke da fuskar ta.

matan ya gaisar shima godiya suka masa sannan ya koma motar ya zauna.

Unaisama shiga tayi ta zauna gefen sa, bayan motar ta tashi ya kalle ta sosai take bashi Mamaki.

Motar su na tsayawa akofar gidan Dada da mijinta na fitowa a tare da alama sunsan da zuwan su, gaba daya gidan ya canza an gyara shi tamkar bashi ba, har wani gini akayi daga gefe sosai abun ya Bata Mamaki, cikin gidan ta nufa, atsakar gidan ta zauna domin ta rasa ma Ina zata shiga, tafi minti talatin azaune sannan Dada ta shigo tana fadin baki shiga ciki ba, taso ki huta.

Gurin sabon ginin ta nufa da ita, baban falo wadda yasha gyara, gaisawa sukayi da Dada cikin rungumar juna bayan sun nutsu Unaisa tai sallah sannan ta kalli Dada tace, ” Dada gurin duk ya canza, Baba ne yai muku gyara?

Wanni Baba Unaisa, wannan duk aikin Modibo ne?, shiyasa jama’ar Unguwa suka sani agaba ana ta cewa na siyar dake, wasu har suna fadin ancire kanki.

Tintsirewa Unaisa tayi da dariya yayin da Dada tace, kuma fah suna da gaskiya, nikaina yadda naga Yana ta turo mana kudi saina shiga zargi, hankalina ya kasa kwanciya, wata rana na Kira shi nasamishi rigima kuka wiwi.

Dariya Unaisa ta sake fashewa dashi, itama Dada dariya tayi yayin da Unaisa tace me yace miki toh?

Dariya yaitayi yace kina nan lafiya kuma kema kitana mgnta har yace min zai saya miki waya, yaron nada hankali ko Unaisa?.

Kaita daga kawai tare da cewa eh.

Kusa da ita Dada tazo ta zauna sannan tace wlh kinyi sa’ar miji, yana da hankali sosai, Kashi yaro ne matashi amman yasan ya kama ta, yanxun nan mafa yace musamman ya kawoki domin ingaya miki yadda zaki fahimta.

Ni? Dada me zaki gaya min?

Mgnr auren sa mana dazai kara.

Wai waye Dada?

Modibo, yace in gaya miki zai kara aure Nan da sati biyu.

Jimmm tayi ciki maduwa ga faduwan gaba wadda ya sameta batare da zato ko tsammani ba, tsintan kanta tayi tana cewa, ” Dada ai Yana fa da mata.

Eh, duk ya gaya min, watace kuma zai kara…..

Mikewa Unaisa tayi aguje tana rike da bakinta, kofar Dada ta tsuna tana kwara uban amai……