
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
page 16
Tsaye kawai take domin a irin wannan lokaci babu yadda ta iya dashi, kallo kawai take binsa dashi.
Shima kallo yabita dashi tsayon lokaci sannan ya tashi daga runfan dayai mata tana wani murmushi kasa kasa tare da fadin, “indai Modibo ne yanzun kika fara ganin abubuwan takaici yariya.
Cikin sauri ta fara tafiya tana waiwayen shi cike da tsana, gurin zama ya nema ya zauna har yanzun be cire idon sa akanta ba, itako Unaisa tafiya take tana waigen sa tana daf da isa Babban farfajitar gidan ta tsaya tana Kara masa kallo tsana tare da fadi, da karfi, tsinanne matsiyaci kawai.
Nagode, ya fada yana kallonta yana murmushi.
Kara kular da Unaisa yayi dan haka ta rufe Ido da tana zagin shi.
Tun Yana binta da kallo kawai har ya miki yana fadin, ke ya ishe ki haka. banaji nan da kika ganni, wlh zan karkarya ki babu abun da ya dame ni, in dakeki in daki banza babu abun da za’ayi wlh.
Wani irin haushine ya kamata, dan haka ta rasa me zatace masa, juyawa tayi ta rarumi wani dutse ta wurka masa saidai be same shi ba, amman Afusace taga yayo kanta, wasu dutsunan ta sake d’i ba tana jefa masa kota Ina, Yana Kara yowa kanta, ganin da tayi babu kowa agurin yasata fara tafiya yayin da ya cigaba da bin ta.
Cikin gudu ta shiga dakin Ammi tana shiga Magaji na shigowa, Ammi ki gayawa wannan yariyar ta fita daga harkata.
Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un Ammi ta fad’a , sannan ta juya ta kalli Unaisa ta kuma Kalli Magaji tana fadin, menene?
Ammi zagi take kare min, wlh zan zane ta, duk ranar da ta kuma zagina niba sa’anta bane.
Baki Ammi ta rike tare da fadin, wai Magaji kana da hankali kuwa? Matar yayan naka zaka Zane?
Toh ni Ina ruwana da auren, Ammi Baki mata mgnr zagin da take min ba sai kawai kice matar yayana ce, ita tasan da haka take bina da zagi da da jefe jefe, batun yauba yariyar nan take son dukana, d’anta ne ni, wlh duk ranar da jifanta ya sami ne saina nakasa ta, yankan rago zan mata.
Cike da fada Ammi tace, dakata, Magaji, mena gaya maka wancen karon da kuka same matsala da Modibo?
Shiru Magaji yayi cikin sunkuyar da Kai, zuwa can yace, Ammi zagina fa tayi.
Cikin sauri Ammi ta kalli Unaisa tace Rahma me yasa haka?
Ammi Munafuki ne fa, tareni yayi abaya, Ina zaune.
Tasowa Mahaji yayi cikin fada yana fadin, ” nine funafuki? wlh ni ubanki zanci babu ruwana da auren ki, kinyi kadan in zauna kina zagina, ki manta lokacin da kike kango azaune, wato an taimake ki an dauko ki har Kika mike kafa kina zagin d’an masu gida, ko da yake dama wasu Basu iyacin dambu da tsinke ba……
Acikin gidan ubana kukaganni Ina zaune ban nemi taima ku ba, bama ku ba tunda nake bantaba nemen taimako gurin kowa ba, kuma banrasa ciba ban shaba, haka kawai sabu da bakin nacin ku kuka shigo min cikin rayuwa, dole kuka dauko ni kaida mayen d’an uwan ka, kuma gidan mu da kake kira kango ni yafi min nan
Sosai yayo Kan Unaisa Yana yana wlh saina daki yariyar nan.
Ammi cekin tsaya take dakarta da Magaji dan haka da ya isa gaban ta ya tsaya kawai.
Kayan dake jere Kan madubin Ammi taita diba tana watsa masa, Magiji fadi yake, Ammi kindai gani ko.
Ke Unaisa bari, ganin ta rufe idon ta jefan sa kawai take tace ke Rahma bari.
Gani tayi kamar batajin ta Dan haka tace Kai Magaji fita.
Ammi bazan fitaba, ita ta kisa in fita sabo da ita ne?, d’akin uwarta ne?
Innalillahi wa Inna ilaihir ru’un Ammi ta sake fada sannan tace, Magaji inka daketa ban yafe maka ba, da bana son Modibo yaji amman tun da Abban ku baya gari dole yaji, wayar ta ta d’aga ta kira Modibo, cikin kankanin lokaci ya shigo yana turo kofar tare da fadin Ammi lafiya kuwa?
Kallo shi tayi sannan ta dube dakin yadda duk aka mata jifa ta turaruka ta tana fadin, ” Duba Modibo fadane wai ake Magaji da Rahma, nayi mgn harna gaji, Ina mgn sunki saurara ta kamar ma Kara zika su nake.
Kwankwaso Modibo ya rike, Yana binsu da Ido daya bayan daya sannan ya koma kan kujera ya zauna tare da fadin, ” aida kin sani bakice musu komai ba, ki barsu suyi kawai.
Modibo zagina fa tayi, ta uwa ta uba, ko agaban Ammi ma zagin ta kare min, ni sa’an ta ne?, inaruwana da ita?
Wani abu ka mata Magaji? Modibo ya tambaya yana kallon Magajin.
Wlh Modibo ganinta kawai nayi ta fara zagina.
A’a Magaji bazai yiyu ba, nasan kawai kai ka fara.
Modibo babu abun da na mata, ai ga Ammi, kaaima yanzun tagama ce dakai maye. Kai me ka mata to?
Juyawa yayi ya kalli Unaisa dake cike tab har yanzun sannan yace, ” a’a karku sani a ciki, ke me ya faru.
Tare ni yayi Ina zaune a baya yana min mgnr banza.
yace me? Modibo ya tambaya yana tareta da idon sa.
eh Ina jin ke kinyi shiru me yace?
Shiru ta sake yi muryan Magaji taji, nifa gani nayi tana zaune agurin tana kuka, shine na dan mata wasa nace dan zakayi aure take koke koke shikenan fa kamar jira take.
Modibo ne ya kalli Unaisa haka ma Ammi ganin haka tai sauri kawar dakanta .
Ammi ce tace wai haka ne Rahma?
Ammi karya yake yi.
kafa daya Kan daya Magaji ya daura Yana cewa nidai abun da nasani kenan idan ba haka bane ke saiki fad’a.
Shiru tayi tsayon lokaci tare da karajin tsanar Magaji mara misaltuwa.
Ammi ce tace, Kai waye ya aike ka Ina ruwanka da ita?, toh Bari kaji karka Kara shiga harkar yariyar nan banaso, ba ruwanka da ita, ai wannan abun kunya ne ma, sai mutane su shigo suga kana fada ta matar dan uwanka, kana zagin ta ta mayar maka, wacce irin lalacewa ce wannan?, toh ka shi ga hankalin ka.
Amsawa yayi yayin da Ammi ta juya ga Rahma tace ke kuma, inya sake miki haka karki tanka masa, kizo kawai ki gaya min, ninasan me zanyi
Magaji ne ya fara fita, sannan Unaisa ma tazo zata wuce, wani dan harara Modibo yai mata, sannan ya maida hankalin sa gurin Ammi Yana fadin, Ammi duk sun Bata miki daki kuma kin barsu sum fita Basu gyara shi ba
Hmmm, Yanzun za’a gyara Modibo karki damu.
*****
Unaisa kwance saman gadon tayi ruf da ciki, hawaye ke zubo mata take sharewa da saurin ta domin bata son Afnan tagani.
Kwance Afnan din take gefen ta tana karatun wani littafi.
Ahankali suji an kwankwasa kofar, Afnan kadaice ta waiga tare da bada Umarnin a shigo.
Tashi zaune Afnan tayi tana fadin, ” Hamma Modibo.
Afnan ya kuke?, ya fada Yana karasa shigowa cikin dakin.
Lafiya lau Hamma saidai ita Rahma yanxun kullum haka take min da daddare bata hira Dani.
Juyawa yayi ya kalli kwanciyar ta yace haka take miki ko?, kenan ko dariyar ma Bata yi yanzun? .
Bata wani yi Hamma duk ta canza, Nina ma kusa komawa dakin Ammi in barmata nan.
A’a kiyi hakuri Afnan zata Bari, Zama yayi agefen gadon yayin da Afnan ke kokarin ficewa yace, zo mana Afnan.
dawowa tayi ta tsaya tsakiyar dakin.
Gefen sa ya nuna mata, ta zauna anan.
kamar yadda yace haka tayi zuwa can taji yace, Afnan ?
na’am
Kinsan kuwa Rahma mata tace?
eh na sani ai.
Toh meyasa bakice mata Aunty, kamar yadda kike kiran Safna.
Hamma ai na bari ne sai an daura auren.
Ai an riga an daura Afnan, rika ce mata aunty, Basu da banbanci da Safna a yanzun, ni kaina Ina kiranta da Auty sabo da ita din ta musamman ce.
Dariya Afnan tayi eh man kana ce mata Aunty kuma Hamma bantaji kace ma wata aunty ba.
Ai bani da ita ne ada Afnan, yanzun jeki gurin Ammi Bari danyi mgn da da ita.
Mikewa Afnan tayi ta fice yana jin Afnan ta sake kofar yace toh aunty tashi ki zauna, Umarni nake baki ba rokon ki nake ba.
Ahankali ta tashi zaune tacan gefe ta maida kanta ta juyo masa baya.
Kijuyo ne ki kalle ni.
‘Kin jiyowa tayi dan haka yace, idan Kika yadda na dawo gaban saina baki Mamaki.
Ahankali ta juyo tana kallon shi sannan ta sunkuyar da kanta kasa.
Ido ya zuba tsayon lokaci sannan yace, Rahma dago idon ki ki kalle ni.
Dagowa tayi ta sata kallon shi kadan Fuskanta babu walwala.
Cikin Ido ya kalleta yace meke saki kuka? amai , saurin fushi da zama cikin kunci?
Cikin sauri ta kawar da kanta can gefe.
Ya isheki, ki bani hankalin ki.
Dagowa tayi ta motsa baki sannan ta sake kawar da kanta can gefe.
Kallon ta yake sama da kasa ahankali ya mika hannun sa yai karaf ya rike nata cikin nashi sosai ya runtse su tare da lumshe Ido yana fadin, ” yi hakuri, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki, damuwar ki tana damuna sosai, kin sani batun yauba banason ganin ki cikin damuwa, na baki dama duk abun da kiga nayi wadda be miki dadi ba ki min mgn, inason auren da zanyi ya daina damun ki…..
Ni bashi bane yake damu na?
Toh menene?
Gidan mu za’a mayar dani, dan bani nace a dauko ni ba, dahar wannan Magajin naku zai gaya min mgn.
Cikin sauri ya daga hannun sa tare da fadin, a’a a nan gurin babu zancen Magaji kuma, Magaji Banza negirman mahaukaci, karamin me hankali ya fishi, kuma banda abun ki ya zakije can sako kina kuka, wannan ai kamar bulayi ne wadda ake kira bara akufai.
Bata gane inda mgnr sa ta nufa ba, dan haka ta fara kokarin juya masa bayan ta, mikewa yayi ya dawo kabanta yana fadin, Dakata hajiya, yanzun mubar wannan mgnr, yaushe zaki tare?
5 comments
Comments are closed.